Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Tubulan Ginin Turke a Wakar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur ta Sa’idu Faru

Citation: Hassan, S. & Darma, A.Y. (2024). Nazarin Tubulan Ginin Turke a Waƙar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur ta Saidu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 76-81. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.010.

NAZARIN TUBULAN GININ TURKE A WAƘAR SARKIN YAWURI MUHAMMADU TUKUR TA SA’IDU FARU

Daga

Sani Hassan
Sashen Nazarin Harshen Hausa,
Tsangayar NazarinIlimin Sakandare Ɓangaren Harsuna,
Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita, Jakar Waya 5007, Dutsin-Ma, Jihar Katsina
08039478054 / 08025164796
hassansanig@gmail.com

Da

Dr. Abdullahi Yakubu Darma
Sashen Nazarin Harshen Hausa,
Tsangayar Nazarin Ilimin Sakandare Ɓangaren Harsuna,
Kwalejin Ilimi Ta Isa Kaita, Jakar Waya 5007, Dutsin-Ma, Jihar Katsina
08036375129 / 07056082213
ayakubudarma@gmail.com

Tsakure

Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin makaɗan fada a ƙasar Hausa. Ya yi wa sarakuna da ‘ya’yan sarakima bambantan waƙoƙi a lokacinsa. Sannan yana daga cikin makaɗa ko mawaƙan da suke sassaƙa ƙananan saƙonni a lokacin da suke ƙulla waƙa. Saboda haka, babbar manufar wannan muƙala ita ce, bayyana tubulan ginin turken da makaɗa Sa’idu Faru yayi amfani da su wajen ƙulla waƙar da ya yi wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur, mai suna ‘Koma Shirin Daga na Bubakar, Gamda’aren Alƙali wan Maza’. An gudanar da wannan bincike ta hanyar karantawa daga bugaggun bayanai da sauraron wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, tubulan ginin turken da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen ƙulla zaren tunanin waƙar sun haɗa da tubalin zumunci ko zumunta da tubalin zambo da tubalin koɗa kai da tubalin tarihi da kuma tubalin habaici.

1.0 Gabatarwa

Alhaji Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin shahararrun makaɗan fada a ƙasar Hausa. Makaɗan fada a ƙasar Hausa su ne makaɗan da suke yi wa sarakuna da sauran waɗanda suka jiɓinci ko suka gaji sarauta waƙa. Makaɗan fada suna isar da mabambantan saƙonni a waƙoƙin da suke rerawa iyayen gidansu. Ma’ana, baya ga babban jigo ko dalilin da ya assasa rera waƙar, wato turken waƙar, suna kuma sassaƙa wasu saƙonni da suke son su isar ga iyeyen gidan nasu ko masu sauraron waƙoƙin nasu. Waɗannan ƙananan saƙonni da suke sassaƙawa a lokacin da suke isar da babban saƙon da waƙar take ɗauke da shi (turken waƙa), su ne ake kira da tubulan ginin turken waƙa. Makaɗa Sa’idu Faru ya rera waƙoƙi masu tarin yawa. Daga cikin waƙoƙin da ya rera akwai na Sarkin Yaƙin Banga Alhaji Sule Ƙauran Namoda da na Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo da waƙar Sarkin Fulanin Bunguɗu Alhaji Shehu da waƙar Turakin Kano Alhaji Amadu da waƙar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur, da dai sauran tarin makamantansu.

Makaɗa Sa’idu Faru, shi ma kamar sauran makaɗan baka na ƙasar Hausa yake, saboda yana sassaƙa ƙananan saƙonni (tubulan ginin turken waƙa) a lokacin da yake ƙuƙƙulla zaren tunaninsa domin ya samu damar isar da babban saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi, wato babban jigo ko manufar da waƙar take son ta isar (turken waƙar). Wannan ya sa wannan muƙala ta yi nazarin waɗannan tubula na ginin turke a wata waƙar da makaɗa Sa’idu ya rera wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur mai suna “Koma Shirin Daga na Bubakar, Gamda’aren Alƙali Wan Maza.” Ko da kafin a tsunduma cikin bayanin waɗannan tubulan ginin turken akwai buƙatar kawo bayanin muhimman batutuwan da wannan batu ya ƙunsa.

1.1 Ma’anar Turke

A ƙamusun Hausa, an bayyana ma’anar turke da cewa, guntun icce da ake kafawa don ɗaure dabbobi a jikinsa (CNHN, 2006:446). Sai dai wannan ma’ana ce ta lugga. Ma’ana ta fannu kuma, wato a fagen nazarin waƙa, turke na nufin gundarin manufa ko saƙon da waƙa take ɗauke da shi, wanda take son isarwa ga mai sauraro. Wannan sai ya yi dadai da jigo, ma’ana, ga masu nazarin rubutacciyar waƙa. Bisa ga ƙa’ida, wannan saƙon kan ratsa waƙa tun daga farko zuwa tsakiya, har kuma ƙarshen waƙa, (Gusau, 2009:370). Sannan an bayyana turke da saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan an ce saƙon kuma, ana magana ne a kan manufar da ta ratsa waƙa tun daga farkonta har zuwa ƙarsshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kansa ba (Gusau, 2008:370) a cikin (Lawal, 2014:426). Ta hanyar yin la’akari da waɗannan ma’anoni, za a iya bayyana ma’anar turke a fagen nazarin waƙa da saƙon da ilahirin waƙa ta ginu a kansa, wato saƙon da mawaƙa suke gina ko shirya waƙa domin shi.

1.2 Ma’anar Tubalan Ginin Turke

Tubulan ginin turke suna nufin wasu maganganu da aka bi aka ƙulla waƙa da su don ta ƙara tsawo, amma ba sune babbar manufar waƙar ba (Gusau, 2003:30). Haka kuma, Gusau (2008:374-375) ya nuna cewa, makaɗan baka sukan yi amfani da ƙananan zantuka ne su ƙulla waƙa don ta ƙara tsawo, sai dai lalle ne su dace da babbar manufar waƙa. Sannan kowane babban turke akwai nau’o’’in ƙananan turakun da suka dace da shi. A wata ruwayar kuma, Auta (2019:229) ya bayyana tubalin ginin turken yabo da ƙananan saƙonnin da makaɗa suke amfani da su wajen gina babban saƙonsu na turken waƙa. Ta la’akari da waɗannan ma’anoni, za a iya bayyana tubulan ginin turke da cewa, wasu saƙonni ne da mawaƙan baka suke sassaƙawa a cikin waƙoƙinsu, waɗanda suka danganci yabo da habaici da zambo da koɗa kai da ‘yancin kai da tarihi ko nasaba da addini, da dai sauraansu, domin su taimaka masu wajen isar da babban saƙon da waƙarsu take ɗauke da shi.

1.3 Ma’anar Waƙa Baka

Yahya (1997:4) ya nuna cewa, “Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum ba.” Shi kuma (Gusau, 2003:8) ya nuna cewa, Waƙa tsararren zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bias ƙa’idojin tsarin daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa amon kari da kiɗa da amshi. Waƙa aba ce da fasihai ke amfani da ita domin bayyana wata manufarsu cikin sauri ga jama’a. Domin kuwa waƙa ta fi saurin karɓuwa ga jama’a, an fi son sauraron ta fiye da wa’azi. Wannan ne ma ya sa yawancin ayyukan malaman jihadi waƙoƙi ne (Sa’id, 1978:66). Waƙa wata kafa ce ta yaɗa manufa cikin gaugawa kamar yadda iska ke kaɗawa ta game ko’ina cikin ɗan ƙanƙanen lokaci (Adamu, 2015:122). Ta hanyar yin la’akari da waɗannan ma’anoni, za a iya bayyana ma’anar waƙa da cewa, tsararren zance ne da ake shiryawa, a rera a cikin hikima da basira da sautin murya mai zaƙi bias tsarin daidaitawa da zaɓen kalmomi domin a isar da saƙon da ake buƙata cikin gaugawa.

2.0 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru

Gusau (2005:117) ya bayyana cewa, an haifi Makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru ta ƙasar Maradon a jihar Zamfara a shekarar 1932. Makaɗa Abubakar ɗan Abdul ɗan Alu mai Kurya shi ne mahaifin makaɗa Sa’idu. Mahaifiyarsa kuwa mutuniyar Banga ta ƙasar Ƙauran Namoda ce. Sa’idu ya yi rayuwar ƙuruciyarsa a garin mahaifiyarsa, watau Banga. Sa’idu bai yi karatun boko ba, haka nan ma bai yi karatun Muhammadiyya mai zurfi ba. Mahaifin makaɗa Sa’idu makaɗin kotso ne, kuma makaɗin sarauta ne. Ashe makaɗa Sa’idu ya yi gadon kiɗan kotso ne kuma ya yi gadon kiɗan sarauta ne daga mahaifinsa Abubakar ɗan Abdu ɗan Alu. Makaɗa Sa’idu ya riƙa bin mahaifinsa yawon kiɗa, daga nan ne ya koyi dabarar rera waƙa, sannan kuma ya daɗa bunƙasa ne domin shi kansa Allah ya yi masa baiwa da fasaha ta yin waƙoƙi. Makaɗa Sa’idu yakan shirya waƙoƙinsa daga gida ne kafin ya je fagen reraŵa. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da cewar yanayin waƙoƙinsa suna da amshi da ƙari ne, kuma yakan binciki sunayen iyaye da kakannin da yake sakawa a cikin waƙoƙinsa. Ko da yake wani lokaci waƙa takan zo masa nan take, kuma ya rera ta (Gusau, 2005:117-122).

Daga cikin yaran Sa’idu waɗanda suke kama masa Waƙa akwai Mu’azu (Ɗan Gadimansa) da Ɗandaudu da kuma Ali. Daga cikin iyayen gidansa kuwa akwai Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar na III da Abubakar Sarkin Ƙauran Namoda (Gusau, 2005:117-122). Allah ya yi wa makaɗa Alhaji Sa’idu Faru rasuwa a shekarar 1987.

3.0 Manufar Bincike

Babbar manufar wannan aiki dai ita ce, bayyana tubulan ginin turken da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen isar da saƙon waƙar da ya yi wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur. Ma’ana, muƙalar ta zaƙulo ƙananan saƙonnin da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen gina turken waƙarsa ta Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur mai suna ‘Koma Shirin Daga na Bubakar, Gamda’arenAlƙali wan Maza’.

4.0 Dabarun Bincike

A ƙoƙarin gudanar da wannan nazari ko samo bayanan da wannan bincike ya ginu a kansu, an bibiyi wasu bugaggun bayanai da aka samu a wasu daga cikin littattafai da kuma maƙalun da aka samu. Haka kuma, an saurari wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu faru a wayar salula da kwamfuta da kuma na’urar mp3. Wanda daga bisani aka tsayar da alƙiblar wannan aiki a kan waƙar da Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur. Har ilayau, aikin ya inganta ƙwarai a sanadiyyar samun wannan waƙa a cikin Diwanin Waƙoƙin Baka Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa da Gusau ya buga a shekarar 2009.

5.0 Tubalan Ginin Turken Waƙar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur

Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wasu daga cikin tubulan ginin turken da sauran mawaƙan Hausa suke amfani da su wajen ƙulla zaren waƙarsu. Don haka, za a iya ganin waɗannan tubalan ginin turken da mawaƙin ya yi amfani da su a wannan waƙa kamar haka:

5.1 Tubalin Zumunci ko Zumunta

Zumunci yana nufin kai ziyara ga ɗan’uwa ko abokan arziƙi ko na hulɗatayya ko kuma bibiyar al’amurra tsakanin ‘yan’uwa da sauran abokan hulɗatayya da nufin kyautata mu’amala don ƙara kyautatuwar dangantaka. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan tubali da ya danganci zumunci ko zumunta a waƙar da ya yi wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur, kuma za a iya ganin wannan al’amari a waɗannan ɗiyan waƙa da suke biye kamar haka:

Jagora: Na zaka in yi ziyara,

Y/Amshi: Ganin Muhammadu ni daɗi yaka yi man.

Jagora: Na zaka in yi ziyara,

Y/Amshi: Ganin Muhammadu ni daɗi yaka yi man.

(Sa’idu faru: Sarkin Yauwuri)

Idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa za a ga cewa, suna bayanin al’amarin da ya shafi zumunci ne. Saboda suna nuna yadda makaɗa Sa’idu Faru da yaransa suka kai wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur ziyara. Kai ziyari a nan yana nufin raya zumunci. Ke nan, tubali na farko daga cikin tubulan ginin turken da wannan waƙa ta Sa’idu Faru ta fara da shi, shi ne tubalin zumunci. Wato saƙon da wannan waƙa ta fara da shi, shi ne na zumunci.

5.2 Tubalin Zambo

Zambo kishiyar yabo ne, kuma a kaikaice yabo ne ga gwarzon waƙar da ake yi. Mawaƙi kan ambaci wasu abubuwa na kasawa da wani ya yi domin ya nuna cewa bai kai na gwarzon da ya yi wa waƙa ba (Yahya, 1997:91). Kenan, za a iya cewa zambo yanayi ne da mawaƙi yake nuna wa aboki ko abokan hamayya cewa gwarzonsa ba gajiyayye ko kasasshe ba ne, kuma ta kowane ɓangare gwarzonsa shi ne gwarzo, don ya fi kowa. A wannan waƙa makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da zambo wajen isar da saƙon waƙarsa. Misali,

Jagora: Inda duk giwa tat tashi tay yi girgiza,

Y/Amshi: Tai miƙa tar rufe wuri,

: Sai ka ga ‘yan namu suna gudu,

: Suna kwanto wasu na kare wasu.

(Sa’idu faru: Sarkin Yauwuri)

Idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙar, za a ga cewa zambo ne makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa abokan hamayyar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur. Wato duk inda gwarzonsa ya bayyana, shi kaɗai ake gani a filin. Su kuma abokan hamayya sai su razana, su yi ta gudu, suna kwanto, har ya zamana wasu suna kare wasu.

Har wa yau, akwai inda makaɗa Sa’idu Faru ya ƙara kawo tubalin zambo a wannan waƙa tasa, inda ya nuna cewa:

Jagora: Ƙaryab banza rijiya takai,

Y/Amshi: Ruwa na gulbi na sani niya.

(Sa’idu faru: Sarkin Yauwuri)

Nan ma, idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa da suke a sama, za a ga cewa zambo ne Sa’idu Faru ya yi wa abokan hamayyar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur. Saboda yana nuna cewa, duk wani abin da abokan hamayya suke da shi ko suke taƙamar sun mallaka to bai kai na wanda yake yi wa waƙar ba. Waɗannan bayanai sun tabbatar da cewa, Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da tubalin zambo wajen rera wannan waƙa ta Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur.

5.3 Tubalin Koɗa-kai

Koɗa-kai shi ne yanayin da ake samun wani mutum ko mawaƙi yana nuna cewa yana da wata basira ko hazaƙa ko hikima da ta fi ta sauran mutane ko mawaƙa ta hanyar wasa kansa da kansa. A wannan waƙa ta Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur, makaɗa Sa’idu Faru ya koɗa kansa a wasu ɗiyan waƙa da yake cewa,

Jagora: Ga waƙa nan wadda nay yi ma,

Y/Amshi: Guda tara ta mun bar takwas gida,

: Sai in kai murnaz zakkuwassu,

: In aika ko yanzu su taho,

: Mu ka kiɗi, mu ak kiɗi,

: Saboda mu Allah yaw wa gudummuwa,

: Da waƙa ha wata na ije wata.

(Sa’idu faru: Sarkin Yauwuri)

Idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa, za a ga cewa akwai koɗa kai a cikinsu. Saboda a nan makaɗa Sa’idu Faru da yaransa sun wasa kansu da kansu ta hanyar kawo ɗiyan waƙar da suka nuna su ne ke yin kiɗi, kuma su ne kiɗi, kuma su Allah ya yi wa gudummuwa, wato ya ba su fasaha ko baiwa ta yin waƙa har wata waƙar tana tarar da watawaƙar. Ke nan, a wannan waƙa an samu tubalin koɗa-kai.

5.4 Tubalin Tarihi

Tarihi a nan, yana nufin Ambaton abubuwan da suka auku a rayuwa yau da gobe, kuma suka shuɗe da suka danganci ainihin rayuwa ta haƙiƙa, (Gusau, 2008:381). Ke nan, tubalin tarihi yanayi ne da ake samun mawaƙi yana kawo bayanan wasu al’amurra ko abubuwan da suka faru a wani lokaci da ya shuɗe. Tabbas a wannan waƙa makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan tubali na tarihi wajen ƙulla zaren tunanin waƙarsa ta Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur. Za a iya ganin su kamar haka:

Jagora: Taron bara da munka zo Kaduna,

Y/Amshi: Ka cirri lamba naj jiya ƙwarai,

: Sarkin Yawuri ɗai aka faɗi,

: Uban tafiya lardin waɗanga duk,

: Sarkin nan ya kammala ƙwarai da kyawo,

: In ji waɗan Rigachikun,

: Sa’ad da Bature yay yi dariya,

: Da yag ga mutanen Yawuri,

: Suna da haske ga wasu na ta wagara.

(Sa’idu faru: Sarkin Yauwuri)

A nan ma, idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa da aka kawo a sama, za a ga cewa suna nuna yadda makaɗa Sa’idu Faru ya kawo bayanin tarihin taron da aka gudanar a Kaduna a shekarar da ta gabaci shekarar da ya rera wannan waƙa. Saboda a cikin su mawaƙin ya kawo bayanin abubuwan da suka faru a taron da suka yi ko suka je a shekarar da ta gabata da irin yadda aka yi murnar cewa Sarkin Yawuri ya lashe ko ya cinye taron. Ke nan, a nan makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da tubalin tarihi wajen ƙulla zaren tunanin waƙarsa ko gina turken waƙar tasa.

5.5 Tubalin Habaici

Habaici ƙanen zambo ne a kowace irin waƙa. A koyaushe, tare suke wajen masu shiryawa da masu nazarin waƙa. A habaici ba a cika kira a faɗa ba, don an fi nune da kalmomi irin su waɗanga da su wane da o’o da waɗancan da waɗansu da abokan adawa, da mahassada da dai sauransu. Habaici akan yi ga mutum ɗaya ko taro, amma ya fi fitowa ga jama’a da yawa. An fi yin Habaici ga waɗanda suka yi ruwa suka yi tsaki na kawo cikas ga abin da ake nema da waɗanda suka ƙi bada kai bori ya hau, (Bunza, 2009:136). Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da tubalin habaici wajen ƙulla zaren tunanin waƙarsa ta Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur, kuma za a iya ganin wuraren da ya kawo habaicin a waɗannan ɗiyan waƙar da aka kawo a ƙasa.

Jagora: Ga wani sarki ba shi da zagi,

Y/Amshi: To kuma sannan bai da guzuri,

: Garin-rogo ɗai suka ta ci da guru,

: Kowane na aza ruwa.

(Sa’idu faru: Sarkin Yauwuri)

 

A nan, idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa, za a ga cewa habaici ne Saidu Faru yake yi wa abokan hamayyar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur ta hanyar ƙasƙantar da wani sarki da mutanensa, shi kuma ya ɗaukaka darajar sarkinsa.

Bayan wannan kuma, akwai wasu ɗiyan waƙar da ya kawo waɗanda suke nuna habaici a wannan waƙar kamar haka:

Jagora: Amma shi ko har da dama-dama,

Y/Amshi: Ga wani sarki na ta kumburi,

: Da yaranai sun sha mashi hura.

(Sa’idu Faru: Sarkin Yauwuri)

A waɗannan ɗiyan waƙa ma da aka kawo a sama, an nuna irin habaicin da makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa abokan hamayyar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur ta hanyar ƙasƙantar da wani daga cikin sarakunan da suke takon-saƙa da shi.

Har wayau, akwai wasu ɗiyan waƙa da makaɗa Sa’idu Faru ya yi da irin wannan tubali na habaici wajen ƙulla zaren tunanin waƙarsa, baya ga wuraren da aka ambata a sama. Misali,

Jagora: Ga wani ƙambolon ubanƙasa,

Y/Amshi: Da yaranai wajjen guda huɗu,

Ba ko mai suturar kwabo huɗu,

Ya shiga mota ya yi tagumi,

Da kwandon ɗunya yay yi guzuri.

(Sa’idu faru: Sarkin Yauwuri)

Idan aka lura da kyau, za a ga cewa a waɗannan ɗiyan waƙar da aka kawo, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da tubalin habaici wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Sannan ya yi habaicin ne ta hanyar nuna kushe da gazawar abokan hamayya ko waɗanda aka yi habaicin domin su. Saboda ɗiyan waƙar sun nuna ƙasƙanci ƙarara ga wanda aka yi wa habaicin, don sun fito da gazawar Ubanƙasar da aka yi wa habaicin.

6.0 Sakamakon Bincike

A wannan bincike ko nazari da aka gudanar, an gano cewa waƙar da makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur mai suna ‘Koma Shirin Daga na Bubakar, Gam da ’aren Alƙali wan Maza.’ Ya yi amfani da wasu daga cikin tubalan ginin turken waƙa wajen harhaɗa zaren tunanin waƙarsa. Saboda bincike ya gano cewa, mawaƙin ya yi amfani da tubalin zumunci ko zumunta da tubalin zambo da tubalin koɗa-kai da tubalin tarihi da kuma tubalin habaici. Sannan binciken ya gano cewa, mawaƙin ya fi yin amfani da tubalin habaici wajen ƙulla zaren tunanin da waƙarsa take ɗauke da shi. Daga nan kuma, sai tubalin zambo.

7.0 Kammalawa

Haƙiƙa, wannan bincike ya fito da tubalan ginin turken da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen gina wannan waƙa ta Sarkin Yawuri. Saboda bincike ya tabbatar da cewa, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da tubalin zumunci ko zumunta da tubalin zambo da tubalin koɗa kai da tubalin tarihi da kuma tubalin habaici wajen gina turken waƙar da ya yi wa Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur. Gindin wannan waƙa ta Sarkin Yawuri shi ne, ‘Koma Shirin Daga na Bubakar, Gamda’aren Alƙali wan Maza’.

Manazarta

Adamu, M. (2015). “Yabo Tubalin Ginin Tallar ‘Yan Takara Cikin Waƙoƙin Ƙarni na Ashirin da Ɗaya: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Siyar Jamhuriya ta Huɗu”. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, Vol. 1. No. 1, p. 122-128. Department of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Auta, A. L. (2019). “Tubalan Gina Turken Yabo a Waƙoƙin Sarauta”. Journal of Humanities, Vol 2, No. 1, p. 229-238, African Languages Department, College of Humanities, Alƙalam University Katsina, Katsina State.

Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Center Limited.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Gusau, S. M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙoƙin Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2005). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka na Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka Zaɓaɓɓun Matanonin Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Centuary and Publishing Limited.

Lawal, N. (2014). “Tubalan Ginin Turke a Waƙar ‘Yancin kan Nijeriya ta Sarkin Taushin Katsina”. Garkuwan Adabin Hausa, A Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo, 425-430. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

Sa’id, B. (1978). “Gudummuwar Masu Jihadi kan Adabin Hausa”. Kundin Digirina Biyu. Jami’ar Bayero Kano.

Yahya, A. B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Sa'idu Faru

Post a Comment

0 Comments