Citation: Darma, A.Y. & Hassan, S. (2024). Nazarin Ararrun Kalmomi a Waƙar Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ta Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 70-75. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.009.
NAZARIN
ARARRUN KALMOMI A WAƘAR SARKIN MUSULMI
MUHAMMADU MACCIƊO TA SA’IDU FARU
Daga
Dr. Abdullahi Yakubu Darma
Sashen Nazarin Harshen Hausa,
Tsangayar Nazarin Ilimin Sakandare Ɓangaren
Harsuna,
Kwalejin Ilimi Ta Isa Kaita, Dutsin-Ma, Jihar Katsina, Nijeriya
08036375129 / 07056082213
ayakubudarma@gmail.com
Da
Sani
Hassan
Sashen Nazarin Harshen Hausa,
Tsangayar Nazarin Ilimin Sakandare Ɓangaren
Harsuna,
Kwalejin Ilimi Ta Isa Kaita, Jakar Waya 5007, Dutsin-Ma,
Jihar Katsina, Nijeriya
08039478054 / 08025164796
hassansanig@gmail.com
Tsakure
Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin makaɗan fadar da suke amfani da kalmomin aro wajen isar da saƙon da waƙarsu take ɗauke da shi a ƙasar Hausa. Ya yi wa sarakuna da ‘ya’yan saraki mabambantan
waƙoƙi a lokacinsa.
Sannan yana daga cikin makaɗa ko mawaƙan da suke zaɓen kalmomin da suke amfani da su wajen sassaƙa ƙananan saƙonni a lokacin da
suke ƙulla
waƙa.
Saboda haka, babbar manufar wannan takarda ita ce, bayyana ararrun kalmomin da
makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen ƙulla waƙar da ya yi wa
Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, mai suna Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari, Sarkin Kudu
Macciɗo ci maraya. An gudanar da wannan bincike ta hanyar
karantawa daga bugaggun bayanai da sauraron wasu daga cikin waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. Bugu da ƙari, binciken ya gano cewa, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da ararrun kalmomin da Hausa ta
aro daga harshen Larabci da kuma Ingilishi wajen ƙulla zaren tunanin
waƙarsa.
Kalmomin da suka samo asali daga harshen Larabci sun haɗa da Duniya da Ilmi da Dalili da Allah da kuma Istingifari.
Har wa yau, akwai kalmomi irin su Almuɗɗafa da Lahira da Wasicci da Azumu da kuma Sunna. Ararrun
kalmomin da mawaƙin ya yi amfani da su na harshen Ingilishi kuwa, sun ƙunshi Bandur da Yadi
da Fam da Biskit da Minti da kuma Sitawut. Haka kuma, akwai kalmomi irin su Lemu
da Soda da Sigari da kuma Benci.
Fitilun Kalmomi: Waƙa, Makaɗa
Sa’idu Faru, Ararrun Kalmomi, Harshen Ingilishi, Harshen Larabci
1.0 Gabatarwa
Aron kalmomi ba baƙon al’amari ba ne a yawancin harsunan
duniya, domin yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke kawo
bunƙasa tare da ɗaukakar harshe. Harshen Hausa yana ɗaya daga cikin harsunan da suka samu ɗaukaka da bunƙasa ta sanadiyyar kalmomin aro. Saboda harshen Hausa cike
yake da kalmomin da ya ara daga wasu harsunan da ya yi mu’amala da su da kuma
waɗanda suka maƙwabce shi. Kalmomin
sun yi matuƙar tasiri ga maganganun Hausawa na yau da kullum, domin da
wahala a fara zance a ƙare shi, ba tare da mai magana ya sako wata kalma da harshen
Hausa ya ara daga wasu harsunan ba. Irin wannan tasiri da kalmomin aro suke da
shi a harshen Hausa, ya sa wannan takarda ta yi nazarin ararrun kalmomin da
makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen rera waƙar da
ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo mai
suna Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari,
Sarkin Kudu Macciɗo ci Maraya.
Shi
makaɗa Sa’idu
Faru, yana ɗaya
daga cikin shahararrun makaɗan
fada a ƙasar
Hausa. Makaɗan
fada a ƙasar
Hausa su ne makaɗan da
suke yi wa sarakuna da sauran waɗanda
suka jiɓanci
ko suka gaji sarauta waƙa. Makaɗan
fada suna isar da mabambantan saƙonni a waƙoƙin da suke rera wa iyayen gidansu ta hanyar zaɓar kalmomin da suke ganin sun dace wa
wanda suke wa waƙa. Ma’ana, ba kara zube suke rera waƙar ba,
a’a, suna zaɓen
kalmomin da suke amfani da su wajen sassaƙa saƙonni da suke son su isar ga iyeyen gidansu ko masu sauraron
waƙoƙin
nasu. Makaɗa
Sa’idu Faru ya rera waƙoƙi masu tarin yawa. Daga cikin waƙoƙin da
ya rera, akwai waƙar Sarkin Yaƙin Banga Alhaji Sule Ƙauran Namoda da waƙar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo da waƙar Sarkin Fulanin
Bunguɗu Alhaji Shehu da waƙar Turakin Kano Alhaji Amadu da waƙar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur, da dai
sauran makamantansu.
1.1 Ma’anar Waƙa
Yahya
(1997:4) ya nuna cewa, “Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi
saƙo
cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar
ta reru ba faɗuwa
kurum ba.” Shi kuma (Gusau, 2003:xiii) ya nuna cewa, waƙa
tsararren zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin
tsarin daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa amon kari da kiɗa da amshi. Waƙa aba
ce da fasihai ke amfani da ita domin bayyana wata manufarsu cikin sauri ga
jama’a. Domin kuwa waƙa ta fi saurin karɓuwa ga
jama’a, an fi son sauraron ta fiye da wa’azi. Wannan ne ma ya sa yawancin
ayyukan malaman jihadi waƙoƙi ne, (Sa’id, 1978:66). Waƙa wata
kafa ce ta yaɗa
manufa cikin gaugawa kamar yadda iska ke kaɗawa ta game ko’ina cikin ɗan ƙanƙanen
lokaci, (Adamu, 2015:122). Sannan an nuna cewa, waƙa tana
zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka waɗanda
ake kira baitoci ko ɗiyoyi
kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman, (Umar, 1980:3) a cikin
(Zainab, 2014:431). Har wa yau, an nuna cewa, waƙa wani
saƙo ne
da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango,
rerawa, kari (bahari, amsa-amo (ƙafiya) da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da
ba lalle ne haka suke a maganar baka ba (Ɗangambo, 2008: 5).
Ta la’akari
da waɗannan
ma’anoni, a iya bayyana ma’anar waƙa da cewa, tsararren zance ne da ake shiryawa, a rera a
cikin hikima da basira da sautin murya mai zaƙi bisa
tsarin daidaitawa da zaɓen
kalmomi domin a isar da saƙon da ake buƙata cikin gaugawa.
2.0 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru
Gusau
(2005: 117), ya bayyana cewa, an haifi Makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru ta ƙasar
Marsden a jihar Zamfara a shekarar 1932. Makaɗa Abubakar ɗan Abdul ɗan Alu mai kurya shi ne mahaifin malam
Sa’idu. Mahaifiyarsa kuwa mutumiyar Banga ta ƙasar Ƙauran
Namoda ce. Sa’idu ya yi rayuwar ƙuruciyarsa a garin mahaifiyarsa, watau Banga. Sa’idu bai yi
karantun boko ba, haka nan ma bai yi karatun Muhammadiyya mai zurfi ba.
Mahaifin Makaɗa
Sa’idu makaɗin
Kotso ne, kuma makaɗin
sarauta ne. Ashe Makaɗa
Sa’idu ya yi gadon kiɗan
Kotso ne kuma ya yi gadon kiɗan
sarauta ne daga mahaifinsa Abubakar ɗan
Abdu ɗan
Alu. Makaɗa
Sa’idu ya riƙa bin mahaifinsa yawon kiɗa, daga nan ne ya koyi dabarar rera waƙa,
sannan kuma ya daɗa bunƙasa ne
domin shi kansa Allah ya yi masa baiwa da fasaha ta yin waƙoƙi. Makaɗa Sa’idu yakan shirya waƙoƙinsa
daga gida ne kafin ya je fagen reraŵa. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da cewar
yanayin waƙoƙinsa suna da amshi da ƙari ne, kuma yakan binciki sunayen iyaye da kakannin da yake
sakawa a cikin waƙoƙinsa. Kodayake wani lokaci waƙa
takan zo masa nan take, kuma ya rera ta. (Gusau, 2005:117-122)
Daga
cikin yaran Sa’idu waɗanda
suke kama masa waƙa akwai Mu’azu (Ɗan Galadimansa) da Ɗan Daudu da kuma Ali. Daga cikin iyayen gidansa kuwa akwai
Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar na III da
Abubakar Sarkin Ƙauran Namoda (Gusau, 2005, sh. 117-122). Allah ya yi wa Makaɗa Alhaji Sa’idu Faru rasuwa a shekarar
1987.
3.0 Manufar Bincike
Babbar
manufar wannan takarda ita ce, bayyana ararrun kalmomin da makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen
isar da saƙon waƙar da ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo. Ma’ana, takardar ta zaƙulo ararrun
kalmomin da makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen gina turken waƙarsa
ta Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo mai
suna Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari,
Sarkin Kudu Macciɗo ci Maraya.
4.0 Dabarun Bincike
A ƙoƙarin
gudanar da wannan nazari ko samo bayanan da wannan bincike ya ginu a kan su, an
bibiyi wasu bugaggun bayanai da aka samu a wasu daga cikin littattafai da kuma sauran
takardun ilimin da aka samu. Haka kuma, an saurari wasu daga cikin waƙoƙin
makaɗa
Sa’idu Faru a wayar salula da kwamfuta da kuma na’urar MP3. Wanda daga bisani
aka tsayar da alƙiblar wannan aiki a kan waƙar da
Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo. Har ila yau, aikin ya inganta ƙwarai
a sanadiyyar samun wannan waƙa a cikin Diwanin Waƙoƙin Baka Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin
Baka na Hausa da Gusau ya buga a shekarar 2009.
5.0 Yanaye-Yanayen Ararrun Kalmomi a Waƙar
Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo
Tabbas
Makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da wasu daga cikin kalmomin da harshen Hausa ya aro
daga wasu harsunan duniya waɗanda
wata mu’amala ta taɓa haɗa su a tarihin ce. A nan za a iya ganin
irin yanaye-yanayen waɗannan
kalmomi da makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da su wajen ƙulla zaren tunanin waƙarsa, wadda ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, mai suna Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari, Sarkin Kudu Macciɗo ci Maraya kamar haka.
5.1 Ararrun Kalmomi Daga Harshen Larabci
Lallai
bincike ya tabbatar da cewa, makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da wasu daga cikin kalmomin da harshen Hausa ya aro
daga harshen Larabci wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke
da shi. Za a iya ganin misalan hakan a waɗannan ɗiyan waƙa da
suke biye a ƙasa.
Jagora: Na Marafa Ɗanbaba mai tara haushi,
Na sarkin Gabas duniya
hori-wawa,
Bai
gadi sake ba Mamman na Baura, …
Idan
aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa, za
a ga cewa makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da ararriyar kalmar da harshen Hausa ya aro daga
harshen Larabci ta ‘duniya’ wajen isar da saƙon waƙansa.
Kenan, kalmar ‘duniya’ ita ce ararriyar kalmar da aka aro daga harshen Larabci,
wadda ‘dunnya’ ita ce asalin kalmar a Larabce, kuma ita ce mawaƙin ya
yi amfani da ita a waƙarsa.
Bayan wannan kuma, akwai wasu ɗiyan waƙar da
yaronsa Mu’azu yake cewa,
Mu’azu: Faɗi
gaskiya Bello kai Shehu yac ce,
Bari masu son duk su maishe ka yaro,
Da kyauta da ilmi
da neman dalili,
Da gode wa Allah
da istingifari,
Da su Bello ɗan
Shehu yat tsarma kowa,
Ka kai kamab Bello ka gadi Moyi,
Y/Amshi:
Saura ka kai inda mai Hausa yak kai.
A nan
kuma, idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa da
Mu’azu ya kawo a cikin wannan waƙa ta Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, za a ga cewa akwai wasu daga cikin
kalmomin da harshen Hausa ya aro daga harshen Larabci. Misali, mawaƙin ya
kawo ɗiyan
waƙar da
ya yi maganar ‘ilmi’ da ‘dalili’, dukkan waɗannan kalmomi ne na Larabci da harshen
Hausa ya aro, wato daga kalmar asali ta ‘ilmun’ da ‘dalil’ a Larabce. Haka
kuma, mawaƙin ya ambaci ‘Allah’ da ‘intingifari’, su ma kalmomi ne da
Hausa ta aro daga Larabci, wato daga kalmar asali ta ‘Allahu’ da ‘istigfar’ a
Larabce. Kenan, a wannan waƙa ta Sa’idu Faru an yi amfani da kalmomin aro na Larabci
wajen isar da saƙon da waƙar take ɗauke
da shi.
Har ila yau, akwai kuma wasu ɗiyan waƙa da
makaɗa
Sa’idu Faru ya sake yin amfani da kalmomin da asalinsu na Larabci ne wajen
jojjona zaren tunanin waƙarsa kamar yadda za a gani a nan ƙasa:
Jagora: Da mutum da dabba da tsuntsu da ƙwaro,
Y/Amshi: Mutum da dabba da tsuntsu da ƙwaro,
Da ƙasa da abin da duk ag ga bayanta,
Komai na duniya
na Almuɗɗafa na,
Garai Shehu yas samu girma da yarda,
Komi na gun Shehu shi ag ga Bello,
Komi na gun Bello shi ag ga Garba
Ko lahira ko muna taƙamatai.
A nan
kuma, idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa, za
a ga cewa inda makaɗa
Sa’idu Faru ya kawo kalmar ‘duniya’ da ‘Almuɗɗafa’ da kuma ‘lahira’, ya yi amfani da
kalmomin aro. Saboda kalmomin da Hausa ta aro daga harshen Larabci ne. Wato
kalmar ‘duniya’ asalinta daga kalmar ‘dunya’, kalmar ‘Almuɗɗafa’ asalinta daga kalmar ‘Almusɗafa’, sai kalmar ‘lahira’ ita kuma
asalinta daga kalmar ‘akirati’. Tabbas waɗannan
bayanai sun tabbatar da cewa makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da kalmomin aro na Larabci wajen isar da saƙon waƙar da
ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo.
Daga nan kuma, akwai wani ɗiyan waƙa shi
ma da yake nuna yadda makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da ararriyar kalmar Larabci wajen isar da saƙon waƙarsa
kamar yadda za a gani a ƙasa.
Jagora: Da biskit da minti da taba sigari,
Y/Amshi: Biskit da minti da taba sigari,
Da lemu da soda da kwalbat sitawut,
Bai yada aza su ko sau guda ba,
Ya ɗau wasiccin da Usumanu yac ce,
Ya ce abincinsu ba namu ne ba,
Yawanci abincinsu daɗi gare
shi,
Kowanmu ne yai ta ci ba ruwanai,
Wancan
na ci sai ta ci bai ci can ba.
A nan
kuma, idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa, za
a ga cewa, makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da ararriyar kalmar ‘wasicci’ ne kaɗai daga harshen Larabci. Wato ya yi
amfani da kalmar ‘wasicci’ daga cikin kalmomin da Hausa ta aro daga harshen
Larabci. Wannan ya ƙara tabbatar da cewa makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da ararriyar
kalmar Larabci wajen ƙulla zaren tunanin wannan waƙar.
Hakazalika, bayan waɗannan
kuma, akwai wasu ɗiyan
waƙar da
suke nuna yadda makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da ararrun kalmomi na Larabci wajen isar da saƙon waƙarsa.
Wato waƙar da
ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, mai
suna Bajimin Gidan Mamman na Yari, Sarkin
Kudu Macciɗo ci maraya. Za a iya ganin wuraren kamar haka:
Jagora: Shi wane girma shi kai bai da wayo,
Y/Amshi: Wane girma shi kai bai da wayo,
Ya togu daidai shina nan bani na,
Ya bar azumi da
kono da sunna,
Sai ya ji goge shi ɗauko
kujera,
A shisshirya benci motsata su zauna,
A aika a ɗauko
kwalebe a buɗe,
Da ka gane ka koma ma Allah,
Shi ad da shi babu mai tsarguwatai.
Idan
aka kalli ɗiyan
wannan waƙa da suke a sama, za a ga cewa makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da ararrun
kalmomi na Larabci wajen ƙuƙƙulla zaren tunanin da waƙarsa
take ɗauke
da shi. Musamman a wuraren da ya ambaci kalmar ‘azumi’ da ‘sunna’. Tabbas waɗannan kalmomi suna daga cikin kalmomin
da Hausa ta aro daga Larabci, wato daga kalmar ‘assaum’ da kuma ‘sunnah’. Sai
kuma inda ya ambaci sunan ‘Allah’, wanda daga kalmar ‘Allahu’ ne ta samo
asalinta a Larabci. Haƙiƙa, makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da ararrun kalmomi na Larabci wajen haɗa wannan waƙa da
ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo.
5.2 Ararrun Kalmomi na Harshen Ingilishi
Dangane da abin ya shafi ararrun kalmomi na harshen
Ingilishi kuwa, makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da wasu daga cikin kalmomin da harshen Hausa ya aro
daga harshen Ingilishi. Ya yi amfani da su wajen ƙullawa,
tare da jojjona zaren tunaninsa, domin waƙarsa ta samu karɓuwa ga
wanda aka rera wa waƙar da kuma masu sauraron waƙar
tasa. Don haka, za a iya ganin misalan ararrun kalmomin da ya yi amfani da su
na harshen Ingilishi wajen shirya wannan waƙa
kamar haka:
Jagora: Baba ya ba mu bandur
guda duk na lailai,
Y/Amshi: Ya ba mu bandur
guda duk na yadi,
Ya ba mu fam goma
yac ce mu ɗunke,
Ga takalumma na fam
shidda-shidda,
Hula kalabus goma yab ban,
Kyauta irin taka jikan Mu’azu,
Don ba a cewa mutum ba kamatai,
Sai Larabawan Masar masu girma.
Idan aka kalli waɗan ɗiyan waƙa, za
a ga cewa lallai makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da wasu daga cikin kalmomin da Hausa ta aro daga
harshen Ingilishi wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke
da shi. Saboda kalmar ‘bandur’ asalinta kalmar Ingilishi ‘bandle’. Haka ma
kalmar yadi’ asalinta daga Ingilishi ne ‘yard’. Kalmar ‘fam’ asalinta daga
harshen Ingilishi ne ‘pound’. Don haka, bincike ya tabbatar da cewa, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wasu
ararrun kalmomin da Hausa ta aro daga harshen Ingilishi wajen rera wannan waƙa ta
Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo.
Bayan wannan kuma, akwai wasu ɗiyan waƙa waɗanda suka ƙara
nuna yadda makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da wasu daga cikin ararrun kalmomin da Hausa ta aro
daga harshen Ingilishi wajen isar da saƙon waƙarsa kamar yadda suka zo a ƙasa.
Jagora: Da biskit
da minti da taba sigari,
Y/Amshi: Biskit
da minti da taba sigari,
Da lemu da soda da kwalbat sitawut,
Bai ya da aza su ko sau guda ba,
Ya ɗau
wasiccin da Usumanu yac ce,
Ya ce abincinsu ba na mu ne ba,
Yawanci abincinsu daɗi gare
shi,
Kowanmu ne yai ta ci ba ruwanai,
Wancan
na ci sai ta ci bai ci can ba.
A nan
idan aka kalli waɗannan ɗiyan waƙa, za
a ga cewa suna nuna yadda makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da ararrun kalmomin da Hausa ta aro daga harshen
Ingilishi wajen jojjona zaren tunanin waƙarsa. Saboda makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da kalmar ‘biskit’ da ‘minti’ da ‘sigari’ da soda da
kuma ‘sitawut’ wajen harhaɗa wasu
ɗiyan
waƙarsa.
Waɗannan
kalmomin suna daga cikin kalmomin da Hausa ta aro daga harshen Ingilishi.
Saboda kalmar ‘biskit’ ta samo asali daga kalmar ‘biscuit’, kalmar ‘minti’ daga
‘kalmar ‘mint’, kalmar ‘sigari’ daga kalmar ‘cigret’. Haka nan, kalmar ‘lemu’
ita ma ta samo asali daga kalmar ‘lemon’, kalmar ‘soda’ daga kalmar ‘sodar’,
sai kalmar ‘sitawut’ daga kalmar ‘starwut,’ kuma dukkansu kalmomi ne na harshen
Ingilishi. Tabbas, wannan mawaƙi ya yi amfani da ararrun kalmomi na harshen Ingilishi wajen
rera waƙar da
ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo.
Har ila yau, akwai wani wuri da za a iya cewa makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da ararriyar
kalmar da harshen Hausa ya aro daga harshen Ingilishi bayan waɗanda aka gani a bayanan da suka gabata.
Za a iya ganin wurin kamar haka:
Jagora: Shi wane gima shi kai bai da wayo,
Y/Amshi: Wane girma shi kai bai da wayo,
Ya togu daidai shina nan bani na,
Ya bar azumi da kono da sunna,
Sai ya ji goge shi ɗauko
kujera,
A shisshirya benci
motsata su zauna,
A aika a ɗauko
kwalebe a buɗe,
Da ka
gane ka koma ma Allah,
Shi ad
da shi babu mai tsarguwatai.
A nan
ma, idan aka lura da waɗannan ɗiyan waƙa, za
a ga cewa makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da ararriyar kalmar ‘benci’ a wajen isar da saƙon da
waƙarsa
take ɗauke
da shi. Saboda ita wannan kalma ta ‘benci’ asalinta kalmar Ingilishi ce ‘bench’
harshen Hausa ya aro. Don haka, bayanai sun tabbatar da cewa makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wannan
ararriyar kalmar da ta samo asali daga harshen Ingilishi wajen isar da saƙon da
waƙarsa
take ɗauke
da shi ga wanda aka shirya ko aka rera wa waƙar da
sauran masu sauraro.
6.0 Sakamakon Bincike
Bincike
ya gano cewa, makaɗa
Sa’idu Faru a waƙar da ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, mai suna Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari, Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya Mawaƙin ya yi amfani da ararrun kalmomin da harshen Hausa ya aro
daga harshen Larabci da kuma na Ingilishi. Bincike ya tabbatar da cewa, ararrun
kalmomin da mawaƙin ya yi amfani da su na harshen Larabci wajen ƙulla
zaren tunanin waƙarsa sun haɗa da Duniya da Ilmi da Dalili da Allah. Har wa yau, akwai kalmomi irin su
Istingifari da Almuɗɗafa da Lahira da Wasicci da Azumi da kuma Sunna. Su
kuma ararrun kalmomin da mawaƙin ya yi amfani da su na harshen Ingilishi kuwa, sun ƙunshi Bandur da Yadi da fam da Biskit da
kuma Minti. Haka kuma, akwai kalmar Sitawut da Lemu da Soda da Sigari da kuma Benci. Waɗannan
bayanai sun tabbatar da cewa, makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da wasu daga cikin ararrun kalmomin da harshen Hausa
ya aro daga harshen Larabci da kuma na Ingilishi wajen shirya wannan waƙa.
7.0 Kammalawa
Wannan
bincike ya yi nazari a kan waƙar da makaɗa
Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo. Bincike ya gano cewa, makaɗa Saidu Faru ya yi amfani da wasu daga
cikin ararrun kalmomin da harshen Hausa ya aro daga harshen Larabci da kuma na
Ingilishi. Mawaƙin ya yi amfani da waɗannan
ararrun kalmomin wajen ƙulla zaren tunanin waƙarsa. Wato ya yi amfani da su ya isar da saƙon da
waƙarsa
take ɗauke
da shi ga Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo da
sauran masu sauraro. Sannan binciken ya fito da ilahirin ararrun kalmomin da
mawaƙin ya
yi amfani da su na harshen Larabci da kuma na Ingilishi a wannan waƙa mai
suna Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari,
Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.
Manazarta
Adamu, M. (2015). “Yabo Tubalin Ginin Tallar ‘Yan Takara
Cikin Waƙoƙin Ƙarni na 21: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin
Siyar Jamhuriya ta Huɗu”. Algaita Journal of Current Research in Hausa
Studies, Ɓol. 1. No. 1, p. 122-128. Department
of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Zaria: Ahmadu Bello University
Press Limited.
Ɗangambo,
A. (2008). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. (Sabon Tsari). Zaria: Amana Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2003). Jagoran
Nazarin Waƙoƙin Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2005). Makaɗa da Mawaƙan Hausa. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin
Baka na Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu.
Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S. M. (2009). Diwanin
Waƙoƙin Baka Zaɓaɓɓun Matanonin Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Centuary and Publishing Limited.
Sa’id, B. (1978). “Gudummuwar Masu Jihadi kan Adabin Hausa”.
Kundin Digiri na Biyu. Jami’ar Bayero Kano.
Yahya, A. B. (1997). Jigon
Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.
Zainab, I. (2014). “Jiga-Jigan Hausa a Bakin Mawaƙin
Hausa: Waiwaye a kan Waƙoƙin Ala na Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau”. Garkuwan Adabin Hausa, a Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo, 431-440. Zaria: Ahmadu Bello University
Press Limited.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.