Citation: Gummi, M.F. & Sarkin Gulbi, A. (2024). Homa Ko’ina Da Ruwanku: Laluben Sarkanci a Cikin Waƙoƙin Fada Na Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 82-91. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.011.
HOMA KO’INA DA RUWANKU: LALUBEN
SARKANCI A CIKIN WAƘOƘIN FADA NA MAKAƊA SA’IDU FARU
Na
Musa Fadama Gummi Ph.D
Sashen Harsuna da Al’adu
Jami’ar Tarayya Gusau, Jihar Zamfara, Nijeriya
Email: gfmusa24@gmail.com, mfadamagummi@fugusau.edu.ng
GSM NO.: +2347065635983
Da
Abdullahi Sarkin Gulbi Ph.D
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto,
Nijeriya
sgulbi@gmail.com, gulbi_abdullahi@udusok.edu.ng
GSM NO.
+2348089949294
Tsakure
Sarkanci muhimmiyar sana’ar gargajiya ce. Irin ayyukan da
masu aiwatar da sana’ar suke yi a cikin al’umma, sun haɗa da samar da kifi, wata halitta da ke ƙunshe da sanadarai masu inganta jiki da
ƙara masa lafiya sannan ga gudunmuwar da
suke bayarwa a fagen kiwon lafiya na gargajiya a al’ummar Hausawa. Waƙoƙin sarauta ko waƙoƙin fada, waƙoƙi ne da mawaƙan Hausa suke rerawa tare da kiɗa domin yabo da gwarzanta sarakunan ƙasar Hausa da nufin ƙwarzanta su da nishaɗantar da su tare kuma da yaɗa martaba da muhibbarsu ga duniyar Hausawa masu saurare
da sha’awar waƙoƙin baka. Babban aikin Sarakuna shi ne mulki da jagorancin
al’umma tare da ba su kariya da yi masu adalci. Aiwatar da sana’o’in gargajiya
aiki ne da ya rataya a wuyan talakawa, amma duk da haka a cikin waƙoƙin sarauta na Hausa, ana samun jirwaye na wasu muhimman
sana’o’in gargajiya a cikin kalaman azanci a
waƙoƙin makaɗan fada, ciki kuwa har da makaɗa Sa’idu Faru. Adabi madubi ne na rayuwar al’umma don haka
ba abin mamaki ba ne idan waƙoƙin fada sun ƙunshi lamurran al’adu na rayuwar al’umma. Ƙudurin wannan muƙala shi ne yin nazari a cikin waƙoƙin fada na makaɗa Sa’idu Faru da nufin zaƙulo lamuran da suka jiɓinci sarkanci ko kamun kifi a cikinsu. An tattaro waƙoƙin fada na makaɗa Sa’idu Faru da dama domin sauraron su
a natse ta yadda za a fito da turaku daban-daban da suka danganci sana’ar
sarkanci. Muƙalar ta gano dalilan da suke sa makaɗan fada saka lamarin sarkanci a cikin
wasu waƙoƙinsu. Daga ciki akwai samun damar yin zambo da shaguɓe ga ‘ya’yan sarauta, tun ma ba a ce masu adawa da sarki
ba. Haka ana saka batu da ya jiɓinci sarkanci domin a nuna alhairi da
sarautar wanda ake wasawa ta haifar ga al’ummar da yake jagoranta, da sauran
abubuwa makamantan waɗannan.
Fitattun Kalmomi: Homa, Lalube, Sarkanci, Waƙoƙi, Fada.
Sarauta tsari ne na shugabanci irin na gargajiya a
Bahaushiyar al’ada kuma ko da iska ta zo, ta tarar da kaba tana kaɗawa. Tsarin sarauta a al’adar Bahaushe abu ne daɗaɗɗe wanda Hausawa ba aro shi suka yi ba
daga kowace al’umma. Ko da Larabawa da Turawan Mishan da ‘yan mulkin mallaka
suka kutso kai ƙasar Hausa, sun tarar da al’ummar Hausawa suna da tsarin
shugabancinsu da ya dace da muhallinsu da al’adunsu. A ƙasar Hausa, Allah mai iko da buwaya ya
hore wa wasu mutane basira da zalaƙa da fikira ta tsara daɗaɗan kalamai da ake iya rerawa cikin
murya mai zaƙi da armashi tare da jan hankali; wadda
kuma akan gwama ta da kiɗa ko busa ta yadda za a sami wani amo
da sautinsa zai tafi bai ɗaya da abin da baki yake rerawa. Waƙar baka ta Hausa aba ce mai muhimmancin
gaske a fagen ba da nishaɗi da isar da saƙo da adana tarihi da al’adu na al’ummar
Hausawa. Daga cikin mutanen da Allah ya yassare wa hikimar tsara waƙa, akwai waɗanda suka duƙufa wajen yi wa shugabanni musamman
sarakuna waƙoƙi domin nishaɗantar da su da yaba masu domin ƙara masu ƙwarin guiwa kan ɗorewa da aikata ayyuka na alheri da suke yi wa
talakawansu na yi masu adalci da jagoranci na gari. Yayin da waɗannan makaɗa suke tsara waƙoƙin nasu, sukan saka batutuwa da dama waɗanda suke saƙa turke da salo na waƙar da kuma warware turken.
Daga cikin irin waɗannan batutuwa da makaɗan fada suke sakawa a waƙoƙin nasu domin fayyace ko warware turke ko turakun da suka
gina waƙoƙinsu, akwai batun da ya jiɓinci sarkanci ko kamun kifi. Duk da cewa sarakuna a ƙasar Hausa suna da wani matsayi maɗaukaki da bisa al’ada yakan hana su aiwatar da wasu
sana’o’i masu wahalar gaske waɗanda galibi talakawa aka sani da su.
Sarkanaci ko kamun kifi yana ɗaya daga cikin ire-iren waɗannan sana’o’i da idan har aka ga basarake yana aiwatar
da su to kuwa yakan zama abin zargi da ka iya janyo masa zambo daga maroƙa ko makaɗan masarauta. Wannan yana nuni da cewa makaɗan fada suna saka zantuka da suka jiɓinci lamarin sarkanci ko kamun kifi a cikin waƙoƙinsu na fada domin wasu dalilai. Makaɗa Sa’idu Faru kasancewarsa fasihi wanda ya naƙalci harshen Hausa sosai, ba a baya
yake ba wajen irin wannan ƙoƙari na amfani da sarkanci a cikin waƙoƙinsa na fada, waɗanda su ne mafi rinjaye sosai a ɗaukacin waƙoƙinsa. Ƙudurin wannan muƙala ne ta bijiro da dalilan da suka
sanya makaɗan fada suke amfani da lamarin sarkanci
a cikin waƙoƙinsu.
2.0 Ma’anonin Tubulan Take.
Taken wannan muƙala an gina shi ne ta hanyar amfani da wasu kalmomi
muhimmai kuma fiatattu, waɗanda su ne tubula. Kalmomin su ne homa
da sarkanci da waƙoƙin fada. Waɗannan kalmomi ne ake son a bayyana
ma’anoninsu ɗaya bayan ɗaya a nan.
2.1 Homa (Koma)
Ƙamusun Hausa na jami’ar Bayero,
(CNHN:2016) ya faɗa cewa homa/koma raga ce da ake saƙawa da zare a ɗaura itace, a yi amfani da ita wajen kamun kifi. Wato
raga ce ta kamun kifi wadda ake ɗaurawa a jikin wasu lanƙwasassun itatuwa waɗanda su ne ake riƙawa a hannu biyu yayin da ake kamun kifi. Masuntan da
suke amfani da irin wannan kaya wajen kamun kifi sukan sami shugaba wanda ake
kira Homa. Wannan yana nufin ko baya ga kasancewar homa kaya na kamun kifi, kalmar
tana kuma kasancewa sunan da ake kiran shugaban duk masunta da suke amfani da
irin wannan raga wajen kamun kifi (Fadama, 2016:439). Yadda aka yi amfani da
kalmar a taken wannan muƙala, tana ɗaukar ma’ana ta biyu, wato sarautar da akan naɗa wa shugaban masu kamun kifi waɗanda suke amfani da homa/koma a matsayin kayan aiki.
2.2 Lalube
Lalube kalma ce ta Hausa wadda take nufin bincika wani
abu da hannu a cikin duhu (CNHN, 2006:300). Baya ga wannan gundarin ma’ana da Ƙamusun Jami’ar Bayero ya kawo, kalmar lalube kalma
ce ta fannu da ake amfani da ita a sha’anin sarkanci ko kamun kifi. Dabara ce
ta kamun kifi wadda yayin aiwatar da ita ake shiga ruwa domin kama kifi ta
amfani da hannu kawai. Masunci kan shiga ruwa da nufin kama kifi ta amfani da
hannayensa biyu. Zai riƙa tattaɓa ƙasan ruwan da niyar ya yi gamon-katar
na kama kifi da hannu. A wannan muƙala, lalube na nufin yin nutso cikin
tarin waƙoƙin fada na makaɗa Sa’idu Faru da nufin nemo ko gano ko
zaƙulo wuraren da aka yi amfani da sha’anin sarkanci ko kamun kifi a cikin waƙoƙin.
2.3 Sarkanci
Asalin kalmar sarkanci ba Bahaushiya ba ce. An samo ta ne
daga kalamar ‘Sorko’ wata al’umma da take cikin tsohuwar daular Sanwai (Songhai).
Al’ummar Sorko ta shahara matuƙa a fannin kamun kifi da fito a kogin nan na Kwara wato River Niger, da kuma fadamun da suke raɓe da shi. Kogin ya ratso cikin ƙasashen Afrika da dama kafin ya shigo Nijeriya a
ƙauyen Bahindi ta ƙaramar hukumar mulkin Bagudo a jihar
Kebbi. Domin faɗaɗa wurin aiwatar da sana’arsu, al’ummar
‘Sorko’ sun yi ƙaura zuwa cikin ƙasar Kabi wadda a wancan lokaci take
wani yanki da ke ƙarƙashin daular Sanwai. Masana tarihi sun tabbatar da cewa
waɗannan mutane na ‘sorko’, sannu a
hankali sun saje da masu masaukinsu ta hanyar auratayya sakamakon karɓuwa da suka samu a yankin Kabi. Shigar ‘Sorko’ a Kabi ta
yi tasirin gaske a lamarin kamun kifi ba yankin kaɗai ba, har ma ɗaukacin ƙasar Hausa. Wannan ya faru ne sakamakon
ƙwarewarsu ga sha’anin kamun kifi, da
kuma ingantattun kayayyakin kamun kifi da suka zo da su. Tun a wannan lokaci,
sai aka riƙa kiran duk wani ƙwararren masunci tilo da suna ‘Basarke’,
jam’i kuwa ‘Sarkawa’ yayin da sana’ar aka riƙa kiran ta da suna ‘Sarkanci’. Ma’anar kalmar ita ce ƙwarewa a sana’ar kamun kifi da laƙantar lamarin ruwa da fito a kogi da
kuma farautar dabbobin ruwa kamar ayu da kada da dorina da karen ruwa da dai
sauran su. Yakan haɗa har da sanin asiran ruwa da sanin magungunan
cututukan da sanyi kan haifar.
2.4 Waƙoƙin Fada
Waƙar baka bisa ma’ana magana ce ta hikima
da akan tsara ta cikin azanci ta amfani da zaɓaɓɓun kalmomi kuma zaunannu waɗanda akan rera da wata murya mai rauji da daɗin sauraro da wani lokaci akan gwama da kiɗa da amshi. Yahya, (1997:58) ya faɗa cewa waƙoƙin sarauta waƙoƙi ne da ake yi wa sarakuna da masu
jinin sarauta. Sarauta ta haɗa da Sarki da hakimi da waziri da ɗangaladima da duk wanda sarki kan naɗa domin taimaka masa gudanar da lamarin mulki a
farfajiyar ikonsa. A can da akwai wasu rukuni na mawaƙan baka da ba sa yi wa kowa waƙa sai wanda ya jiɓinci sarauta. Waƙoƙin da aka rera domin Sarki ko wani mai
alaƙa da fada su ake kira waƙoƙin sarauta ko waƙoƙin fada. Makaɗa Sa’idu Faru wani babban misali ne na makaɗan fada kasancewarsa ba ya yi wa talaka waƙa duk kuwa yawan ƙasurarsa ko yawan dukiyarsa.
3.0 Taƙaitaccen tarihin Makaɗa Sa’idu Faru
Allah a cikin ikonsa da buwayarsa ya rayar da wasu
mashahuran mawaƙan ƙasar Hausa a yankin Zamfara. Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin waɗannan mawaƙa na ƙasar Hausa da suka rayu a farfajiyar
yankin Zamfara na ƙasar Hausa. Akwai saɓanin ra’ayi dangane da shekarar haihuwar wannan mashahuri
kuma haziƙin mawaƙi. A wani ƙauli, ana ganin cewa an haifi makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru na gundumar Faru a ƙaramar hukumar mulkin Maradun ta jihar
Zamfara a cikin shekara ta 1932 (Gusau, 1996:117). A wani ƙauli kuwa, ana kyautata fahimta cewa an
haifi Sa’idu Faru ne a
shekara ta 1916[1]. Sunan mahaifin Sa’idu Faru shi ne Makaɗa Abubakar wanda mutumin Faru ne ta ƙasar Maradun. Mahaifiyarsa kuwa,
mutumniyar Banga ce ta ƙaramar hukumar mulki ta Ƙauran Namoda a jihar Zamfara. Makaɗin ya yi rayuwarsa ta ƙuruciya a garin mahaifiyarsa wato
Banga. Da ya tasa, sai makaɗa Sa’idu Faru ya koma Faru wurin
iyayensa.
Makaɗa Sa’idu Faru ya yi biyar mahaifinsa a
wajen yawon waƙa. Wannan ne ya ba shi damar koyon kiɗa da waƙa a wajen mahaifin nasa, Makaɗa Abubakar. Sa’idu Faru bai fara cin gashin kansa a
sha’anin kiɗa da waƙa ba sai bayan da Allah ya yi wa
mahaifinsa rasuwa. A wannan lokaci ne Sa’idu ya maye gurbin mahaifin nasa a
matsayin jagora na tawagarsu ta waƙa. A cewar Gusau, (1996: 119), waƙarsa ta farko da ya yi bayan samun cin
gashin kansa ita ce wadda ya yi wa Sarkin Yamman Faru Ibrahim wadda gindinta
shi ne:
Gindin Waƙa: Bi da maza ɗan Joɗi na Rwafi
Iro magajin Shehu da Bello
Hasken hitila ba ɗai da wata ba
Tauraro haskenka subahin
Dawaya kora ɗimau na Wakili
Uban Sarkin Zagi Bello da Yari
Ruwa da kada ɗibgau na Magaji
Sai tsohon wawa ka shigas su.
(Gusau, 1996:119)
Makaɗa Sa’idu Faru mashahurin
makaɗin fada ne da ba ya yi wa kowa waƙa face sarakuna da masu
alaƙa da sarauta kamar ‘Yangaladimomi da masu riƙe da muƙaman gargajiya. Wannan ya fito ƙarara a cikin wani ɗan waƙa tasa da ya yi wa Sarkin Sudan na Wurno, Alhaji Shehu Malami inda yake
cewa:
Gindin Waƙa: Muzakkarin Sarki ɗan Abdu,
Abin biya Shehu na Ali.
Jagora: Ɗan talakka komi yac cika huska, x2
‘Y/Amshi: Sa’idu ni ba ni kiɗa mai. x2
Jagora: Ɗan talakka komi ya aje ƙarhe,
‘Y/Amshi: Sa’idu ni ba ni kiɗa mai.
Makaɗa Sa’idu Faru ya faɗa a wani ɗa na waƙar da ya yi wa Turakin Kano, Alhaji Ahmadu cewa idan dai waƙar fada ce, kowace aka ji ko saurara koma bayan tasa ce domin kuwa su suka
iya ta. Ɗan waƙar na cewa:
Gindin Waƙa: Tsakin tama na Abashe,
Ana shakkar haye ma Amadu,
Mai daraja na Wambai,
Ɗan Hashim ƙanen Sarkin Kano.
Jagora: Sa’idu Faru ka waƙa iko,
‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya akai,
Jagora: Sa’idu ka waƙam mulki,
‘Y/Amshi: Komi kaj jiya ƙarya akai.
(Gusau, 2009:162)
A tsawon rayuwarsa, Sa’idu Faru ya yi wa manya da ƙananan sarakuna da hakimai (Iyayen ƙasa) daban-daban daɗaɗan waƙoƙi masu ratsa zukata, waɗanda suke cike da hikima da basira da zalaƙa.
Duk da kasancewa Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa
sarakuna da dama waƙoƙi daban-daban, Magirma Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi
Abubakar na III (Allah ya lulluɓe su da rahama) shi ne ubangidansa. Tabbacin haka ya bijiro a wani ɗan waƙa tasa da ke cewa:
Gindn Waƙa: Farin cikin Musulmin duniya,
Mai martaba na Abubakar,
Ci fansa Alhaji Macciɗo.
Jagora: Ban wuce gonata da irina ba, x2
‘Y/Amshi: Inda Sarkin Kudu nits tsaya.x2
Makaɗa Sa’idu Faru makaɗi ne da ya rabauta da baiwa ta naƙaltar harshen Hausa
sosai. Yana da yaransa da suke taimaka masa wajen amshin waƙa da yi masa ƙari da tarbe. Yaransa su ne:
i. Mu’azu Daudun kiɗa (ƙanen Sa’idu)
ii. Ɗandaudu
iii. Ali
Allah mai iko da buwaya ya ƙarɓi rayuwar Makaɗa Sa’idu Faru gabanin maigidansa Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu
Macciɗo ya hau karagar mulki ta Sarkin Musulmi. Sa’idu ya bar duniya ne a shekara
ta 1987. Ya rayu tsawon shekaru 71.
4.0 Karatun Sarkanci A Bakin Sa’idu Faru
Yanzu muƙalar za ta yi nitso cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru domin lalubo yadda malamin waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ya kawo lamarin sarkanci a cikin waƙoƙinsa. Za a rarraba zantukan na sarkanci kamar yadda makaɗin ya kawo a saka su
rukuni-rukuni kamar muhallin sarkanci, dabarun sarkanci kayan aikin sarkanci da
dai sauransu.
4.1 Muhallin Sarkanci
Sarkanci kamar yadda aka
bayyana baya kaɗan, sana’a ce da ta jiɓinci shiga ruwa domin a kama kifi. Kifi kuwa ba ya da wani muhalli da ya
wuce ruwa. Nan marayarsa take don haka a nan ake kambaɗarsa. Ruwa, marayar kifi
kan haɗa da na gulbi da tafki da ƙoramu da fadamu da madatsun ruwa. Yanzu bari a bibiyi waƙoƙin a ga yadda ya saka waɗannan muhallai na kifi a cikin waƙoƙinsa sannan a zaƙulo hikimar amfani da kowane muhalli da aka kawo.
4.1.1 Gulbi
Gulbi na nufin ƙaramin kogi. Ƙarancin kuwa ta fuskar yawan
tazarar wuraren da ruwansa ya ratsa ne. Tazarar da ruwan kogi ya ratsa ya fi na
gulbi tsayi sosai. Ƙoramu ne da rafuka ko gebe suke kwaso ruwa su zuba shi a gulbi. Gulbi kuwa
yakan malala ruwan da ya kwaso ne a cikin kogi. Wani lokaci idan aka yi mamakon
ruwan sama, gulbi kan cika da ruwa ta yadda ruwan kan rinjayi gaɓar gulbin don haka sai
ruwan ya malala a karkara musamman fadama. Irin wannan yanayi alheri ne sosai
ga masunta da ma manoma. Yanayi ne da yake wanzar da bazuwar kifi zuwa tafkuna
da nufin hayayyfa. A irin wannan yanayi ne ake samun kifi ya yi gala, wato ya
fito daga wani ruwa zuwa wani ko da kuwa zai biyo ta taɓo ne. Da haka sai
masunta su riƙa kama kifin a kan tudu, cikin sauƙi. Wannan yanayi wani
lokaci makaɗa Sa’idu yake ambato a wasu
waƙoƙinsa. A wani ɗa na waƙar da ya yi wa ubangidansa Sarkin Kudun Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo, Sa’idu yana cewa:
Gindin Waƙa: Ya yi Sarki daidai wa da mai yanzu yar riƙa,
Alhaji Macciɗo jikan Mamman mai
dubun bara
Jagora: Gulbi ya ba
da ruwa,
Hwadama dut ta shahe.
‘Y/Amshi: Masu hito
has sun hwara hwaɗin,
Yanzu
tai yi kai.
A nan Makaɗa Sa’idu ya kawo zancen
gulbi da yadda idan ya cika ya tumbatsa ruwansa yakan malala a cikin fadama. Irin wannan yanayi yana faranta wa masunta da
manoma shinkafa rayuwa domin irin tarin arzikin da za a iya samu ta fuskar
adadin kifin da za a iya kamawa, wani lokaci cikin sauƙi idan kifi ya yi gala; da kuma yadda shinkafa za ta sami wadataccen ruwa
har ya zuwa lokacin da ta isa yanka. Masu fito da jiragen ruwa za su sami aiki
na ƙetarar da mutane da kaya daga wannan tsallake zuwa wancan. Wannan a fakaice
yana nufin naɗa Muhammadu Macciɗo kan karagar Sarkin Kudun Sakkwato ya zama alheri ga al’umma ta hanyar
samar da buɗuwar arziki ga talakawa ta yadda aka sami wanzaruwar yalwa da wadata da buɗi na taskokin arziki ta
fuskar bunƙasar tattalin arziki da walwala ga jama’a.
Ba a wannan waƙa kaɗai Makaɗa Sa’idu ya kawo zancen gulbi ba. A waƙar Sarkin Ƙayan Maradun Tambari, akwai irin wannan daidai wani ɗan waƙa da ke cewa:
Gindin Waƙa: Wada kab bi da maza,
Na za ka gaishe ka da ƙwazo,
Bajimin Bello na Attahiru Sarkin riƙa taro.
Jagora: Gulbi ya ɓaɓɓako ruwa da yawa,
Ya taushe hwadammu,
Duk an ɗaure jirage,
‘Y/Amshi: Jama’a tsugunne ikon
Allah ɗai suka dibi,
Ba mai hwara shiga ciki, x2
Mai ƙarhi aka tsoro. x2
Makaɗa Sa’idu ya shigo da
lamarin sarkanci a cikin wannan waƙa ta fada, musamman yanayin muhallin kamun kifi domin ya kwatanta shi da
irin yadda idan sarauta ta faɗi ba kowane ɗan Sarki yake iya kutsawa wajen neman ta ba, sai mai ƙarfi da kuma muruwa. Ga sarauta ta faɗi amma magadanta sun yi jangwam kowa ya kasa kutsawa wajen nema domin
shakku da tsoro. Yadda ruwa yake da barkwanci, ko sarauta ta gaji hakan. Ruwa ko da mutum ya iya shi (iyo) to yana da haɗarin gaske domin irin
barkwancin da aka san yakan yi wa gwaninsa.[2] Dalilin irin barkwancin
da ruwa kan yi, Bahaushe a wata karin magana yake cewa:
‘Gwanin ruwa shi ruwa
kan ci’.
A wani ɗa na waƙar da Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu, ya kawo zancen ruwa
kamar haka:
Gindin waƙa: Toron giwa kana da martaba,
Usmanu na Bungudu,
Uban Marafan Keku,
Na Atto mai wuyak
karo.
Jagora: Kwaɗɗo na can na kiran
ruwa, x2
Ya tattake kiran su ɗai ya kai
An yi yayyahi waɗanga sun wuce, x2
Ya tattake kiran su ɗai ya kai, x2
An yi yayyahi waɗanga sun wuce,
Sai ga Allah ya
shirga ruwa
Gulbi ko ya ɓaɓɓako ruwa, x2
Sai ga kwaɗɗo tun da jijjihi, x2
‘’Y/Amshi: Wai za ya
biɗat tudun da yah haye
Jagora: Nic ce mashi
kwaɗɗo ina iyali?
‘Y/Amshi: Yac ce ƙyale ni Maikiɗi, x2
Tahi dan nan ba ni
son batun ba’a
A tunanin wannan muƙala, Makaɗa Sa’idu Faru ya kawo wannan zance ne
domin ya nuna yadda wasu ‘yangaladimomi masu adawa da Sarki kan yi fata har da
addu’a domin sarautar da suke jira ta faɗi. Sukan manta da cewa sau da yawa kwaɗo yakan kira ruwa sai ruwan ya ci shi kamar yadda makaɗa Sa’idu Faru ya fassara Karin maganar ta hanyar kawo
hoto cikin bayani. Ɗansarki ya yi fatar sarauta ta faɗi, hakan ya tabbata amma kuma ya kasance bai sami
sarautar ba. Sakamakon jayayya da gwagwarmayar neman sarauta da ya yi da sarki,
wato ya kasance abokin adawa da Sarki, tun bai sami sarauta ba, sai ya zare
jikinsa a gefe, ya zama ɗan kallo.
4.1.2 Kaya/Makaman Kamun Kifi
Kamun kifi galibi ana aiwatar da shi ne ta amfani da wasu
kayayyaki ko makamai domin samun nasara. Makaɗa Sa’idu Faru fasihi ne sosai kuma masanin
al’adun Hausawa. Duk da kasancewarsa ba masunci ko basarke ba, Sa’idu ya laƙanci harkar Sarkanci dalilin kasancewar
sana’ar tana gudana a
kusa da muhallin da ya rayu. Gulbin Sakkwato da ya ratso tsakiyar Zamfara, ya
bi ta Gusau ne da Bungudu da Maru da Maradun da Bakura sannan ya malala Gandi
da Raɓa a cikin jihar Saakkwato. Ba mamaki
Sa’idu ya fahinci harkar Sarkanci ne ta hanyar la’akari da yadda sana’ar take
gudana a waɗannan wurare da gulbin ya ratso wanda
ba wata tazara sosai da garin Faru. Daga cikin kayayyakin kamun kifi da Makaɗa Sa’idu Faru ya ambata a cikin waƙaƙinsa akwai taru da fatsa.
A cikin waƙar da ya yi wa Sarkin Kudun Sakkwato,
Alhaji Muhammadu Macciɗo, Makaɗa ya kawo maganar taru a wani ɗan waƙa da ke cewa:
Gindin Waƙa: Bajimin gidan Bello Mamman na Yari,
Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.
Jagora: Na Marafa Ɗanababa,
‘Y/Amshi: Mai tura
haushi, na Sarkin Gabas,
Duniya hori wawa.
Jagora: Babban dutci
a hange nesa, x2
‘Y/Amshi: A ishe ka soronka
ya tcarma kowa, x2
Da ɗai babu geben da yak
kai ga gulbi, x2
Ruwan Maliya sun wuce
masu taru. x2
Daga cikin kayan kamun
kifi na gargajiyar Bahaushe dala ce kaɗai ragar kamun kifi mafi girma da ta ɗara taru. Taru raga ce da ta sami sunanta daga irin yadda sai jama’a kama
daga huɗu zuwa biyar suke iya sarrafa ta domin kamun kifi, wato aiki ne na taro.
Duk da yawan da ragar taru take da shi da kuma haɗaka na jama’a wajen
amfani da ita a kama kifi, to ruwan maliya ya fi ƙarfin a yi sarkanci a ciki ta amfani da taru. A nan Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna
fifikon da gwarzonsa yake da shi idan aka kwatanta shi da
waninsa. Irin abin nan ne da Bahaushe yake cewa ‘bakin rijiya ba
wurin wasan makaho ba ne’, kuma gwarzon nasa tamkar itaciyar rimi ne kere
itace. Iyakacin masunta amfani da taru a gulbi amma ruwan teku kam (maliya) ya
fi ƙarfin masuntan taru.
Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda, Alhaji Abubakar Garba tana ɗauke da wani ɗan waƙa inda Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da wata kalma ɗaya daga cikin kayan
kamun kifi inda yake cewa:
Gindin Waƙa: Gwabron giwa na Shamaki baba uban Gandu,
Abu gogarman Magaji
mai kansakalin daga.
Jagora: Abu baban
Shamaki na Jekada,
Dangalin gabas na
Isau ɗan Mudi.
‘Y/Amshi: Ƙashi tahi giggilme ƙargage,
Hwarah hwatsa cin ki
sai ga mai ƙararrin kwana,
A ciki a kwan rirriƙan mutum za shi garin kewa.
Fatsa[3] da Makaɗa Sa’idu ya faɗa a wannan ɗan waƙa wata ƙugiya ce tilo da ake ɗaura wa wani dogon zare. Daga saman wurin da aka ɗaura ƙugiyar, kimanin taƙa biyu ko abin da ya fi haka, ana ɗaura abin da masunta suke kira karu[4] . Sauran zaren kuwa sai
a ɗaura shi jikin wata ‘yar sanda ko karan dawa mai ƙwari. Wannan kara ko sanda ne ake riƙawa yayin da ɗan fatsa ya saka fatsarsa
a ruwa domin kama kifi. Akan saka ƙoto na tana ko fara ko sabulu mai ƙanshi a jikin ƙugiyar domin jawo kifi. Kifin duk da ya kuskura ya ci ƙoto ko abincin da aka maƙala a fatsar sai ƙugiya ta kama shi. Karun da aka ɗaura zai nutse a ruwa. Hakan na nuna alamar fatsar ta yi kamu.. Irin wannan
kifin kuwa kwanansa sun ƙare domin ƙarshe a cikin tukunya zai ƙarasa.
A wannan ɗan waƙa, Makaɗa ya yi amfani da zancen fatsa domin ya nuna cewa gwarzonsa ba ya ɗaukar raini kuma duk
wanda ya faɗa masa ba daidai ba to kuwa zai wahala matuƙa, ya kasa samun sukuni; ya kasa zama ya kasa tsayi domin ya takalo abin da
ya fi ƙarfinsa. Wannan yana nuna in ba wanda ila ta faɗawa ba, ba wanda zai iya
ja da Sarki, sai kuwa wanda yake da rabon wahala.
4.1.3 Sunayen Kifaye
Allah a cikin ikonsa da buwayarsa ya albarkaci ƙasar Hausa da ni’mar koguna da gulabe da tafkuna da ƙoramu da fadamu masu ajiye ruwa. A
cikin ruwan, akwai nau’ukan kifaye daban-daban da suke rayuwa. A Bahaushiyar
al’ada, akwai azuzuwan kifi nau’i biyu. Akwai farin kifi da kuma baƙin kifi. Ana samun kowane daga cikin waɗannan nau’uka a ƙasar Hausa. Makaɗa da mawaƙan Hausa sukan saka sunayen kifaye
daban-daban a cikin waƙoƙinsu tun ma ba na fada ba. A waƙar Sarkin Banga, Alhaji Ahmadu, Makaɗa Sa’idu yana cewa:
Gindin Waƙa: Bai sake ba na Gardaye,
Ginshiƙin Sarkin Baura,
Hattara ba togewa,
Kamdaren Bunu ɗan Mamman.
Jagora: In dai ana
babbkag giwa,
‘Y/Amshi: Ba a jin ƙaurin gawo,
Jagora: In dai ana
yammatar goge,
‘Y/Amshi: Ba a jin daɗin molo.
Gawo wani nau’i ne na baƙin kifi da ake kira da sunaye daban-daban a ƙasar Hausa. A Hausar gabas, ana kiran sa da suna gaiwa. A Sakkwatanci kuwa
ana yi masa suna gawo. A ƙasar Argungu da ɗaukacin ƙasar Kabi suna kiran sa da suna boɗami. Kifi ne mai yawan juriya da idan ruwan da yake ciki ya ƙafe a lokacin rani, sai ya yi wata ‘yar sheka da zai zauna a cikin har sai
ruwan sama na damina mai zuwa ya sauka, sannan ya fita daga shekar ya koma
ruwa. A jikinsa ba ya da ƙaya sai dai wata jijiya da ta ratsa shi tun daga cikin wuyansa har zuwa
jelarsa. Rasin ƙaya a jikinsa ya sanya ba ya sukar mutum sai dai ya yi cizo da baki don
kuwa yana da wasu ‘yan haƙora sirara masu kaifin gaske. Galibi wasu suna tadar cin kifin domin an
camfa cewa cin jijiyarsa yana raunana ƙarfin al’aurar namiji. Akan babbaka shi domin a cire fatar jikinsa
wadda take da ɗan kaushi-kaushi gabanin a soya shi ko a yi bandar sa.
A wannan ɗan waƙa na sama, Makaɗa Sa’idu ya yi ƙoƙarin nuna ɗaukaka da girman da gwarzonsa yake da ita fiye da waninsa. Wato ya yi ƙoƙarin fassara karin maganar nan da take cewa ‘wurin bindiga
wane ƙyastu’? Wato ya nuna rinjaya da ɗaukaka da girma da Sarkinsa ya fi koma bayansa.
A wata waƙa ta daban, wato waƙar Sarkin Yaƙin Banga, Sale Abubakar, Makaɗa Sa’idu Faru ya kawo wani ɗan waƙa mai ɗauke da sunan wani kifi da yake rayuwa a cikin gulabe da tafkunan ƙasar Hausa. Ɗan waƙar na cewa:
Gindin Waƙa: Gwabron giwa uban Galadima,
Ɗan Sambo ginshimi,
Gansheƙa Amadu na Maigandi,
Kai a uban Zagi.
Jagora: Ko jiya na
iske gamdayaƙi da tuji,
Sun iske jinjimi,
To sun ko murɗa gardama,
Sun iske su bubuƙuwa ruwa.
‘Y/Amshi: Dan nan ni
ko ina gaton gaɓa,
Sai nik kwaɗa gaisuwa,
Su ko sun daƙile ni dud,
Ni ko niƙ ƙara gaisuwa,
Dan nan kulmen da
ac cikin gurbi,
Ya amsa gaisuwa.
Kulme da Makaɗa Sa’idu Faru ya faɗa a cikin wannan ɗan waƙa wani nau’i na kifi ne da ake kira tarwaɗa. Tarwaɗa kuwa tana cikin kifin
nan da Sarkawa kan saka cikin rukunin baƙin kifi. Idan tarwaɗa ta girma sosai, ana
kiran ta kulme. Wato kulme tarwaɗa ce da ta ƙosa ta girma sosai. Galibi tarwaɗa ta fi zama a gurbi mai zurfi musamman idan ta girma ta zama kulme. Kifi ne da yake da wasu gasu biyu a gefen bakinsa. A daidai kumatunsa kuwa, yana da wata ƙaya mai ƙwari wadda take taimaka masa wajen yin iyo a ruwa kuma da ita yake kare
kansa daga duk wata barazana domin ita yake soka wa duk abin da ya kai masa
farmaki. Yana da wata ƙaya mai ƙwari da ta ratsa ɗaukacin jikinsa tun daga wuyansa har zuwa jela. Ƙayar tana da wasu rassa da suka yi layi a duk faɗin jikin nasa. A bisa
al’ada, wasu Hausawa sukan yi tadar cin wannan kifi domin ɗaukar da suke yi cewa
yana haifar da ko ƙara haɓaka cutar zafi (kuturta).
Duk tsuntsayen da Makaɗa Sa’idu ya kawo a cikin
wannan da ma ɗan waƙa na gaba, ya kawo su ne domin ya jaddada karin magana da sauran maganganun
azanci kamar: ‘ko baba da babansa’ da ‘ko gaba da gabanta’. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi ƙoƙari ya nuna Sarkin da yake wasawa ya fi ƙarfin duk mai adawa da shi kuma ma duk ya haɗiye su kamar yadda bubuƙuwa ta gangame su duka ta laƙume.
4.1.4 Dabarun Kamun kifi
Kamun kifi ko sarkanci sana’a ce mai wahalar gaske sannan kuma tana tattare
da haɗura da dama na kamuwa da cutar sanyi da cizo ko sukar ƙayar kifi da dai sauransu. Wannan ne ya sanya akwai dabaru da dama da
sarkawa ko masunta sukan bi domin samun nasara a kan sana’ar. Wasu daga cikin irin waɗannan dabaru sukan sami ambato a cikin waƙoƙin fada. Makaɗa Sai’du Faru ya kawo ko ya ambaci wata dabara ta kama kifi a wani ɗan waƙa da ya yi wa Sarkin Yaƙin Banga Alhaji Sule inda yake cewa:
Gindin Waƙa: Gwabron giwa uban Galadima,
Ɗan Sambo ginshimi,
Ganshiƙa Amadu na Maigandi,
Kai a uban Zagi.
Jagora: Jan zakara ya
yi ƙiƙiriƙi, x2
Ya tsare garkag gidan
Ubanai, x2
‘Y/Amshi: Ya bak kwaɗɗo shina cikin rami,
x2
Ya lanƙwashe tsara.x2
Jagora: Ni,
‘Y/Amshi: Bana sai na
yi lalaben kwaɗɗo,
Na kai gaban wuta.
jagora: Kai ni bana
sai,
‘Y/Amshi: Sai na yi lalaben
kwaɗɗo na kai gaban wuta.
Lalube ɗaya ce daga cikin
dabarun kamun kifi. Akan shiga ruwa ne a yi kambaɗar kifi domin kama shi
da hannu kawai ba tare da raga ko tarko ba. Wani zai yi mamakin ai makaɗa kwaɗo ya ambata ba kifi ba.
Masunta sukan kama kwaɗi domin sayarwa ga ƙabilun da kwaɗo yake cimakarsu. Abokin adawar Sarki ne makaɗa ya kira kwaɗo domin ƙara ƙasƙanta shi, duba da cewa darajar kwaɗo ba ta kai ta kifi ba a tunanin Bahaushe. Da yake mazaunin kwaɗo a ruwa ne, to lalabo
shi za a yi domin saka shi a wuta kamar yadda ake yi wa kifi da sauran halittun
ruwa.
4.1.5 Sauran halittun
Ruwa
Baya ga halittar kifi
akwai wasu halittu daban-daban masu tarin yawa da Allah cikin ikonsa yake rayarwa
a cikin ruwa. Misalin waɗannan halittu ya haɗa da dabbobi kamar dorina da ayu da karen ruwa da kada da tsari da kunkuru
da tsuntsaye kamar bubuƙuwa da ƙirinjijiya da kazar ruwa da zalɓe da takau da sauransu. Wasu daga cikin waɗannan halittu na ruwa
sukan sami ambato a cikin waƙoƙin fada na Makaɗa Sa’idu Faru. Halittar ruwa kamar kada ta sami ambato sosai musamman idan
ana son a nuna haɗarin da yake ga ruwa sai a ce
akwai kada a cikinsa. Ruwa da kada kuwa yana da wuyar shiga. Irin wannan ne
makaɗan fada suke ambato a cikin waƙoƙinsu domin su nuna gwarzonsa ba banza yake ba, yana da wuyar a shige masa
ko a yi masa kutse cikin sauƙi. Makaɗa Sa’idu Faru ya ambaci halittar kada a wasu ɗiya na waƙoƙinsa kamar waƙarsa ta farko wadda ya yi Sarkin Yamman Faru Ibrahim inda yake cewa:
Gindin Waƙa: Bi da maza ɗan Joɗi na Rwafi,
Iro magajin Shehu da Bello.
Jagora: Ruwa da kada, x2
‘Y/Amshi: Ɗibgau na Magaji,x2
Sai tsohon wawa ka shigas su.
A wannan ɗan waƙa Makaɗa Sa’idu kwatanta Sarkinsa da ruwa wanda kada yake rayuwa a cikisan. Ruwa
da kada a ciki kuwa wawa ne kaɗai zai iya ratsa shi. Dalili kuwa shi ne
akwai haɗari mai yawan gaske, shiga ruwa irin wannan.
Waƙar Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo tana ɗauke da irin wannan
zance a mabambancin muhallin da ma’ana. Ɗan waƙar na cewa:
Gindin Waƙa: Kana shire baban ‘Yanruwa,
Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
Jagora: Gurbin giwa sai ɗanta,
‘Y/Amshi: Daudu zaman gurbi sai ɗan kada.
Jagora: Gurbin giwa sai ɗanta,
‘Y/Amshi: Zomo anka aza yab bag gidan.
A nan Makaɗa Sa’idu ya yi amfani da
kalma ɗaya mai dibilwa wadda a kowane bagire da aka saka ta tana da wata ma’ana ta
daban. Wannan kalma ita ce ‘gurbi’. A saɗara ta farko na ɗan waƙar, gurbi na nufin mazauni ko wurin da ake kwanciya. Haƙiƙa mazaunin giwa sai ɗanta kaɗai zai iya shigarsa ya zauna lami lafiya. A saɗara ta biyu kuwa kalmar
‘gurbi’ na nufin ƙasa ko ƙarshen zurfin ruwa. Zama ƙasan ruwa kuwa sai ɗan kada don su aka gadar wa haka. A nan Makaɗa Sa’idu Faru ya nuna
cewa Muhammadu Macciɗo kaɗai ya dace ya da shugabantar jama’a a duk sha’anin kamar siyasar zamani, da
kuma uwa uba, hawan halifar Sarkin Musulmi Abubakar na III domin shi babban ɗansa ne kuma ya gado
halaye da kyawawan ɗabi’un mahaifinsa.
Makaɗa Sa’idu Faru ya sake kawo sunayen wasu halittu na ruwa waɗanda suke ‘yan zuriya ɗaya ko ‘yan dangi duk da
cewa suna da ɗan bambanci kaɗan a wajen halittarsu. Wannan ya zo a cikin waƙar Sarkin Tudun Falale, Alhaji Muhammadu Ƙwazo. Ɗiyan waƙar na cewa:
Gindin Waƙa: Ya riƙa da gaskiya Muhammadun Muhammadu,
Dangalin gidan
Maisaje shirinka ya yi kyau.
Jagora: Da ihihiya da
kunkuru, x2
‘Y/Amshi: Shawara
guda sukai, x2
Jagora: Da bisshiya
da beguwa,
‘Y/Amshi: Shawara
guda sukai,
Jagora: Da kurciya da
hasbiya,
‘Y/Amshi: Shawara
guda sukai,
Jagora: Bubuƙuwa da jinjimi,
‘Y/Amshi: Shawara
guda sukai
Dub babu wanda yaz zo
haji, x2
Dub babu mai nihwaz
zuwa. x2
A saɗara ta farko, Makaɗa ya kawo halittun ihihiya
wadda wasu suka fi sani da suna ƙififiya da kuma kunkuru ‘yan zuri’a ɗaya ne don haka sun yi kama da juna. Halittu ne da suke da wata ƙunba a gadon bayansu wadda take mai ƙwari ce sosai. Hasali
sukan ɓuya ta saka kansu da ƙafafuwa a cikin ƙumbar yayin da suka fuskanci barazana daga wata halitta da ka iya cutar da
su. Dukkansu suna rayuwa ne a fadama inda ake samun wadatar ruwa. Bubuƙuwa da jinjimi tsuntsaye ne da suke rayuwa a bakin fadama. Sun yi kama da
juna sai bambancinsu shi ne bubuƙuwa tana da ƙaton baki, yayin da jinjimi ya yi kama da zalɓe.
Makaɗa Sa’idu ya siffanta
wasu ‘yan Sarki ne da waɗannan halittu domin ya yi masu bugun kaɗanya ta aibata su da
zambo cewa duk jirgi ɗaya ya kwaso su. Ba su taɓa aikata wani abin kirki ba kuma ba su da niyar aikata hakan ko da a wani
lokaci nan gaba.
5.0 Sakamakon Bincike
Wannan muƙala ta yi ƙoƙarin ƙara tabbatar da maganar da manyan masanan adabin Hausa suka yi cewa adabi
madubi ne na rayuwar al’umma (Ɗangambo,1982). Yunƙurin muƙalar na zaƙulo yadda Makaɗa Sa’idu Faru malamin waƙa, mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ya yi amfani da kalmomin fannu na sha’anin
sarkanci a cikin waƙoƙin fada ya daɗa gaskata waccan magamar. Haƙiƙa, makaɗin ya nuna bajintarsa da ƙwarewarsa ga harshen Hausa inda ya zaƙulo kalmomin fannu na
sha’anin Sarkanci ya kuma yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa na fada. Abu ne tabbatacce cewa Sarakuna da ‘ya’yansu sha’anin mulki da
tafiyar da shi suka gada, don haka sha’anin Sarkanci da aiwatar da shi bai
shafe su ba kai tsaye, abu ne da ya rataya a wuyan talakawa. Duk haka aka tarar
da cewa waƙoƙin da ake yi wa jama’ar fada suna ɗanfare da kalmomin Sarkanci a cikinsu. Dalilan da ke sa makaɗan fada saka lamarin
sarkanci a waƙoƙinsa ya haɗa da yi wa abokan adawar Sarki zambo da aibata su da sana’ar da ba ta
kamace su ba. Ana daɗa nuna yadda kwaɗo kan kira ruwa amma
kuma a ƙare ta ruwan ya ci shi. Hakan yakan kasance ne yayin da ɗangaladima zai yi ta
fatan sarautar gidansu ta faɗi amma idan hakan ta tabbata sai ya kasa kai ga gaci na cikar burinsa na
zama Sarki. Makaɗan fada suna amfani da muhallin sarkanci wato ruwa da irin mugayen halittun
da ake samu a ruwan domin su nuna gwarzonsa tsayayye ne ko kaɗan ba abin rainawa ba ne
da za a iya a faɗa masa kai tsaye, yin haka kuwa sai wawa ko tsohon mahaukaci. Makaɗan sukan kuma kwatanta
cancantar gadon sarauta da wani gurbi mawuyaci da sai ɗan sarki wanda yake kusa
ga magabata ko iyaye zai iya hawa kan wannan karagar.
6.0 Kammalawa
Makaɗa Sa’idu Faru kusan ana
iya cewa shi ne makaɗi tilo da mafi rinjayen waƙoƙinsa na fada ne. A kan haka, malamin waƙa mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba ya ciri tuta a tsakanin makaɗa da mawaƙan Hausa domin kacokam waƙoƙinsa na fada ne. Makaɗi ne da Allah ya yi wa basira da fasaha da zalaƙa ta shirya waƙa da rera ta ta tafi daidai kai ka ce karantawa yake yi. A fagen sani da ƙwarewa haɗe da amfani da harshen Hausa, Sa’idu ba kanwar lasa ba ne. Wannan ne ya ba
shi damar amfani da kalmomin fannu na sarkanci a cikin waƙoƙinsa na fada kai ka ce Sa’idu masunci ne. Kamar yadda aka gani a cikin wannan muƙala, amfani da kalmomin fannu na sarkanci a cikin waƙoƙin abu ne da ya ƙara wa waƙoƙin armashi da ma’ana sosai. Ganin yanzu yadda zamananci da kayan kaɗe-kaɗe da yanayin waƙa irin na Turai ya yi kutse har yake yi wa waƙoƙin Hausa na gargajiya barazana, ya dace matuƙa a taskace waɗannan waƙoƙi na Sa’idu Faru da ma wasu makamantan nasa domin kare su daga
salwanta. Yin haka ba ƙaramar kariya ba ce ga al’adu da kuma harshen Hausa. Ya dace ya kasance a manyan
makarantu da ake nazartar ilimin harshen Hausa a bijiro da kwasakwasai masu cin
gashin kansu a kan Sa’idu Faru da sauran taƙwarorinsa ba wai kawai a dunƙule ba a kwas ɗaya a wajen nazari a aji. Yin haka zai ƙara farfaɗo mana tare da isar da nagartaccen ilimin harshen Hausa, musamman adabinsa
da al’adunsa ga ɗalibai ta yadda za su ƙara alfari da tinƙaho da Harshen. Ba wannan kaɗai ba, haƙiƙa ɗaliban za su iya koyon kimiyya da falsafa da ilmin zamantakewa da naƙaltar mulki da dai fannonin ilmi da dama duk a cikin waƙoƙin.
Manazarta
Abubakar, A.T. (2015) Ƙamusun
Harshen Hausa. Zaria: Northern Nigeria
Publishing Company Ltd.
Alkali, M.B. 1969 “A Hausa
Community in Crisis: Kebbi in the Nineteenth Century.” M.A. Thesis. Zaria: Ahmadu Bello University.
Bargery, G.P. (1993) A
Hausa-English Dictionary and English- Hausa Vocabulary (2nd Ed.). Zaria: Ahmad Bello
University Press.
Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash
Islamic Publication Centre Ltd.
CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Fadama, M.G. (2015) Sarkanci A Gundumar
Sakkwato. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsunan Nijeriya. Sokoto:, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo University.
Fadama,
M.G. (2016) Tsarin Shugabanci A Sana’ar Sarkanci. In Malumfashi, I. A. M., Yakasai,
S. A., Abdullahi, I. S. S. (eds) The
Hausa People, Language and History. Past, Present, and
Future. Pp.435-448
ISBN: 978-978-956-169-8.
Gusau, S. M.
( ) Waƙoƙin Makaɗan Fada:
Sigoginsu Da Yanayinsu Musamman A Ƙasar Sakkwato. Kundin Digiri Na Uku.
Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Gusau,
S.M. (1996) Makaɗa Da Mawaƙan Hausa. Kaduna:
Fisbas
Media Services.
Gusau, S.M., (2003) Jagoran
Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark
Publishers Ltd.
Gusau, S.M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni Na Waƙoƙin Baka Na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Company.
Yahya,
A.B. (1997) Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.
[1] Alhaji Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin
Magaji ya kawo wannan ƙauli a sakamakon hira da ya yi da iyalan makaɗa Sa’idu
Faru. Ya saka zancen a wata tattaunawa a dandalin watsup da aka buɗa domin
musayar ra’ayi game da wannan taro da aka shirya kan Makaɗa Sa’idu Faru. Ya
saka bayanin a ranar 9/02/2024.
[2] Dubi abin da makaɗa Ibrahim Narambɗa yake
cewa game da gulbi:
Gindin Waƙa: Ya ɗau girma ya ɗau yabo,
Mu za mu ga Alƙali Abu.
Jagora: Kul ka
ishe gulbi ya cike,
In
ba kowa ka iya,
‘Y/Amshi: Koma ka tsaya ganga ka kwan
[3]
Fatsa
kayan kamun kifi ce da ke yi da ƙugiya. Ita kuwa ƙugiya, Hausawa na amfani da
ita domin kama kifi tun gabanin su shaƙu da wata al’umma daga ƙetare. Hasali ma
maƙera baƙi masu ƙera kayan ayyukan noma suke ƙera ta da baƙin ƙarfe. Wannan ta
yanzu mai launi mai haske ko fari irin na silba, wadda kamfani yake samarwa
daga waje ta shigo ne daga baya. A da can, wadda fasahar maƙeranmu suke samarwa
ake amfani da ita.
[4] Karu wani soso ne ko kara ko duk abu marar nauyi da
masunta suke da ɗaura wa wasu kayan haƙo na kamun kifi domin dalilai biyu. Na
farko ana saka shi ne domin ya hana ƙugiya ko raga sauka ƙasan ruwa. Haka kuma
idan ƙugiya irin ta fatsa ta kama kifi to karu ne yake ba da labarin haka domin
shi yake nutsewa a ruwa ko riƙa motsi yayin da kifin yake fisge-fisgen kuɓuta
daga tarkon.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.