𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu. Naga amsar da ka bayar. Ni ba a sake ni ba, amma ina zaune ne don ba yadda zan yi saboda Ya'ya. Idan sun ci nice, in sun Sha nice, duk wani takalifin rayuwarsu nice. Bala, insa da sharri bai barmu ba. Zalinci ko ban taɓa ganin wanda ya kai shi ba. Aiyuka biyar nake yi in na tashi daga wannan in tafi wanna don in ɗauki nauyin kaina da ya'yana. Na tsane shi, na yi alkawarin ko yau ya mutu sai na yi sallah raka'a 100 na gode Allah. A ba ni shawara. Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam Wa Rahmatullah wa Barakatuhu:-
Subhanallah Subhanallah Subhanallah. Shi Aure
Ibada Ne, Kuma Aure Ni'ima Ne, Aure Tufafin 'Ya Mace ne, Aure Alkhairi Ne ga Ɗan Adam, Sai dai ace
Fitina ta Shigo Cikin sa. Sabida Allah bai taɓa Umarni akan abin da ba Alkhairi bane.
Ta dalilin Aure ne Ake Samun Aljannah idan an yi Abin
da ya dace a cikin wannan zamantakewar Auren. Ta dalilin Aure ne Ake Samun
Mutane daban-daban Nagari. Wani Mai dinbin Ilimi, Wani Mai Tsantsar Tsoron
Allah, Wani Shugaban Al'umma, Wani ya Zama Jagoran Al'umma, wani ya zama Mai
Ilimantar da Al'umma, wani ya Zama jami'in Tsaron Al'umma kuma ya bayar da
Lafiya ga Wannan Al'ummar, wani ya Zama Likita da zai rika Baiwa Al'umma gudumuwa
ta Fuskar Lafiyar su, wani ya Zama Silar Shiriyar Wani da ya kangare daga
hanyar Allah, wani ya Zama Mai Ɗaukar Nauyin Wani, Wanda kuma Kowanne a Cikin su ɗin nan da na Lissafo, Masu Taimakon Al'umma ne.
Kuma duk Uwar da Uban da suka Samar da ɗaya daga cikin waɗannan Mutanen da
na Lissafo, za su yi Farin Ciki. Kuma za su sami lada mai Tarin yawa. Asali ma
Sadaka Ce Mai Gudana, ace an Samar da Mutum Na Gari wanda Al'umma za su amfana
da Shi.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce:
MAFI ALKHAIRIN MUTANE, SHINE WANDA AL'UMMA SUKA FI AMFANAR SA.
Ta dalilin Aure ne ake Samun Dangantaka, Tsakanin
Dangin wane da Dangin Wacce. A Sami Dinkewar juna. A yaɗa Zuri'a, a yi Zumunci. Ta dalilin Aure ne ake Samun
Taimakakkeniya ta dangi. Wanda idan wani Abu ya fada Wani hali na kangin Rayuwa
ko Rashin Lafiya. Sai yan uwan sa su zo su Fitar da shi Kunya. Su ɗauki Nauyin Jinyar sa. Su Zauna masa zaman jinya har sai
ya Warke.
Sabida haka ne ake Kallon Mutumin da yake da Aure
a Matsayin wani Abu da yake da Daraja da Kuma kima a Idon Al'umma. Saɓanin Wanda ba shi da Aure. Sabida haka kenan waɗannan dalilan suna daga Abin da ake Kallo a Kan Abin da
zai Zaunar da Mace a gidan Mijin ta. Musamman ma idan an sami Hayayyafa da
Juna.
Kowacce Mace, tana Son ta ga Mijin ta ya Zama
Nagartaccen Mutum, Mai Addini, mai Lafiyayyan Hankali da lafiyayyen Tunani, mai
sanin darajar Matar sa da yayan da ya Haifa, mai Fita Hakkin Aure, mai Mutunci,
Mai Sanin darajar Mutane.
Haka Zalika Shima Miji, yana son ya ga Ya Sami
Mace mai irin waɗannan Dabi'a da
ta dace da Musulunci. Sai dai Kuma, Akwai Jarrabawa a Rayuwa. Sabida haka, kar
Muke Mantawa da waɗancan Alkhairan
da Aure ya ke janyowa. Muna Kallon Sharrin da Muke Fuskan ta a Cikin sa.
Kowanne Mutum da irin Jarrabawar sa.
Shiyasa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya
ce: KADA ƊAYANKU YAYI
FATAN ACE DA MA YA MUTU YA HUTA, SABIDA WATA MUSIFA DA TA SAME SHI, KO SABIDA
WATA JARRABAWA DA AKA SAUKAR MASA. SAI DAI YA CE, YA ALLAH KA KARƁI RAYUWA TA IDAN MUTUWA
TA CE TA FI ZAMA ALKAIRI, YA ALLAH KA RAYA NI, IDAN RAYUWA TA CE TA FI ZAMA
ALKHAIRI.
Sabida haka kenan, ba za ki ce kina zaman 'Yayan
ki ba. Zaman Aure kike yi. Domin a yau ɗin nan idan
mijin ki ya bar duniya, dole za ki yi masa Takaba. Yayan ki kuma sun zama
marayu.
Sabida haka kenan, wannan Rayuwar da kika zaɓarwa Kanki, ba ta dace da Koyarwar Musulunci ba. Ma'ana
kina jiran Mijin ki ya Mutu ki yi Murna. Ba Mamaki sai ke za ki Riga shi
Mutuwa. Duk da ma wannan shine tunanin Kusan Akasarin Matan da Muke Aure. Na
cewar Mijin su Shine zai Riga su Mutuwa. Kaɗan ne ba su da irin wannan Tunanin.
Wanda kuma a yau ɗin nan idan ya Mutu. Za ki gane Cewar yana da daraja a
Wajen ki. Tunanin Mazajen su za su Riga su Mutuwa ne Ma Yasa Wasu Matan Suke
Lissafin Gadon da zai Mutu ya bar Musu. Idan ya Mutu yayan ki za su zama
marayu. Kema kuma za ki Shiga wani hali. Duk da wannan abin da kike faɗi.
Abin da ya Kamata shine. Kina yi masa Addu'a ta
Alkhairi, da kuma Addu'a ta Shiriya. Kina Haɗawa da Yi masa Nasiha a koda yaushe. Mijin ki ne, a yau
idan ya zama Na Gari, Sai kin fi kowa Murna. Kina yin Haka Wallahi Lokaci ɗaya sai ki ga Allah ya gyara miki kayan ki. Sai ki ga ya
dawo yana kawo wa yaran ki Abinci wanda Kema za ki ci, har ki bayar, Sannan
kuma sai ki ga ya dawo ya Nemi Ya fiyar ki kun ci gaba da Zaman Auren ku yadda
kike so. Sabida Mun ga Irin Wannan da yawa.
Akwai Wanda Na Sani, Kullum sai ya sha Giya yake
Shigowa Gidan sa. Kuma su cikin dare zai Shigo. Ya yiwa Matar sa Fitsari a
Kwance, yayi mata Amai, da safe ta ba shi Wasu kayan ya sa, waɗancan Kuma ta Wanke Su. Sabida suna da yara. Amma da ta
dage da Addu'a da Nasiha. Wanda a baya ma da har tana ganin ma ta gaji da yi
masa Nasihar. Amma Allah ya Shirya Mata Shi. A yanzu tafi kowa jin dadin sa.
Wanda da ta ɗauki wani mataki da
yanzu Sunan Yayan ta ya ɓaci. Sai a wayi
Gari ma ba Wanda zai auri yayan sa. Amma da ta yi Hakuri sai Allah ya kawo mata
Mafita da ita da shi da kuma yayan sa.
Amma cewar idan ya Mutu, za ki yi Farin ciki, har
da Salloli da Nuna Godiya ga Allah. Wannan ba Daidai bane. Da ace a yanzu zai
fadi ya Mutu. Wallahi sai kin yi da na sanin wannan Maganar da kika fadi. Domin
ba Zaki Iya yin Nafilar ba. Idan kuma Mijin ki ya Mutu aka wayi Gari Kike yiwa Allah
godiya a gaban gawar sa. Sai mu ce gaskiya ba ki da Imani.
A karshe dai Shawara guda biyu zan baki. Wanda
Wannan Su kaɗai ne Mafita a gare ki.
1. Ko dai ya sake ki. Sai Ki tafi ki bar masa
Yayan sa. Domin Shine yake da Hakkin Rike Su Ba ke ba, Allah zai Raya Miki Su.
Kin ga kin sami damar da za ki je kiyi Auren ki. Ba Mamaki Allah ya Chanja Miki
Mafi Alkhairi.
2. Ko kuma Ki yi Hakuri ki ɗauki wannan rayuwar taki akan Jarrabawar da Allah ya
Saukar Miki a Rayuwar ki. Domin Wasu sun fiqi Shiga Irin wannan damuwar. Sannan
Kuma ki ci gaba da yin Addu'ar Allah ya Shirya Muku Shi ke da 'yayan ki. Allah
ya san halin da kike ke Lada ma kike samu sosai matukar kina yin komai da
zuciya ɗaya ne toh Lada Allah zai Kara nimka miki da Kara daga
Darajar ki.
3. Ko Kuma idan zai yiwu, ki kai kukan ki wajen
Alwalan sa da Alwalan ki wato Waliyyin ki da Waliyyin Sa, ku Zauna ku Tattauna
a Sami Bakin Zaren, a Binciko inda matsalar take. Sai ku ga hanyar da za ku bi
ku gyara. Ba Mamaki Allah ya kawo Muku Mafita.
Amma idan har Irin wannan zaman kike yi, toh ba ki
da Ladan Aure gaskiya. Sabida ke a Tunanin ki ma ba zaman Aure kike yi ba.
Zaman yadda za ki Tallafi Rayuwar Yaran ki kike yi. Wanda kuma wannan Al'amarin
na yadda Rayuwar yaran ki zata kasance, Ba a Hannun ki take ba, A Hannun Allah
take. Rayuwar ki ta Kanki ma, a Hannun Allah take ba a Hannun ki ba. Bare kuma
Rayuwar yaran ki. Sabida haka a Chanja Tsari a Koma Rayuwa Irin ta Aure. Sai ki
ji daɗin zamantakewar Auren ki kamar yadda shima zai ji daɗin Auren sa.
Allah Shine Masani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.