HUKUNCIN MA’AURATA SU RIƘA FAƊIN SIRRINSU A CIKIN GROUP (SOCIAL MEDIA):
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mene ne hukuncin ma’aurata su riƙa faɗin sirrinsu a cikin group na social media?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh;
Ƙullin aure a Musulunci ƙulli ne mai ƙarfi ƙwarai da gaske,
kamar yadda Allaah ya faɗa:
وَكَیۡفَ تَأۡخُذُونَهُۥ وَقَدۡ أَفۡضَىٰ بَعۡضُكُمۡ إِلَىٰ
بَعۡضࣲ وَأَخَذۡنَ مِنكُم مِّیثَـٰقًا غَلِیظࣰا
Kuma ta yaya za ku karɓe shi (watau sadakin da kuka ba wa matan ku), alhali kuwa
sashen ku ya sadu da sashe, kuma sun riƙi alƙawari mai ƙarfi daga wurin ku.
(Surah An-Nisaa’: 21)
Kamar kuma yadda ya ambaci irin wannan alƙawarin game da manyan
Annabawan sa: Ulul-Azmi Minar Rusul:
وَإِذۡ أَخَذۡنَا مِنَ ٱلنَّبِیِّـۧنَ مِیثَـٰقَهُمۡ وَمِنكَ
وَمِن نُّوحࣲ وَإِبۡرَ ٰهِیمَ وَمُوسَىٰ وَعِیسَى
ٱبۡنِ مَرۡیَمَۖ وَأَخَذۡنَا مِنۡهُم مِّیثَـٰقًا غَلِیظࣰا
Kuma ka tuna lokacin da muka riƙi alƙawarin Annabawa, kuma
daga gare ka, kuma daga Nuuh da Ibrahim da Musa da Isaa Bn Maryam, kuma mun riƙi alƙawari mai ƙarfi daga gare su.
(Surah Al-Ahzaab: 7).
Bayan an ɗaura aure a
tsakanin ma’aurata kamata ya yi su zama abu guda, masoya kuma mataimaka juna.
Kuma bai kamata su bari a riƙa jin tsakanin su ba.
Hanyoyin warware matsalolin da kan taso lokaci
bayan lokaci a tsakanin ma’aurata sanannu ne a cikin Al-Kitaab Was Sunnah a
wurin malamai.
Daga cikin hanyoyin korewa da maganin matsalolin a
dunƙule kuma a taƙaice akwai:
1. Su riƙa yin maganganu da ayyukan junan su kyakkyawar fassara, tare da neman
fassara da ƙarin bayani a
kan duk abin da ya shige musu duhu na wannan ɗin.
2. Su riƙa zama suna tattauna matsalolin su da ya shafe su ko ya shafi ɗayan su, maimakon fitar da matsalar zuwa waje.
3. Su mayar da matsalar da suka kasa warwarewa ga
malami ko limamin unguwar su ko wanda ya ɗaura musu auren,
shi ya fi da su kai maganar ga iyayen su.
Domin malami yana da ƙarin masaniya game da Ayoyi da Hadisai da
maganganun malamai a bayan gogewa a kan al’amuran rayuwa da zamantakewar jama’a na zamanin baya da wannan zamani.
Yawanci idan matsalar ma’aurata ta kai ga iyayen
su, sukan samu damuwa da tashin hankali sosai, kuma sukan daɗe ba su manta ba ko da kuwa su ma’auratan sun daɗe da yin sulhu a tsakanin su.
Abu ne sananne cewa: Shafukan tashoshin sada
zumunta da na’urorin wayoyin tafi-da-gidan ka ba wurare ne na sakin bayani ko
ajiyewa balle ma adanawa ko ɓoye sirri ba.
Shi kuwa Musulmi yawancin al’amuran sa duk suna buƙatar sirri, don tsare mutuncin sa da martabar sa.
Amma duk wanda ya shigar da wani rubutu ko wata
magana ko hoto a cikin irin waɗannan shafukan
na sada zumunta ko wayoyin hannu, toh kuwa suna nan har abada kuma ko kusa ba ɓoyayyu ba ne.
Don haka, bawai ’ya’ya da jikokin ma’auratan da
suka saka maganar ba, har tattaɓa-kunnen su ma
za su zo su ga wannan abin, matuƙar dai sun yi bincike a kan wannan shafin.
Don haka, dai wajibi ne mutane su san irin abin da
za su saka a cikin kowane irin group na social media, domin ko ba komai akwai
tambayoyi da za su biyo baya a kan hakan a gaban Ubangijin Halittu a ranar
Lahira.
Abun bakin Ciki ka ga Matar Aure ce ta zauna a
cikin group na koyar da styles na Jima'i ko wani group daban ta rika bayyana
Sirrin Mijin ta duk Kalan Kwanciyar da yake yi da ita da Yawan daɗewa ko rashin daɗewa da baya yi
duk sai tayiwa Yan group ɗin bayanin wai
ga halin da take ciki Mijin ta baya gamsar da ita ko Bukatar ta baya biya, daga
lokacin da na Furta hakan shikenan Yan Lesbian ko Yan Zina su ki bi ta private
suna miki magana ana tura miki video na Batsa da hotunan Batsa ace miki ko nawa
kike so za su ba ki kawai ki zo kuyi Madigo ko Zina ki koma.
Wannan shi ne rayuwar Matan Aure ko zaurawa suke
fama Matan Aure dayawa ana Madigo da su dalilin wannan, matan Aure dayawa ana
Zina da su domin sun bayyana Sirrin Mijin su kuma sun ji an ce musu za a gamsar
da su yadda suke so sa'annan ga kuɗi har da motar
shiga, Idan ke da malamin Addini ne a group naku kina iya Yi masa Bayanin komai
za ki ba ki shawara sosai yadda zai taimake ki ba tare da kowa ya ga Sirrin ki
ko na Mijin ki ba, amma ki zauna a group wai kin kusan yin Aure wanne irin
style za a koya miki wadda za ki yiwa Namiji don kada ki ji Kunya a Daren ki na
farko, wannan Kuskure ne kuma Jahilci ne wannan domin babu inda Addinin ki ya
ce ki je ki shiga group a Koya miki style.
Sabida haka Hakan Matan Aure da Yan Mata wallahi
ku ji tsoron Allah, ba wayewa bane wannan, kowa zai je ya amsa tambaya a ranar
Alqimaya ko ba ki so wallahi Allah ya shirya ya tsare. Allaah ya shiryar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.