𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Ailaikum warahmatullah
Malam ina da tambaya. Ina cikin tashin hankali mamana ba ta kula da addini Sam. 1. ba ta rama Azumi na ramadan idan Tasha Azumi haka har wani Azumi zaizo ba ta rama bah yanzu haka lissafi nake A yanzu haka yaka yi 50 Wanda Ake binta. 2. ya sheikh tana wasa da sallah sosai idan ta yi asuba da wuya ta yi sauran. 3. malam ana binta bashi kusan miliyan 1 yanzu haka Wanda take kan ramawa. duk da yawan bashin ake binta baya hana ta ɗauka wani bashin. 4. na karshe malam na yi duk wani hanya dan naga ta daina amma yagagara Akan wannan halin nata, na zauna da mahaifina Akanta munyi magana Shima ya ce min yayi yaga ta chanza Amma ina yakasa Malam ina bukatan shawaran ataimakamin nagode Allah yakara hazaka da illimi Ameeen yarabbi🙏 Allah yabada ikon Amsawa Ameeen
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatullah wa Barakatuhu:-
Allah kenan Idan ya so sai ya jarrabi Mutum da
Yayan sa, wani kuma da matar sa, wani kuma da Mahaifiyar sa, wani kuma da Ɗan sa. Wanda duk Waɗannan Sune Babbar Jarrabawa da Allah yake yiwa bawan sa,
Sabida babu yadda za a yi da Al'amarin. Yaya za ka yi da Mahaifiyar ka? Yaya
zaka yi da Ɗan ka? Yaya za
ka yi da Matar ka idan kuna da Manyan yara Irin ka.?
Sai dai Kawai kai da Mahaifin ka tunda Kun yi kun
kasa, toh Kuna yi mata Addu'a. Domin Allah ya jarrabe ku da ita akan Ibadar da
ba ta yi, wannan Tsakanin ta ne da Allah.
Domin ba zai yiwu ku rama mata Azumin ba, haka
Zalika ba zaku rama mata Sallolin da ba ta yi ba, Alhalin tana Raye. Ko ta
Mutu, ta ki ta yi Azumi da gangan. Babu wani Maganar Ramuwa da wani Zai yi
Mata, Sai dai kawai Kuna Nema mata gafarar Allah.
Bashi Kuma idan ta ci, Kar ku Biya mata, Ku bar ta
idan Aka yi mata Hukuncin da Shari'a ta Tanadar, sai ta dena. Daman dai Shari'a
ta Tanadi Yiwa Mutum Hukunci ne dan ya Kiyaye.
A baya can wata mata ta yi min waya, Cewar sai
Mahaifiyar ta, ta yiwa Mijin ta waya, Wai ya kawo Mata Kuɗi Kamar dubu ɗari. Wanda ko a
irin wannan lokacin da ta ke yi masa waya ya kawo Mata wannan Kuɗin, shi kansa ba shi da kuɗin da ya kai dubu biyu ma. Amma a haka zai ci bashin ya
kawo mata. Tana ta zubar mata da Mutunci a wajen Mijin ta, da sauran Al'umma.
Sa'annan a haka zata ci bashin Mutane na kuɗi da yawa, Kamar dubu ɗari biyar, dubu ɗari Bakwai. Ita
da Mijin ta suna Biya mata Gudun kar a wulakan ta Mahaifiyar ta.
Amma wannan ba zai sa ta dena ba. Sai daɗa cin bashin ma take yi. Idan an Biya wannan sai ta ci
wani. A haka na ce ta yi Hakuri, ta bari idan ta ci kayan Mutane. An kulle ta a
wajen Hukuma ta dena ci.
Sabida su Kansu ta talautar da Ɗiyar ta, Ta talautar da
Mijin ta. Kai wallahi Wasu Mutanen ma ba su san abin da ya kamata ba. Sabida
haka ku ci gaba da yi mata Nasiha. Idan ba zata dena ba. Sai ku Fita harkar ta.
Hukuncin da ya dace shi za a yi mata.
Allah ya ce a kyautatawa iyaye. Amma kai a yanzu
babu yadda za ka yi da wannan Mahaifiyar ta ka. Sai dai Kuma Nasiha da Addu'a.
Amma idan Kun waɗanda idan sun gaya mata magana tana Jin maganar su toh ku
je gaban su kuyi musu bayanin komai idan ma ba a gari suke ba ku biya musu
ku6din abun Hawa su zo har inda ta ke domin yi mata Nasiha da Wa'azi a sa ta
hanyar In Sha Allah idan an yi haka ganin girman waɗannan waɗanda ta ke Jin
maganar su zata dena ibadar ma za ta Koma yin sa yadda ake so. idan kuma babu
toh sai dai Addu'a domin babu abun da ya gagari Allah. Allah ya tsare ya shirye
ta Ameen.
Allah shine Masani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.