Ticker

6/recent/ticker-posts

Turancin Direba Sai Fasinja: Nazarin Karin Magana a Bakin Makada Sa’idu Faru

Citation: Sarkin Gulbi, A. & Abdullahi, M. (2024). Turancin Direba Sai Fasinja: Nazarin Karin Magana a Bakin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 50-55. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.006.

TURANCIN DIREBA SAI FASINJA: NAZARIN KARIN MAGANA A BAKIN MAKAƊA SA’IDU FARU

Daga

Dr. Abdullahi Sarkin Gulbi
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Kibɗau: gulbi.abdullahi@udusok.edu.ng 

Da

Musa Abdullahi
Sashen Harsuna da Al’adu,
Jami’ar Tarayya Gusau
abdullahiji707@gmail.com  
0803776541

Tsakure

Karin Magana wani babban jigo ne daga cikin rassan adabin bakan Bahaushe tun gabanin ya sadu da baƙin al’ummu a duniya. Hakan ya sa ake samun tsarmin sa cikin magangannu yau da kullum a tsakanin mutane har ma a cikin waƙoƙinsu. Dangane da haka, sanin waƙa sai ɗaliban nazari, domin kuwa, su ne ke da alhakin shiga waƙa don su tono wasu asiran da ke cikinta. A dalilin hakan ne ya sa wannan nazari ya ƙudurci shiga wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru domin ya lalubo irin yadda yake tsarma karin magana a cikin ɗiyan waƙoƙinsa., inda za a ga irin yadda yake kawo karin maganar kai tsaye ba tare ya canza shi ba, ko ya yi luguden karin maganar, ko ya rage maganar, ko ya ƙirƙiro karin maganar ko kuma ya yi takin saƙa da yadda ma’ana da tsarin amfani da karin maganar take. Domin cimma nasarar hakan an yi amfani da dabarar sauraren wasu daga cikin waƙoƙinsa da himmar taskace kutsen karin magana a waƙoƙin, a ƙarshe ana hasasshen takardar ta gano gurbin karin magana wajen isar da saƙon a tafashen makaɗa Sa’idu Faru

Fitillun Kalmomi: Nazari, Karin Magana, Makaɗa, Saidu Faru

1.0  Gabatarwa

Wannan muƙala an gina ta ne da ƙudurin lalubo irin yadda Sa’idu Faru yake cusa karin magana a wasu daga cikin fitattun waƙoƙinsa. Tsarma karin magana a cikin waƙoƙin baka ko rubutattu ba sabon abu ba ne, sai dai duk da haka, manazarta da masana ba su cika bai irin wannan salon isar da saƙo muhimmanci ba. Hakan ya sa takardar ta himmatu wajen shiga wasu daga cikin waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru domin a ga yadda yake saƙala karin magana a cikin ɗiyan waƙoƙinsa. Takarda ta yi amanna da cewa da za a cire kason da karin magana ya mamaye a cikin wasu waƙoƙinsa, da waƙoƙin ba su sami isar da saƙon da aka gina su ba.

2.0 Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru

An haifi makaɗa Sa’idu Faru a garin Faru ta cikin ƙasar Maradun a shekarar 1932. Sunan mahaifin Sa’idu Faru shi ne makaɗa Abubakar ɗan Abdu, shi kuwa Abdu makaɗa , Alu mai Kurya ya haife shi. Dangane da haka za a yanke hukunci a kan cewa babu tababa ya gadi kiɗa ne ga mahaifinsa da Kakansa Alu mai kuryar yaƙi.

Dangane da kurciyarsa da iliminsa, sai a ce a farko ya tashi ne a gidan Kakarsa ta wajen uwa da ke garin Banga ta Kaurar Namoda, daga bisani ya dawo gidan mahaifinsa Makaɗa Abubakar, kuma bai yi zurfi a karatun addini ba, bai kuma shiga makarantar boko ba, sai duk da haka Allah ya yi masa fikira a fagen shirya waƙa. A fahimtata Makaɗa Sa’idu Faru ya gadi amfani da karin magana tun a cikin waƙar mahaifinsa ta “Sarkin Yaƙin Banga wadda makaɗa Abubakar ya yi masa, in da yake cewa”

Jagora: Gogarman Nassarawa mai gari,

: Bunƙasa burje gume sai sarki.

‘Y/Amashi: Sa maza jin tsoro gogarman Nassarawa,

: Mai gari bunƙasa burje gume sai sarki.

: Karfin hali haɗewar sheɗa,

: Shaƙo kukan bebe,

: Yaro bai saba, wani na kukan mata

Naƙaltar waƙa ga Sa’idu Faru ba abin mamaki ba ne domin tun yana ɗan shekara goma (10) yake biyar mahaifinsa yawon waƙa gari-gari, bayan ya shekara goma sha shida (16), sai ya fara kar~in waƙa tare da ƙanensa Mu’azu[1].

3.0 Karin Magana a Tafashen Sa’idu Faru

A nan nazarin zai ja mu ga sanin ma’anar karin magana da wasu daga cikin dalilan da ya sanya makaɗa da mawaƙan Hausa suke amfani da salon sanya karin magana a cikin waƙoƙinsu.

3.1 Ma’anar Karin Magana

Masana Harshen Hausa sun fassara karin magana gwargwadon fahimtarsu. Daga ciki akwai:
 
Ɗangambo (1984) da ya ce, “Karin magana dabara ce ta dunƙule magana mai yawa a cikin zance ko yan kalmomi kaɗan, cikin hikima”.

Yahaya, Zariya, Gusau, da ‘Yar’aduwa (1992) , “Karin Magana Tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare da bayar da maana gamsasshiya, mai faɗi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki.

Kenan idan aka lura sosai, za a ga cewa ita karin magana, magana ce dunƙulalliya wacce ba kowa ne zai iya gane ta ba tare da an yi masa cikakken bayani ba. Yau da gobe da kuma yawan amfani da ita, musamman a zamunan da suka shuɗe, da ake yawan tsarma ta a cikin zance, sai ya zama shi Bahaushe yana iya gane abinsa. Ba a cikin zancen yau da kullum ba har a cikin waƙoƙi akan sami tsarmen karin magana domin a nuna kwarewar harshen.

3.2 Dalilan Tsarma Karin Magana a Cikin Waƙoƙin Hausa

Daga cikin dalilan da suke sa makaɗa da mawaƙan Hausa amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu sun haɗa da;

1.   Taƙaita doguwar magana.

2.   Nuni, gargaɗi, da faɗakarwa cikin nishaɗi, sannan kuma a taƙaice.

3.   Bayyanar da ƙwarewa da fasaharsu wajen ƙulla waƙa da shirya ta.

4.   Adon harshe. Abin da ake nufi da adon harshe a nan, shi ne cewa karin magana yana ƙara wa zance kyau da kuma armashi.

5.   Wata kafa ce ta kambama wanda ake yi wa waƙa da kuma kushe abokan hamayyarsa.

3.3 Tsarmen Karin Magana a Tafashen Makaɗa Sa’idu Faru

A nan za a ga irin yadda Sa’idu Faru yake kawo karin maganar kai tsaye ba tare ya canza shi ba, ko ya yi luguden karin maganar, ko ya rage maganar, ko ya ƙirƙiro karin maganar ko kuma ya yi takin saƙa da yadda ma’ana da tsarin amfani da karin maganar take.

3.3.1 Tsarmen Karin Magana Kai Tsaye a Cikin Waƙa

A ƙarƙashin wannan fasali, za a nazarto ɗiyan waƙar da Makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da Karin Magana kai tsaye ba tare da sauya su ya ba. Misali a waƙar Sarkin Kudu Macciɗo ya yi amfani da salon karin magana a cikin wani ɗan waƙa in da yake cewa;

 Gidin waƙa: Farin cikin Musulmin duniya,

: Mai martaba na Abubakar.

 Jagora: Sa’idu malamin waƙa,

‘Y/Amshi: Mai kwana ɗumi na Mamman na Balaraba

 Jagora: Ban wuce gonata da irina ba, inda Sarkin kudu na tsaya,

 ‘Y/Amshi: Ban wuce gonata da irina ba inda Sarkin kudu na tsaya.

 (Waƙar Sarkin Kudun Sakkwato, Muhammadu Macciɗo)

A nan makaɗa yana son ya nuna irin yadda ya tsaya cak ga maigidansa Sarkin Kudu Macciɗo wajen aiwatar da waƙarsa, kasancewar shi ne maigidansa a cikin tsarin waɗanda yake yi wa waƙar fada. A bisa al’ada, idan Bahaushe ya ce an wuce gona da iri, ke nan an yi wani kutse na wuce ƙa’idar yin wani abu.

A cikin wani ɗa na wannan waƙar, Makaɗa Saidu yana cewa:

 Jagora: In wani ya samu,

‘Y/Amshi: Wani ya rasa,

 : Ita duniya haka nan take.

Jagora: Kuma in maganar zaƙi a kai,

‘Y/Amshi: Kuma im maganaz zaƙi akai,

 : Kowa na kurɓa ruwan zuma,

 : ba ya koma tad da batun maɗi.

(Waƙar Sarkin Kudun Sakkwato, Muhammadu Macciɗo)

Malamin waƙa a nan yana kwatanta tauraronsa ne da wasu a wani yanayi na musamman, inda yake ganin idan ana maganar sarkin Kudu Macciɗo, to ba a kawo wani ɗan sarki a Sakkwato. Domin ya zamanto katangar zuma ne kowa ya taɓa ta, sai ya lasa.

A cikin wani ɗan waƙa da ya yi wa Muhammadu Macciɗo, makaɗain ya yi amfani da wani karin magana inda yake cewa:

 Gindin Waƙa: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,

: Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.

Jagora: Babban dutsi a hange ka nesa,x2

 ‘Y/Amshi: A ishe ka doronka ya tcar ma kowa,x2

: Da ɗai babu geben yak kai ga gulbi.

: Ruwan Maliya sun wuce masu taru.

 (Waƙar Sarkin Kudun Sakkwato, Muhammadu Macciɗo)

A nan, mawaƙin yana ƙoƙarin ya nuna cewa duk fa ‘yan sarkin da Muhammadu Macciɗo ya yi zamani da su, ba su kai ba kamarsa ba, inda yake kwatanta Sarkin Kudu da cewa shi fa ruwan maliya ne , wanda ya fi ƙarfin ‘yan taru.

A cikin waƙar Sarkin Banga Alahaji Sale Abubakar, Makaɗa Sa’idu Faru ya kawo wata karin magana ta Hausa mai cewa ‘ɗaki ko yana ruwa ya fi waje’. Ɗan waƙar ya zo kamar haka;

Gidin Waƙa:Gwabron giwa uban Galadima ɗan Sambo ginshimi,

:Gamshiƙa Amadu na Maigandi kai a uban Zagi.

Jagora::Ni ɗaki ko yana ruwa,

:Mu’azu don ya ɗara wuri,

‘Y/Amshi::Ko da Sarkin Yaƙi na yi na rowa,

: Ka bab biyaw wani.

Jagora:: Ko da,

‘Y/Amshi: Sarkin Yaƙi na yi ma rowa,

: Ka ba biyaw wani.

(Waƙar Sarkin Yaƙin Banga, Alhaji Sale Abubakar)

A cikin wannan ɗan waƙar, an fito da karin maganar don makaɗin ya nuna tsantsar dangantaka mai ƙwari da ke akwai tsakanin mawaƙin da wannan Sarki. Banga Alhaji Sale. Mahaifiyar Sa’idu a garin Banga aka haifi ta kuma hasali ma a nan garin makaɗa Sa’idu ya yi ƙuruciyarsa. Wannan kyakkywar dangantake ce Sa’idu yake son ya nuna ta amfani da karin magana. A ra’ayin Sa’idu, ko da ba ya samun komai a wurin Sarkin Banga, to yana nan a matsayin ubangidansa..

A cikin waƙar Ɗan Hashim Kanen Sarkin Kano in da makaɗa Sa’idu Faru yake cewa

Gindin Waƙa: Bi da maza na Abashe,

: Ana shakkah haye ma Amadu’

: Mai daraja na Wambai.

: Ɗan Isa ƙanen Sarkin Kano.

Jagora: Da ɗai wayo ba ya sai da taba,

 :In dai na sha ta babu daɗi watsarwa nikai,

 ‘Y/Amshi: In tai mu biɗo wata inda mai daɗi take.

 (Waƙar Ɗan Isan Kano Amadu)

A cikin wannan ɗan waƙa za a ga cewa makaɗa ya yi amfani da karin maganar Hausawa mai nuna wayo ba ya sayar da taba, in da yake yi wa wani gidan rediyo zambo a cikin waƙarsa saboda rashin ba shi kuɗi a lokacin da ya aka yi shiri da shi.

A cikin waƙar sarkin Fulanin Bunguɗu, Makaɗa Sa’idu Faru ya kawo wata karin magana ta Hausa mai ‘ramar giwa kunyar jeji’. Ɗan waƙar na cewa;

 Gindin Waƙa: Koma shirin yaƙi,

: Jan damishin gidan Kure Shehu.

 

Jagora:Sai ka yi man mota,x2

‘Y/Amshi: Dul lardin ƙasag ga mu ab ba mota,x2

Jagora: Ramag giwa kunyad daji,

‘Y/Amshi: Abin da anka yi man,

: Dun na dogara wajen ikon Allah.

Jagora: Ramag giwa kunyad daji,

‘Y/Amshi: Abin da sunka yi man,

Jagora: Dun na dogara wajen ikon Allah

(Waƙar Sarkin Fulanin Bunguɗu, Alhaji Shehu)

A nan mawaƙin yana ƙoƙarin ya ja hankalin sarki game da buƙatarsa kyautar mota da yake so Sarki ya ba shi. Mai yiwuwa makaɗa ya roƙi mota a wurin iyayen gidansa amma kuma buƙatar ba ta biya ba. Da haka ya ƙara jaddada wannan buƙata tasa kuma ta tunatar da Sarki cewa rashin samun mota ko duk tauyewar jin daɗin ko walwalar rayuwa ga mawaƙi, ba fa laifin kowa ba ne face na iyayen gidansa.

A cikin waƙar sarkin Falale Muhammadu Tudun Falale ya yi amfani da irin wannan salo na cusa karin magana kamar haka:

 Gindin Waƙa: Ya riƙa da gaskiya Muhammadun Muhammadu,

 : Karsanin gidan mai saje shirin ka ya yi kyau,

 Jagora: Sun dai yi mirgiɗar dutci sun gaza imai,

: ‘Yan hannuwansu sun gaza,

‘Y/Amshi: Na Abdu ko da ƙarfin Allah kana shiga gidan.

 Jagora: Icce mai kama ka ɓota,

 ‘Y/Amshi: Haka nij ji gun Basakkare,

 (Waƙar Sarkin Tudun Falale, Muhammadu Ƙwazo)

Idan aka lura da kyau ya yi amfani da karin maganar Hausa mai cewa “ icce mai kama ka ɓota” in da yake son ya kururuta sarki Tudu cewa ai ko ba a faɗa ba, ya fi dacewa da zama sarki, saboda ya cika dukkan sharuɗɗan zama sarki, idan aka kwatanta shi da sauran ‘yan sarkin Gummi a wannan lokaci, domin ya fi su kuɗi da biyan buƙata ga mawaƙa.

A can cikin wani ɗan waƙa ga abin da yake faɗa kamar haka;

 Jagora: Ban cin kokuwa akwai maraba,

 : Ɗan aruguma ya bar faɗa maka Muhammadu.

Jagora: Ko uwaye mata kuna,

 ‘Y/Amshi: Kuna da tcetcere da ɗan marar abin wuya,

: Ɗan karuwa dub ɓaci kaj jiya da muke.

(Waƙar Sarkin Tudun Falale, Alh. Muhammadu Ƙwazo)

A nan ma ya tsarma karin maganar da ke ɗauke da saƙon cewa ba don akwai masu shiga tsakani ba da neman sarauta da shi ba zai yiyu ba. Domin cikin ɗan lokaci zai kayar da abokin neman sarautar.

A cikin waƙar sarkin Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Ɗangwaggo Bunguɗu, makaɗa Sa’idu Faru ya yi amfani da karin maganar Hausa mai cewa ‘wasu kaya sai amali’. Ga abin da ya ce a ɗan waƙar:

Gindin Waƙa: Bajini birni bajin dawa,

: Na dai gaishe ka da ƙoƙari,

: Ɗan Maidaga na Abubakar,

: Usman kai niz za ka in gani.

Jagora:: Manyan kaya manya ganwo,

‘Y/Amshi:: Jakki kankambar banza garai,

: Wasu kaya sai bisa raƙumi..

(Waƙar Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu) 

Kamar yadda aka gani a cikin wannan ɗan waƙa, Makaɗa Sa’idu ya yi amfani da wannan karin magana domin ya nuna cewa kyauta babba tana fitowa ne daga babban mutum. Ƙaramin alhaki duk yadda ya so ya yi irin wannan kyautar ba zai iya ba domin rashin zarafi. Idan muka dubi ɗiyan waƙa da suka bi bayan wannan, za a ƙara fahimtar manya kaya, manyan ganmo Ɗan waƙar yana cewa:

Jagora: Baban Buda mai babbar kyauta,

‘Y/Amshi: Abin da yas sa ban hau doki,

: Na Bunguɗawa shi muka son hawa

Jagora: Abin da yas sa ban hau doki ba

‘Y/Amshi: Na Bunguɗawa shi nika son hawa.

Usman Ɗangwaggo Bungudu ɗan sarautar Bungudu ne. Yana cikin ‘yan boko na farko a tsohuwar Arewa masu Yamma. Hasali ma shi ne mutum na farko da ya sami digirin farko kan aikin lauya a Ingila. Ya taɓa zama babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a a tsohuwar jihar.

A wani ɗa na wata waƙa, makaɗa Sa’idu Faru a cikin azanci da hikima ya yi amfani da karin maganar nan mai cewa ‘alheri ya fi mugunta’ ko ‘alheri ya ɗara mugunta’ da karin maganar da ‘alheri danƙo ne, ba ya faɗuwa ƙasa banza Haka kuma duk a cikin wannan waƙa, Sa’idu ya fassara karin maganar Hausa mai cewa ‘ƙarya fure take ba ta yaya’ da kuma karin magana nan ‘gaskiya dokin ƙarfe. A cikin wasu ɗiyan waƙa makusantan juna, a waƙar da ya yi wa Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu. Ɗiyan waƙar kuwa su ne:

Gindin Waƙa : Gwabron giwa kana da martaba,

: Usumanu na Bunguɗu,

: Uban Marafan Keku,

: Na Atto mai wuyak karo.

Jagora: Alheri dai bai zama mugunta,x2

‘Y/Amshi : Don komi tad daɗe hita yakai,x2

: Haka nij ji ana hwaɗi Gusau jiya.x2

Jagora:: Ni dai na hore ku ‘yan ɗiyana,x2

: Kowa nak kai ga gaskiya,x2

‘Y/Amshi: Ya riƙe ta a yi sama a yi ƙasa.x2

Jagora : Ƙarya kowa nat tara ta yah haye,

: Ko an tcinkaye shi ko’ina,

: Hwaɗowa za ta yi ta wargaje,

‘Y/Amshi: Ka ishe shi buƙu shina rabon ido.

Jagora: Dawowa za ta yi ta yamutce,

‘Y/Amshi: Ka ishe shi buƙu shina rabon ido,

: Sai ya rasa ko kwabon sayen dawo.

A cikin waƙar Ɗanmalikin Gidan Goga a ƙasar Maradun, jihar Zamfara, mawaƙin ya yi amfani da karin magana nan mai cewa ‘ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, shirin faɗa ne.’ Ɗan waƙar yana cewa:

Gindin Waƙa: Mai Gidan Goga,

: A ji tsoronka,

: Sanda gwarzon malam Nuhu,

: Toron giwa Ɗanmaliki.

Jagora: : Ko can zamanin ana yaƙi,x2

: Azna sun san da Gidan Goga,x2

‘Y/Amshi: Azna na ganin ga fili ya faskara,

: Ja da baya ga rago,

: Ai Daudu na hwaɗa masu,

: Ba tsoro na ba,

: Gyara kayan hwaɗa yakai.

Jagora: Ja da baya ga rago,

‘Y/Amshi: Ba tsoro na ba,

: Gyara kayan hwaɗa yakai

(Waƙar Danmalikin Gidan Goga, Alhaji Umaru)

Haƙiƙa, Makaɗa Sa’idu Faru a cikin waƙoƙinsa ya nuna shi fasihi a sha’anin tsarma karin magana a cikin waƙoƙinsa. Duba yadda a cikin wani ɗan waƙa na Sarkin gabas na Talata Mafara, Alhaji Shehu Sarkin gabas yake cewa a wani ɗan waƙa:

Gnidin Waƙa: Ƙi garaje uban Shamaki Shehu,

: Ɗan Muhamman Sarkin riƙon taro.

Jagora: Karen masara da ɗai ba shi yin gyamro,

‘Y/Amshi: Yaushe talaka ka haihwa ɗan Sarki,

: Bunsuru ba shi yin layya ga rago,x2

A nan jagora ya fara ɗan waƙa da karin magana, yan amsa sai suka ƙara haske ko fassara abin da karin maganar take nufi a muhallin da aka yi amfani da ita. Wato yadda karan masara ba ya zai taɓa yi gyamro ba, haka talaka ba zai haifi Sarki domin a bisa al’ada ta Bahaushe, sarauta aba ce da gadon ta ake yi. A nan habaici ne makaɗin yake yi wa wani ɗan talaka da yake ganin ya ƙasura. Duk da ɗaukaka da yake gani ya samu, ba fa zai taɓa zama sarki ba.

A cikin wannan waƙa har yanzu, Saidu ya sake tsarma wata karin magana a wani ɗan waƙa da ke biye da wanda aka kawo a sama. Wannan ɗan waƙa yana cewa:

Jagora: Ƙafar kuturu mutuncinta takalmi,x2

‘Y/Amshi: Ran dub bai da su ba ya jin sosai.x2

A cikin waɗannan ɗiyan waƙar, za a ga makaɗa Sa’idu Faru yana yi wa masu jayayya da sarkin gabas Shehu zambo ta amfani da karin magana a cikin hikima da taƙaita zance.

Haƙiƙa waƙar Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usmanu Ɗangwaggo Bunguɗu tana ƙunshe da ɗauke da hoto cikin bayani game da ma’anar wata karin magana mai cewa ‘kwaɗon da ya kira ruwa shi ruwa kan doka.’ Wani ɗan waƙa na cewa:

Gindin waƙa: Toron giwa kana da martaba,

: Usmanu na Bungudu,

: Uban Marafan Keku,

: Na Atto mai wuyak karo.

Jagora: Kwaɗɗo na can na kiran ruwa, x2

: Ya tattake kiran su ɗai ya kai

: An yi yayyahi waɗanga sun wuce, x2

: Ya tattake kiran su ɗai ya kai, x2

: An yi yayyahi waɗanga sun wuce,

: Sai ga Allah ya shirga ruwa

: Gulbi ko ya ɓaɓɓako ruwa, x2

: Sai ga kwaɗɗo tun da jijjihi, x2

’Y/Amshi: Wai za ya biɗat tudun da yah haye

Jagora: Nic ce mashi kwaɗɗo ina iyali?

‘Y/Amshi: Yac ce ƙyale ni Maikiɗi, x2

: Tahi dan nan ba ni son batun ba’a.

Bayanin da za a iya ƙyallarowa sh cewa wani ɗan sarki ne makaɗa ya yi wa zambo, ya kira shi kwaɗo. Kwaɗo yana ta addu’ar sarautar gidansu ta faɗi, kenan kwaɗo ya kira ruwa. Sarautar ta faɗi, ya nema amma kuma bai samu ba, ruwa ya ci shi.

4.0 Sakamakon Bincike

Nazarin karin magana a da’irar waƙa wani fage ne mai cin gashin kansa, kuma wanda ke buƙatar a bai wa muhimmancin gaske. Akan haka ne wannan takarda ta himmatu wajen tuno wasu daga cikin karuruwan magana da Makaɗa Sa’idu Faru ya tsarma a cikin wasu fitattun waƙoƙinsa, inda a ƙarshe hasashen da aka gina takardar ya tabbata wajen gano cewa akwai nason amfani da salon karin magana a cikin waƙoƙin Sa’idu Faru musamman a lokacin da yake ƙoƙarin Kam~ama tauraronsa ko gwaninsa a cikin waƙa, ko kuma idan yana son ya yi wa magabtansa zambo ko habaici ko arashi ko guga zana da sauransu dabarun isar da saƙon waƙa. A ƙarshe za a ga cewa an nazarci waƙoƙin Sa’idu Faru guda goma, aka taskace misalai guda goma da suke ɗauke da tsarmen karin magana don tabbatar da kyakkyawan sakamako.

5.0 Kammalawa

Kamar yadda aka gani a cikin muƙalar, an gi nasarar nazarar yadda Sa’idu Faru yake cusa salon karin magana a cikin waƙoƙinsa na fada, an kuma bayyana wasu daga cikin dalilan da suke sanya makaɗa da mawaƙa suke amfani da salon karin magana a cikin waƙoƙinsu domin nuna naƙaltar harshe da kwarewa da samar da nishaɗi da zambo da habaici da kuma uwa uba taƙaita zance cikin hikima.

Manazarta

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Kano. Maɗabaar Kamfanin Triumph Gidan Saadu Zungur.

Gusau, S. M (1984). Makada da Mawaƙan Hausa. Zaria. ABU Press.

Gusau, S.M., (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Ltd.

Gusau, S.M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa Kano: Century Reseach and Publishing Ltd.

Junaidu I. da ‘Yar’Aduwa T.M. (2002) Harshe da Adabin Hausa a Kammale, Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan .Spectrum Books Limited, Ring Road.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M., da ‘Yar’aduwa T.M. (1992) Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandire 1. Ibadan: University Press PLC.

Zarruƙ R.M., Kafin Hausa A.A. da Alhassan B.S.Y. (1987) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Biyu. Ibadan. University Press PLC.



[1] Gusau, S. M 1985: Makada da Mawaƙan Hausa. Zaria shafi 117-118.

Sa'idu Faru

Post a Comment

0 Comments