Duk wanda ya taso zai ga Masallatan Izala a ware suke daga sauran Masallatai na sauran al'ummar Musulmi. To wannan ya sa gama gari suke tambayar; me ya sa hakan ya faru, alhali dukkan kungiyoyi suna ikirarin su Musulmai ne?
To duk wanda
ya san Tarihin fitowar Izala ya san cewa Izala ta ginu ne a kan kyamar Bidi'a
da 'yan Bidi'a, musamman 'yan Darikun Sufaye a wancan lokaci. Wanda har lamarin
ya kai ga 'yan Izalar sun kauracewa wa 'yan bidi'ar a harkokin Addini, da wasu
mu'amalolin rayuwa, har suka ware Masallatansu. Kuma za a iya cewa; - a dunkule
- har yau lamarin haka yake.
Bayan haka,
a yanzu muna wani zamani da Muslunci ya fara zama bako, kamar yadda ya faro a
bako. Saboda jahiltar Addinin ya yawaita a tsakanin al’umma, da rashin sanin
tafarkin Sunnar Manzon Allah (saw), da Manhajin Musulman farko. Wannan ya sa
jahilai suke tuhumar Izalar da raba kan al'umar Musulmi.
Su kuma ‘Yan
boko wadanda suka jahilci Addini - imma saboda jahilci, ko mugun nufi - suna
ganin babu dalilin da zai sa banbancin Addini, da banbancin ra’ayi da Akida ya
sa a yi adawa da yanke alaka da kaurace wa juna. Wannan ya sa suke ganin hatta
Kiri*stoci ba za a nuna musu ada*wa ba, sai dai a dauke su abokai, abin kauna.
Balle kuma
tsakanin Musulmai, mabiya Akidu mabanbanta. Don haka suke tsangwamar 'yan
Izala/Wahabiyawa/'yan Salafiyya a kan kaurace wa 'yan Darika da 'yan Shi’a,
-wai- su a ganinsu Musulmai duka daya suke.
Me zai sa
kowa ba zai rike Akidarsa ba, a zauna tare?!
Me ya sa ba
za a hada kai ba, a so juna, kowa ya rike fahimtarsa, babu raddi wa juna?!
Shi dan Boko
Jahilin Addini haka yake gani.
Alhali duk
wanda ya fahimci Addinin Muslunci ya san cewa: Alkur’ani cike yake da hana mu
daukar kafirai a matsayin majibinta masoya, sai dai kawai a yi zaman lafiya da
su, idan sun nemi hakan.
To haka su
ma ‘yan Darika da ‘yan Shi’a, idan ka bibiyi tafarkin Sunna da Manhajin
Magabata za ka san cewa; ana hada kai ne a kan Akida guda daya ingantacciya,
tafarki guda daya, shi ne tafarkin Annabi (saw) da Sahabbansa. To amma hakan ba
zai yiwu ba, saboda dole al’umma sai ta rarrabu zuwa kungiyoyi 73 masu Akidu
mabanbanta. Dukkansu a kan ba ta suke sai kungiya guda daya, ita ce: kungiyar
da take kan tafarkin Annabi (saw) da Sahabbansa.
Don haka
sauran kungiyoyi 72 din duka kungiyoyin bidi’a ne. Magabata sun kaurace musu,
saboda ladabtarwa, da kuma saboda gudun kada su ba ta wa mutane Akidarsu ta
Muslunci da Sunna.
Imam
al-Bagwaiy ya ce:
"قد أخبر النبي صلى
الله عليه وسلم عن افتراق هذه الأمة، وظهور الأهواء والبدع فيهم، وحكم بالنجاة لمن
اتبع سنته، وسنة أصحابه رضي الله عنهم، فعلى المرء المسلم إذا رأى رجلا يتعاطى
شيئا من الأهواء والبدع معتقدا، أو يتهاون بشيء من السنن أن يهجره، ويتبرأ منه،
ويتركه حيا وميتا، فلا يسلم عليه إذا لقيه، ولا يجيبه إذا ابتدأ إلى أن يترك
بدعته، ويراجع الحق.
والنهي عن الهجران فوق الثلاث فيما يقع بين الرجلين من
التقصير في حقوق الصحبة والعشرة دون ما كان ذلك في حق الدين، فإن هجرة أهل الأهواء
والبدع دائمة إلى أن يتوبوا".
شرح السنة للبغوي
(1/ 224)
To kaurace
wa 'yan Bidi'a shi ne tafarkin Magabata da Manhajinsu, shi ya sa Imamuna Malik
ya hana mu bin 'yan Bidi'a Sallah, inda ya ce:
"قال: وقال مالك: لا
ينكح أهل البدع، ولا ينكح إليهم، ولا يسلم عليهم، ولا يصلى خلفهم، ولا تشهد
جنائزهم".
المدونة (1/ 177)
“Ibnul Qasim
ya ce: Malik ya ce: Ba a aura daga ‘yan bidi’a, kuma ba a aurar musu, ba a yi
musu sallama, ba a yin Sallah a bayansu, kuma ba a halartar jana’izarsu”.
Kuma ya ce:
"قال: كان مالك يقول:
إذا علمت أن الإمام من أهل الأهواء فلا تصل خلفه ولا يصلى خلف أحد من أهل الأهواء".
المدونة (1/ 176)
“Ibnul Qasim
ya ce: Malik ya kasance yana cewa: Idan ka san cewa; Limamin dan Bidi’a ne to
kada ka yi Sallah a bayansa, ba a yin Sallah a bayan wani daga cikin ‘yan
Bidi’a”.
Imamu Ahmad
ma an ruwaito irin wadannan daga gare shi:
"الأثرم عن أحمد، قيل
له: رجل قدري أعوده؟، قال: «إذا كان داعية إلى الهوى فلا» ، قيل له: أصلي عليه؟
فلم يجب، فقال له إبراهيم بن الحارث العبادي وأبو عبد الله يسمع: «إذا كان صاحب
بدعة فلا تسلم عليه، ولا تصل خلفه، ولا تصل عليه» قال أبو عبد الله: «كافأك الله
يا أبا إسحاق وجزاك خيرا»".
شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (4/ 809)
Ma'ana; An
tambayi Imamu Ahmad a kan Sallar jana'iza ga dan bidi'a, sai ya yi shiru. Sai
abokinsa Ibrahim bn al-Harith ya ce:
"Dan
bidi'a ba za a masa sallama ba, BA ZA A YI SALLAH A BAYANSA BA, ba za a masa
Sallar jana'iza ba".
Sai Imamu
Ahmad ya ce:
"Allah
ya biya ka ya kai Baban Ishaq, Allah ya saka maka da alheri".
Irin wannan
shi ne dalilin da ya sa 'yan Izala suka ware Masallatansu, suka raba gari da
'yan Bidi'a a duka harkokin Addini. Kuma wannan shi ne Manhajin Magabata, kamar
yadda aka ruwaito daga gare su:
Ibnu Abbas
(ra):
"عن ابن عباس قال: لا
تجالس أهل الأهواء، فإن مجالستهم ممرضة للقلوب".
الشريعة للآجري (1/ 452)، الإبانة الكبرى لابن بطة (2/ 438)
“An ruwaito
daga Ibnu Abbas (ra) ya ce: kada ka zauna da 'yan bidi'a mabiya son zuciya, don
zama da su yana cutar da zuciya".
Haka Hassan
al-Basariy ya fada, babu banbanci:
"عن الحسن قال: لا
تجالسوا أهل الأهواء، فإن مجالستهم ممرضة للقلوب".
الإبانة الكبرى لابن بطة
(2/ 438)
Imamu Ahmad
ya ce:
"أصول السنة عندنا
التمسك بما كان عليه أصحاب رسول الله - صلى الله عليه وسلم - والاقتداء بهم وترك
البدع وكل بدعة فهي ضلالة وترك الخصومات وترك الجلوس مع أصحاب الأهواء...".
شرح أصول اعتقاد أهل السنة والجماعة (1/ 176)، طبقات
الحنابلة (1/ 241)
Ma'ana; daga
cikin Tushen Sunna akwai barin Bidi'a, DA BARIN ZAMA DA 'YAN BIDI'A.
Wani zai ce:
ai wadannan maganganun Magabatan da ka kawo sun yi su ne a kan wadanda
Bidi’arsu ta kafirci ce.
To sai mu ce
maka: a’a, ba masu Bidi’ar kafirci ake nufi ba, shi ya Imam al-Bagwaiy ya ce:
"ثم هم مع هجرانهم
كفوا عن إطلاق اسم الكفر على أحد من أهل القبلة، لأن النبي صلى الله عليه وسلم
جعلهم كلهم من أمته".
شرح السنة للبغوي
(1/ 227)
"Sannan
su Ahlus Sunna, duk da suna kaurace wa 'yan Bidi'a, amma sun kame bakinsu daga
jefa kalmar kafirci, ga duk wani Musulmi mai Sallah, saboda dukkan kungiyoyi 72
Annabi (saw) ya sanya su daga cikin al'ummarsa".
A takaice,
wannan Manhaji ne na Magabata. Kuma shi ne abin da Ahlus Sunna Mabiya Salaf
suke kansa a kowane zamani, suna kaurace wa ‘yan Bidi’a gwargwadon hali.
To wannan
shi ne dalilin da ya sa tun farko 'yan Izala suka kyamaci 'yan Dariku, suka
kaurace musu, har suka ware Masallatansu daban, da nisantarsu a sauran
mu'amaloli da suka shafi Addini.
Saboda haka
muke tunatar da 'yan Izala, kada su manta da Manhajinsu na asali. A cigaba da
kaurace wa 'yan Bidi'a, amma gwargwadon Maslaha, da samun iko.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.