Ticker

6/recent/ticker-posts

Mabudin Turken Darsashin Zuciya: Kebabben Nazari Kan Mabudin Turken Darsashin Zuciya a Wasu Daga Cikin Wakokin Alhaji Garba Maitandu

Citation: Shinkafi, R.H. and  Ibrahim, A.A. (2024). Mabuɗin Turken Ɗarsashin Zuciya: Keɓaɓɓen Nazari Kan Mabuɗin Turken Ɗarsashin Zuciya a wasu daga cikin waƙoƙin Alhaji Garba Maitandu. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 458-461. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.057.

MABUƊIN TURKEN ƊARSASHIN ZUCIYA: KEƁAƁƁEN NAZARI KAN MABUƊIN TURKEN ƊARSASHIN ZUCIYA A WASU DAGA CIKIN WAƘOƘIN ALHAJI GARBA MAITANDU

Rabi’u Hassan Shinkafi
Sashen Hausa na Kwalejin Ilmi ta Maau, Jahar Zamfara

Da

Aminu A. Ibrahim
Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari, Jihar Sakkwato

Tsakure:

Waƙoƙin ɗarsashi ko rinjayen zuciya, waƙoƙi ne da kan wanzu a sakamakon wani abu da ya motsa wa mutum rai, da ya danganci farin ciki, ko farin rai, ko akasin haka, wato bakin ciki. Waƙoƙin ɗarsashin zuciya sun ƙunshi bayyana farin ciki ko bakin ciki bisa wani abu da ya faru ga mutun ɗaya ko ƙungiya wasu mutane, ko gari ko ƙasa (Gusau, 2008).Wannan maƙala za ta zaƙulo mabuɗin turken waƙoƙin ɗarsashin zuciya na Alhaji Garba Maitandu. Manufa a nan ita fito wa da mabuɗin turken waƙoƙin Garba Maitandu, wato in da aka fito da turken a bayyane. Duk abin da zai biyo bayan wannan mabuɗin turke tamkar warwarar turke ne da ake yin amfani da ƙananan tubalai domin gina babban turke.

Fitilun Kalmomi: Mabuɗi, Turke, Ɗarsashin Zuciya, Waƙoƙin baka, Garba Maitandu

Gabatarwa

Duk da yake akwai bambancin mazhabobi na masana, akan abin da ya shafi turke/jigo, wasu masana sun tafi da ra’ayin cewa a cikin rubutattun waƙar ne ake samun jigo, wasu kuwa suna ganin a tasu mazahaba ba a kiran sa  jigo a cin waƙoƙin baka, sai a kira shi turke. Wani abin sha’awa a nan shi ne, jigo da turke a cikin kowace waƙa rubutacciya ko ta baka duk dai ma’anar su ɗaya. A kowace waƙa dai ana nufin dalili, ko musabbabi, ko manufar ko saƙon da ake son isar wa a cikin waƙa. Wannan bincike an dora shi a bisa mazhabar Gusau, wanda ya kira shi turke a cikin waƙoƙin baka.

 

 

2.0Ma’anar Turke

Turke a ƙa’idar masu nazarin waƙar baka na nufin, saƙon da waƙa take ɗauke da shi. Idan an ce saƙo ana magana ne kan manufar da ta ratsa waƙa, tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta, ba tare da karkacewa daga ainihin abin da ake zance a kan sa ba (Gusau, 2008). Kamar yadda Gusau ya bayyana saƙon da mawaƙi/makaɗi yakan zaɓa ya gina waƙarsa ta hanyar tauye kansa da kansa ya zuba ɗiyanta bisa wasu zaɓaɓɓun kalmomi da za su doshi wata babbar manufa ɗaya shi ake kira turke.

2.1Mabuɗin Turke

Galibin waƙoƙin baka na Hausa suna da gundarin saƙon da su ke isar wa ga masu sauraro. Akan gane gundarin turke ne galibi cikin ɗan waƙa ɗaya. A yayin waƙar ne mawaƙi kan yi amfani da wasu ƙananan turaku masu nasaba da babban turkensa, waɗannan ƙananan turaku su ake kira tubalan ginin turke waɗanda su ne ake amfani da su don kaiwa ga babban turke.

Saƙon da ke fitowa fili a cikin ɗan waƙa shi ake kira mabuɗin turke. Mabuɗin turke kan bayyanar da manufar makaɗi a fili cewa ga saƙon da yake son isarwa ga al’umma, kuma duk abin da zai biyo baya watau ɗiyan waƙoƙin da ke biyo wa a baya a matsayin matallafa ne kawai.

2.2Hanyoyin fitar da Mabuɗin Turke

Akwai hanyoyi da yawa da makaɗa ke amfani da su wajen fitowa da mabuɗin turke yadda mai sauraro ko mai nazari kan iya fitar da manufar mawaƙi a zahiri.

i.        Bayyana turke ɓaro-ɓaro a farkon waƙa ko a tsakiya.

ii.      Fadin turke a gindin waƙa

iii.   Amfani da wata ƙarina wadda za ta ayyana turken waƙa (Gusau, 2008).

2.3Mabuɗin Turke a Cikin Waƙoƙin Garba Mai Tandu

Kamar sauran makaɗa da suka yi zarrah a waƙoƙin baka na Hausa. Garba Maitandu ba ƙashin da ake tsotsewa ba ne a jefar. Garba Maitandu ya yi waƙoƙi daban-daban waɗanda suke da turaku mabambanta a ɓangaren turken raɗaɗin zuciya Garba Maitandu zakaran gwadin dafi ne. Ya yi waƙoƙin kamar haka:

Waƙar kunama

Waƙar Yawon duniya

Waƙar Kanari

Waƙar Jaki

Waɗannan waƙoƙi dukansu na ɗarsashin zuciya ne, sabodahaka za a ɗauki waƙoƙin ɗaya bayan ɗaya don a gayadda mabuɗin turke kowace waƙa ya fita, ta hanyar amfani da dabarun da (Gusau, 2000) ya bayyana.

 

 

2.3.1Waƙar Kunama

A cikin wannan waƙa, mawaƙin ya yi amfanida salon faɗin turken waƙa a gindin waƙarsa. Kamar haka:

Mai gida:Kunama zan wa kiɗi,

Zama ciwo ag gareta,

Ta halben na jiya.

Wannan gindin waƙa ya fitar da mabuɗin turke ɓaro-ɓaro, in da makaɗin ya bayyana wa jama’a cewa zai yi wa  kunama waƙa ne sabo ciwon da ake ji idan ta harbi mutum.

Don haka, duk ɗiyan waƙoƙin da suka biyo cikin waƙar za a tarar cewa karin bayanine, ko suna bayyana irin halinrayuwar da mutum ke shiga yayin da kunama ta harbi shi. Da wannan ne ya yi amfani a tubalai ƙanana don cimma babban turkensa.

Don tabbatar da masifar da mutum ke shiga idan kunama ta harbe shi, Garba Maitandu muhallish shahidi ne, domin ya ce “ciwo aggare ta ta halban na jiya”. Hakan ta sanya Garba Maitandu fitar da furucin guddarin turke kamar haka:

“Ran Lahadi kunama,

Ni Garba tayi man Doki,

Ango sai ta sai maku sirdi

Ba mu buƙatar sirdinta,

Tunda shegen sirdi takai

Da amsar sirdinta,

Gara da ƙaiƙan tomashe

A tsaga ko targaɗe.

(Garba Maitandu: WaƙarKunama).

Idan an lura da kyau, za a fahimci cewa, abin daya haddasa waƙar ta fito a fili (Turke) watau karonsa da kunama. Sai ya kawo abin cikin hikima ya ce “Ta yi mai Doki”, duk sauran abin da ya biyo baya cikin waƙar yana da nasaba da harbin da ta yi masa, da kuma halayyar da wasu suka shiga a yayin da ta harbe su. A cikin sauran ɗiyan waƙoƙin Garba Maitandu galibi ya yi amfani da ƙaramin turkan raki da salon kambamawa don ya nuna kasawar mutanen da kunama ta harba a yayin raɗaɗi da zojin harbin ta. Misali Tubalin Raki

 

 

Sarkin rawa yana noma nai

Ya gama noma nai,

Kuyyar da za ya tashi,

Yas sha ƙari,

Da ta halbai ya ajik ke kalme

Sai yaz zuba da gudu,

Ya biyo wajen Alhaji,

Ta ishe ya ce mai lahiya?

Sai yacce lahiya kaɗan ce,

In ban mace ba yau ban mutuwa,

Alhaji ya ce “Isiya ka daina raki”,

Sarkinrawa ya ce,

In kazo gida ka shaida ma mutane gari,

Su sa wani sarkin Rawa,

Ga hali ni na wuce.

Isiya sarkin rawaya bayar da gari, domin a tsammaninsa ba zai rayu, ba shi yasa ya bar wasiyya wajen Alhaji cewa su zaɓi wani Sarkin Rawa shi karshen sa ya zo.

Haka kuma ya yi amfani da salon kambamawa domin ya ƙara nuna lahanin kunama misali:

Mai bindiga kai hesa sai ka zubi,

Kunama yawo takai,

Da durinta cikin ciki.

Watau Maitandu ya nuna cewa kunama ba ta jira, sha yanzu magani yanzu ce da ka taka ta ba ta kure sai ta harbe. Kuma ba a yi mata kwanto.

2.4Waƙar Yawon Duniya

Hausawa kan ce “Tuni ke sanya maraya kuka”. Garba Maitandu a cikin wannan waƙa, ya tuno min da karin maganar Hausa mai cewa “Ko wa ya tuna baya bai ji daɗin gaba ba”. a gindin wannan waƙa ta yawon duniya Garba Maitandu ya fara buɗewa da kalmar “wuya” wanda hakan ke bayyanar da cewa a yayin wannan yawo, na waƙa da suka tafi sunfunskaci wasu matsaloli waɗanda suka haifar da waƙar. Hakan ya sanya kawo kalmar “wuya” a matsayin mabuɗin turken ɗarsashin zuciyarsa. Misali:

“Wuyar yawon duniya

Sai ka zo garin wasu

Ba a san ka ba ciki”.

 

Makaɗin ya yi amfani da ƙananan tubalai da yawa don ya tabbatar da irin matsalolin da ake iya huskanta. Misali:

Ka sauka garin wasu ba kuɗi

Haraka sai ta zan biyu.

In kai mai dako ne

Ba a baka kaya ba a sanka ba kwarai,

Ka kwan ka hwalka da sahe ba kuɗi

Bale a ci tuwo”.

Wannan ya nuna cewa in kana bako ga wuri tsoronka ake ji ta yadda ko aikin ƙarfi ana gudun a ba ka. Daga ƙarshe Maitandu ya yi wa kansa kasheɗi cewa ba ya sake zuwa ko’ina in ba sana’a za ta kai shi ba. Misali:

Ba ni koma zuwa,

Yawon da ya wuce Gusau

In ba kai gyaɗa ba.

Gamu tsakar hanya wasu na cikin ɗaki,

Sai mu kwan wuri,

Wani gu sa ka sha hura,

Wani gu sai ka ci ƙasa,

Na sauka Caranci kwana tara,

Maitan ga hura mu sha,

Kuma yarana ga tuwo mu ci,

Nama sosayye mu ci mu ba yar

Ga goro hwarhwaru

Katsina nik kwan wallah maikidi

Can na sha wuya baƙa,

Da mau kuɗi yag ga budurwa da kuka

Ya hizga da karhi

Amshi: Amma ba shi ɗai ba,

Had da kai uban waƙar ka hagi tuwo

(Garba Maitandu: Waƙar Yawa Duniya)

2.5Waƙar Dajin Kwale

Wannan waƙa tana cikin waƙoƙin Maitandu da muka iya ba laƙabin “jiki magayi” domin a cikin ta wajen fitar da mabuɗin ɗarsashin zuciya, ba a turken waƙar ya fito ba kamar waƙar kunama. Wannan waƙar ta faru ne a sakamakon tuna baya, watau irin artabun da suka yi da ɓarayi tsakanin dajin Katsira da Sabon Birnin Gobir. Makaɗa ya bayyana a fili cewa tuni ne ya yi misali:

Ai zuwa na hwakai nit tuna,

Cikindajin Katsira

Garba mai kiɗi wani wuski yat tare

Yab buga mini tsawa

Sai mun ka yadda ‘yan kayan waƙa

Day yau ba mu koma shawagi ƙasa,

Mota muka biɗa ciki kowa ba bugun mu

(Maitandu Dajin Kwale).

Maitandu ya yi amfani da ƙanana tubalai a wurare da yawa cikin waƙar domin ya bayyana ɗarsashin zuciyarsa misali:

Ƙato huɗu sun ka kurgumomu,

‘Yan yara na naf fashe,

Uban kiɗi ni ɗai ab ban guda ba,

An ka kwace man turu,

Anka anshe ‘yan kuɗɗi na ban ɗuma ba

Ga kai hi to tsini

Su magu Daudu su ay ‘yan dokan dawa

Maitandu sun sa shi hursunar ƙarhi

Sai ya gama ta x 2

(Garbar Maitandu: Waƙar Dajin Kwale).

2.6 Waƙar Kanari

A cikin wannan waƙa, Garba Maitandu ya bayyana yadda wannan rashi na kanari ke damunsa. Musamman ganin yadda ya zuba zunzurutun kuɗi wajen sayansa, da irin hidimar da ya ke yi masa saboda sha’awarsa da yake yi, amma cikin ɗan lokaci kaɗan tsuntsun ya gudu. Hakan ya tabbatar mana da cewa jin ciwon ɓacin ran rabuwa da tsuntsun shi ya haddasar da waƙar. Misali:

“Na dawo da Sakkwato wurin waƙa,

Nig ga kanari cikin daji,

Ni Garba nit taya sule ashiri da bakwai,

Cinikin mu yaƙ ƙare

Nik kare su nit tusa

Da nik kawo ɗan tsuntsu gida

Buhu huɗu ni sai mai

Kin gin tiya guda

Dan tsuntsun don ya yi ƙiba

Da yay yi ƙiba ya kakkare karan keji

 

 

 

 

Dus sun yamutse, da ya uhwa

Ya bar mai kiɗi abu kejin dai ak kahe sama

(Garba Maitandu: Waƙar Kanari).

Kammalawa

Hausawa kan ce “Yabon gwani ya zama dole” Garba Maitandu ya zama zakaran gwadin dafi idan ana maganar ɗarsashin zuciya.A wurinsa waƙoƙinsa na ɗarsashin zuciya ganan ne shi ba jiyan ba, ma’ana duk abin ya faru ne a kansa kafin ya yi tunanin yiwa abin waƙa. Misali a waƙarsa ta kunama, ya gaya wa jama’a cewa ita fa zai yi wa kiɗi domin ciwo gareta ta halbe shi ya jiya. Haka kuma a waƙar yawon duniya ya bayyana irin yadda suka tagayyara a cikin tashar Kaduna. A waƙar sa ta Dajin kwale ya bayyana yadda suka haɗu da yan fashin daji. Daga ƙarshe cikin waƙarsa ta Kanari ya bayyana irin yadda tsuntsun ya gudu bayan ya saye shi da tsada kuma ya wahala da shi, lokaci guda ya tsere ya bar shi da karan keji.

Ashe kenan duk cikin waƙoƙin ba wani hasashe ko kirdado, abin da ya shafe shi ne kai tsaye.

Manazarta

Bunza, A.M. (2001) “Radaɗi da Zogin Cuta a Ma’aunin Bahaushe. Tsokaci Cikin Waƙar Garba Maitandu. Cikin Hausa Studies Reading in Hausa Language, Literature and Culture.

Gusau S.M. (1988). “Waƙoƙin Fada: Sigoginsu da Yanaye-Yanayensu” Kundin Digiri na uku Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeirya, Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano. Benchmark Publisher.

Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Benchmark Publishers Limited.

Shinkafi, R.H. (2012). Garba Maitandu Shinkafi da Waƙoƙinsa. Kundin Digirin na Biyu Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo


Waka

Post a Comment

0 Comments