Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummawar Habaici Ga Gyara Halaye Da Dabi’un ‘Yan Siyasa: Tsokaci Daga Wasu Wakokin Siyasa

Citation: Dangulbi, A.R. (2024). Gudummawar Habaici ga Gyara Halaye da Dabi’un ‘Yan Siyasa: Tsokaci Daga Wasu Waƙoƙin Siyasa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 448-457. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.056.

GUDUMMAWAR HABAICI GA GYARA HALAYE DA ƊABI’UN ‘YAN SIYASA: TSOKACI DAGA WASU WAƘOƘIN SIYASA

Aliyu Rabi’u Dangulbi

Jami’ar Gwamnatin Tarayya Gusau

Tsakure: Shugabanci wani jagoranci ne na jama’a na kowane nau’i, wato na gargajiya da na siyasa. Wannan muƙala mai take gudummawar habaici ga gyara halayen ‘yan siyasa : Tsokaci kan wasu waƙoƙin siyasa.Manufar wannan muƙalar ita ce ta tattauna kan miyagun ɗabi’un ‘yan siyasa na rashin cika alƙawari da yaudarar alumma da ƙarya da ha’inci da zalunci da rashin adalci da sauransu. Shugabanci abu ne mai buƙatar mutane masu gaskiya da riƙon amana da sauran kyawawan ɗabi’u waɗanda za su taimaka a sami mulkin adalci a cikin al’umma. Zaman lafiya da cigaban tattalin arzikn ƙasa ba su samuwar sai shugabanni sun yi adalci a mulkinsu.Makaɗa da mawaƙan Hausa musamman na siyasa suna amfani da habaici a cikin waƙoƙinsu, domin su jawo hankalin al’umma su gyara miyagun ɗabi’unsu kafin su shigo neman muƙami a siyasa.Zaɓen mutane nagari masu gaskiya da riƙon amana da cika alƙawari shi ke kawo cigaban ƙasa.. Habaici wani salo ne na isar da saƙo ga al’umma ta hanyar yi wa ‘yan siyasa gargaɗi da haska masu fitila domin su gyara kurakuransu da ɗabi’unsu, muddin suna son a zaɓe su, su wakilci al’ummarsu a gwamnatin farar hula.Wannan maƙala za ta mai da hankali ne ga nazarin rawar da habaici yake takawa wajen gyara miyagun halaye da ɗabi’un ‘yan siyasa, waɗanda suka dabaibaye siyasar zamani, suka hana ci gaba a Nijeriya. Amfani da habaici da mawaƙa irin su Aminu Alan Waƙa da Ibrahim Yala da Dauda Kahutu Rarara da sauransu suka yi a cikin waƙoƙinsu ya taimaka wa ‘yan siyasa wajen gyara ɗabi’u da halayensu kafin su shiga fafatakar neman kowane irin muƙami a siyasa. An ɗora wannan bincike bisa ra’in makisanci, wanda ya nuna cewa ya kamata adabi ya kasance makami na siyasa, kuma makamin gabatar da ci gaba. Sannan adabi ya bayyana fasaha da muryar talakawa, wato ya kasance bangare na siyasa, (Lenin 1905).

Fitilun Kalmomi: Habaici, Gyara Halaye, Dabi’u, ‘Yan Siyasa, Waƙoƙin Siyasa

Gabatarwa

Kamar yadda aka sani cewa, ‘yan siyasa suna amfani da mawaƙan Hausa na siyasa su rera masu waƙoƙi domin su sami damar isar da saƙon manufofinsu da na jam’iyyunsu daban daban ga al’umma.Wannan muƙala mai take, ‘Gudummawar habaici ga gyara halaye da ɗabi’un ‘yan siyasa: Tsokaci kan wasu waƙoƙin siyasa, za ta bayyana irin gudummawar da habaici ke bayarwa wajen kyautata halaye da ɗabi’un ‘yan siyasa ta hanyar amfani da habaici a cikin waƙoƙinsu. Waƙoƙin siyasa waƙoƙi ne da mawaƙan siyasa na zamani ke amfani da su wajen tallata jamiyyu da ‘yan takara domin su sami karɓuwa ga al’umma. Saboda haka, habaici wani jigo ne mai muhimmanci a cikin waƙoƙin siyasa da ake amfani da shi domin a jawo hankalin jamaa su fahimci saƙon da ake son isar wa gare su.Ɗangambo (1984:) ya nuna cewa, habaici wani ɓaci ne a fakaice ta hanyar amfani da karin magana ko kalmomin shaguɓe da yi wa wanda ake yi wa habaici hannunka-mai- sanda ko gugar zana dangane da wasu ɗabi’u ko halaye masu kyau ko marasa kyau, da wasu ‘yan siyasa suke aikatawa.Wannan maƙala za ta mai da hankali ga ɗabi’un ‘yan siyasa marasa kyau da suka haɗa da, yaudara da ƙarya da hainci da zalunci da rashin adalci da kuma rashin cika alƙawari. Mawaƙan siyasa suna amfani da habaici domin su yi masu gargaɗi su gyara ɗabi’unsu ta yadda za su sami karɓuwa ga al’umma.

Burin kowane ɗan siyasa ya sami karɓuwa ga mafi rinjayen jama’a masu jefa ƙuria domin ya samu nasarar lashe zaɓe da ake gudanarwa a lokuta daban daban. Wannan takarda za ta nazarci yadda habaici yake da tasirinsa ga gyara ɗabi’un ‘yan siyasa da kuma wayar wa mutane kai su zaɓi shugabanni nagari waɗanda za su taimaka siyasa ta tsayu da ƙafafunta. Saboda haka ƙudurin wannan muƙala shi ne,nazarin gudummawar da habaici ke bayarwa wajen tallata kyawawan ɗabi’un ‘yan takara domin su sami karɓuwa ga al’umma kafin a tsayar da su takarar kowane muƙami na siyasa. Habaici yana taka rawa wajen jawo hankalin jama’a su aminta da ɗan takara nagari,da faɗakar da al’umma su fahimci kyawawan manufofin kowace jam’iyya kafin su yarda da ita su zaɓe ta a zaɓuɓɓuka daban daban. Mawaƙan siyasa suna faɗakar da ‘yan siyasa ta hanyar amfani da habaici su fahimci cewa kyawawan ɗabi’u su ne gimshiƙin samun ɗaukaka a fagen kowane lamari na rayuwar yau da kullum, musamman cikin lamurran siyasa. Haka kuma habaici yana gargaɗin ‘yan siyasa da su daina yaudarar al’umma da ƙarya da hainci da ɗaukar alƙawurran ƙarya da sauransu, a lokacin da suka zo neman amincewar jamaa su yarda da su, da kuma jam’iyyunsu.

1.3 Habaici

Habaici wata magana ce taƙaitata da ake furtawa zuwa ga wani mutum ko wasu mutane a matsayin gargaɗi ko hannunka- mai- sanda ko shaguɓe, domin wanda aka yi wa ya ji, ya gyara munanan halayensa da ɗabi’unsa da ake zarginsa da su. Masana da manazarta daban daban sun yi bayanai dangane da ma’anar habaici. Bargery (1934:), da Dangambo (1984:), da Dangulbi (1996:), da Garba (1990:),duka sun bayyana cewa, habaici wata ɓoyayyar magana ce da ake furtawa ‘yar gajeruwa a kan wani mutum da nufin isar da saƙo gare shi domin ya gyara ɗabi’unsa.

Malumfashi da wasu (2014: ), sun bayyana habaici da cewa, ‘nuna ƙaunar abu ɗaya daga cikin abubuwa biyu ko fiye da haka ya faru a lokaci ɗaya’, to sai kalaman habaici su riƙa giccewa a tsakanin mutanen. Wato, bisa ga al’ada irin ta ɗan adam ba ya son ya haɗa, ko ya yi tarayya da wani a kan abu ɗaya. Dalilin haka ya sa Bahaushe yake jifar abokan hamyyarsa ko ‘yan adawa da habaici domin ya nuna rashin amincewarsa ga tarayya a kan abin da yake so da wani mutum. Umar (1987: ), ya ta’allƙa habaici ga kishin da mata ke yi da juna idan suka haɗa miji ɗaya. Koko (1989: ), ta bayyana cewa, ‘’habaici magana ce ta nuna tsoro da ake furtawa cikin sifar arashi ko takalar magana a fakaice’’, wadda mata suka fi yin haka a tsakaninsu. A taƙaice habaici wani salo ne ko dabarar isar da saƙo da mawaƙa ke amfani da shi domin su isar da saƙon faɗakarwa ko gargaɗi ga ‘yan siyasa da sauran jama’a baki ɗaya cikin raha da nishaɗi domin su gyara ɗabi’unsu kafin su nemi wani matsayi na siyasa. Wato, habaici magana ce ko dabarar jawo hankalin al’umma su fahimci saƙon da ake son isarwa gare su. Mawaƙan sarauta suna amfani da habaici domin su soki ko musguna wa yanyan sarauta da abokan hamayyar sarki. Haka a fagen siyasa, mawaƙan siyasa suna amfani da habaici su gargaɗi ‘yan siyasa su gyara ɗabi’unsu, su zamanagari domin su samu karɓuwa ga al’umma baki ɗaya.

1.4 Gudummawar habaici ga gyara ɗabi’un ‘yan siyasa

Habaici yana taka muhimmiyar rawa wajen kyautata ɗabi’un ‘yan siyasa ta fuskar faɗakar da su game da illar da rashin ɗabi’u managarta ke haifarwa a cikin al’ummarsu. Da yawa ‘yan siyasa suna ganin cewa, kowane irin yanayi ka kasance, mutane ba zu kyamace ka ba,matuƙar kana ba da kuɗi. To, amma abin ba haka yake ba ga al’ummar da ke son cigaba ta hanyar samun shugabanni nagari masu gaskiya da riƙon amana.Misali; Murtala Mamsa Jos a cikin waƙarsa ta A.P.C. Sabuwa ta zo,yana cewa:

Kun ji wancan ma babban cikinsu ya ce da tasun ba ta da tarbiya

Su da kansu suke furucin haka ba ta zuwa na zauna lafiya.

(Murtala Mamsa: Waƙar A.P.C., Sabuwa ta zo).

A wannan zamani na siyasa, yaudara da ƙarya da hainci da zalunci da rashin adalci da rashin cika alƙawari, sun yi wa zukatan yan siyasa katutu. Saboda rashin sanin muhammancin riƙon amana a shugabanci ya sa, ‘yan siyasa suke amfani da damarsu wajen yaudarar al’ummarsu da sunan suna neman amincewarsu su zaɓe su. Don haka, za a yi bayani dalla-dalla game da waɗannan miyagun ɗabi’u da ‘yan siyasa suka ɗauka ba komi ba, amma kuma su ne muhimman abubuwa da ke tabbatar da nagartarsu a idon al’umma kafin a amince masu su wakilci jama’a. Ga abubuwan kamar haka: Rashin cika alƙawari, da yaudara, da ƙarya da hainci da zalunci ko zamba da kuma rashin adalci.Misali, Ibrahim Yala yana cewa:

Ita gaskiya dokin ƙarfe ce,

Hawanta ba kowa ke ba,

Gaskiya rigar- ƙarfe ce,

Saka ta ba kowa zai ba,

Duniya ta yarda Janar,

 ya sa rigar ba zai tuɓe ba.

(Ibrahim Yala:Waƙar A.P.C. 2015).

Ƙa’ida ce ta kowace jam’iyya ta tabatar ta tantance kowane ɗan takara kafin a tsayar da shi takara. Dole mutum ya kasance mai gaskiya da riƙon amana da kirki da haƙuri da son mutane (faraa) kafin ya nemi amincewar jamaa su zaɓe shi ga kowane irin muƙami na siyasa. A samu mutum mai irin waɗannan ɗabi’u shi ne ya fi cancanta ya jagoranci jama’a a siyasance. Mawaƙan siyasa irin su Ibrahim Yala Hayin banki wanda ya yi waƙar A yi gangami a ceci ƙasar nan ya tabbatar da haka awa ɗiyan waƙar da suka gabata a sama. Dauda Kahutu Rarara,wanda ya yi waƙar masu gudu su gudu ya yi wa ɓarayin Nijeriya habaici yana gargaɗin su da su bar ƙasar tun kafin Buhari ya waiwayo kansu.Yana cewa:

Ku gaya wa ɓarayin can su gudu,

Ko way yi sake Janar ya rutsa.

(Dauda Rarara: Masu gudu su gudu A.P.C.).

Sata ga shugabanni da manyan ma’aikatan gwamnati ta zama abir ƙawa a Nijeriya.Saboda haka mutane ke ta gaggawar su tsaya takarar kujerar shugabanci tun daga sama har ƙasa, wato, tun daga kujerar shugaban ƙasa da yan majalisun tarayya da na jihohi har zuwa ga kujerar kansila. Mafi yawan yan siyasa suna neman muƙami ne ba don su yi wa jamaar da suka zaɓe su aiki ba, a’a sai dai don abin da za su samu.Wannan dalili ne ya sa aka samu yawan sace-sacen dukiyar ƙasa ga masu mulki da masu riƙe da muƙaman gwamnati daban daban. Sata tana daga cikin manyan miyagun ɗabi’u da al’umma take ƙyama, saboda haka ya sa mawaƙan siyasa suke amfani da habaici doin su faɗakar da mutane su lura da duk wanda zai yi takarar muƙamin siyasa ya kasance mai gaskiya da riƙon amana ne. Idan aka samu irin waɗannan mutane, to, za a iya samun shugabanni nagari su gudanar da mulkin ƙasa cikin adalci. Mawƙin ya tsoratar da masu aƙidar satar kuɗin gwamnati don su ɗau taitayinsu domin Buhari ba zai lamunta da ɓarayi ba. Shi ya sa Duda Rarara ya yi masu habaici cewa, ‘Ku gaya wa ɓarayin can su gudu’.

Shi kuma Aminu Alan waƙa da waƙarsa baƙar malfa baƙar jarfa mai shanye jinin jikin talaka mawaƙin yana cewa:

An zaɓu ruba-ruba namu

Da sunan wai wakiltarka

A ba su kuɗi su miƙa mu

Hannu ƙwarya hannu baka

Tunanensu iyalansu

Su tara abin da ba tamka.

(Aminu Alan waƙa A.P.C.)

Mawaƙan siyasa da dama sukan yi amfani da basirarsu ta hanyar amfani da habaici wajen jawo hankalin mutane da su lura da mutane masu kyawawan ɗabi’u kafin su zaɓe su. Yin haka zai sa a sami managartan shugabanni da za su yi wa talakawa adalci,wanda shi ne tushen samun zaman lafiya da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma tsaro. Domin rashin adalci shi ke haifar da rashin aikin yi ga al’umma har su faɗa cikin tunanin yadda za su fitar da kansu cikin mawuyacin halin da suke ciki na yunwa da fatara da rashin tsaro. Mawaƙa da dama sun yi amfani da habaici domin su faɗakar da kuma gargaɗin ‘yan siyasa su gyara ɗabi’unsu kafin su nemi goyon bayan al’umma su zaɓe su. Misali,a fannin rashin adalci, mawaƙa daban daban sun tofa albarkacin bakinsu a kan illar rashin adalci ga shugabanni kamar yadda misalai da suka gabata suka nuna.

1.4.1 Rashin Adalci

Kamar yadda aka sani, ‘yan siyasa sukan yi wa talakawa alƙawurra da dama a lokacin da suke fafutukar yaƙin neman a zaɓe su, su kafa gwamnati. Daga cikin alƙawurran akwai tabbatar da cewa za su yi adalci tsakani mutanensu. Adalci shi ne tsare gaskiya da tsoron Allah ga aiwatar da al’amurran jagorancin jama’a (Bargery,1934:4),da (AL-Mallah,2011:180),sun bayyana cewa ‘’adalci yana nufin baiwa kowane ɗan ƙasa haƙƙinsa daidai da kowa ba tare da nuna bambancin ƙabila ko addini ko ɓangaranci ba’’, musamman a fannin rabon arziki da samar da ababen more rayuwa da samar da ayyukan yi ga ‘yan ƙasa, kuma duka ga ɗan jam’iyyarsu da ɗan jam’iyar adawa. Saboda haka, rashin adalci ne, a sami shugabanni ko masu mulki su nuna son kai, ko bambancin ƙabila ko ɓangaranci wajen rabon arzikin ƙasa ko muƙaman gwamnati. Idris (2016:183), ya ce, rashin adalci wata sifa ce, ta rashin gaskiya.Wato, rashin adalci shi ne rashin adana wani abu ko wulaƙantar da shi ko kuma amfani da abu fiye da kima. Masana da malaman falsafa sun bayyana cewa rashin daidaito wanda yake kishiyar daidaito ne, da ya danganta daga al’ada zuwa al’ada. A wannan marra ta siyasar zamani, za a samu ‘yan siyasa suna nuna rashin adalci a fili, musamman wajen fifita ɗan ɓangarensu ko ɗan jam’iyarsu ko kuma addininsu.Wato rashin adalci ne a ba da wani abu ko a ɗora wani abu ga bagiren da bai dace da shi ba.Misali, da zarar ‘yan siyasa suka ɗare kujerar mulki, sai giyar mulki ta fara bugun su, su fara nuna rashin adalci a tsakanin al’umma. Duk wani matsayi na gwamnati ba a ɗora wanda ya dace, idan ba ɗan jam’iyarsu ba, ko da ya fi kowa cancanta. A nan rashin adalci sai ya fara haifar da rashin zaman lafiya da ayyukan ta’addanci a cikin al’umma. A wannan bagire ne mawaƙan siyasa suke amfani da habaici domin su jawo hankalin shugabanni ko yan siyasa su tuna da alƙawurran da suka ɗauka na yin gaskiya da adalci a tsakanin al’ummarsu, kowace jam’iyya sake yi, kuma kowane bangare ko addin suka fito ko suke bi. Misali, Aminu Abubakar Alan waƙa yana cewa:

Mulki daga al’umma ake

Cikin zaɓe na son ranka

Ana yi don mutane ne

Misalin ba ka ‘yancinka

(Alan waƙa: Waƙar A.P.C.)

Mawaƙin ya nuna illar da ke akwai ga rashin adalci da shugabanni ke yi a lokacin da aka zaɓe su bisa mulki. Saboda haka sai mawaƙin ya yi amfani da habaici don ya gargaɗi duk mutumen da ke neman a zaɓe shi a kowane muƙami na siyasa, to ya gyara ɗabi’unsa kafin ya fito takara.Wato, rashin adalci kan sa mutane su rasa samun ‘yancinsu daga azzalumai mayaudara, maƙaryatan shugabanni marasa tausayi da taushe haƙƙin talakawa a lokacin da suke mulki.

Shi kuma Yusuf Fasaha ya nuna cewa rashin adalcin shugabannin jam’iyyar P.D.P. mai mulkin ƙasa kusan tsawon shekaru goma sha shidda da suka yi kan mulki sun kasa bai wa talakawa haƙƙin da ya dace su ba su. Wannan ba ƙaramin rashin adalci ba ne shugabanni su tauye wa talakawa haƙƙinsu. Misali Yusuf yana cewa:

Tuni mu kan mun ƙara hankali,

Mahaukata ba sa yaudare mu ba.

(Yusuf Fasaha: Mu bi A.P.C. al’ummar ƙasa).

Yaudara wata ɗabi’a ce ta rashin adalci da shugabanni ke yi wa talakawa, wato su laɓe ga wasu kyawawan ɗabi’u da ba nasu ba domin talakaw su yarda da su. Idan suka hau kujerar mulki saisu koma ga ɗabi’unsu na ainihi. Saboda rashin adalcin shugabanni na tauye wa talakawa haƙƙinsu na arzikin ƙasa ya sa talakawa suka shiga wani mawuyacin hali na talauci da rashin abinci da rashin zuwa makaranta ga ‘ya’yansu. Saboda haka mawaƙan siyasa suke gargaɗin talakawa da su kula da halayen duk wanda ya tsaya takarar kujerar siyasa kafin su zaɓe shi, to su tabbatar da shi mutum ne mai kyawawan ɗabi’u da riƙon amana.

Waɗannan mawaƙan da aka kawo misalai daga waƙoƙinsu, sun yi amfani da habaici a matsayin wata dabara ta jawo hankalin ‘yan siyasa su fahimci irin illolin da miyagun ɗabi’u ke haifarwa na rashin adalci a shugabanci. Saboda haka, a nan mawaƙan siyasa suna amfani da habaici domin su gargaɗi ‘yan siyasa da su kasance masu kyawawan halaye da ɗabi’u managarta domin su kasance shugabanni masu adalci a mulkinsu; saboda a sami zaman lafiya da walwala a tsakanin talakawa da masu mulki.

1.4.2 Yaudara                                     

Yaudara ita ce mutum ya faɗi abin da ba zai aiwatar ba cikin sigar amfani da kalmomin jawo hankalin masu saurarensa. Wasu suna amfani da addini wajen neman ra’ayin al’umma alhali, ba da gaske yake yi ba.Yana amfani da addini domin ya sa mutane masu imani su yarda da shi bisa ga abun da na gaskiya ba. Bargery (1934:1112),ya bayyana yaudara kamar haka(Decieve or trick) wato, faɗar wani abu da ba shi ake nufi ba, ko haƙa wa wani tarko don ya faɗa. Wato yaudara tana nufin bayyana kyawon abu ga jama’a don su so shi, amma a baɗini mummuna ne.‘Yan siyasar wannan zamani suna yaudarar jama’a ta hanyar yin amfani da kalmomin addini, ko kuma wani matsayi ko dukiya da suka mallaka su nuna wa mutane za su amfanar da su da ita domin su jawo hankalin magoya bayansu su amince su zaɓe su a muƙamin siyasa ko wani matsayi na daban. Wato, suna amfani da addini idan suka buƙaci a amince da su, a zaɓe su su jagoranci al’umma. A duk lokacin da suka je yakin neman zaɓe, za su riƙa amfani da addini ta hanyar kawo ayoyin Alƙurani ko Hadisai domin su nuna wa mutane su masu gaskiya ko tsoron Allah ne; alhali abin da suka faɗa iyakarsa a bakunansu bai kai a cikin zukatansu ba. Mafi yawan lokuta sukan ɗauki alƙawurra da cewa, idan aka zaɓe su, za su yi wa talakawa ayyukan raya ƙasa da tallafa wa matasa su sami aikin yi ko, su tallafa masu da jari su bunƙasa kasuwancinsu.Aminu Abubakar Alan waƙa yana cewa:

Ruɓaɓɓu a cikin namu,

Suna kuma ci da bautarka,

Suna inuwa ta addini,

Suna cutar da bayinka.

(Alan waƙa: Allah kaɗa guguwar sauyi A.P.C.).

‘Yan siyasa suka yaudari al’umma ta hanyar kawo wa mutane Allah kusa da su domin su yaudare su a lokacin da suke zagayen neman goyan bayansu. Mawaƙin ya sifanta irin mayaudaran yan siyasa da cewa, ruɓaɓɓu ne, wato mutane ne da aka jaraba su aka ga irin tasu rawa dangane da alƙawurran da suka dauka kuma suka kasa cikawa.Saboda haka sai mawaƙin ya kira su da ruɓaɓɓu domin ya hankaltar da jama’a su gane cewa kuskure ne su sake zaɓen waɗannan mutane a zaɓemai zuwa.A layi na biyu ya bayyana wa mutane irin ɗabi’un wasu ‘yan siyasa na ci da addini, wato su shiga inuwar addini su yaudari mutane don su zaɓe su. Mawaƙin ya nuna cewa, waɗannan ‘yan siyasa ba komi suke so ba illa su ga sun jawo ra’ayin jama’a su amince wa zaɓen su amatsayin shugabanni. Da zarar an zaɓe su sai su yi ta cutar jama’ar da suka zaɓe su ta hanyar danne masu haƙƙinsu da kuma wawure dukiyar ƙasa su mallaka wa kawunansu.Irin wannan ɗabi’a ta yaudara da addini ita ce mawaƙan siyasa suke jifar masu ita da habaici domin su faɗakar da al’umma su ƙaurace wa zaɓen irinsu domin a sami mulkin gaskiya da adalci. Sannan a bangaren ‘yan siyasa mawaƙan suna gargaɗin su da su gyara ɗabi’unsu matuƙar suna son jamaa su yarda da su, su ba su goyon baya ɗari-bisa ɗari.

Haka kuma ɗauki alƙawurran ƙarya da yan siyasa ke yi yana daga cikin halaye na yaudar al’umma, cewa, idan sun kafa gwamnati, za su kula da lafiyar al’umma da samar da tsaro da kare mutumcinsu da dukiyoyinsu daga kowace irin barazana ta ‘yan zauna- gari-banza. Suna rantsuwa da Allah domin su jawo hankalin mutane su amince da su bisa ga manufar yaudarar talakawa, amma ba da gaske suke yi ba. Dangane da wannan ɗabi’a ta yaudarar da ‘yan siyasa suke yi wa talakawa a lokacin da suka je yaƙin neman a zaɓe su. Mawaƙan siyasa sukan yi amfani da wannan dama su riƙa amfani da habaici domin su gargaɗi ‘yan siyasa su san cewa jama’a sun gaji da gafara sa- ba su ga ƙaho ba. Saboda haka idan suna son buƙatunsu su biya a zaɓe su, to su gyara halayensu, su daina yaudarar al’umma da inuwar addini.Ibrahim Yala yana cewa:

Sai ƙarya kuke da addini mayaudara,

Da kun shiga jama’a ku rinƙa faɗin kabbara,

Bayan zuciyarku kun sa ta ta guttsura,

Ba kwa tausayin talaka Nijeriya.

(Yala hayin banki: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

Wannan mawaƙin ya bayyana ɗabi’un ‘yan siyasar Nijeriya a fili, musamman masu amfani da ayoyin Alƙurani da Hadisai suna yaudarar mutane domin a amince masu. Wato, sukan faɗi abin da ba shi ne a zukatansu ba domin talakawa su su yarda da su cewa, su masu gaskiya ne.Yin amfani da ayoyin alƙurani da hadisan manzon Allah ya zama wani salo da yan siyasar wannan zamani suke amfani da shi domin su yaudari alumma su amince masu. Allah (s.w.a.),ya yi kakkausar suka da hani ga masu amfani da addini suna faɗar abin da ba su aikatawa. Kuma laifi ne babba mutum ya faɗi abin da bai aikatawa kamar yadda ya zo a cikin Alƙurani mai girma inda Allah yake cewa: ‘’Ya ku waɗanda suka yi imani! Don me kuke faɗin abin da ba ku aikatawa? ‘’ Ya girma ga zama abin ƙyama a wurin Allah, ku faɗi abin da ba ku aikatawa’’.( (Ƙ61:2-3).

Mawaƙin ya faɗakar da ‘yan siyasa cewa, a halin yanzu al’ummar da suke yaudara sun gano yaudarar da suke yi masu. Saboda haka, lokaci ya yi da ‘yan siyasa za su dawo daga rakiyar amfani da addini suna yaudarar talakawa don su zaɓe su. Wato, yaudara da addini da nuna matsayi don a jawo ra’ayin mutane wata dabara ce da ‘yan siyasa suke amfani da ita don su sami goyon bayan talakawa.Yawancin musulminmu ‘yan siyasar arewa, su suka fi amfani da matsayi ko addini suna yaudarar mutane, alhali abin da suke faɗa ba gaskiya ba ne.Haka abin yake ga wasu mutane masu addinai daban da na Musulunci sun fake wa da addininsu na kiristanci suna yaudarar ‘yan siyasa domin su nemi goyon bayansu. Duk abin da suka faɗa yaudara ce kawai don su jawo hankalin talakawa su aminta da su. Saboda haka duk ‘yan siyasar da ke irin waɗannan ɗabi’u su daina su gyara halayensu kafin su nemi jama’a su zaɓe su a muƙaman siyasa daban daban.

1.4.3 Ha’inci

Ha’inci na nufin tauye wata dama da aka bai wa wani mutum da shugabanni ko waɗanda aka ɗora masu alhakin kula da mutane suke yi.Saboda haka danne haƙƙoƙan jama’a ko neman wani abun amfani ga mutane ta hanyar amfani da matsayi na siyasa ko muƙamin gargajiya kafin a ba shi wani abu ko yi masa. shi ne ake nufi da ha’inci.Wato,a gudanar da mu’amula cikin sifar aminci, amma a cuci wanda ake mu’amular da shi, ko shugabanni su cuci hukumar da ta ba su nauyin gudanar da al’amurran jama’a. Ƙamusun Hausa (2016: ), ya nuna cewa, ‘’Ha’inci’,yaudara ce da ta shafi kowane fanni na rayuwar zamantakewar ɗan adam ta yau da kullum. Wato, wannan bayani yana da alaƙa da bayanan da ke nuna cewa, cin hanci da rashawa da shugabanni ko ‘yan siyasa ke karɓa kafin su bai wa wani aiki, shi ma ha’inci ne. Idan aka duba za a fahimci cewa matsalar ha’inci ta watsu cikin kowane fanni na rayuwar ‘yan siyasar Nijeriya tun daga ma’amalar yau da kullum tsakanin al’umma har zuwa ga abin da ya shafi kasuwanci da kuma fannin ayyukan hukuma.Irin wannan ha’inci ya bazu makarantu da tashoshin mota da ofisoshin ma’aikatu da asibitoci da sauran wuraren mu’amalar jama’a. Hakan ya nuna mana cewa, ha’inci yana faruwa a kowane fanni na rayuwar al’umma, sai dai ya fi ƙarfi ga ‘yan siyasa inda suke ba da cin hanci ga talakawa domin a zaɓe su. A fannin kasuwanci akan sami ‘yan kasuwa su riƙa cakuɗa abu mai kyau da maras kyau domin abinsu ya yi afki. Haka kuma tauye ma’auni ko sikeli a wajen kayan da ake aunawa shi ma ha’inci ne. Ya zo a cikin Hadisan Manzon Allah (S.A.W.), cewa Sayyidina Umar (R.A) kullum ba ya cin abincin dare sai an yi yekuwa a Madina ko akwai wanda bai ci abinci ba. Da aka tambaye shi dalilin haka, sai ya ce, ‘don kada Allah ya tambaye shi a ranar hisabi cewa, yaya an ba shi kiwon mutane, amma ya bar ɗaya da yunwa, shi ko ya kwana a ƙoshe? Haka kuma yakan ce, ‘Wallahi in raƙumi ya mutu da ƙishirwa ko ya faɗa rame, ya yi rauni a ƙasar Islama, ni ne da alhaki’. Irin wannan koyarwa ce ta musulunci ya kamata ‘yan siyasa su koya domin kauce wa mulki cikin ha’inci.

Idan ‘yan siyasa ko ‘yan takara suka yi amfani da kuɗi kafin a zaɓe su, wanan ha’inci ne. Idan har ɗan takara ya cancanta ga muƙamin da yake nema, babu buƙatar ya ba da cin hanci ga talakawa. Yin haka, zai ba da dama a zaɓi ruɓaɓɓun mutane waɗanda za su ha’inc al’umma ga dukiyar ƙasa da aka ba su amana. Misali, Ibrahim Yala yana cewa:

Ka zo ka fitar da mu a ƙuncin damuke ciki,

Yau mun sha wuya a kullum sai farmaki,

Ana satar kuɗinmu a yau ba shamaki,

Ka ji halin da mu muke ciki Nijeriya.

Tanko da Babalola suna ta halin tsiya,

Mu da kuɗinmu gashi duk an muna murɗiya,

Shi yassa muke biɗar yau mai gaskiya,

Wanda idan ya zo za ya gyara Nijeriya.

(Yala: waƙar A.P.P 2003).

Dangane da wawure dukiyar al’umma da shugabanni ke yi saboda ha’inci, Ibrahim Yala ya yi wa wasu ‘yan siyasa da ke mulkin ƙasa da habaici domin ya faɗakar da su su gyara ɗabi’unsu. Ya ambaci sunayen wasu mutane da ya kira da ‘Tanko da Babalola’ ya ce su ne suka sace kuɗinsu kuma suna ta halin tsiya,wato rashin adalci da ha’intar dukiyoyin al’ummar Nijeriya domin su arzita kansu da wanda suke so.Ya yi kira ga Muhammadu Buhari ta hanyar faɗa masa halin da ‘yan Nijeriya suke ciki saboda ha’intar su da shugabannin P.DP. suka yi na satar dukiyar al’umma ba tare da wani shamaki ba saboda ƙarfin iko da suke da shi suna kaiwa ƙasashen ƙetare sun ɓoyewa. Wannan ba ƙaramin hainci ba ne ga waɗanda aka bai wa amanar dukiyar al’umma, maimakon su yi abin da zai amfani talakawa, sai suna sace kuɗin don amfanin kansu. Mawaƙin ya ci gaba da yi masu habaici yana cewa:

Ku da kuke ta sukan Buhari uban ƙasa,

Ku ne kun ka kwashe Fetur da kuɗin ƙasa,

Don tsabar rashin mutuncinku cikin ƙasa,

Har ma dukiyar marayu kun murɗiya.

(Ibrahim Yala: Waƙar A.P.P)

A nan mawaƙin ya kawo kalmar lamirin ‘ku’ don ya yi wa waɗanda ake magana da su habaici dangane da ha’incin da suke yi na sace dukiyar ƙasa, amma sai sukar Buhari suke yi domin su hana talakawa su goya masa baya a zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

1.4.4 Zalunci

Zalunci yana nufin danne wa mai haƙƙi haƙƙinsa ta hanyan amfani da ƙarfin iko, ko ƙarfin cin tuwo.Bargery (1934), ya bayyana cewa, zalunci wani abu ne da ke gudana a tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka ta hanyar danne haƙƙin marasa ƙarfi, ko dukiyar ƙasa da ƙarfin iko. Bayani ya gabata cewa, matuƙar masu mulki suka kasa bai wa talakawa haƙƙoƙansu da suka rataya a wuyansu, to zalunci ya shiga ke nan a tsakaninsu. Domin rashin riƙe amana da gaskiya ga amanar da aka ɗora a kan shugabanni shi ne zalunci. Wato, idan shugabanni suka kasa riƙe amanar dukiyar da aka ɗora masu amana, sai suka mayar da ita mallakar kansu, to yin haka ya zama zalunci. A dalilin zalunci da ‘yan siyasa suke tafkawa ya sa al’amurran siyasa suka canja. Rikicin siyasa da ta’addanci da bangar siyasa da sara-suka da sauran miyagun ɗabi’u da suka saɓa wa aladar ‘yan Nijeriya suna faruwa ne a dalilin zaluncin da shugabannin siyasa suka haifar. Mawaƙan siyasa sun ba da gagarumar gudummawa wajen faɗakar da ‘yan siyasa da sauran mutane game da illar zalunci da shugabanni ke yi a lokacin da aka zaɓe su a muƙamai na siyasa daban daban. Misali, Ibrahim Yala, a cikin waƙarsa da ya yi wa jam’iyyar APP, mawaƙin ya yi wa masu mulkin ƙasa na jam’iyyar PDP habaici, inda ya nuna cewa saboda zaluncin da suka tafka na wawure dukiyar ƙasa ya sa suka shiga cikin halin damuwa da yunwa da talauci da uwa uba rashin tsaro. Don haka mawaƙin yake kiran Muhammadu Buhari ya zo ya ceci ‘yan Nijeriya daga mawuyacin halin da ‘ya’yan jam’iyya mai mulki ta jefa su ciki.Yana cewa:

Ka zo ka fitar da mu a ƙuncin da muke ciki,

Yau mun sha wuya a kullum sai farmaki,

Ana satar kuɗinmu a yau ba shamaki,

Ka ji halin da mu muke ciki Nijeriya.

(Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa a kan zaluncun da ‘yan siyasa suke tafkawa a lokacin da suka hau kujerar mulki. Alfazazi ya bayyana cewa shugabannin jam’iyya mai mulki sun zalunci al’umma ta hanyar sake dukiyar ƙasa. Wannan zalunci da suka yi, ya zama sanadiyar jefa talakawa cikin halin talauci da tsadar rayuwa da rashin aikin yi ga matasa. Mawaƙin yana cewa:

Jam’iyyar da ta ke mulkin ƙasar ta zame mana tarkon dattsiya,

In ta samu na kirki sai ta janye shi,sai ta sa ya sha wuya

Ta kama ƙasar ta maƙure za ta sa mu mu faɗa rijiya,

Jama’a ku fito mui gangami don mu ceci ƙasar Nijeriya.

(Alfazazi: Waƙar A.P.C.)

Babu ko shakka shugabanni da ‘yan siyasa suna amfani da damar da Allah ya ɗora masu ta shugabancin al’umma, su riƙa zaluntar mutane ta hanyar kwashe dukiyar ƙasa su mallaka wa kansu. Wannan zalunci ne babba inji Alfazazi, wanda ya jefa al’ummar ƙasa cikin mawuyacin halin da suke ciki na barace-barace da tallace- tallace a kan titunan ƙasar nan da sauran wuraren taron jama’a.Saboda haka, idan ana son a gyara waɗannan matsaloli, todole ne mutane su fito kwansu da kwarkwatarsu su jefa ƙuri’arsu ga mutumin da ake sa ran shi kaɗai zai iya ceto ƙasa daga mawuyacin halin ta faɗa.

1.4.5 Rashin cika alƙawari

Rashin cika alƙawari yana da cikin alamomin munafucci kamar yadda ya bayyana a hadisIn manzon Allah.(S.A.W.) a cikin Riyadhus salihina hadisi na 689, shafi na 87.Wato saɓa alƙawari yana daga cikin alamomin munafuki, wanda wannan ɗabi’a ta zama tsoka da jini a zukatan ‘yan siyasar zamani.Da wannan hadisi ne mutane suke kafa hujja cewa,siyasar Nijeriya ta kafu bisa ga tsarin munafucci, domin an ce alamar munafuki guda uku ce,idan ya yi magana ya yi ƙarya, idan an bashi amana sai yayi ha’inci idan kuma ya yi alƙawar ya saɓa.‘Yan siyasar Nijeriya sukan ɗauki alƙawurra da dama a lokacin da suke neman goyan bayan jama’a su zaɓe su. Bayan sun haye kujerar mulki, sai su manta da alƙawurran da suka yi wa talakawa.Wannan ɗabi’a ta ‘yan siyasar zamani ta haifar da abubuwa da dama na rashin tabbas ga samun mutane na kirki masu gaskiya da riƙon amana da cika alƙawari da za a dogara gare su. Saboda haka, sai mawaƙan siyasa suka riƙa amfani da habaici suna gargaɗin jama’a da su ƙaurace wa zaɓen mutanen da ba su da amana. Wasu mutane suna ganin idan aka yi wa shugabanni marasa cika alƙawari habaici, to kamar an tozartar da su ne a idon duniya. Abin ba haka yake ba, domin ga manufar yin amfani da habaici cikn waƙa yana nufin yi wa shugabanni hannunka-mai-sanda ne, ko faɗakar da su da tunatar da su dangane da alƙawurran da suka yi wa mutane domin su gyara kurakuransu. Ibrahim Yala hayin banki, yana cewa:

Su suka rusa ilimi yau Nijeriya,

Su suka ɓata tattalin yau Nijeriya,

Lantarki ƙasarmu yau yaz zama na iya

Allah ya isa macutan Nijeriya.

(Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

‘Yan siyasa sukan yi wa talakawa alƙawari idan suka shiga lungu da saƙo na garuruwan birane da ƙauyuka domin neman goyon bayan jamaa su zaɓe su. Misali za ka ji suna cewa, ‘‘ku zaɓe mu, idan muka kafa gwamnati za mu gina maku ɗakunan shan magani da magani kyauta ga maras lafiya don inganta kiyon lafiya a birane da karkara. Sannan su ɗauki alƙawurran samar da ingantaccen ilimi kyauta ga yayan talakawa da gina sabbin makarantu da gyara ajujuwa da kuma samar da wadataccen takin zamani don inganta noman damina da na rani. Haka kuma su ɗaki alƙawarin samar da wadataccen ruwan sha da samar da kyawawan hanyoyin sufari don sauƙaƙa zirga-zirgar jamaa da ɗaukar kayan amfanin gona zuwa kasuwanni da kuma gina rijiyoyin murtsatse a ƙauyuka’’. Rashin cika waɗannana alƙawurra ga talakawa da shugabnni da ‘yan siyasa ke yi, ba ƙaramar illa yake haifarw ba a siyasance. Saboda haka, sai mawaƙan siyasa su riƙa amfani da habaici domin su jawo hankalin yan siyasa ko masu mulki su gyara ɗabi’unsu na rashin cika alkawari domin a sami shugabanci nagari a ƙasa. Mawaƙin ya yi amfani da habaici domin ya jawo hankalin ‘yan Nijeriya su ƙaurace wa zaɓen mutane da ba su ciki alƙawurran da suka yi wa talakawa na samar da ilmi da sauran abubuwan more rayuwa da aka ambata a sama. Dangane da haka sai Dauda Rarara da yake tallata Muhammadu Buhari, yake kira ga al’ummar Nijeriya da su zo ga saƙo ya zo masu da shi na gina ƙasa da waɗancan masu mulki suka kasa cika masu alƙawurran da suka ɗauka. Mawaƙin yana cewa:

Al’ummar birni da ƙauyuka akwai wani ɗan saƙo,

Baba ya ce a gaya wa ɗan gari ko kuma baƙo,

Mui ta noma, kiyo, abinci ba zai yanke ba.

(Dauda Rarara: Damana gatan tsirrai).

Wasu mawaƙan siyaa sukan so su tallata ɗan takararsu ga jama’a,amma sai sun yi amfani da habaici don su soki shugabannin da ke bisa mulki.Wannan wata dabara ce ta jawo hankalin mutane domin su fahimci saƙon da ake son isarwa gare su. Saboda haka ne Rarara ya yi amfani da wannan salo domin ya faɗakar da ‘yan siyasa game kurakuran da suke tafkawa wajen zaɓen mutanen da ba su da alƙawari.

1.5 Kammalawa

Habaici a cikin waƙoƙin siyasa wani babban makami ne da mawaƙa ke amfani da shi wajen yaƙar duk ɗan siyasar da ba shi da ɗabi’u nagari. Wato, mawƙan siyasa suna amfani da habaici a matsayin wata dabarar yaƙi da miyagun mutane da ke fafatakar tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyun siyasa daban daban. Wannan yaƙin da mawakan siyasa ke yi ta hanyara amfani da habaici cikin waƙoƙinsu wata dabara ce ta jawo hankalin ‘yan sisasa da su kansu mutane ko talakawa su tsayar da hankalinsu su binciki ɗabi’un kowane ɗan takara kafin su yarda da shi ya wakilce su a muƙaman siyasa. Yin haka shi zai sa a kauce wa zaɓen ɓai-gurbin ‘yan siyasa marasa kishin ƙasa. Mawaƙan siyasa suna amfani da habaici cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin al’umma su zaɓi mutane nagari da za su wakilce su a muƙaman siyasa daban daban. Habaici wani salo ne na isar da saƙo ga al’umma ta hanyar yi wa ‘yan siyasa gargaɗi da faɗakar da su game da muhimmancin kyawawan ɗabi’u da ake buƙatar kowane ɗantakara ya kasance ya mallake su kafin ya nemi goyon bayan jama’a su zaɓe shi. Mawaƙan sukan jefi mutane da ba su da ɗabi’u nagari ta hanyar amfani da habaici domin su jawo hankalinsu, su gyara ɗabi’unsu, muddin suna son a zaɓe su, su wakilci al’ummarsu a gwamnatin farar hula.

 1.6 Sakamakon Bincike

 Waƙoƙin siyasa wasu hanyoyi ne da ake amfani da su wajen isar da sako cikin gaggawa ta hanyar yin amfani da dabarun jan hankalin masu saurare su fahimci abin da ake son su sani. Wannan bincike ya gano irin muhimmiyar gudummawar da habaici da mawaƙan siyasa ke amfani da shi cikin waƙoƙinsu yake bayarwa wajen gyara dabi’un ‘yan siyasar zamani domin a sami shugabanci nagari. Amfani da habaici cikin waƙoƙin siyasa ya taimaka wajen gyara ɗabi’u da halayen ‘yan siyasa kafin su shiga fafatakar neman a zaɓe su su wakilci al’umma a muƙaman siyasa. Haka kuma bincikien ya gano gudummawar da habaici yake bayarwa ga masu saurare wajen samar masu da nishaɗi da jawo hankalinsu su fahimci saƙon da ake isarwa gare su cikin sauƙi.Ta hanyar amfani da habaici cikin waƙoƙin siyasa ya sa ‘yan siyasa suke fahimtar cewa, shugabanci abu ne da ke buƙatar mutane nagari masu gaskiya da riƙon amana, don haka cilas ne su kasance nagari muddin suna son su zama shugabanni. Bugu da ƙari habaici ya taimaka wa ‘yan siyasa ta hanyar faɗakar da su cewa, duk mutumin da ba shi ɗabi’u nagari bai kamata a tsayar da shi takarar kowane muƙami ba a cikin siyasa. Saboda a tsayar da mutane marasa ɗab’u nagari a takara wata babbar hasara ce ga jam’iyyar da ta tsayar da su, domin sukan jawo wa jam’iyyar rashin samun cikakken goyon baya daga al’ummar ƙasa. Wannan dalili ne ya sa mawakan siyasa ke amfani da habaici cikin waƙoƙinsu domin su gargaɗi ‘yan siyasa da al’umma baki ɗaya, su yi amfani da basirarsu wajen tantance mutum kafin su amince ya shugabance su.

Habaici yana taimaka wa masu ra’ayin yin shugabanci su yi bincike mai zufi game da halayensu da yadda mutane suka ɗauke su. Hausawa suna cewa,’ idan ba ka san asalinka ba ,to ka shiga siyasa; yanzu za ka san wurin da ka fito, da kuma mene asalinka da ɗabi’unka. Wannan magana tana da tasiri wajen kyautata ɗabi’un duk mutumin da yake neman ya shiga siyasa har ya nemi a tsayar da shi wata takara ta kujerar siyasa. Daga ƙarshe, habaici ya ba da gagarumar gudummuwa ga bunƙasa da tsabtace harkokin siyasa, musamma wajen tallata mutane masu kyawawan ɗabi’u har jama’a su yarda da su. Ta hanyar amfani da habaici cikin waƙoƙin siyasa ya sa mawaƙan siyasa kan fito da hoton kowane ɗantakara a fili, har mutane su gamsu da irin ɗabi’unsa su zaɓe shi. Duk wanda ba shi da ɗabi’u nagari, kuma ya gano cewa, jama’a ba su ba shi goyon baya, sai ka ga ya gyara halayensa da ɗabi’unsa, ya zama mutumin kirki, mai gaskiya da riƙon amana da cika alƙawari. Haka kuma ya bar yaudara da ƙarya kafin ya nemi ya shiga harkokin siyasa.

Matsalar da ta tusgo a cikin harkokin siyasar Nijeriya ita ce, ta cin hanci da rashawa, wadda ta zama ƙarfen ƙafa ga cigaban siyasa mai ɗorewa a ƙasar nan. Wannan ɗabi’a ta ba da kuɗi kafin a zaɓi ɗan takara ta rushe duk wani tsari na aiwatar da shugabanci na gaskiya da riƙon amana. Ta hanyar ba da kuɗi da ‘yan siyasa suke yi, ya sa aka fara mantawa da cancantar ɗan takara matuƙar zai ba da kuɗi, to ya gama cin zaɓe. A halin yanzu duk ɗan siyasar da ba ya ba da kuɗi ga talakawa kafin a zaɓe shi, to ya zama ‘sorry’, wato ba zai sami biyan buƙata ba. Sai dai kuma yanzu talakawa sun fara sanin yancinsu domin ta hanyar amfani da habaici da mawaƙan siyasa ke yi ya kawo wani salo na a karɓi kuɗin ɗan siyasa, sannan a zaɓi wanda ya cancanta. Haka ya faru a zaɓen 2023, a wasu jihohi, inda talakawa suka amshi kuɗi kuma suka ƙi zaɓen waɗanda ba su cancanta ba. Ana iya cewa wannan dabara ta a amshi kuɗi a zaɓi wanda ya cancanta wani cigaba ne a salon siyasar Nijeriya.

Manazarta

AL-Mallah H. Y. (2011),The governmental system of the Prophet Muhammad. A comparative study in constitutional Law,Lebanon Dar AL-Ilmiyah.

Bargery, G.P.(1934), Hausa-English anda English-Hausa Vocabulary, London: Oxford University Press

Birniwa, H.A (2013) Waƙoƙin siyasa a matsayin Gishirin Siyasar zamani. Takardar da aka gabatar a Taron ƙasa kan Harshe ,Adabi, da Al’ada, Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano Jmi’ar Bayero,

Dangulbi, A.R.(2003),Siyasa A Nijeriya: Gudummawar marubuta waƙoƙin siyasa na Hausa ga kafa Dimokuraɗiyya a jamhuriya ta haɗu, zango na farko. Kundin Digiri na biyu, Sashen Harsunan Nijeriya, Sokoto; Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ɗangulbi A.R. (2013) ,Tasirin Habaici a cikin Waƙoƙin Siyasa:Nazarin waƙar Sarkin Yamman Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko ta Alhaji Ibrahim Aminu Ɗandago, Journal Of Language And Lisguistic Inquiry. Katsin, Federal College of Education.

Dangambo A. (1984), Rabe-raben Adabin Hausa da muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa. Kano, Triumph Publishing Company.be-rabensa

Gummi A. M. (19), Tarjamar Alƙurani mai girma

CNHN (2006) Ƙamusun Hausa, Kano, Jamiar Bayero.

Idris Y. (2016), Jigon Bijirewa a Rubutattun waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa 1903-2015. Kudin Digiri na uku,’Department of African Languages anda Cultures, Zaria. Ahmadu Bello University

Siyasa

Post a Comment

0 Comments