Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwatanta Tubalan Gina Turken Wakar Hauwa Maituwo Ta Mamman Shata Katsina Da Ta Tafada Mai Tuwo Ta Mamman Gawo Filinge

Citation: Gwammaja, K.Ɗ. (2024). Kwatanta Tubalan Gina Turken Waƙar ‘Hauwa Maituwo ta Mamman Shata Katsina da ta Tafada Mai Tuwo ta Mamman Gawo Filinge. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 406-414. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.051.

KWATANTA TUBALAN GINA TURKEN WAƘAR ‘HAUWA MAITUWO TA MAMMAN SHATA KATSINA DA TA TAFADA MAI TUWO TA MAMMAN GAWO FILINGE

Kamilu Ɗahiru Gwammaja

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano

Tsakure

Wannan bincike an aiwatar da shi a kan waƙoƙin fitattun mawaƙan Hausa guda biyu (Mamman Shata Katsina na Nijeriya da Mamman Gawo Filinge na Jamhuriyar Nijar). Waƙar Mamman Shata da aka nazarta ita ce “Waƙar Hauwa Mai Tuwo”, sannan ta Mamman Gawo ita ce “Waƙar Ta Fada Mai Tuwo”. An nazarci turakun waƙoƙin, ta hanyar kwatantawa da fitar da abubuwan da suke nuna turakun waƙoƙin iri ɗaya ne. An fitar da kwatancin zambo da habaici daga ɗiyan waƙoƙin, wanda ya nuna mawaƙan sun nuna gwaninta wajen iya samar da mabambantan waƙoƙi a kan masu sana’a iri ɗaya, kuma waƙoƙin su ɗau turke iri ɗaya. an gano mawaƙan gwanaye ne wajen ƙirƙirar waƙa mai jan hankali da isar da saƙo da ƙayatarwa.

Fitilun Kalmomi: Kwatance, Tubali, Turke, Waƙoƙin Baka, Mamman Shata Katsina, Mamman Gawo Filinge

Gabatarwa

Wannan takarda ta ƙunshi bayanai ne a kan wasu mashahuran mawaƙa na Hausa, wato Alhaji Mamman Shata Katsina na ƙasar Nijeriya da Alhaji Mamman Gawo Filinge wanda yake jamhuriyar Nijar. Takardar ta karkata ne ga nazarin tubalan ginin turke a waƙoƙin da waɗanan mawaƙa suka yi wa masu sana’ar siyar da tuwo. Shi dai tuwo abinci ne da ake yi da garin dawa ko gero ko masara ko kuma ake yi da shinkafa aka tuƙa da tafasashen ruwa, aka kwashe. Ana ci da miyar kuɓewa ko kuka ko kuma yakuwa.

Mamman Shata ya yi wa Hauwa mai tuwo ne waƙar, kasancewar an samu Shata ya yi wa Hauwa mai tuwo waƙa biyu, ɗaya a gindin waƙar yana cewa “Hauwa mai tuwo matar Lado”, sannan ɗayar kuma yana cewa “Hauwa mai tuwo Innar Dije”, to a wanna takarda an zaɓi wadda yake cewa Hausawa mai tuwo matar Lado, kuma da ita aka yi amfani. Shi kuma Mamman Gawo ya yi wa Tafada mai tuwo ne tasa waƙar. Haka kuma wannan takarda ta kawo bayanan masana a kan tubalan ginin turke a waƙoƙin baka na Hausa, sannan an kawo bayanai da misalan yadda mawaƙan suka yi amfani da tubalai iri ɗaya a waƙoƙin nasu. Wannan takarda ta gano tubalan da waɗannan mawaƙa suka yi amfani da su a waɗannan waƙoƙi guda goma sha ɗaya ne kamar haka:

  1. Ambaton wadda aka yi wa waƙa.
  2. Bayyana Iyali.
  3. Fifikon iya girki
  4. Kambame.
  5. Zumunci da Kyakkyawar alaƙa.
  6. Fifikon ciniki
  7. Aika saƙo.
  8. Mazaunin siyar da tuwo.
  9. Mahaɗin siyar da tuwo.
  10. Maciya tuwo.
  11. Habaici da zambo.

1.1 Taƙaitaccen Tarihin Mamman Shata da Yanayin Waƙoƙinsa.

Alhaji Dokata Mamman Shata shahararren mawaƙin baka ne na Hausa, wanda waƙoƙinsa suka mamaye kusan dukkanin inda harshen Hausa ya kai. A iya cewa kusan duk inda Hausawa suke a duniya ko kuma inda wasu al’umma suke magana da harshen Hausa to sun san waƙoƙin Shata, sannan tun farkon shaharar Shata zuwa yau waƙoƙinsa suna da matuƙar tasiri idan an kwatanta su da sauran waƙoƙin makaɗan baka na Hausa, shi ya sa ma ake yi masa kirari da: Mahadi mai dogon zamani. Akwai bayanai da dama a kan shekarun Mamman Shata daga masana daban-daban. Misali: Gusau (1996:192) ya kirdado cewa an haifi Mamman Shata ne a shekarar 1925. Su kuwa marubuta littafin Shata Ikon Allah a shafi na 43 sun bayyana cewa an haif Shata ne a shekarar 1923. Saboda Ƙanƙara (2013:30) ya yi bayanin haihuwar Shata ne a shekarar 1922. Saboda haka a iya cewa masana da manazarta har yanzu suna ta ƙoƙarin tantance haƙinanin shekarun Shata ne ta hanyar kawo hujjoji da za su tabbatar da hakan, domin Sheme da Wasu (2006) sun rawaito ra’ayoyin masana da dama dangane da hasashen shekarun Mamman Shata na haihuwa. Amma Gusau (2018:2) ya bayyana gamsuwa da hujjojin sheme da wasu (2006) a kan haihuwar Shata a 1923.

Gusau da Sheme da Wasu (2006) da Ƙanƙara (2013) da Gusau (2018) sun tabbatar an haifi Shata a gundumar Musawa ta cikin jihar Katsina ta yanzu. Sanna sun tabbatar Shata ya yi karatu a makarantar allo irin yadda sauran yara suke yi a ƙasar Hausa in sun ɗan tasa, amma bai yi karatun boko ba. Haka kuma sun kawo bayanai cewa Shata ya yi sana’ar siyar da goro, a cewar Ƙanƙara (2013) da Sheme da Wasu (2006) bayan sana’ar goro ya haɗa da sana’ar siyar da alewa, waɗanda ana kyautata zaton a sanadiyyarsu ya samo sunansa na Shata, walau ta shato goro da yake in an zo siya, ba tare da ƙirgawa ba, ko ta hanyar talan alewa yana cewa a sha ta alewar. Sannan Sheme da wasu (2006 sun ruwaito cewa Shata ds kansa ya bayayna cewa ya samu sunan Shata saboda in ya samu kuɗi ba ya tanadi sai kashewa kawai, shi ya sa wasu suke kiransa da Shata watomai ɓarnar kuɗi. Ko ma dai ta ina ne sunan Shata ya samu kuma ya bi shi. Har ila yau sun bayyana cewa Shata tun yana yaro a lokacin yana sana’ar goro ya fara yin waƙoƙin asawwara waɗanda samari da ‘yanmata suke yi a da can. Gusau (1996) ya bayyana cewa Shata har wakiltar garinsu na Musawa yake yi a ƙasar waoƙiƙn asawwara waɗanda Unguwanni da samari kan shirya domin nishaɗantar da kansu ko domin wani buki, saboda zaƙin muryarsa tun yana matashi.

Mahadi mai dogon zamani kamar yadda Ƙanƙara (2013) ya kira shi, ya yi waƙoƙi a kan mabambantan turaku da dama. Usman (2016) ya bayyana cewa Shata ya yi waƙoƙi a kan turken talla irin su waƙar “Sabon Robb na magani” da waƙar “engo na magani” da waƙar “Maganin ciwon kai Kafinol da sauransu.

Sannan ya yi waƙoƙi masu turken zambo irin su waƙar “Ɗan ‘Yarbayye da waƙar “Ɗanmani Caji” da sauransu. Haka kuma ya yi waƙoƙi masu turken tafiye-tafiye kamar waƙar “Yawon duniya mafarki ne a tafi a dawo” sanna ya yi waƙoƙin wayar da kai da dama kamar waƙar “Mu tashi ma farka ‘yan arewa” da waƙar “Naira da kwabo sabbin kuɗi” da waƙar “Allah rayan jihar Katsina” da sauransu. Har ila yau Shata ya yi waƙoƙi da dama masu ɗauke da turken ta’aziyya kamar waƙar “Allah jiƙan Ɗahiru Modibbo’ da waƙar “Y Allah ji ƙan Murtala Muhamman’ da waƙar “Aminu Kano Malam na Gwammaja” da waƙar “Allah ya jiƙan UK Bello” da waƙar ‘Allah y yi ƙan Habibu fari da sauransu.Shata ya yi waƙoƙi a kan muhimman abubuwa kamar Kumbo Apollo 11 da waƙoƙi masu turken koɗa-kai da waƙoƙi masu turken faɗakarwa da masu turken zuga da waƙoƙi masu turken yabo da sauran turaku da dama, wato dai da wuya a samu wani turkn da makaɗa suke yin waƙa a kan wanda Shata bai baje kolinsa a kai ba. Haka kuma Shata ya yiwa kusan kowanne rukuni na al’umma waƙa, kama daga sarakuna da shugabannin ƙasa da malamai na addinin da na boko da sojoji da ma’aikatan gwamnati da attajirai da direbobi da masu sana’o’i iri-iri da talakawa maza da mata da tsofaffi da matasa da sauransu.

Mamman Shata yana yin waƙoƙinsa ne a tsari ƙungiya tare da ‘yan amshi da makaɗa da kuma maroƙi (sanƙira), a wasu lokatan. Ga yadda tsarin rera waƙoƙin Mamamn Shata yake:.

Jagora + ‘Y/Amshi + (Ciko + G/ Waƙa) - Kari (Tarbe/ Bayeyeniya) + Kiɗa
Jagora: Yai girma
: Yai tsawo,
: Ya ɗan duƙa kaɗan.
‘Y/Amshi: Hassan Sarkin Dogarai
(Waƙar Hassan Sarkin Dogarai).

Jagora: Kowa ya tsaya zuciya guda,
: A wuri nasa Annabi Muhammadu,
: Ba ya taɓewa a duniya,
: Ba ya taɓewa a lahira,
: Mu dai tsaya ga Annabi Muhammadu,
‘Y/Amshi: Na tsaya ga Annabi Muhammadu.
(Waƙar Na Tsaya ga Annabi Muhammadu).

Gusau, (2018:6) ya bayyana cewa Allah ya yi wa Dr. Mamman Shata rasuwa ranar Juma’a 18 ga watan Yuni, shekara ta 1999 a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano wato AKTH.

1.2 Taƙaitacen Tarihin Mamman Gawo Filinge da Yanayin Waƙoƙinsa

Mamman Gawo makaɗi ne haifaffen Jamhuriyar Nijar. An haife shi a garin Gao-Harodo cikin gundumar filinge, a shekarar 1938, ya rasu a ranar Lahadi 25/01/2016. Ya shahara a ƙasar Nijar da wasu sassa na Nijeriya. Makaɗi ne sa’an Mamman Shata wanda ya yi waƙoƙi da dama, daga cikin waƙoƙinsa akwai: “Nijeriya da Nijar” da “Ya Allah Gyara: Wahabu ka Taimaki ‘Yan Nijar” da “Ya rabbi Sarki mai Jima’a” dasauransu. Mamman gawo yanaamfani da makiɗa biyu, ɗaya nayi masa kiɗan kalangu, yayin da ɗayan kuma ke yi masu kiɗan da kuntukuru. Haka kuma yana da ‘yan amshi mata. Yana da ƙungiyar kiɗa kamar haka:

Jagora + ‘Yan Amshi + Karɓeɓeniya + Kiɗa
Ga misalin wani ɗan waƙarsa
Jagora: Allah Sarki yab ba su sa’a
: Kuma shi yal ba su sani da yawa,
: Yadda sunka so dus sai su yi yau,
: Amma su bar safka ga wata, .
‘Y/Amshi: Su yi ƙoƙari su yi wata hikima,
: Su zan yin ruwa in an yi hawari,
: Ko ko da hawari su yi hadari,
: Su yo ruwa donamfani jima’a,
: Ya Rabbi Sarki mai jima’a,
:A taimake mu don ranal jima’a.
(Waƙar Ya Rabbi Sarki mai Jima’a).

Mamman Gawo Filinge ya yi waƙoƙi masu tarin yawa, waɗanda suke ɗauke da mabambantan turaku. A ɓangaren turken yabo ya yi waoƙi irin su gyara, Wahabu ka taimaki ‘yan Nijar da sauransu. Sanna ya yi waƙoƙi masu ɗauke da turken zuga kamar waƙar Sarkin Filinge Rashidu ɗan Gawo da waƙar Narwa mai ƙarhi da waƙar Yalwa ɗiyar Laman da sauransu. Har ilya yau ya yi waƙoƙi masu turken faɗakarwa kamar waƙar Ya Rabbi Sarki mai jima’ ka taimake mu don ranar jima’a da waƙar Nijeriya da Nijar da sauransu. Sannan a turken siyasa ma ya yi waƙoƙi irin su waƙar C.D.S Rahama da waƙar Fartin Tarayya da waƙar M.S.K Nasara da sauransu. Gawo Filinge ya yi waƙoƙi masu ɗauke da turken rinjayen zuciya kamar waƙar mai baru mai mashaya da waƙar Taimakarmu Alah ai ruwa da sauransu. Sanna y ayi waƙa a kan turken ayyukan ibada kamar waƙarsa ta Makka da Madina. (Gwammaja, 2018:144-147).

2.0 Tubalai a Fagen Nazarin Waƙar Baka

Masana da dama sun bayyana ma’anar tubali a fannin adabi na waƙa kamar haka:

Gusau, (2003, sh. 30) ya bayyana ma’anar tubali da cewa: “Wasu maganganu ne da ake bia ƙuƙƙulla waƙa da su don ta ƙara tsayi, amma ba su ne babbar manufar waƙaar ba. Misali idan turken waƙa na ‘yabo’ ne a cikin waƙar za a iya kawo wasu abubuwa waɗanda lale sai a kna yabo suke magana ba, amma za su iya ƙara wa waƙar kyau da armashi”.

Haka kuma Gusau (2008, sh. 374-375) ya daɗa fayyace ma’anar tubali a waƙa kamar haka:

Waƙoƙin baka na Hausa akan jejjefa wasu ƙananan maganganu na daban ƙari a kan manyan manufofin da aka gina su a kansu. Makaɗan baka sukan yi amfani da waɗannan ƙananan zantuka ne su ƙuƙƙulla waƙa don ta ƙara tsawo, sai dai lalle ne su dace da babbar manufar waƙa. Sanna kowane babban turke akwai nau’o’in ƙananan turakun da suka dace da shi. Misali babban turke na yabo zalla akan daɗa faɗaɗa shi ta ambaton addini ko asali ko zuriya ko jaruntaka ko iya mulki ko kyauta ko karimci ko baiwa ko wani hali nagari da makamantansu. Amma babban turke na siyasa akan yi masa ƙari ne ta fito da sanin makamar tafiyar da jama’a ko laƙantar dabarun jawo hankalin jama’a ko ƙwarewa a yaƙin neman zaɓe ko juriya da jarumtaka ko wanin haka. Domin haka kowane babban turke da tubalan da ake amfani da su wajen gina shi.

Satatima (2009, sh. 82) ya yi ƙairnhaske a kan ma’anar tubalan ginin turke kamar haka:

Cikin hikima ne mawaƙan baka sukan zaɓi turken waƙarsu, su kuma ƙayatar da shi, ta amfani da ƙananan turaku wato tubalan ginin turke ko kuma raɓa-dannin turke kamar yada wasu sukan kira su. Alal mislai idan waƙa turkenta yabo ne to sai ka ga mawaƙi ya taɓo asaba da riƙo da addini da kyauta ya lanyace wanna yabo nasa dasu.

Duba daga bayanai da ra’ayoyin da masana suka ce a kan ma’anar tubali a nazari a iya cewa:

Tubalai wasu abubuwa ne waɗanda ba su ne babbar manufar (turken) waƙa ba, amma suna da matuƙar muhimmanci wajen gina turken waƙa, a wani lokacin ma su ne za su tallafi turken waƙar ya fito fili a fahimce shi a kuma gane shi, ko kuma su zamo abubuwan da kan ƙara ɗanɗano a cikin waƙa. (Gwammaja 2018:72-74).

2.1 Tubalan Ginin Turakun Waƙar Hauwa mai Tuwo da ta Tafada Maituwo

Wannan takarda ta fahimci Mamman Gawo da Mamman Shata suna da alaƙa ta kyakkyawar mu’amala, domin shi kansa Mamman Gawo akwai inda ya yi wa kansa laƙabi da Shata kamar haka:

Jagora: Muhammadu Shatan Nijar ne yaz zo,
: Muhammadu mai waƙa,
: Shatan Filinge ne yaz zo,
: Muhammadu ɗan Filinge ba a ci masa alwashi,
: Tsohon birni da a kai ma shi alwashi,
: Garin nana na filinge ba wnai be ba,
: Tsuntsuwar mugunta da ta zo filinge guda tay yi,
: Don ta ga tsumin ƙasarga da ba ci mata alwashi,
: Ku taimaki duk ‘yan garinmu da ƙiwa nai ba,
‘Y/Amshi: Muna murna ‘yan Nijeriya duka baki ɗai,
:Farar hula su su kai gwamnati mai daɗi.
(Mamman Gawo, waƙar “Farar Hula Nijeriya”)

Sannan Mamman Gawo ya tabbatar mana cewa saboda kyakkyawar alaƙarsa da Mamman Shata har matarsa ya biya wa aikin haji, a lokacin da Mamman Gawo ya biya wa kansa, sannan ya tabbatar mana Shata har gidan ya taɓa kai wa Mamman Gawo ziyara, ya kuma kwana a garin Gawo-hadoro cikin gundumar filinge da ke jihar Talebere ta jamhuriyar Nijar. Haka kuma Mamman Gawo ya tabbatar min cewa; yakan kawo wa Mamman Shata ziyara har gida, sannan a wasu lokuta ma Shata yakan nemi ya rera masa wasu waƙoƙin, kuma yakan rera wa Shatan waƙoƙin ne tare da yaransa[1], wannan ne ma ya haifar da waƙar da Mamman Gawo ya yi wa Shata. Ga abin da yake cewa:

Jagora: To, za mu yabonka sarkin waƙa,
: Shata babban ɗan Katsinawa,
‘Y/Amshi: Za mu yabonka sarkin waƙa,
Shata babba ɗan Katsinawa.
Jagora: Ya Allah ka ba ni fusaha,
: In yi yabon Muhammadu Shata,
‘Y/Amshi: Za mu yabonka sarkin waƙa,
: Shata babba ɗan Katsinawa.
Jagora: Duk sarkin mawaƙan niyya,
: Ba Najeriya ita ɗai ba,
‘Y/Amshi: Za mu yabonka sarkin waƙa,
: Shata babba ɗan Katsinawa.
Jagora: Gonarkin mawaƙan niyya,
: Ko nome da mai-mai shata,
: Waƙa don mutum zai niyya,
: Sai ka ji tasa kwaikwayi shata,
‘Y/Amshi: Za mu yabonka sarkin waƙa,
:Shata babba ɗan Katsinawa.
(Waƙar Shata Babba ɗan Katinsawa).

Haka kuma (Gusau, 2018:8) ya bayyana cewa: “Irin hikima ta Alhaji Mamman Shata da kuma matsayinsa na makaɗi mai baiwar Allah, yakan saurari waƙoƙin wasu makaɗa, daɗa manyan makaɗa ne ko ƙanana, kamar Alhaji Ɗanƙaura Maikalangu Daura da Ibrahim Narambaɗa da Salihu Jankiɗi da Abdu Karen Gusau da wasu sanƙirorinsa da makamantansu. Shata yakan yi amfani dawasu daga cikin azance-azancesu ko maganganu na waƙoƙinsu, nan take kuma ya yi musu na hankaka.

Saboda haka a iya cewa; ire-iren waɗannan alaƙoƙi na zumunci da suke tsakanin Mamman Shata da Mamamn Gawo su ne suka haifar musu da yin amfani da tubalan ginin turke irin ɗaya wajen gina turakun waƙoƙinsu na Hausa mai tuwo da ta Tafada mai tuwo. Ga bayanai tare da misalai daga ɗiyan waƙoƙinsu, waɗanda suka tabbatar da haka:

2.1.1 Ambaton wanda aka yi wa Waƙa

Mamman Shata y yi amfani da tubalin ambaton wadda aka yi wa waƙa, domin cimma burin waƙarsa ta Hausa mai tuwo, kuma ɗan waƙar ya tabbar Hauwa mai tuwo ya yi wa waƙar. Ga abin da ya ce a ɗan na 34 na cikin waƙar.

Jagora: Ina Hauwa mai abincin saidawa,
‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Haka shi ma Mamman Gawo ya yi amfani da irin wannan tubali a waƙarsa ta Tafada mai tuwo, kuma ɗan babban ginshiƙi ne a waƙar, domin a cikinsa ne aka fito ƙararar aka ambaci wadda aka yi wa waar. Ga abin da yace a ɗana 2 dake waƙar:

Jagora: Kun ji kiɗan Tafada mai tuwo,
‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.2 Bayyana Iyali

Mamman Shata ya yi amfani da tubalin bayyana suna iyali a waƙar Hauwa mai tuwo, domin ya fito fili ya ambaci suna ‘yar Hauwa mai tuwo a ɗa na 2 kamar haka:

Jagora: Hauwa Kululu mai tuwo innar Dije,
‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Sannan a ɗa na 29 ya sake ambaton wata ‘yar tata wadda suke takwara kamar haka:

Jagora: Kululu Hauwa babbar Uwar Hauwa,
‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Shi ma Mamman Gawo ya yi amfani da irin wanna tubali na ambaton iyali a waƙar Tafada mai tuwo, kuma shi ma ‘yar ta mace ya ambata, sanna ya yi amfani da sunan ‘inna’ a matsayin mahaidiya kamar yadda Mamman Shata ya yi. Ga abin da ya ce a ɗa na 4 na cikin waƙar:

Jagora: Innal Fati Tafada mai tuwo,
‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.3 Fifikon Iya Girki

A ƙoƙarin Mamman Shata na cimma burin waƙarsa ta Hauwa mai tuwo ya yi amfani da tubalin bayyana fifikon girki a ɗa na 26 da kuma na 27, a inda ya bayyana sa ‘yan birni ne suke cin tuwonta, sanna in an yi baƙin kuny akae siyo tuwon Hauwa a kai musu. Ga ayadda ya furta a ɗiyan waƙoƙin:

Jagora: Tsaya Kululu matar Lado,
: Tsaya Kululu Gwaggon Dije,
: In kin yi miyarki ta ‘yan birni,
: Ita za ni saya in ba ƙi,
‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.
Jagora: A’a tai tuwo na gwamnati mai tsada,
: Shi za na saya in ba ƙi,
‘Y/Amshi: Shauwa mai tuwo matar Lado.

Har ila yau shi ma Mamman Gawo ya yi amfani da irin wanna tubali na bayyana fifikon iya girki, domin saisaita kammaluwar cikar turken waƙarsa ta Tafada mai tuwo domin ya fito ƙarara ya bayyana Tafada ta fi dukkanin mat aiya yin tuwo da miya. Ga abin da ya ce:

Jagora: Innal Fati Tafada mai tuwo,
: Ta fi su tuwo Tafada,
: Ta fi su miya Tafada mai tuwo,
‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.4 Kambame

Mamman Shata ya yi amfani da kambame a ɗa na 17 da na 18, a matsayin wani babban tubali a waƙarsa ta Hauwa mai tuwo, a inda ya kururuta martaba da matsayin Hauwa, wanda a cewarsa in dai wata mai siyar da tuwo ta yarda suka sami saɓani da Hauwa, to ta daina ciniki, sai da idan ta je ta tuba, ko kuma ita da sake samun kasuwa sun yin hannun riga. Ga abin da ya ce:

Jagora: Kurum kuma snai na ja Hauwa,
: Ga shi nai tuwo ban saida, ba,
‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.
Jagora: Ni kau sai na ce bari yin kuka,
: Tafi ki tuba can a wurin Hauwa,
‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Haka kuma a ɗa na 42 ya sake kambama matsayin Hauwa mai tuwo, a inda ya nuna dukkanin masu siyar da tuwo ita ce babbarsu. Ga abin da ya ce:

Jagora: Gama duk ga ‘yan tuwo ita ab babba,
‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Shi ma Mamman Gawo a ƙoƙarinsa na smaun tubalin da zai tallafi waƙarsa ta Tafada mai tuwo ta kai ga nasara, ya yi amfani da tubalin kambame a ɗa na 10 da na 11. Ga abin da ya ce:

Jagora: Kowacci tuwonki,
: Bai zuwa wuta,
‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

Jagora: Kowacce tuwonki,
: Ba shi ƙonuwa,
‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

Wato a waɗannan ɗiyan da suka gabata Mamma Gawo yana kambama matsayin Tafada mai tuwo ne, a inda ya bayyana duk wanda ya ci tuwonta, to, a ranar lahira ba shi ba shiga wuta, sai dai ya wuce Aljanna kawai, saboda ya ci tuwon Tafada.

2.1.5 Zumunci da Kyakkyawar Alaƙa.

Har ila yau Mamman Shata ya yi amfani da tubalin nuna zumunci da kyakkyawar alaƙar dake tsakaninsa da Hauwa, a ƙoƙarinsa na samar da tubalan da za su tallafi waƙarsa ta Hauwa mai tuwo ta kai ga nasara. Ga abin da ya ce a ɗa na 7 da na 8.

Jagora: Inna ‘yan garam da maroƙana,

: Har ‘yan’amshi har ku makaɗa,

: N ayi maku hanyar karyawa,

: Muddin mahassada ba su ɓata ba,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Jagora: Matuƙar na sauka Kanon Dabo,

: Ka sanba za ni kwana da yunwa ba,

: In Hauwa na tuwo matar Lado.

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Shi ma Mamman Gawo ya yi amfani da tubalin nuna zumunci da kyakkyawar alaƙa a tsakaninsa da Tafada mai tuwo, domin ya tallafi turken waƙar ya kai ga nasara. Ga abin da ya ce a ɗana 12:

Jagora: Ni zan ni gurin Tafada in ci nau,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.6 Fifiko Ciniki

Alhaji Mamman Shata ya yi amfani da tubalin bayyana fifikon ciniki a matsayin ɗaya daga cikin manyan tubalan da suka azagawa turken waƙarsa ta Hauwa mai tuwo, domin ya nuna dukkan mai siyar da tuwon da ta ja Hauwa da rigima, to, ta daina ciniki, saboda haka ma har kokawa sauran massu siyar da tuwon suke yi a kan cewa: Hauwa ta fi su su ciniki, kuma su kullum sai sun yi kwantai, kowa ya zo sai tuwon Hauwa zai siya. Ga abin da ya ce a ɗa na 57 da 58 da kuma 59.

Jagora: Ku kuka iza ni har naj ja Hauwa,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Jagora: Gashi nai tuwo ban sai da ba,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Jagora: Na yi talla an ƙi a duba ni,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Har ila yu shi ma Mamman Gawo ya yi amfani da irin wanna tubali na nuna fifikon ciniki domin ya daɗa kakkange turken waƙarsa ta Tafada mai tuwo, saboda ya tafi ɗoɗar ya cim ma burinsa, domin ya fito ƙarara ya bayyana sunan wata mai tuwo mai suna Yawo a inda ya ce; ba a siyan tuwonta, in dia tuwon Tafada bai ƙare ba. Ga abin da ya ce a ɗa na 15.

Jagora: In Alhajiya Tafada na tuwo,

: Bari ba a siya tuwon su Yawo ma,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.7 Aika Saƙo

Alhaji Mamman Shata ya yi afani da tubalin aika saƙon shawara ga Hauwa mai tuwo a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka daɗa armasa turken waƙar. Ga abin da ya ce a ɗa na 35:

Jagora: Ke riƙa tsare gida Hajiya Hauwa,

: Ka da maci abinci ya raina ki,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Haka shi ma Mamman Gawo Filinge ya yi amfani da irin wannan tubalin na aika saƙo, ta hanyar aika saƙon gaisuwa ga Tafada mai tuwo, kuma tubalin ya daɗa ƙawata waƙar. Ga abin da ya ce a ɗa na 34:

Jagora: To, na gode Tafada,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.8 Mazaunin Siyar da Tuwo

Mamman Shata ya yi amfani da tubalin bayyana wurin da Hauwa take siyar da tuwo a matsayi ɗaa daga cikin manyan tubalan ginin turken waƙar ta Hauwa mai tuwo. Ga abin da ya ce a ɗa na 33:

 

Jagora: Birnin Kano a Tashar Kuka,

: Nan Hauwa ke abinci na saidawa,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Shi ma Mamman Gawo ya yi amfani da irin wanna tubali wajen bayyana wurin da Tafada take siyar da tuwo, kuma ɗan waƙar bababn tubali ne wanda ya yi matuƙar taimaka wa waƙar, har kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Ga abin da ya ce a ɗa na 26 da kuma na 27.

Jagora: Ai Ballen-Yari nan take tuwo,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

Jagora: Dabra da tasah nan take tuwo,

: Wasu ‘yan namu an fa jeru duk,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.9 Mahaɗin Siyar da Tuwo

Mamman Shata ya yi amfani da tubalin bayyana mahaɗin kayan daɗin da Hauwa take amfani da su wajen ƙawata tuwonta, domin ya daɗa bambanta nagarta tuwonta da na wasu, kuma tubalin ya daɗa ƙawata waƙar. Ga abin da ya ce a ɗa na 19 da kuma na 20.

Jagora: Gama Hauwa tai miyar naman shanu,

: Hauwa ga miyar naman kaji,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Jagora: Tsaya Hauwa ga miyar naman zabbi,

: Hauwa ga miyar naman kaji,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Mamman Gawo ma ya yi amfani da irin wanna tubali ta hanyar bayyana kayan daɗin mahaɗin tuwon Tafada, domin ya cim ma burin waƙar, kuma tubalin ya daɗa fito da armashin waƙar. Ga abin da ya ce a ɗa na 28.

Jagora: Wasu ‘yan zabi ga su soye nan,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.10 Maciya Tuwo

Alhaji Mamman Shata ya yi amfani da tubalin bayyana maciya tuwon Hauwa, a inda ya bayyana ‘yan birni ne suke siyan tuwonta, kuma tubalin ya taimaka sosai wajen cikar turken waƙar. Ga abin da ya ce a ɗa na 34:

Jagora: Na hori Hauwa dai matar Lado,

: In kin yi abinci na ‘yan birni,

: Kin haɗa shi kin kuma gyara shi,

: In ‘yan birni suka zo su saya,

: Kowanne ya riƙe kwano nai,

: Ya ja layi zai sayi tuwo,

: Riƙa tsare gida Hajiya Hauwa,

: Kada maci abinci ya raina ki,

‘Y/Amshi:Hauwa mai tuwo matar Lado.

Haka shi ma Mamman Gawo ya yi amfani da irin wannan tubali a waƙarsa ta Tafada mai tuwo, kuma shi ɗin ma ‘yan birni ya bayyana a matsayin maciya tuwoon Tafada, sannan tubalin ya yi matuƙar tasiri wajen cikar turken waƙar: Ga abin da ya ce a ɗa na 6 da kuma na 7.

Jagora: Bari ‘yan birni ba su cin tuwo,

: Sai Alhajiya Tafada na tuwo,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

Jagora: Duk ‘yan birni sai suna faɗin,

: Ga kwano na Tafada ba ni nau,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

2.1.11 Habaici da Zambo

Mamman Shata ya yi amfani da tubalin habaici domin daɗa ƙawata waƙarsa ta Hauwa mai tuwo, sannan tubalin ya tallafi turken waƙar wajen kammaluwar saƙonsa. Ga abin da ya ce a ɗa na 48:

Jagora: Wata tana tuwonta cikin birni,

: Tana abin ta daidai ƙarfinta,

: Aka iza ta har taj ja Hauwa,

‘Y/Amshi: Hauwa mai tuwo matar Lado.

Wanna ɗan waƙar habaici ne zalla, saboda Shata ne kaɗai zai iya bayyana ainihin wanda yake yi wa habaicin.

Shi ma Mamman gawo ya yi amfani da irin wanan tubali, sai dai shi zambo ya yi ba habaici ba, domin ya fito ƙarara ya ambaci sunan wadda ya yi wa zambon wato Yawo, sannan tubalin ya taimaka wa turken waƙar wajen daɗa fayyace shi tare da haskaka waƙar. Ga abin da ya ce a ɗa na 19 da na 20:

Jagora: Yawo ba tuwo ba, ba miyar ƙwarai,

: Su Yawo mai tuwo, miya yama-yama,

‘Y/Amshi: Alhajiya Tafada mai tuwo.

Jagora: Su Yawo mai tuwo, miya taɓar-taɓar,

: Alhajiya Tafada mai tuwo.

3.0 Kammalawa

A wannan takarda an kawo bayanan bincken masana da manazarta a kan tarihin Mamman Shata da Mamman Gawo, sannan aka kawo wasu bayanan masana a kan tubali a nazarin waƙar baka. Har ila yau an kawo wasu tubalai guda goma sha ɗaya, waɗanda su ne aka fahimci waɗannan mawaƙa suka ɗauka suka yi amfani da su a matsayin tubalan samar da turakun waƙoƙinsu na masu tuwo tare da armasa waƙoƙin. Takardar ta kawo misalai tare da sharhin tubalan daga ɗiyan waƙar Hauwa mai tuwo ta Mamman Shata da waƙar Tafada mai tuwo ta Mamman Gawo. Kuma takardar ta tabbatar tubalan da suka yi amfani da su iri ɗaya ne.

Manazarta

Aliyu, L. (2012). Kwatancin Salo da Jigo a Waƙar Muhamamdu Gawo Filinge da ta Musa Nadada. Kundin Digiri na Farko. Zariya: Sashen Koyar da Harsuna da Al’adu. Jami’ar Ahmadu Bello.

Bunza, D.B. (2014). Sama Jannati a Mahangar Marigayi Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina da Mamman Gawo Filinge. Maƙala wadda aka Gabatar a bikin ranar Harshen uwa (International Mother Language Day) da UNESCO. Yamai: Jamhuriyar Nijar.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa, Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press Limited.

Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2010). “Hanyar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya a Taƙaice” Maƙala a Taron Ƙarawa Juna sani a Tsakanin Malamai da Ɗalibai a Sashen Hausa na Jami’ar Bukr Abba Ibrahim. Yobe.

Gusau, S.M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya. Kano: Bayero Uniɓersity,

Gusau, S.M. (2018). Diwanin Waƙoƙin Baka: Juzu’i na Uku Matanonin Wasu Waƙoƙin Alh. Dr. Mamman Shata Katsina, Kano: Century Research and Publishers Limited.

Gwammaja, K.Ɗ. (2018). Nazarin Turke a Waƙoƙin Mamman Gawo Filinge. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Ƙanƙara, (2013). Mahadi mai Dogon Zamani

Satatima, I.G. (2009). Waƙoƙin Ɗarsashin Zuciya na Makaɗan Hausa. Kundin Digiri na Uku: Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sheme da Wasu (2006) Shata Ikon Allah

Usman, H.S. (2016). Nazarin Turken Ta’aziyya a Waƙoƙin Dr. Mamman Shata Katsina. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.



[1]. Hira da Mamman Gawo a gidansa dake Gawo-Hadoro cikin gudumar Filinge dake jihar Talebere a Jamhurar Nijar a ranar 2 zuwa 5 ga watan Mayu, 2015.

Post a Comment

0 Comments