Citation: Bunza, A.M. (2024). Kukan Kurciya Jawabi Ne Sai Mai Sani Ka Ganewa (Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo a Ma’aunin Makaɗa Sa’idu Faru). Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 21-28. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.003.
KURCIYA JAWABI NE SAI MAI SANI KA GANEWA
(Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo a Ma’aunin Makaɗa
Sa’idu Faru)
Daga
Aliyu
Muhammadu Bunza
Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya
Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Tsakure
Ayyukan da
aka yi kan adabin waƙa sun fi na kowane ɓangaren adabi yawa a nazarin Hausa. Mawaƙan baka na
Hausa ba lungun rayuwar Hausawa da ba su waƙe ba. Sa’idu
Faru a cikin makaɗan fada ba ƙyalle ne ba.
Alhaji Muhammadu Macciɗo Sarkin Kudun Sakkwato ne maigidansa. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Sarkauna da ‘ya’yan sarauta da yawa waƙa, amma na
Sarkin Kudu Macciɗo sun fi yawa da shahara. An yi amfani da dabarar
bincike ta ga-wuta-ga-masara wajen tace waƙoƙinsa domin a
hango wuraren da ya yi kukan kurciya game da yadda maigidansa zai kasance. A taƙaice, duk
wanka da kamar jurwayen da ya yi
na fatar Sarkin Kudu Macciɗo ya kasance jagoran gidansu da hawa gadon sarautar Sarkin
Musulmi sun tabbata bisa ga kasancewarsa Sarkin Musulmi na (19). Tunaninsa na
yadda zaɓen Sarkin Musulmi Macciɗo
zai kasance ya tabbata. Yadda ya yi hasashen mutuwarsa haka ya kasance. Da yawa
jifa cikin duhu yana
kasancewa kamar ga bakin boka, haka ko ta kasance. Akwai buƙatar manazarta adabi su fara tunanin
nazarin adabinsu a kimiyance fiye da tsayawa kan salo da jigo da turakun tussan
adabinsu. Sakamakon wannan ɗan
nazari ya nuna muna ruwa na ƙasa
sai ga wanda bai tona ba. Samun sababbin abubuwa cikin adabin yanzu aka fara.
Kowane zango na adabi da ire-iren abubuwan da za a tsinta a ciki.
Gabatarwa
Adabin baka babbar
taska ce ta binciken kowane ilmi na rayuwar mutanen da suka rayu da shi, domin
babu cigaban duniya da ya fara da rubutu. Ashe rubutu wata fasaha ce da ta
tsira bayan da tunanin mutane ya kammala, kimiyyar fannonin rayuwa da yawa sun
bunƙasa,
sai fasahar taskace su ta bayyana da baya. Daga cikin ressan adabin baka, babu
mai gwada tsawo da adabin waƙa ba
ta yi masa kere ba. Ga alama, da waƙar baka da magana zozo-zozo suke tafiya
a tarihinsu. Don haka, a ƙunshiyar
waƙar
baka babu irin saƙon
da ba a tsinta a ciki, sai dai wanda hangen mai hange bai hango ba. Tunanin
wannan takarda shi ne, ɓarke laya na wasu kuramen ɗiyan waƙar makaɗa Sa’idu Faru a kan rayuwar maigidansa Sarkin
Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III waɗanda ya yi a matsayin wanka da kamar
jirwaye
kuma suka kasance kamar a bakin boka bayan su duka sun bar duniya (Allah Ya
gafarta musu). A lokacin da makaɗa
Sa’idu ya yi su, suna matsayin “kukan kurciya”; bayyanar da suka yi gare mu a
yau ƙiri-ƙiri muka kasance masana ga manufarsu.
Kwakkwahe Tunanin Matashiya
A
zatona, babu mai musun kasancewar babbar matashiyarmu “karin magana”. Haka kuma, karin magana
wani babban kogi ne daga cikin manyan kogunan adabin baka. To, riwayoyin karin maganar nan akan ji su ga bakunan magabata da
ajin kalmomi daban-daban kamar haka:
a. Kukan kurciya jawabi ne mai hankali ka ganewa.
b. Kukan kurciya jawabi ne sai mai sani ka ganewa.
c.
Kukan kuricya jawabi
ne sai mai hankali da mai lura.
Abubuwan
kula gare mu ɗalibai shi ne, tattare da sassaɓawar muhallin kalmomi da daɗi ko ƙari cikin waɗannan riwayoyi za mu ga kowace daga
cikin su ta kawo:
a. Kalmar kurciya sananniyar tsuntsuwa ce a ƙasar Hausa.
b. Kukan da kurciya ke yi.
c. Cikin kukan akwai hikimomi/saƙon da ya kamata a kula.
d. Kukan da yake ba magana ne buɗe ba, da ilmi ake fashin baƙinsa.
e.
Masanan su ne, waɗanda aka yi gaban idonsu ko ma’ilmanta su
yi kirdado.
A ɗan nawa bincike, wai ko, anya! Asalin
karin maganan ba “kukan kuricya” kawai yake ba? Dalilina kuwa shi ne, kalmar
jawabi “Larabci” ce daga “jawab” kuma ga alama “kurciya” ta riga ‘Larabci”
shigowa ƙasar
Hausa. Haka kuma, adabin Larabci bai kawo kurciya a ƙarƙashin inuwar hikimomin da Bahaushe ya
saka ta ba.
Hanyar Ɗora Bincike
Ba zan ɗora bincike bisa tafarkin ‘yan duba ba, domin makaɗa
Sa’idu Faru da maigidansa Sarkin Musulmi Muhammadu Maccidɗo
Abubakar III, ba su bi hanyar nan ba. Wannan ya sa na yi tunanin ɗora binciken a kan wasu fitattun zantukan makaɗan fada masu cikakken ilmin fada da
sanin mutanenta da ire-iren yanaye-yanayenta. Na farko, na lalubo maganar marigayi
Aliyu Ɗandawo
a fagen da yake wasa Sarkin Kabi Isma’ila a faɗarsa:
Jagora: Magaba abin da sun ka hwaɗi,
Yara: Ai mai da hwaɗi ɓanna
na,
Gindi: Shugaban tahiya Sarkin Kabi mai Sudani,
: Ila
marin rugga ɗan Yaƙuba sa gurfani.
Babu
shakka idan magabaci ya gawurta da yawa za a taras da cewa, maganarsa nashin ƙasa ce babu kure. Sakamakon ganin abu yau, da gobe, da ire-iren
sauye-sauyen da yake yi, ke sa su yanke hukunci a taras sun sara a kan gaɓa. Makaɗa Ibrahim Narmabaɗa ya taɓa wata magana da yake cewa:
Jagora: Maidamma,
: Ya
hwaɗi sai an yi ka sarki.
Yara: Ta ko tabbata ka yi.
Gindi:
Iya gaba ginshimin Malam Dikko ɗan Buhari.
Magabata
sun hango sai ya hau gadon mahaifinsa sai ga shi Allah Ya tabbatar da shi
sarki. Wanda duk aka haifa a gidan sarauta yana fatar ya wayi gari a kan gadon.
Ire-iren waɗannan hasashe da ake yi wa ‘ya’yan
sarauta ana kiran su “fata”. Idan fata ta cika ita ce, “Kukan kurciya” da mawaƙi ya yi. Idan kushe ɗan sarauta aka yi aka nisantar da shi ga
gadon gidansu a al’adance an “kafa masa kara” idan karan ya tsayu “baki” ya
kama shi. Dubi misali a wata da’awar Dr. Narambaɗa da ke cewa:
Jagora: Ka ga ɗan Sarki da kunnuwa da hwaɗi,
Yara: Ga shi da ƙarya ga shi da rowa,
Yara: Ko ga girmama shi ba shi sarki.
Gindi: Masu gari mazan gabas tsayayye,
: Sarkin
Rwahi ya wuce a rammai.
A
cikin wata waƙar
Sarkin Bukkuyum Alhaji Muhammadu Makaɗa na
cewa:
Jagora: Ɗan sarki mai gajeren wuya,
Yara: Shi ƙarshe nai ginak kwakwara.
Gindi:
Muhammadu mai gida Bukkuyum.
Kunnuwa
da faɗi, da ƙarya, da rowa, duk ba su hana a yi
sarauta in an ƙaddaro.
Haba! Yaushe gajeren wuya ya zama wani dalili na naƙasa ga siyasa? Waɗannan duk “kafa kara” aka yi, in sun
tabbata baki ya kama mai su. To ire-iren waɗannan ɗiyan waƙar makaɗa Sa’idu Faru da suka ambaci Sarkin
Musulmi Muhammadu Macciɗo nike son in ɗan taɓo gwargwadon fahintata. Don haka na dahi
kafaɗar Dr. Ibrahim Abdulƙadir Maidangwale Tubali Narmabaɗa a zancensa na yi wa magabata hangen sa a faɗarsa:
Jagora: Ɗan bajini shi ka zama bajini,
Yara: Yai bobakali yai tozo,
Yara: Ɗan akuya na kallo.
Gindi: Na yaba ka da girma Audu ƙanen mai daga,
: Kanda
mu san kowa kai mun ka sani Sardauna.
Hausawa
sun ce, sanin asali kan sa kura cin kanjilo. A ce bajini ya haifi ɗa, ba abin mamaki ba ne ya zama bajini.
Fatar da ake yi masa ke nan, kuma fatar ta cika ya kasance bajini.
Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo
Sarkin
Musulmi Muhammadu Macciɗo ɗa ne
ga Sarkin Musulmi Abubakar III (1903-1988). An haife shi ranar 20 ga Afirilu,
shekarar 1928 a garin Dange. Shi ne Sarkin Musulmi na 19. Allah Ya yi masa
rasuwa cikin haɗarin
jrigin sama na kamfanin Aviation
Development Company (ADC) da ya tashi daga Abuja zuwa Lagos ranar 29 ga
Oktoba, 2006. Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III na da gurabu guda bakwai
gare mu ɗaliban bincike:
a.
Shi ne ɗaya daga Sarakunan Musulunci da ya gada
daga mahaifinsa.
b.
Shi ne na biyu daga
cikin Sarakunan Musulunci da suka yi karatun Boko.
c.
Shi ne na biyu daga
cikin Sarakunan Musulunci da suka hau mulki zamanin mulkin Soja.
d. Shi ne Sarkin Musulmi na farko da ya riƙa muƙamin siyasa.
e.
Shi ne Sarkin Musulmi
na farko da ya mutu sanadiyyar haɗari.
f.
Shi ne Sarkin Musulmi
na biyu da ya
hau bayan tumɓuke wanda ke kan karaga.
g.
Shi ne Sarkin Musulmi
na farko da aka yi wa taron ilmin nazarin waƙoƙin da mawaƙinsa ya yi masa.
Makaɗinsa Sa’idu Faru mawaƙin sarauta ne, ya yi waƙoƙi da yawa ga sarakuna, da ɗiyan sarauta, daban-daban amma
kasancewar Macciɗo mai gidansa, waƙoƙin da ya yi masa sun zarce na sauran
yawa.
Kukan
Kurciya a Ma’aunin Adabi
Ba Sa’idu Faru ya fara yin kukan kurciya a waƙoƙinsa
ba, hasalin ma gabanin a haifi Sa’idu Faru akwai karin maganar kukan kurciya. Muradin kukan kurciya a adabi shi ne:
a. A yi hannunka-mai-sanda ga wani abu gabanin aukuwarsa.
b. Ya zo ya auku ko kusa ko da nisa.
c. Mutanen da suka shaida shi suna da masaniyar an ce zai
kasance.
d. Masana kaɗai ke da asirin sanin kukan kurciyar
bisa ga gogewarsu
Ga ɗan misalin share fage daga cikin sassan
adabin Bahaushe da al’adunsa:
“Da
haka muka fara kuturu ya ga mai ƙyasfi”.
Kuturu
a nan shi ne masani kuma malamin da ya san halayyar cutar kuturta. Ya san da
cewa, ba a dare ɗaya kawai za a tashi a rasa yatsu ba ko
jiki ya bushe, fuska ta ƙaƙƙamure. A’a, kaɗan-kaɗan abin ke faruwa har ya game jiki. Wa
ya san da haka? Wa ke da wannan ilmi? Sai wanda ciwon ya kama ko waɗanda suka gaji cutar a gidansu. Don
haka, “kyasfi” a nan, zaman kukan kurciya yake masu masaniya a kansa su ne
kutare. Idan muka nazarci ɗan gajeren labarin da na samo a Sakkwato
wajajen shekarar 1982 a unguwar Giɗaɗawa
za mu ƙara
fayyace kukan kurciya a al’adance:
An
ce wani Bayarbe ne ke zaune a garin (Wurno/Raɓa?) tun wajajen shekarar (1950s). Ya aikata
wani laifi aka kai shi kotun Alƙali
Umaru na garin. Alƙalin
ya ci shi tara ta wajen “fam biyar”. An ce, a lokacin sai ya share shekara
biyar bai gama biyan tarar ba, domin kuɗi
sun ƙaranta
a hannun mutane. Ya yi ta biya shekara da shekaru kotu kawai yake yi wa biɗa. Alƙali Umaru Alƙalin kotun Musulunci ne da sai wanda ya
goge ga karatun zaure za a ba kotu. To! wata rana Bayarbe na ganinsa, ga wani
yaro almajiri ya zo yana bara, sai ya daka masa tsawa da cewa: “Tafi ki ba mu
wuri, ka da ki sake tahowa sagonmu, in kin sake, za mu buge ki, shegiya kawai,
mutumin
banza”. Matar Bayarbe ranta ya ɓaci da ganin mijinta na zagin ɗan yaro rataye da allo don ɗai ya zo bara shagonsu. Ta ce wa mijin;
“Haba Oga, yaya za ka yi haka? Laifin me ya yi maka? Ai yaro na kowa ne. Kai! Wannan ba cau”. Mijin ya ce: “Rufe
bakinki, mutumin
banza, ai irinsu ne, in ta girma ta zama Alƙali
Umaru”.
Shi
“Oga” kukan kurciya ya gani ya san su Alƙali Umaru daga ƙaratun allo aka fara, daga nan kuwa in
an ƙasaita
sai a zama Alƙali
a yi ɗanyen hukunci irin wanda aka yi masa.
Macciɗo a
Ma’aunin Sa’idu Faru
Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo yana
da rawanin Sarkin Kudu a zamanin mulkin mahaifinsa Sarkin Musulmi Abubakar III.
Sarautar Sarkin Kudu
sarauta ce da ake ba ɗiyan sarakuna. Sarauta ce kamar kowace
sarauta da ake bai wa ɗiyan sarki, sai dai ta Sarkin Kudu Macciɗo ta fi shahara musamman a tafashen
Sa’idu Faru. Bisa ƙa’idar
tsarin waƙoƙin Sa’idu Faru na Sarkin Kudu Macciɗo za mu ga hoton kukan kurciya kamar
haka:
Hangen
Wasu Ɗabi’u
na Ɗaukaka
Kowane makaɗin fada ƙoƙari yake ya gamsar da masu sauraronsa cewa, maigidansa maɗaukaki
ne. Idan muka dubi irin yadda makaɗa Sa’idu Faru ya tsaro irin ɗaukakar
Sarkin Kudu Macciɗo, za mu ga kukan kurciya ne yake ƙoƙarin yi
na buƙatar da ke gaba. Ga yadda ya tsara kukan
kurciyar:
Jagora:
Maganag ga da za ni hwaɗa maka,
: Gagarau
ɗan Alu kai min gafara,
Yara: Wada duk aka gadon ɗaukaka,
Yara: Wada
duk aka gadon ƙasura,
Yara: Wada duk aka gadon cigaba,
Yara:
Mamman ka gadi Abubakar.
Gindi: Kana shire baban ‘yan ruwa,
: Na Bello jikan Ɗanhodiyo.
Roƙon da
makaɗa Sa’idu ya yi na faɗar a gafarta masa da abin da ya biyo
bayan roƙon gafarar ba su yi kunnen doki ba. Roƙon gafarar kukan kurciya ne domin abin
da ya biyo baya fata ce ake yi masa. Yi wa ɗan sarki fatar hawan gadon mahaifinsa
yana tare da abubuwa guda biyar:
a.
In dai uban ya rasu a
gada.
b.
In ko an tuɓe uban a gada.
c.
In uban ya yi murabus
a gada.
d. In an hukunta uban da laifin da bai cancanci dogewa ba. Shi
sauka,
a gada.
e.
In ko uban ya aje da
kansa bisa wani uzuri ya nemi alfarma a ba ɗa.
Babu
mai fatar waɗannan abubuwa biyar ga mahaifinsa. Dole
ko sai ɗaya ya wakana za a gaji uba. Waɗannan abubuwa dukkansu a yi jaje ne ba
na madalla ba, don haka ya roƙe
shi gafara. Kamar ga bakin boka, a ƙarshen mulki Sarki Abubakar zamanin
mulkin Shagari ƙarƙashin jam’iyyar NPN, an ce masarautar
Sakkwato ta nemi a ɗauke wa Sarki Abubakar III nauyin aikin
sarauta a ba Sarkin Kudu, wanda a lokacin yana kwamishina a mulkin Gwanna Shehu
Muhammadu Kangiwa. Masu jiran gado suka yi tsaye da cewa sai dai ya yi murabus,
a yi zaɓe sabo. Kukan kurciya ya tabbata a nan,
ai a rufe ɗan
waƙar
cewa ya yi:
“Mamman
ka gadi Abubakar”.
Gindin
waƙar
ma, wani kukan kurciya ne “Na Bello”, “Jikan Ɗanhodiyo”. Ɗanfodiyo ya jagoranci jihadin tabbatar ɗaular Musulunci, Bello ne Sarkin Musulmi na farko don haka, Sarkin
Kudu sai ya yi. Waɗannan abubuwa duk sun bayyana bayan
mutuwar makaɗa Sa’idu Faru.
Ɗora Shi
Gadon Mahaifinsa
Makaɗa Sa’idu Faru a cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa
yana kukan kurciya da nuna kai tsaye sai Sarkin Kudu Macciɗo ya
gaji mahaifinsa. Babu wai, kowane ɗan sarki fatarsa ke nan kamar yadda makaɗa Dr.
Ibrahim Abdulƙadir
Maidangwale Tubali Narambaɗa ke cewa:
Jagora: Kowane ɗan sarki,
: Son shikai shi zan sarki.
Yara: Sai in ba ta samuwa,
: Ta tabbata ko ban hwaɗi ba,
: In gandu yas samu ya hi gamana.
Gindi: Ibrahimu na Guraguri,
: Mai Shinkahi bajinin zagi,
: Mu
dai Allah Shi bar muna kaya.
Makaɗa Sa’idu Faru ya yi wa Sarkin Kudu kukan
kurciya da cewa:
Jagora: Ka gadi Bello ka gadi Moyi,
Yara: Saura ka kai inda Maihausa yak kai,
: Na Magaji Maimartaba ɗan Mu’azu.
Gindi: Farin cikin Musulmin duniya,
: Maimartaba na Abubakar,
: Ƙi fansa Alhaji Macciɗo.
Ƙoƙarin kawo waɗanda Macciɗo ya gada musamman Bello, da Moyi, da
“Maihausa” kukan kurciya ne na nuna hawa sarautar Musulunci ta gaba ɗaya. A dubi ɗan waƙar farko na gindin waƙar cewa ya yi:
“Farin
cikin Musulmin duniya.”
Sarkin
Kudu aka yi wa waƙar, amma aka nuna farin cikin duniyar
Musulmi ne gaba ɗaya. Waɗannan abubuwa duk martabar mahaifinsa ce
ake yi mishi kukan kurciya da ita, tun
yana Sarkin Kudu, har Allah Ya ƙaddare
shi da hawa gadon mahaifin nasa.
Ambaton
Sa Magajin Mahaifinsa
A koyaushe makaɗa Sa’idu Faru na nuna bai wuce gona tai
da iri ba ga Sarkin Kudu ya tsaya a ‘yan waƙe-waƙensa.
Abin da yake ƙoƙarin nuna wa duniya shi makaɗin ɗan Sarkin
Musulmi ne, bai kai ga darajar yi wa Sarkin Musulmi waƙa ba, amma kuma yana ƙoƙarin kwatanta Sarkin Kudu da Sarkin Musulmi. Ga zancen ƙarara daga makaɗa Sa’idu:
Jagora: Halin ga da Bubakar yar riƙa.
Yara:
Macciɗo ɗai
ka shirin gado haka.
Sa’idu
Faru ya yi wa Muhammadu Macciɗo waƙa a lokacin yana Sarkin Kudun Sakkwato
kuma Sarkin Musulmi Abubakar ke sarauta. Ya nuna irin halayen da Sarkin Musulmi
Abubakar III ke da su ya ce:
“Macciɗo ɗai
ka shirin gado haka.”
Cewar
da ya yi “Macciɗo ɗai” ɗai ɗin
nan tana zaman shi kaɗai a cikin ‘ya’yan sarautar lokacinsa. Ya ƙara da cewa, “shirin” wato ya riga ya
shirya a koyaushe lalurar hawan gado ta taso. Hausawa sun ce, shirin shiga ruwa
tun tudu ake kimtsa shi. Makaɗa Sa’idu Faru ya yanke hukuncin Sarkin
Kudu ya san hanya kamar yadda malamin kiɗi
Dr. Ibrahim Narmabaɗa ke cewa:
Jagora: Ah! Ji wanda bai san hanya ba,
: Ya yi sabko amma fa ya ɓace ya dawo.
Yara: Ila da yat tahi bai ɗora tambayar kowa ba.
Gindi: Ginshimin Haliru Uban zagi na
Malam Isa,
: Gagarau
jikan Shehu Iro mai Shanawa.
Babban kukan kurciya a nan shi ne faɗar “Gado haka”. Bisa ga hasashe makaɗa Sa’idu ya yanke hukuncin Sarkin Kudu Macciɗo zai gaji Sarkin Musulmi Abubakar. Ga
irin hasashen Sa’idu Faru kai tsaye Sarkin Kudu zai kasance Sarkin Musulmi
bayan ƙare
sarautar Sarkin Musulmi Abubakar. Mai ƙaddarowa ya ƙaddaro da haka, amma cikin wani tsari irin nasa tsari
sai da Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi ya yi sarautar Musulunci Sarkin Kudu
Macciɗo ya yi. Kukan kurciya dai ya tabbata ga
fassarar da aka samu ta kasancewar Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo Sarkin Musulmi na (19). Yadda duk
al’amari ya kasance an sara a kan gaɓa.
Kiran Sa Sarkin Musulmi Kai tsaye
Daga
cikin fatar da makaɗa Sa’idu Faru ke yi wa Sarkin Kudu
Muhammadu Macciɗo shi ne, ya zama Sarkin Musulmi. Duk
wata magana da ya yi mai nuna zuwa ga wannan batu ba ta yi ficen wannan ɗan waƙa ba:
Jagora: Dubi ƙahwakka zuwa bisa hannuwa,
Yara: Ka san Shehu na ba wata za’ida.
Jagora: Sarkin Musulmin wataran kake,
Yara: Da
imani da mu’ijjiza na nan ga Malam Macciɗo.
Wannan
zance ya tsallake wanka da kamar jirwaye ya zama filin wuri dabon Ɗankama. An ambaci abu ƙarara ba a sa rana ba balle a ƙayyade lokaci an dai ce: “Wataran” Bahaushe
ko cewa ya yi: “Wataƙila
mai hana wa Bature ƙarya”.
Da “wataƙil”
da “wataran” ma’auninsu ɗaya a nahawu da sarfu da Balaga
Bahaushiya. Yau ga shi, abu kamar ƙaddara
in ji Buzu da ya sha kayen raƙumi. Wannan kukan kurciya fashin baƙinsa a fili yake domin Sarkin Kudu ya
kasance Sarkin Musulmi bayan da Sa’idu Faru ya riga ya koma wa Mahaliccinsa. Ga
al’ada da nahawu, idan ɗan’adam ya ce wani abu
zai auku wataran, ba a tsammanin abin ya faru yana raye. Don haka Hausawa suke
da karin maganar da ke cewa, “Wata rana sai labari.” Ke nan, kukan kurciyar
Sa’idu Faru ya tabbata, Alhaji Muhammadu Macciɗo ya zama Sarkin Musulmi bayan da Sa’idu
Faru ya koma ga Mahaliccinsa. Allah Masani!
Yi Masa
Tarbo Irin na Sarkin Musulmi
Fatar da makaɗa Sa’idu Faru ke yi wa Sarkin Kudu ya sa, ya kawo jawabin
yadda aka yi masa tarbon ban kwana da zai je aikin Haji irin tarbon da ake yi
wa Sarkin Musulmi na kowane zamani. Ya fara da cewa:
Jagora: Bajiri ɗan gagara gasa amalin sarakuna,
Yara: Toron giwa ɗan Audu ƙanen Ali Ɗan’iya,
Jagora: Zuwan da kai Haji na Alu,
Jagora: Sai murna kaɗai mukai,
Yara: Sai babbar fata wadda akai sauka lafiya.
Jagora: Garin da kaz zo Mafara sai murna
kaɗai akai,
Yara: Alƙalin Mafara yai tariyar baba makaye.
Jagora: Da mun zo Maru ko Banaga yai tariya.
Yara: Duk da mutane nai mun ka ishe zaune godabe,
Jagora: Sannu Banaga an sarki ya gaishe
ka,
Yara: Sannu Banaga Allah shi yi ma albarka,
Yara: Sai wata rana ɗan mainasa babba ya wuce,
Jagora: Da mun ka tai Danmarke,
Yara: Mun ishe Sarkin Fillani Bunguɗu ya kawo,
Jagora: Duk da mutane nai sui tariyab baba makaye,
Jagora: Gasau da kaz zo Sarkin Kudun Gusau
yai tariya,
J/Yara: Mai ‘Yandoto Gusau da shi da
Kwatarkwasawa,
Yara: Ga Ƙaura ta kawo, ga kuma Zurmi da Moriki,
Jagora: Ga kuma Zurmi da Moriki ga kuma
Isa Maradun,
Yara: Ga kuma Sabon Birni,
Jagora: Mamman ya kwana Gusau,
Yara: Ya isa Filin Jirgi,
Jagora: Ga sauran sarakuna,
Yara: Za su wurin ban kwana,
Jagora: Ga shi ga Sarkin Daura ga Alhaji
Nasiru,
Ga
kuma Sarkin Gwandu.
Irin
wannan tariya babu wanda ake yi wa irinta in ba Sarkin Musulmi ba. A duba
sosai, an tattaro sarakunan daular Zamfara da Gobir da Gwandu da Daura gaba ɗaya tarbon Sarkin Kudu. Anya! Ba Sarkin Kudu
ne za a yi wa tarbo ba, kukan kurciya ne na kasancewarsa Sarkin Musulmi na gaba
in Allah Ya so. Alhamdu lillahi Allah kuwa Ya so. Wannan kukan kurciya
karatunsa sambai yake.
Hoton Sarkin Kudu Macciɗo a Karagar
Sarautar Musulunci
Makaɗa Sa’idu dai ya yanke hukuncin Sarkin
Kudu ya riga ya hau gadon sarautar Musulmunci a wata waƙar Sarkin Kudu da yake cewa:
Jagora: Toron giwa yana abin da ya kai,
: Ya shigo dawa.
Yara: ‘Yau namu suna ta gaisai,
Jagora: Suna ba da gaskiya,
Yara: Bil’amu na cikin sabara.
Jagora:
Ya soke kainai,
Yara: Zomo
ya taho ya wuce ya gai da toro.
Jagora:
Shi yi yarda Allah ka wa kowa nagarta.
An
riga an yi zaɓe, toron giwa ya kere kowa an zaɓe shi an naɗo sarakuna sun zo sun yi caffa. Babu
ikon da zai rasa masu adawa, da ‘yan-ba-mu-so, ƙin miƙa wuya da Bil’amu ya yi, bai hana wa
zomo zuwa ya yi caffa ba. Zomo ya yarda da cewa sarauta ta Allah ce, ba da ƙarfin tuwo ake zuwa a ɗebo ta ba. Wataƙila zomo ya tuna da karatun malamin
gidansu Dr. Narambaɗa da ke cewa:
Jagora: Sarauta ban da nufin Allah ce,
Yara: Da ɗibat ta akan yi da ƙarfi,
Yara: Waɗanga da nag gaza ganewa,
Yara: Da sun ga ana haka nan da sun yi,
Jagora: Wane a dangana tun ga uwaye,
Yara: Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki.
Gindi: Gogarman Tudu jikan Sanda,
Maza
su ji tsoron ɗan Maihausa.
Matsalar da Sarkin Kudu Zai Ci Karo da
Ita a Zaɓe
Babu
shakka a wajen Allah taskokin gaibi suke babu wanda ya san su sai shi kaɗai. Wannan ba za ta hana a furta wata
magana ta yi daidai da wani gaibi ba, domin da mai maganar da gaibi, duk wanda ya
yi gaibi, da mai magana, ya yi su. A bagiren nazarinmu sai muka kira shi “kukan
kurciya”.
Makaɗa Sa’idu Faru ya ce:
Jagora: Gurbin giwa sai ɗanta,
Yara:
Zomo anka aza yab bar gidan na.
Da
Sarkin Musulmi Abubakar III ya rasu (Allah Ya gafarta masa), sai Allah Ya ba,
Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi (Allah Ya gafarta masa). Bayan cire Sarki Dasuƙi,
sai Allah Ya ba Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo (Allah Ya gafarta masa). Da ya rasu
sai ɗan Sarki Abubakar Muhammadu Sa’adu ya
hau, har yanzu dai tana nan gurbin Sarkin Musulmi Abubakar kamar yadda Hausawa ke
ce wa: “Ja ya faɗo, ja ya ɗauke”. Kukan kurciya a nan, fashin baƙinsa a bayyane yake.
Kirdadon Mutuwar Sarkin Kudu a kan Gadon
Sarautar Musulunci
‘Yan
maganganu da ke fita daga
bakin makaɗa Sa’idu Faru game da Sarkin Musulmi
Muhammadu Macciɗo sun cancanci a nazarce su. Ni, a ɗan nawa bincike makaɗa Sa’idu Faru ya yi hasashen mutuwar Sarkin Kudu a kan abubuwa uku:
a.
Na farko a kan gadon
sarautar Musulunci zai mutu.
b.
Na biyu jirgin sama
zai kashe shi.
c.
Na uku Sa’idu Faru zai riga Sarki Macciɗo mutuwa.
Mu ɗan nazarci wannan ɗan waƙa cikin natsuwa mu ga saƙon yadda yake:
Jagora: Jirgi ya tashi bisa,
Yaro: Jama’a sai hwaɗin sukai,
Jagora: Lafiya dai ɗan Audu,
: Hattara da girgije.
Yara: Manya sun ishe manya,
: In ji mutanen Jidda.
Jagora: Suna ziyartar juna,
Yara: Bawan Allah jikan bawan Allah na Alu,
Jagora: Muna gare ku idan mun ka haɗe,
: Gobe
lahira.
Fashin Baƙi
a.
A cikin jirgin sama
ya yi haɗari su 100 suka mutu.
b.
Jirgin sai da ya
tashi ya daidaita sama’u sosai ya yunƙura.
c.
Daidaitar jirgi a
sararin samaniya an keta hazo a shiga giragizai.
d. Zancen hattara da girgije ya yi canjaras da daidaitar jirgi a
sararin Subhana.
e.
Manya sun ishe manya,
ma’ana manyan duniya sun ishe manyan duniya da lahira (Allah), wato Allah Ya
kira su.
f.
Ziyartar juna ishara
ce da ba za a dawo
ba,
zaman duniya ya ƙare.
g.
Faɗar “bawan Allah jikan bawan Allah” ai
ta’aziyya ce makaɗa Sa’idu ke yi na rashin uban gidansa.
Allahu Akbar!
h.
“Muna gare ku idan mun ka haɗe gobe lahira” nuni ne ga Sa’idu zai
riga wucewa, to in ya riske shi suna fatar samun ceto gobe lahira. Allah Ka
cece mu!
i.
Rufe ɗan waƙar nan da faɗar “gobe lahira”. Kukan kurciya ne sai mai sani ka ganewa.
Sakamakon Bincike
a. Kukan kruciyar makaɗa
Sa’idu Faru a kan samun sarautar Ubangidansa Muhammad Macciɗo ta
tabbata, ya zama Sarkin Musulmi na 19.
b. Hasashensa na maye gurbin Sarkin Musulmi Abubakar daga cikin
‘ya’yan cikin Abubakar ta tabbata ga sarakuna biyu, Macciɗo da Sa’adu.
c.
Hasashen mutuwarsa ta
sanadiyyarta da
tazarar mutuwarsa tsakaninsa da uban gidansa ta tabbata. Allah Shi ne mafi
sani.
Naɗewa
Na
yarda da Hausawa suke
cewa, duk abin da wayo ya ɓoye hankali na gano shi. Da yawa
abubuwan da ke fitowa a bakunan mutane sai a ga sun zamo kamar an san da za su
auku. A al’adance, tsananin soyayya ga wani abu, ko tsananin ƙiyayya gare shi, ko daɗewa tare da shi, ko cikinsa, na sa a ji
zantuka barkatai da wasu daga ciki su kasance. Makaɗa Sa’idu ya rayu da marigayi Sarkin Kudu
Macciɗo a zamanin da yake Sarkin Kudun
Sakkwato. Ya yi masa waƙe-waƙe da yawa da fata daban-daban, waɗanda da yawa daga cikinsu Allah bai nuna
masa su ba. Allah Ya yi rasuwar makaɗa Sa’idu
Faru a matsayin
makaɗin Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu Macciɗo Abubakar III haka kuma, Allah Ya yi wa
Sarkin Kudu Macciɗo rasuwa a matsayin Sarkin Musulmi na
(19) a daular Sakwkato. Allah Ya ji ƙansu da mu, Amin! A koyaushe ake
tattauna irin wannan bagire na rayuwa a riƙa tunawa da tunanin Bahaushe da ke cewa,
sanin gaibu sai Allah; maganar kowa jifa cikin duhu ce ta Allah kaɗai ce nashin ƙasa babu kure. Alhaji Umaru Nasarawa
Wazirin Gwandu na cewa:
Wanda bai wuce shi yi kwana ba,
Bai wuce shi mance abinai ba,
Wanda bai san rabonai ba,
Yaushe
za shi gano min nawa?
Manazarta
Bunza,
A. M.
(2009). Narambaɗa, Lagos: Ibrash Publication Centre 31,
Adelabu Street.
Bunza,
A. M.
(2013). In ba ka San Gari ba Saurari Daka: (Muryar
Nazari Cikin Tafashen Gambo)
Cairo: Elkods Printing Press House.
Burton,
S. H.
(1954). The Critism of Poetry. London:
Longoman.
Daba,
H. A. (1978). “Hausa Oral Poetry: A Case Study of
Adamu Ɗanmaraya
Jos”, M.A. Thesis, Khartum: University of Khartum.
Ɗandatsi,
A. (1975). “The Role of Oral Singer in Hausa/Fulani Society: A Case of Mamman
Shata”, PhD, Thesis, Indiana: Indiana University.
Furniss,
G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in
Hausa,
International African Library, London: Edinburgh Library Press.
Gusau,
S. M.
(1983). Jagorar Nazarin Waƙar Baka, Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau,
S. M.
(1988). “Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanaye-Yanayensu”
Kundin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.
Hamidi, M. F. (1992).
“Garba Supa: Rayuwarsa da Waƙoƙinsa”, Kundin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Omar,
Y. M.
(1970). Kissar Annabi Yusuf, Zariya: NNPC.
Rasmussen,
D. (1974). How Does A Poem Mean? New York: Houghten Mifflin.
Umar,
L. D.
(1981).
“Sa’idu Faru da Waƙoƙinsa”, Kundin BA, Zariya: Jami’ar Ahmadu
Bello.
Yahya,
A. B.
(1997). Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas Media Services.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.