Citation: Gusau, S.M. (2024). Mabuɗin Tarihin Rayuwa Da Fasahohi Da Matakan Shiryawa Da Aiwatar Da Waƙoƙin Makaɗa Sa'idu Faru (1932-1987). Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 29-36. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.004.
Banga, Kaurar Namoda, Faru
MABUƊIN TARIHIN RAYUWA DA FASAHOHI DA MATAKAN SHIRYAWA DA AIWATAR DA WAƘOƘIN MAKAƊA SA'IDU FARU (1932-1987)
Sa’idu Muhammad Gusau
Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano
1.0 Gabatarwa
Tun ran gini ran zane, tun da Hausawa suka
zauni Ƙasar Hausa suke shiryawa da aiwatar da waƙoƙin Baka na Hausa. Haƙiƙa, Hausawa sun jima ainun suna rera waƙoƙin baka da ka har kuwa zuwa lokacin da suka ƙirƙiri wasu sinadarai na gwama waƙar baka da kiɗa.
Kamar yadda ake nunawa, a Ƙasar Hausar Hausa[1] an fara waƙoƙi ne na dandali da na soyayya[2]. Da Hausawa suka sami fasaha ta kayan kiɗa, sai suka durmuya cikin waƙoƙi na farauta da na tauri da na siddabaru ko wobuwa ko waɗanda suke da wata ɗaukaka a rayuwa ta mutane da makamantan waɗannan.
Daga nan ne makaɗa suka saki jiki suka
dinga yi wa Sarakuna da sauran masu jini na Sarauta Waƙoƙi (Gusau, S. M. (1983).
2.0 Tasowar Waƙoƙin Sarauta ko Fada
A yayin da Hausawa suka fara shiryawa da aiwatar da waƙoƙin baka na masu Sarauta sun fahimci Sarakuna su ne masu iko na zartar da abubuwa, masu ƙarfi a zucci da zahiri, masu faɗaɗa garuruwa da ƙarfin tuwo da na takobi, masu yin yadda suke so bisa yadda suke bukata. A daidai wannan lokaci Hausawa sukan kira waƙoƙin waɗannan mutane da waƙoƙin Sarakuna ko waƙoƙin Masu Sarauta ko Sarauta ko fada[3].
Bisa zakuɗe-zakuɗen Masarautu a Ƙasar Hausa, manyan garuruwa da Dauloli da yanaye-yanayen ƙiriniyoyinsu ne suka sanya suka sami wani kaso na makaɗan fada, wato:
a) Makaɗan Sarauta ko Fada
kawai
Haka kuma bayan kama Mulkin Turawa
(1903-1960) sai aka sami makaɗan suna yi wa kowane mutum mai Sarauta waƙa, daɗa:
b) Sarki ne ko
c) Uban Ƙasa ko
d) Dagaci ko
e) Mai’unguwa ko
f) Kowane mutum mai jinin Sarauta
Tun lokacin da Sa’idu Faru[4] ya fara gudanar da waƙoƙi na masu Sarauta, ba abin da ya zamanto a bakinsa sai ƙirƙira da shirya waƙoƙin Sarauta. Makaɗi ne wanda ya yi matuƙar dagewa wajen samar da nagartattun matakai na aiwatarwa da sadar da taraku da tubalai da ɗiya na waƙoƙin fada. Sannan ya sadar da rauji cikin kiyaye daidaito na auna kiɗa da zaɓen kalmomi da suka dace da waƙar. Bisa rerawar ce kuma makaɗa Sa’idu Faru yake ayyana saƙonni, manya da ƙanana, a ingantattun matanoni da ɗiyan waƙa da a saɗarun waƙa da a gaɓoɓi da mabambantan madiru da masaukai na waƙar baka kai da duk ma sauran ƙunshe-ƙunshe ko tarkace-tarkace na waƙar baka ɗaya ko waƙoƙin baka.
A tarihin na yunƙurin rubutu a fasahohin kiɗa na makaɗa Sa’idu Faru waɗanda suka nasu har suka yi jirwaye a shiryawa da gabatar da waƙoƙinsa, na jima[5] da fahimtar wasu abubuwa a cikinsu. Waƙoƙin Sa’idu Faru, waƙoƙi ne da suka ƙunshi falsafofi a garwaye da cusa hikimomi da balagar harshen Waƙoƙin Baka a kuwa yawancin waƙoƙin da ya aiwatar.
A bisa wannan hidima ta waƙoƙin baka Sa’idu Faru ya sami aƙalla shekaru arba’in (40) yana sadar da waƙoƙi na baka, musamman ma waɗanda suka shafi Sarauta da majiɓintanta.
2.1 Muhimman ayyuka na Nazari waɗanda na fitar daga waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru waɗanda ya yi yunƙurin rubutawa sun haɗa da:
‘Sa’idu Faru and the
Deɓelopment of Hausa’
Oral Poetry (Ibadan:1991).
Na so na gabatar da wannan muƙala a Sashen Koyar da Ingilishi, Jami’ar Ibadan a wani taro na shekara-shekara da ake yi a Sashen. Wanda aka nufin gudanarwa a tsakanin 8-11, April, 1991.
2.2 A Littafin Makaɗa da Mawaƙan Hausa, S. M. Gusau
Ɗab’in Fisbas Media Serɓices, Kano 1987-1996
an kawo;
Kashi na Uku sh:
Makaɗan Sarakuna na II
102
Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun 104
Alhaji Sa’idu Faru 117
Sarkin Taushi Muhammadu Ɗanbunguɗu 128
Muhammadu Ango Maitabshi 140
Umaru mai Sa’a Tubali 153
Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo 163
Alhaji Sa’idu Maidaji Sabon Birni 171
Alhaji Abu Ɗankurna Maru 176
Muhammadu Maidamma Sarkin Taushi 186
2.3
A kuma Littafin Diwanin
Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Ɗaya, S.M. Gusau, 2009 Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa: Century Research and Publishing Limited
Kano, an zo da waɗannan matanoni na wasu waƙoƙin Sa’idu Faru;
1.45 Gwabron Giwa Uban Galadima 145
Sarkin Yaƙin Banga, Alhaji Sule Ƙauran Namoda
1.46 Kana Shirye Baban ‘Yanruwa 152
Sarkin Kudu Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III
1.47 Bajinin Gidan Bello Mamman na Yari 158
Sarkin
Kudu Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III
1.48 Koma Shirin Yaƙi 159
Sarkin
Fulanin Bunguɗu Alhaji Shehu
1.49 Tsakin Tama na Abashe 161
Turakin Kano Alhaji Amadu
1.50 Dangalin Maza Jikan Shehu Sarkin Kudu 165
Sarkin
Kudu, Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III
1.51 Koma Shirin Daga Bubakar 170
Sarkin
Yawuri Muhammadu Tukur (1955-1981)
2.4 Shi kuwa Littafin Diwanin
Waƙoƙin Baka, Juzu’i na Biyu, S.M. Gusau Century Research and
Publishing Limited, Kano, 2014
ya kawo matani na
wanan waƙa ne:
1.4 Sa’idu Faru 27
Gwauron
Giwa Jirayi Gaba na Amadu
Alhaji
Amadu Sarkin Kiyawa na Ƙauran Namoda
2.5 A LittafinWaƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa:
Yanaye -Yanayensu da
Sigoginsu, S. M. Gusau,
Benchmark Publishers
Limited, Kano, 2008 an yi
Bayanai da suka
danganci waɗannan abubuwa:
1.2.5 Sarakunan Tsohuwar Daular Zamfara 23
1.2.8 Sarakunan Maru da Bunguɗu 31
2.1 Tarihin Kiɗa a Ƙasar Hausa 53
3.1 Asali da Tasowar Makaɗan Baka na Hausa 110
5.0 Turke da Nau’o’insa a Waƙoƙin Baka na Hausa 369-390
5.5 Wasu Ginduna na Waƙoƙin Baka na Hausa:
Gindunan Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru (1932-1987) 404-408
2.6
Fasahohi da Falsafofin
Sa’idu Faru
Sa’idu Faru, makaɗi ne wanda waƙoƙinsa suke a tumbul da fasahohin da ya yi ta shisshiryawa
yana sadar da su a waƙoƙinsa na masu Sarauta. Idan aka nutsu sosai ainun za a
fahimci duk da ƙarancin shekaru na Makaɗa Sa’idu Faru, makaɗi ne wanda ya ciri
tuta a wajen sarƙa kalmomin waƙa masu kaifafa
tunani, masu janhali, masu sanya a ƙure adaka a
tsinkayowa da fahimtar madosa ko mahangoginsu. Ga wasu misalai na waɗannan fasahohi da
dabaru kamar haka:
2.6.1
Sa’idu Faru Yakan yi
Dabarar Mutuntarwa da Dabbantarwa
Sa’idu Faru ya ƙware a Jingina wasu ayyuka na mutane ga wasu dabbobi da
ba nasu ne bisa asali ba kuma yakan ɗauki halaye na dabbobi ya ɗora wa mutane da ba a
san su da su ba irin dabarun nan ne manazarta suke ambata da jinsartarwa ta mutuntarwa
ko ta dabbantarwa.
Sannan kuma ana jin makaɗan baka na Hausa su
ne suka fara ɗaukar gabata a sarƙa irin dabaru na
mutuntarwa ko dabbantarwa.
Haka kuma ana ganin kamar Sa’idu Faru ne ya
yi fice a sahu na makaɗan baka masu zalaƙa da baiwa ta shirya
maganganun jan hankali da sukan ta’allaƙa da mutuntarwa ko
dabbantarwa, wato dai mutane ko dabbobi. Ga wasu misalai daga waƙoƙin Sa’idu Faru kamar haka:
Jagora: Duka,
‘Y/Amshi: Al’amarin duniyang ga sai Allah,
: Ɗansambo Rungumi.
Jigogi:
Ko jiya na iske gamdayaƙi da tuji,
: Sun sarƙa gardama,
: To sun ko mirɗa gardama,
: Sun iske su bubuƙuwa ruwa,
: Dannan sai ni ko ina gaton gaɓa,
: Sai nik ƙwala gaisuwa,
: Su ko sun dwaƙile ni duk,
: Ni ko nik ƙara gaisuwa,
: Dannan gurbin da ac cikin gurbi,
: Ya amsa gaisuwa;
(Sa’idu
Faru, Gwabron Giwa, sh: 149)
Jagora
(Mu’azu): Can nak kusa kai wa Zariya,
: Dannan Daudu ni ko sai nit tsaya,
: Sai Sarkin Zazzau nig gani,
: Ya ce man Muhamman ya tai Haji,
: Sai nis saki hanya niy gabas,
: Can na taɓa yat tafiya kaɗan,
: Sai ni ishe Suda na kiwo,
: Tana ta waƙar Sarkin Kudu,
: Rainai ya daɗe Sarkin Kudu,
: Ala Sabbinani ɗan Amadu,
‘Y/Amshi: Allah shi ƙara ma nasara. Ɗ2
Mu’azu:
Nic ce Suda waƙa a kai,
: Ta ce lalle waƙa nikai,
: Waƙam Mamman Sarkin
Kudu,
: Waƙam nan da Ɗan Umma yai mashi,
: Baicin uwat tsuntsaye nike,
: In da kamam mulki na nikai,
: Da nai mai wasiƙa yai min kiɗi
(Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa, Juzu’i na Ɗaya, S. M. Gusau, 2009)
2.6.2
Salon Magana ko Wasa
da Harshe
Har wa yau kuma
Sa’idu Faru yana daga cikin makaɗan baka da suka fara shigar da dabara ta wasa da harshe
ko ƙarangiya ko maimaita kalmomi masu sauti iri ɗaya a gaɓoɓinsu ko magana mai salo,
irin na salon magana. Ga misalai:
Jagora: Yaro in taƙamar salon magana kaka yi,
: Ce tsare tsara,
'Y/Amshi: Tahi
tsantsamin tsantsara,
: Ka tsantsame tsari tsab ga tsamiya,
Jagora: Tunkuɗa tunku cikin tukar rukuɓu,
: Tukuɗin Tumba yai tuɓus,
'Y/Amshi: Tumba taho
yau da ke da Tab da Taɓo,
: Da tuɓus da 'Yattuɓus.
Akwai kuma:
Jagora: Ban da gudu
ban da razana,
'Y/Amshi: Ka san
Sarki ba shi waiwaya,
Jagora: Ban da gudu
ban da razana,
'Y/Amshi: Ka san
Sarki ba shi waiwaya,
: Ko da jan Gwamna ya gani,
: Ko da jan Zaki yag gani.
(Gwabron giwa Uban Galadima, Waƙar Alhaji Sule, Sarkin Yaƙin Banga, Diwani na Ɗaya, 2009, S.M. Gusau)
Sai kuma:
Jagora:
Gwabro mai shekara guda ag gwabro,
: Ba dai biyat ba.
‘Y/Amshi:
Gwabro mai shekara bakwai,
: Shi wannan ya zama gwarangwani.
(Sa’idu Faru: 1.45 Gwabron Giwa Uban
Galadima, sh: 151)
2.6.3 Rarrabe Halaye na
Mutane
Sa'idu Faru ya
zayyana yanayi da yadda mutane suka rarrabu da sauran halittu na Allahu. Allah
bai halicci mutane a duniya su zama suna da halaye da yanaye-yanayen rayuwa iri
ɗaya ba. Kowane mutum yana da yadda aka ƙaddara masa rayuwa a duniya. Dubi yadda Sa'idu Faru ya
rarrabe nau'o'i na mutane kamar haka:
Jagora (Mu'azu): Tun
ran da Allahu yai duniya,
: Nan ya yi mutum mai
ƙoƙari,
: Nan ya yi mutum mai
kyawo,
: Kuma ya yi mutum mummuna,
: Nan ya yi mutum mai
haske,
: Kuma ya yi mutum
mai dauni,
: Nan ya yi mutum mai
samu,
: Kuma ya yi mutum
mai rauni,
: Nan ya yi mutum mai
ɗan Sarki,
: Kuma ya aza bawan
Sarki,
: Nan ya yi mutum iko,
: Kuma ya aza mai roƙonai,
(Sa'idu Faru: 'Kana Shire Baban 'Yanruwa',
sh:154, Diwani na Ɗaya, 2009)
2.7 Makaɗi da Ubangida
Babu shakka Sa'idu
Faru, Allah ya jiƙan sa da gafara, ya yi wa Alhaji Muhammaaddu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi
Abubakar III waƙoƙi da dama a matsayi na Ubangidansa. A lokacin kuwa yana bisa
matsayin Hakimi, mai riƙe da Sarautar Sarkin Kudun Sakkwato, sannan kuma tun yana
riƙe da Sarautar Uban Ƙasa ta garin Talata Mafara
a cikin Jihar Zamfara a yau.
Amma saboda hangen
nesa da sanin falsafar rayuwa ta Hausawa, Sa'idu Faru bai yi wa Ubangidansa
zurum ba. Ya yi wa Sarkin Kudu Macciɗo Abubakar III addu'o'i na ya gaji iyaye da kakanninsa,
shi ma ya zama Sarkin Musulmi. Allah kuma ya ƙaddara hakan cikin yardarsa da amincewarsa da ikonsa[6]. Ga misali:
Mu'azu (Jagora): Faɗi gaskiya Bello kai
Shehu yac ce,
: Bari masu su son
duk su maishe ka yaro,
: Da kyauta da ilimi
da neman dalilin,
: Da gode wa Allah da
istigfari,
: Da su Bello ɗan Shehu ya tsarma
kowa,
: Ka kai kamab Bello
ka gaji Moyi,
(Sa'idu Faru: Bajimin
gidan Bello Mamman,
Diwani ya Ɗaya, 2009, sh: 158)
A wani ɗan waƙa Sa'idu Faru yana cewa:
Jagora (Mu'azu):
Maganag ga da za ni faɗa maka,
: Gagarau ɗan Aliyu kai man
gafara,
: Wada duk aka gadon ƙasura,
: Wada duk aka gadon ɗaukaka,
: Wada duk aka gadon
ci gaba,
: Mamman ka gaji
Abubakar,
: Ko da sayen halin
nan akai,
'Y/Amshi: Baba hali da kakai kuɗɗi shikai,
: Kana shirye baban
'yanruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
(Sa'idu Faru: Diwani na Ɗaya, 2009, sh: 154)
3.0 Kammalawa
Tun a farkon wannan dunƙulallen tarihin Makaɗa Sa'idu Faru an nuna an haife shi a shekarar 1932, a cikin mazauni na Banga, Ƙaurar Namoda a Jihar Zamfara[7]. Sa'idu Faru ya fara kiɗan kotso a garin Banga da Kiyawa da Ƙauran Namoda da Zurmi da Wurno har kuwa ya fito zuwa Kano da Talata-Mafara da Sakkwato da sauran wurare, manya da ƙananan garuruwa a farfajiya ta Ƙasar Hausa.
Mahaifin Sa'idu Faru Makaɗa Abubakar Faru ne jagaban kiɗa na Sa'idu Faru da shi kuwa da dukkan ƙannensa, musamman ma Mu'azu Rungumi. Ya ɗora su bisa hanya kyakkyawa wadda take cike da laduban kiɗa bisa tafarki na Hausawa.
Makaɗa Sa'idu Faru ya yi kiɗan noma da kuma kiɗan Sarauta waɗanda dukka ya gaje su
daga wajen mahaifinsa.
Daga cikin waƙoƙin Faru na farko akwai wadda aka yi tsakure nata kamar haka:
G/Waƙa: Bida maza ɗan Jadi na Iro,
: Iro mgajin Shehu da Bello,
Jagora: Ruwa da kada ɗibgau na Magaji,
'Y/Amshi: Sai tsohon wawa ka shigar su.
Kamar yadda aka bayyana a baya, Sa’idu Faru
ya yi biya ta kiɗa. Ya yi waƙoƙi na gayauna a inuwar waƙoƙin kotso na yaƙi da na noma da kuma
na fada. Daga nan ne Sa’idu Faru ya zama masanin kiɗa na waƙoƙin Sarauta. Kuma har ya zama makaɗin Sarkin Kudun
Sakkwato, Alhaji Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III (1938-1988).
Ƙungiyar Sa'idu Faru ta Kiɗa (Kotso):
Sa'idu Faru: Jagora
Mu'azu: Rungumi/Marafa, Ƙulli, Ƙari/Amshi
Ɗandolo: Kiɗa da Amshi
Lawali : Kiɗa da Amshi
Ibrahim Fari: Kiɗa da Ƙari da Ƙulli/Amshi
Ibrahim Makaɗa: Kiɗa da Ƙulli da Ƙari/Amshi
Ƙungiyar Makaɗa Sa'idu Faru ta Kiɗan Kotso
Makaɗa Sa'idu Abubakar Faru mutum ne mai kaifin basira, mai azanci, masanin balagar harshen Hausa, mai iya ɗora kowace magana a muhallinta da lagonta da kuma madosarta ko madirarta a zance na baka.
Akwai bukatar masu nazari da bincike da ƙoƙarin rarrabe ko yi wa waƙoƙin Sa'idu Faru sharhi cikin kadadu su dinga tantancewa da waƙoƙin da Sa’idu Faru ya aiwatar a muhallu mabambanta. Alalmisali, akwai waƙoƙin da ya yi masu yawan gaske da suka dangance kiɗan yaƙi ko kiɗan noma, kai hatta ma da kiɗan jarumai.
Har wa yau, makaɗa Sa'idu Faru ya yi kiɗa na gayauna ga Sarkin yaƙin Banga da gayaunar kiɗan noma ga jagabannin noma kamar Sarkin Noma da Gojen Noma da Ƙauran Noma da makamantansu. Ya kuma yi gayaunar waƙoƙin wasu iyayen ƙasa tun kuwa yana yin waƙa ƙarƙashin mahaifinsa Makaɗa Abubakar Faru.
Haƙiƙa daga bisani ne Sa'idu Faru ya haɗu da Alhaji Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar III suka shaƙu da juna, suka ƙaunaci juna, har Sa'idu Faru ya zama makaɗinsa, shi kuma macciɗo ya zama ubangidansa na ƙut-da-ƙut.
Kamar yadda aka nuna a baya, Makaɗa Sa'idu Faru ya zauna a ƙarƙashin Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III tun kuwa yana riƙe da muƙamin Sarkin Kudun Sakkwato kuma Uban Ƙasar Talata-Mafara. A zamanin Muhammadu Macciɗo yana ɗan Sarki mashahuri, mai sharafi, masoyin kowa da kowa[8].
Hakazalika, yana da kyau a fahimci, makaɗan Hausa waɗanda suka biyo bayan Sa'idu Faru sukan wadatu da wasu dabaru na waƙoƙinsa waɗanda sukan jejjefa su a cikin waƙoƙinsu sa'i da lokaci. Dubi wasu sassa na zubin waƙoƙi, kamar ƙulli ko ƙari da wasu makaɗan sukan aro dabaru na Sa'idu Faru su alkinta su da waƙoƙinsu.
Wani abin la'akari a nan shi ne, masu nazari da bincike da sharhin waƙoƙin baka a jami'o'i mabambanta, waɗanda ake kyautata fahimta su ne suke dagewa su gabatar da ayyukan fasahohin baka na waƙoƙin makaɗan baka. Waɗannan masu jaddada ƙoƙari da himmatuwa da jajircewa ya dace su yi ta zaƙulo waƙoƙin waɗanda Sa'idu Faru ya yi da shi da ƙaninsa Mu'azu Rungumi sannan su ƙalailaice su, su rairaye tsakuwa cikin tsaki.
Haka kuma abu ne mai matuƙar alfanu al’ummar Hausawa su jimri biya suna ƙwaƙwalo waƙoƙin da Sa'idu da Mu'azu suka aiwatar kuma suka sadar, musamman ma tun daga lokacin da suke zaune a ƙarƙashin mahaifinsu Makaɗa Abubakar Faru suna cin gayauna ta waƙa. Yin haka zai daɗa sa ba za a taɓa mantawa da waƙoƙin da su Faru suka yi na baya ba, ballantana har a tattaru a waƙoƙin Alhaji Macciɗo Abubakar III.
Yin nazari na waƙoƙin Sa'idu Faru ba tare da ambato na waƙoƙinsa na baya ba, ai kamar an tuɓe masa taguwa an bar shi sanye da riga kawai.
Makaɗa Sa'idu Faru, makaɗi ne wanda ya sami laso[9] biyu a rayuwarsa ta waƙa a duniya tun daga lokacin da ya fara waƙar baka har zuwa rasuwarsa (a 1987).
A wannan takarda ana jin Sa'idu Faru ya sami aƙalla shekaru arba'in (40) tun daga ƙuruciya zuwa rasuwa yana yin waƙa.
Amma duk da waɗannan shekaru da ya samu a duniya, Allahu ya ba shi hikima da zalaƙa na yin waƙa cikin shirya kalmomi da jumloli masu sajewa da waɗanda yake yi wa waƙoƙi. Yana kuma da harshe na kyautata zubi da rauji da sanin masaukar ko madirar ɗan waƙa. Allahu kuma ya ƙunsa masa fahimta ta yin manuni da wasu halittu kamar tsuntsaye da dabbobi da ƙwari da kifaye da kadonni da dorinu da sauran halittu na cikin ruwa da na tudu da Allah ya mallaka masa fahimtarsu.
Allahu ya gafarta wa Alhaji Sa’idu Abubakar
Faru da ƙaninsa Mu’azu da ɗansa Ibrahim Fari da dukkan zuriyya tasu tun daga iyaye
da kakanni. Muna roƙon Allah ya lulluɓe su da rahamarsa, ya karɓi ayyukansu kyawawa.
Muna roƙon Allah ya sanya harshensu a waƙa ya zama abin koyi mai shiryawa zuwa Musulunci.
1. Manazarta
2. Abdulƙadir, D. (1975) The Role of an Oral Singer in Hausa
/Fulani Society: A Case Study of Mamman Shata. Ph. D. Thesis. Indiana University.
3. Bello,
M. (2020) A History of Modern Industries in Gusau. TETFUND: Tertiary
Education Trust Fund. TETFUND/DESS/UNI/GUSAU/AMB/2018-2019/1. Sokoto: University
Press Limited, Usmanu Ɗanfodiyo University.
4. Garba,
M. (1995) Nazarin Azanci a Cikin Waƙoƙin Makaɗan Baka na Hausa. Binciken Digiri na Biyu. Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami'ar Bayero.
5. Gusau,
S. M. (1983) 'Waƙoƙin Noma na Baka'. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Harsunan
Nijeriya. Kano: Jami'ar Bayero.
6. Gusau,
S. M. (1988) 'Waƙoƙin Fada: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu'. Kundin Digiri na
Uku. Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami'ar Bayero.
7. Gusau,
S. M. (1991) 'Sa'idu Faru and the Development of Hausa Oral Poetry'. Takarda da aka Ƙudurci Gabatarwa a Taro na Goma na Shekara-Shekara a
Adabi a Afirka. Wamda Sashen Koyar da Ingilishi, Jami'ar Ibadan yake Shiryawa.
8. Gusau,
S. M. (2000) 'Kirari a Waƙoƙi Makaɗan Hausa' a Cikin Hausa Studies, Ɓol.II, No 2. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo.
9. Gusau,
S. M. (2001) 'Waƙar Gogarman Tudu ta Ibrahim Narambaɗa a Mazubin Nazari'.
a Cikin Algaita: Journal of Current Research in Hausa Studies, Ɓol. 1, No. 1, Noɓember 2001. Department of Nigerian Languages Series 1. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero.
10. Gusau,
S. M. (2008) Waƙoƙin Baka a Ƙasar
Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu, Kano:
Benchmark Pubishers Limited.
11. Gusau,
S. M. (2008/2009) 'Jirwayen Cimakar Hausawa a Waƙoƙin Baka na Hausa' a cikin Proceedings of the 2nd
International Conference on Hausa Studies. Africa and European Perspectiɓes. Kano: Bayero University
and Napoli: University Degli Studi di Napoli 'L,'Oriental'.
12. Gusau,
S. M. (2009) Diwanin Waƙoƙin Baka. Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Juzu'i na Ɗaya, Kano: Century Research and Publishing Limited.
13. Gusau,
S. M. (2011) 'Tarihi da Hanyar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya a
Taƙaice: Department of Hausa, Katsina, Federal College of
Education & Kano: Century Research and Publishing Limited.
14. Gusau,
S. M. (2019) 'Sarki Majiɓincin Makaɗi' a cikin Algaita: Journal of Curreent Research in
Hausa Studies, Ɓol. 12, No. 2 December 2019. Department of Nigerian
Languages Series 1. Kano: Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero .
15. Gusau,
S. M. (2021) 'Feɗe Waƙar Jarumar Mata Bisa Gadon Nazari na Waƙar Baka Bahaushiya ta Makaɗi Hamisu Yusuf
Breaker a Algaita: Journal of Current Research in Hausa Studies, Kano:
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero.
16. Gusau,
S. M. (2014) Diwanin Waƙoƙin Baka. Juzu'i
na Biyu, Kano: Century Research and Publishing Limited.
17. Gusau,
S.M. (2014) 'Makaɗan Hausa Jiya da yau' a Cikin Garkuwan Adabin Hausa: A
Festschrift in Tribute to Abdulƙadir Ɗangambo. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar
Bayero.
18. Gusau,
S.M. (2019) 'Harshen Makaɗi a Zubin Diyan Waƙa Bahaushiya', A
cikin Algaita Journal of Cuurrent Research in Hausa Studies. Kano: Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero.
19. Gusau,
S.M. (2021) 'Aiwatarwa da Sadarwa a Waƙoƙin Baka na Hausa' a cikin A Great Scholar and
Linguistics: A Festschrift in Honor of Professor Ibrahim Ahmad Mukoshy. Kaduna:
Amal Printing Press Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu
Danfodiyo.
20. Gusau,
S.M. (2023) Tarihin Rayuwar da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a Aiwatarwa da Sadar da Waƙoƙin Baka na Hausa (Lead Paper 1) a cikin Studies on the
Poetic Dynasty of Musa Ɗanƙwairo Maituru Ƙanen Makada Maradun.
Proceedings of the 30 Years. Commemoratiɓe Confrence of Musa Ɗanƙwairo Maradun. Published for the Department of Nigerian
Languages, Bayero University, Kano: Kano Printing and Publishing.
21. King,
A. Ɓ. (1967) 'Music at the Court of Katsina'. London University
of London.
22. MaiKafi,
S. (1977) 'Waƙoƙin Mata Hausawa na Gargajiya: Musamman Waƙoƙin Niƙa da na Daɓe'. Sashen Harsunan Nijeriya. Kano: Jami'ar Bayero.
23. Sada,
S. Y. (1979) 'The Social and Prosodic Features of Oral Poetry'. M. A. Thesis.
Kano: Jami'ar Bayero.
[1]
a) Tun da farko waƙar
baka a Ƙasar
Hausa a rere ake yin ta, da ka da kuma fatun baki.
b) Waƙar baka wadda take a tare da jijjiga ko
karkaɗa ko doddoka sassan jiki kamar
tafuna da duwawu da ƙirji
da ƙafafu da
sauransu.
c) Waƙar baka tana amfani da wasu kayan aiki na
mata ko na maza, waɗanda ba
an yi su domin a yi kiɗa ba.
Daga cikinsu akwai shantu da dutsin niƙa da turmi da taɓarya
da madaɓi da ƙwarya da dabarun raino da saƙa da hannuwa da ƙirji da makamantansu.
d) Sannan akwai kaya da Hausawa suke
tankawa suke yin kiɗa da su kawai
kamar kalangu da zari da ganga (fara ko baƙa) da kuwaru da kotso da sauransu da yawa.
e) Kayan kiɗan
da Hausawa suke sarrafa su daga wasu sassa na jikunkunan dabbobi, misali ƙaho da tantani da tsarkiya da
yisga, musamman ta doki da fatunansu suna harhaɗa
abubuwan kaɗawa ko busawa ko
ire-irensu.
f) Wasu kayan kiɗa
baƙi waɗanda
bisa yau da gobe suka shigo ƙasar
Hausa har kuma Hausawa suka saba da amfani da su.
Misali
kotsayen Filani da Mikirifon da Miksa da Tsintsiya da sauran kaya na ɗakin
Sitidiyo da na kiɗan Disco da
makamantansu (Gusau, 1988).
[2]
a) Akwai wata tafiya da muka yi a Khartoum, babban birnin Sudan. A wannan
tafiya mun ziyarci wasu mashahuran makaɗa
a Sudan (Muganni ko Almuɗrab ko
Fannan) da suka yi fice a waƙar
baka ta Sudan kamar Usman Hisen (ya rasu 2008). Mun ziyarce shi a zango na
la’asar sakaliya, muna gidansa har zuwa sallar isha’i. Wani abu ne kuwa ya faru
wanda ya riƙe
mu. Jim kaɗan bayan gama
sallar magriba, shafaƙi
ya ɓuya, duhu ya shiga. Sai Makaɗin
ya ji yaran Unguwa sun kama waƙe-waƙe. Sai ya daina sauraronmu ya koma
yana jiwo waƙe-waƙen ‘yan mata na dandali daga nesa.
Sai can kawai muka ji ya fara yin waƙa, har ya tashi a tsaye yana tafi. Haka
kuma na kallaci wata tattaunawa da aka yi da Muhammad Wardi (ya rasu
19/02/2012) a 1991 a Talabijin da ta Bidiyo. A tattaunawar da Muhammad Wardi ya
yi irin wannan bayani. Kuma ya nuna sukan sarrafa kayan kiɗansu
daga abubuwan da suke samowa a daji na yankinsu, ba su da bukatar su tafi wani
waje ko wani wuri daban.
A yayin da muka ci gaba da tattaunawa da waɗannan
makaɗa sun bayyana mana waƙoƙin na asali a Arewacin Sudan su ne waɗanda
samari da ‘yan mata suka dinga aiwatarwa a hirar su ta cinye dare. Daga nan kuma
muka fahimci waƙoƙin dandali na ‘yan mata da ‘yan
maza ne suka zama na farko-farko a Arewacin Nijeriya.
b) Wasu Al-Muɗrab
ko Al-Muganni ko Alfannan da aka yi a Sudan Khartoum su ne Kamar:
1.
Usman Hisen (2008 Rasuwa)
2.
Muhammad Wardi (Fannan) (19/12/2012 Rasuwa)
3.
Muhammad Al-Amin
4.
Kamal Tarbas (Yana a Raye)
5.
Ibrahim Hesen (Yana a Raye)
6.
Salah ibn- al-Badiya
7.
Ahmad Rayya (Yana a Raye)
8.
Salman Al-Farisi (Fannan a Sudan) yana a raye
9.
da sauransu.
[3]
Ana ji a lokacin Sarakuna sun daɗa
bunƙasa
garuruwa zuwa dauloli marasa ƙayyadaddun
iyakoki ko masu iyakoki (Dauloli a Ƙasar Hausa, 2024) Makaɗi
yakan nauyaya alkadarin Daula, ya ƙarfafa ta, ya fifita ta, ya fito da nauyi
na ƙarfinta
ba tare da nuna tsoro ba. Shi makaɗi
ba a kan kashe shi a yaƙi
ba, akan ɗaura wa makaɗi
laya wadda za ta hana a iya kama shi a yaƙi. Haka kuma idan ya sami dama ya kaɗa
gangarsa akan ƙyale
shi. Sai dai idan aka rinjayi rundunarsa a yaƙi, yakan koma ƙarƙashin rundunar da ta rinjayi tasa, kuma ya
zama makaɗinta ba tare da nuna
wata kunya ba.
[4]
Sa’idu Faru makaɗi ne wanda ya
gaji kiɗa da iyaye daga
kakanninsa. Sa’idu Faru ya yi kiɗa
na jarumai ne da suka shafi mayaƙa kuma masana dazuzzuka da abubuwan da
suka tattaru da su. Ya laƙantu
da sanin wasu fasahohi ba na ɗan’adam
ba har na tsuntsaye da dabbobi da dazuzzukan da suke zazzaune a cikinsu.
Akwai
Umma, matar ƙanen
mahaifinsa da shi kansa Sa’idu Faru da ‘yan’uwansa na kiɗa
dukka sun yi wa Sa’idu Faru kirari a kan zalaƙoƙin da Allahu ya yi masa. Misali:
·
Kundumin
Kiɗan Fada
·
Mai Kwana
Ɗumi
·
Na Mamman
na Balaraba
·
Ɗan Umma Rungumi ko Kandami
·
Ɗan Tumba Rungumi
[5]
Lura da ilhamomin da Allahu ya danganta shi da su, ko ya hore masa su.
[6] Allahu
cikin kun-fa-ya-kun, da amincewarsa da yardarsa, ya yi wa Alhaji Muhammadu
Macciɗo Sarautar Sarkin Musulmi a shekara
ta 1995-2007. Shi kuma Makaɗa Sa’idu
Faru ya rasu a shekara ta 1987. A kuma wannan lokaci na rasuwar Sa’idu Faru ya sami
shekaru kusan ashirin (20) daidai, sannan Allah ya nufi Alhaji Macciɗo
ya zama Sarkin Musulmi.
[7]
A halin yau garin Ƙaurar
Namoda ya zama gunduma kuma yanki na Ƙaramar Hukuma a cikin Jihar Zamfara wadda
Janar Sani Abacha ya ƙirƙiro ta a 1/10/1996.
[8]
Kamar yadda aka bayyana a baya, kafin Allah ya karɓi
ran Alhaji Muhammadu Macciɗo, sai da
ya ci Sarauta ta Sarkin Musulmi, ya gaji mahaifi da kakanninsa. Muna roƙon Allahu ya yi masa gafara, ya jiƙan sa, ya lulluɓe
shi da rahama da shi da kuma makaɗinsa,
Marigayi Sa'idu Faru.
[9] A bisa zamantakewar
Hausawa, Laso, yana yin nuni ne a kan shekaru 20. Ke nan shekara ashirin sau
biyu, arba'in daidai (40). Sa'idu Faru daga 1932-1987.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.