Jagoran Jawabi a Wajen Buɗe Taron Ƙasa Da Ƙasa Da Sashen Nazarin Harsuna Da Al’adu Na Jamii’ar Tarayya Ta Gusau, Jihar Zamfara Nijeriya Ta Shirya Domin Karrama Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Sarkin Musulmi Na Goma Sha Tara (19), Ta Nazarin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, Makaɗin Sarkin Kudu Macciɗo Da Wasu Manyan Sarakunan Ƙasar Hausa, Ranar 5/5/2024.
Ø Ɗanmajisar Wakilai ta Tarayya mai
wakiltar Ƙananan Hukumomin Maru da Bungudu,
Hon. Abdulmalik Zubairu (Zannan Bunguɗu).
Ø Shugaba da ‘Yan Majalisar Dokokin
Jihar Zamfara.
Ø Maigirma Kwamishinan Ilmi na Jihar
Zamfara, Alhaji Wadatau Mawaki.
Ø Manya- Manyan baƙin
da ke wakiltar Iyalan Gidan Sarkin Musulmi na Sha Tara (19), Alhaji Bello Muhammadu
Macciɗo
Abubakar na III.
Ø Iyalan Gidan Alhaji Sa’idu Faru ƙarƙashin
Jagorancin Makaɗa
Ibrahim Sa;idu Faru.
Ø Manya- Manyan masana na nesa da
na kusa waɗanda
suka samu damar halartar wannan taro.
Ø Maimartaba Sarkin Zamfaran Anka
kuma Shugaban Majalisar Masarautun Jihar Zamfara, Alhaji Attahiru Ahmad
Muhammad (CON).
Ø Wakilin Mai’alfarma Sarkin
Musulmi Dr. Muhammad Sa’ad Abubakar III CFR, Sarkin Katsinan Gusau, Alhaji
Ibrahim Bello OFR.
Ø Babban Maimasaukin baki, Shugaban
Jami’ar GwamnatinTarayya ta Gusau Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau.
Ø Masu Martaba Sarakunan Talatar
Mafara, Maru, Kwatarkwashi da Shinkafi.
Ø Sauran jama’a maza da mata.
Assalamu alaikum wa rahamatul
lahi ta’ala wa barakatuhu.
Bayan
gaisuwa ga manyan baƙi, an nemi in yi jawabi a kan
taron ƙasa da ƙasa
game da tarihin rayuwa da kuma waƙoƙin
Makaɗa
Sa’idu Faru, Allah ya yi masa gafara, amin.
Haɗuwarmu
a wannan bagire a yau, domin mu karrama Mai’alfarma Sarkin Musulmi na goma sha tara
(19), ta fuskar nazarin waƙoƙin
da Sa’idu Faru ya aiwatar zuwa ga Sarakunan ƙasar
Zamfara da kuma waɗanda
ya yi wa babban Ubangidansa Sarkin Kudun Sakkwato kuma Sarkin Musulmin Daular
Usumaniyya (1996-2006).
Alu
Maikurya Bagobirin da ya yi zamani da Sarakunan Daular Gobir yana yi musu kiɗan
yaƙi. Bayan watsewar Daular Gobir,
sai ya koma yi ma Sarakunan Zamfara kiɗan fada tsawon zamani, wannan shi
ne kakan Sa’idu Faru. Domin shi Alu, mahaifi ne ga Abubakar Kusu, mahaifin Sai’du
Faru.
Mahaifiyar
Sa’idu sunanta Halimatu mutumniyar ƙasar
Banga ce. Banga yanzu gunduma ce a cikin ƙasar
Ƙauran Namoda, ta jihar Zamfara.
An
haifi marigayi Makaɗa
Sa’idu Faru a garin Faru, gundumar Masarautar Maradun da ke Jahar Zamfara a
shekarar 1916.
Sa’idu
Faru ya fara halartar fagaigan waƙar mahaifinsa yana ɗan
ƙarami tun bai iya saka bante ba,
wato bai san me ake ce ma waƙa ba (1920). Mahaifinsa yana yawo
da shi gidajen Sarakuna bisa kuturin doki domin aiwatar da waƙa.
Daga bisani sai ya zama ɗan karɓin
waƙa. Duk wannan ya faru tun kafin
Sa’idu ya kai shekaru bakwai da haihuwa. Har yana shaida wa Alhaji Hamza Sanusi
Funtuwa wanda ya shirya wata tattaunawa da shi inda yake cewa ko da na fara zuwa
amshin waƙa ina ɗan
ƙarami har in nish sha hura cikina
sai ya yi kamar tulu haka nan sai in yi ta kwana har a gama waƙa
ban san an yi an gama ba (yayidariya).
Tun
ina ɗan
amshi har na fara jan ragamar waƙa. Sa’idu Faru bisa shawarar da
suka yanke (tsayar) da ‘yan uwan haihuwarsa (Alhaji Mu’azu, da Mamman) cewa su dakatar
da (hana) mahaifinsu yin kiɗa, domin a fahimtarsu mahaifinsu
ya wuce a ce yana goggoriyon waƙa da shi da makaɗan
wannan lokaci saboda shekarunsa sun yi nisa, sai suka hutar da shi da ƙarfi
da yaji. Sakamakon haka ne, Sa’idu ya ɗauki shugabacin jagorancin ragamar
kiɗan
gidansu.
Waƙar
farko da Sa’idu ya fara yi a matsayin mai cin gashin kansa ita ce ta Sarkin
Yamman Faru Alhaji Ibrahim ɗan Sarkin Ƙayan
Maradun Abubakar, wato ya fara da gida ke nan.
Kai
ay yau ko gobe Maradun2x,
Turawa
sun ba da wasiƙa,
Baabu
mazan da ka ja maka2x,
jikan
Atto bani Usumanu Atiku2x
Ruwa
da Kada ɗibgau na
Magaji2x,
Sai
Tsofon wawa ka shi gar su,
Dawaya
kora ɗimau na
Wakili2x
Wato wannan ita ce waƙa
ta farko da Sa’idu ya fara gabatarwa yana mai cin gashin kansa bayan sun
dakatar da mahaifinsu daga kiɗa.
Daga
Faru sai ya fara fita, inda ya mai da gabansa shi ne Banga, wato inda aka auro
mahaifiyarsa. Sa’idu ya gadi Sarakunan Banga ta fuskar kiɗa
a wajen mahaifinsa, saboda maihaifinsa ya yi wa Sarakunan Banga kiɗa
cikinsu har da Sarkin Yaƙi Abdu. To sai Sa’idu ya fara da
Sarkin Yaƙin Banga Saleh Abubakar, wanda ya
yi Sarauta daga 1934-1963.
Daga
nan sai Mesa tas so ta haɗe Sa’idu Faru. Domin Marigayi Maigirma
Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda, Abubakar Garba
(1952-1960) shi ya ɗauko
Sa’idu daga Banga ya mayar da shi zuwa Ƙauran
Namoda.
Daga
can ne Zurmi suka ji amon Sa’idu Faru a lokacin Sarkin Zamfaran Zurmi Sulaiman
Muhammadu Sambo (1951-1970). Wato yana Ƙaura,
yana Zurmi yana komawa Faru.
Ana
cikin wannan yanayi, sai ƙaddarar Allah ta riga fata, aka ɗauko
Muhammadu Bello Macciɗɗo Sarkin Kudu ɗan
Sarkin Musulmi Abubakar na III Allah ya gafarta musu, aka kawo shi Mafara a
matsayin Uban ƙasa a shakarar 1953, wannan ne
sanadin da Sa’idu Faru ya ji ƙamshin gidan Mujaddi, sai yas sheƙa
da gudu zuwa Mafara yak kama Sarki Muhammadu Macciɗo.
Ga abin da yake cewa a cikin ɗiyan waƙarsa
da ke biye:
Mahamman
dalilinka nis sanTalata,
Muhamman
dalilinka niz zamni Hausa.
Bayan an mayar da Marigayi Sarkin Kudu
Muhammadu Bello Macciɗo garin Sakkwato a shekarar
1956, Sa’idu bai dai yarda a bar shi baya ba, sai ya sa takalminsa ya bi shi.
Sakamakon shaƙuwa da soyayyar da ke tsakaninsa
da ubangidansa har ta kasance Sa’idu Faru bai iya hita waƙa
zuwa wani gari sai Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
ya amince. Za mu fahimci haka, domin ko a cikin waƙoƙin
da ya yi wa Sarkin Kudu, wadda ya kira a matsayin bakan damiya mai gindin waƙa:
Kana
shirye baban ‘yan ruwa,
Na
Bello jikan Ɗanfodiyo
Wannanyaɗauke
ta a matsyinbakandamiya tai ta Sarkin Kudu Macciɗo,
ya ce duk inda yaj je hira, jama’a suna neman su ji wannan waƙa,
to haka nan wannan tare tac cigaba ana ta yi.
Sa’idu
Faru yana shiga wurare da dama, wasu wurare idan ya yi waƙa
sai a yi tsammanin Sarkin Yanka ne aka yi ma waƙa.
Misali a waƙar Sarkin Tudun Falale Marigayi
Muhammadu Bala ɗan
Sarkin Mafaran Gummi Muhammadu Maidabo
Sarkin
Tudun Falale,
Gogarman
Magaji Ummaru,
Ba
yau ko mazan jiya sun san kana da martaba,
Ya
riƙa da
gaskiya Muhammadun Muhammadu,
Karsanin
gidan Maisaje shirinka ya yi kyau,
Yac
ce maihwadaɗaniyya,
Ga
sarkin kiɗinku ya
zaka,
na
so a bani doki wani sansami abin suka,
Idan
ka ji wannan waƙa za ka yi tsammanin sarkin yanka
ne, to a lokacin shi Tudun Fafale marigayi Muhammadu Bala ɗan
Sarkin Mafaran Gummi Muhammadu Maidabo, dagaci ne.
Haka
ya kasance, wani lokacin sai ka ji kamar wannan sarki na ƙoƙarin
tashi ya farma wata ƙasa lokacin da aka aika Sarkin
Gabas Shehu ɗan
Sarkin Bauran Dange Muhammadu Ɗangwaggo, ɗan
Malam Usuman ɗan
Sarkin Musulmi Mu’azu, ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu
Bello, ɗan
Mujaddadi Shehu Usmanu bn Fodiyo tammada hullahu bi Rahamatihi, a garin Talata
Mafara a matsayin uban ƙasa. Shi ma akwai waƙoƙin
da ya yi masa, sai ka yi tsammanin matsayin Shehun ya kusan kai ga na Sarkin
Kano.
Madara
da zuma na jekadiya Shehu,
Baaba,
jikan Alu babba Maisaje,
Suna
ta tsoronka, kai baka jintsoro,
Baba
halin Abu yay yi Mai Rabah,
Mun
yi hwarin-ciki, sai arerewa,
Da
kar riƙa duniya
ta yi kyau Shehu,
Yau
Mahwara hwarautarmu ta yi nama,
Mun
yi hwarin-ciki sai arerewa,
Mai
biyas sarkin ƙauye
wawa na,
Shi
mi yac ci, mi za shi ba taro,
‘yaƙ ƙasa tai
kwatancin ta Garbadu
Irin
wannan sai mutane su zaci Sa’idu Faru ya yi ma Sarkin yanka waƙar ne.
Ana
cikin irin wannan yanayi Sai ya soma zuwa Yawuri wurin Marigayi Maimartaba
Alhaji Muhammadu Tukur Abdullahi (1955-1981) ciki ya yi maganganu masu hikima inda
ya ke koɗa
kansa, ya ce ga waƙa nan guda tara ta niy yi ma
amma na baro takwas gida sai in ka yi murna da zakkuwammu, in aika ko yanzu su taho
cewa da su waƙoƙin
tara. Mu ka kiɗi
in ji Sa’idu, don mu Allah yaw wa gudummuwa da waƙa
har wata na ije wata, saboda isa irin ta Sa’idu Faru.
Daga
Yawuri sai margayi Sa’idu yag gangara zuwa Kano, wajen Sarkin Kano Ado Bayero
yay yi masa waƙa, yaw wasa shi. Daga Kano yaw
wuce Zariya a lokacin naɗin Maimartaba Sarkin Zazzau
Alhaji Dr. Shehu Idris a shekarar 1975, ya yi masa waƙa
mai nuna yanzu shi ne babba a gidan Sambo. Ya ce Allah ya biya maka buƙata,
kai ab babba a gidan Sambo.A nan ne ya ɗan
shaguɓanci
‘yan Sarki yana cewa, da a ce ba a ba ni Sarki, gara a ba ni a yi mini gori,
komi nij ji ban ji zahi ba.
Shi
Sa’idu Faru waƙarsa sarauniyar waƙa
ce, ta sarakuna, ba ya zuwa garkar kowa da turunai in ba sarki ko ɗan
sarki ko mai riƙe da wata sarauta ba. Idan akwai
to masana suna saurare.
Haka
Sa’idu Faru ya cigaba da yi yana nan mallaƙe
da Muhamadu Bello Macciɗo ɗan
Sarkin Musulmi Abubakar na III ɗan Malam Usman ɗan
Sarkin Musulmi Mu’azu, ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu
Bello, ɗan
Shehu Mujaddadi Tagammadahul lahu bi Rahamatihi.
Haka
suka yi ta yi har zuwa lokacin da Allah ya yi ma Sa’idu Faru wafati a shekarar
1987. Cikin waƙoƙin
Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ya riga ya ba shi Sarauta. Shi
gare shi Sarkin Musulminai ne. Don a cikin wata waƙarsa
ta Macciɗo
yana faɗin
cewa:
Sarkin
Musulmin wata ran kake,
Da
Imani da mu’ijjiza
Na
nan gun malamMacciɗo tun
ga Alu mai Saje nij jiya
Ka
kai kamab Bello sassakiya
Da
kyauta da mulki da ban gaskiya
Haka za ka ji ya jero abubuwanshi,
yana nuna ma mutanen duniya, shi fa garai Muhammadu Macciɗo
Sarkin Musulminai ne.
Sarkin Musulmin wata ran ka ke,
sai ga wata ranar ta faru Allah bai gwada ma Sa’idu Faru ba, Allahu Akbar!!!.
Wato taren Sa’idu Faru da Muhammadu
Macciɗo
ta kai tare ta kai ƙud da ƙud,
domin a wata tattaunawa da na ji an yi da shi a gidan Rediyon Jihar Kaduna
(KSMC) a ranar 15/8/1970 karkashin jagorancin Malam Hamza Sanusi Funtuwa yana tambayarsa
kamar haka:
Malam
Hamza: To wai kai Sa’idu kullum sai
in ji kawai kullum kana maganar Sarkin Kudu Macciɗo,
shin Sarkin Kudun ga shin wane ne nashi?
Sa’idu
Faru: At! Kai ranka ya daɗe
ba ka san Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo ba?
Malam
Hamza: Ah a ah
Sa’idu
Faru: Shin wane gari kake?
Malam
Hamza: A Funtuwa nike.
Sa’idu
Faru:
Af toh kai ba ni mamaki, da Katsina kake da sai in ce Sarkin Kudu ya amshe tutan
nan ta Mujaddadi da anka bayat Katsina, amma tunda Funtuwa kake, ba ni ganin laihinka.
Don
Sarkin Kudu Macciɗo saboda
adalcinshi, to ni ina ganin ni ban ma san abin da zance ma ba, don ni ban da
shi, ban san kowa ba.
Ga
shi a cikin waƙoƙinai yana
faɗin
Ban
wuce gonata da irina ba,
Inda
Sarkin Kudu nits tsaya
Saboda
haka wannan tare ta haifar da alkhairurrukkah (alkhairai)
Saboda
Sarkin Kudu Macciɗo,
Mun
san manya mutane ƙwarai,
Mun
san ƙananan mutane
kuma,
Mu
shidda, ni da makaɗana muna
kammale
Kowa
ta shi ƙawa ta
isai,
Sarkin
Makaɗa yay
taiɓa yay ƙaton ciki,
Kowag
gam mu zanne ga inuwa,
Ko
da Makaɗin
Sarkin Masar yag,
Ga
Sa’idu sai rai nai yay haki.
To yanzu wani abin al’ajabi da
ya faru, da niƙ ƙirga ainihin ƙungiyar
Sa’idu wadda khalifansa Malam Ibrahim Sa’idu ke jagoranta sai nig ga su bakwai
ne, nic ce ahah, ikon Allah, ko gado ne?
Bayan wafatin Sa’idu Faru a 1987,
ya bar matan aure biyu,ya bar ɗiya sha biyu (12) Shidda maza shidda
mata cikinsu hadda shi wannan Malam Ibrahim ɗin
Taren ba ta ƙare
ba tskaninsu da shi Sarkin Kudu Macciɗo. Shaidu ni ke watan Apirilu na
shekarar 1996 lokacin da Allah ya tabbatar ma da Sa’idu fata tai, ga Sarkin
kudu Muhammadu Macciɗo,
Gwamnatin Jahar Sakkwato a ƙarƙashin
jagorancin Kanal Yakubu Mu’azu (Ritaya) ta faɗi
cewa an bai wa Muhammadu Macciɗo sarautar Sarkin Musulmi na 19,
Shi Ibrahim Tabbas a gabana yaz zo da turaye, ya yi waƙoƙi
waɗancan
da suka yi tare da mahaifinsa yak kuma yi nashi, yana cewa:
Sarkin
musulmi Macciɗo
Muhammadu
Ɗan
Bello,
Gidan
Mamman Bello duk yau yana hannunka,
Muhammadu
Ɗan
Bello
Gidan
Mamman Bello duk yau yana hannunka,
Wato wannan na nuna ainihin
tare, waccan tare ce da ankayi da mahaifin Ibrahim da Sarkin Musulmi Muhammadu
Macciɗo
tun shi na Sarkin Kudu, bai yanke wannan
tare ba.
Yanzu ga mu tare da Maigirma
Ubandoman Sakkwato, Hakimin Sabon Birni Alhaji Malami Sheik Muhammadu Macciɗo
sun zo saboda girmamawa da karramawa,da mutuntawa, na tabbatar da shi Malam
Ibrahim ƙila bai rasa ce ma Ubandoma wani
abu ba don wannan tare ta ƙara tashi.
Da wannan nike cewa masananmu da
suka taru zuwa anjima zai baje koli wanda zai sa a samar da wani kundi wanda ba
za a mance ba, wanda zai koma abin bibiya domin tuna rayuwa da kuma fasahohin Marigayi
Sa’idu Faru ɗan
Abubakar Kusu, ɗan
Alu Mai Kurya, Bagobirin da yac canye Zamfarawa.
Wassalamu Alaikum wa rahmatul
lahi ta’ala wa barakatuhu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.