Citation: Baba, I., Waziri, I.A., Mukhtar, K.B. & Abubakar, M.I. (2024). Zuga Gishirin Waƙa: Nazarin Tubalan Zuga a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 109-116. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.015.
ZUGA GISHIRIN WAƘA: NAZARIN TUBALAN ZUGA A WASU WAƘOƘIN MAKAƊA SA’IDU FARU
Daga
Ibrahim Baba
National Teachers Institute, Kaduna.
+2347066366586/ +2348125351694
ibrahimba182@gmail.com
Da
Isma’il
Aliyu Waziri
Sashen Koyar da Harshen Hausa
Kwalejin Addinin Musulunci da Koyon Ayyukan Shari’a ta
Aminu Kano
08069144170
ismailaliyu@gmail.com
Da
Kamilu Bashir Mukhtar, Ph.D
Sashen Nazarin Harshen Hausa
Kwalejin
Koyon Aikin Shari’a da Addinin Musulunci ta Aminu Kano
08039641126
Da
Musa Isah Abubakar
Department of Hausa
School of
Languages, Jigawa State College of Education, Gumel
+2347064833646
musaisahabubakar@yahoo.com
Tsakure
Kusan an gina waƙoƙin baka a kan zuga da yabo da kambamawa da kirari da habaici
da ba’a da sauran dangogin waɗannan zantuka na
hikima. Akan zuga mutum ta hanyar abin da ya sani ko yake da shi, ko kuma
akasin haka, sannan akan yi zuga domin munana wa wani ko ɓata masa, musamman ta hanyar ambatar abin da wani kininsa
yake da shi, ko ya shahara da shi.. Wannan bincike, ya yi ƙoƙarin fito da tubalan zuga a wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru,
inda binciken ya keɓanci waƙoƙi guda bakwai kacal, wanda a cikinsu ne aka ciro waɗannan tubalai na zuga. A binciken, an gano yadda Makaɗin ke ƙulla tubalan zuga
ta hanyar amfani da yabo, kirari da sauran dangogin zantukan hikima yayin
aiwatar da zuga ga wanda yake yi wa waƙa, da kuma yadda zuga take sanya armashi a cikin waƙoƙinsa ga masu sauraro da kuma waɗanda ya yi wa. An bibiyi ayyuka makamantan wannan aiki a
yayin wannan bincike, sannan aka ɗora shi a kan
ra’in Gusau na Waƙar Baka Bahaushiya
(2015). A ƙarshe, an ƙarƙare binciken da fito da sakamako tare da rufewa da bayanan
kammalawa.
Muhimman Kalmomi: Zuga, Gishirin Waƙa, Tubala, Makaɗa
Sa’idu Faru
1.0 Gabatarwa
Makaɗan baka na Hausa shahararru ne wajen aiwatar da zuga a cikin
waƙoƙinsu, inda sukan yi wannan zuga ta hanyar yabo ko kirari duk
don su ingiza wanda suke zugawa ya fito ya aikata abin da ya saɓa da hankalinsa, wanda in ba domin wannan zugar ba, da ba
zai aikata ba. Babbar manufar zuga a cikin waƙoƙi kuwa ita ce tunzura
ko harzuƙa wanda aka yi wa,
shi ya sa idan aka kalli waƙoƙin makaɗan baka na Hausa,
za a iske cike suke da zuga; musamman ta hanyoyin yabo ko kambame ko kirari da
sauransu.
Ganin yadda wannan al’amari na yin zuga a waƙoƙin baka na Hausa
ya zama gaskiya, sannan ya zame wa makaɗan
hantsi leƙa gidan kowa, ya
sanya wannan bincike zai yi ƙoƙarin fito da turakun da Makaɗa
Sa’idu Faru ya yi zuga, tare da yin tarkensu a taƙaice. Yin wannan aikin, zai taimaka wa masu bincike samun
wasu abubuwan karatu a wannan fage, ilimi kuma zai ƙaru, abin karatu za su daɗu,
sannan za a sake gano wasu hikimomi na yin wannan zugar.
1.1 Ma’anar Waƙar Baka
Idan ana batun ma’anar waƙar baka, akan bibiyi ayyukan masana da manazarta. Don haka a
nan, ga abin da wasu daga cikinsu suka ce: Sa’id (1981:235) ya bayyana ma’anar
waƙar baka da cewa, “Waƙar baka ita ce wadda ake rerawa don jin daɗi, a ajiye ta a ka, a kuma yaɗa
ta a baka”. Shi kuwa Umar (1987:28) cewa ya yi, “Waƙar baka ita ce nau’in sarrafafen harshe da ake gabatarwa da
sigar gunduwoyin zantuka da ake kira baitoci ko ɗiyoyi
(ɗiya), waɗanda ake ginawa a
kan kari ƙayyadajje, kuma
ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman.” Gusau (2003:XIII) kuwa, yana
ganin “Waƙar baka wani zance
ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin
tsari da daidaitawa, a rere cikin sautin murya da amsa-amo na kari da kiɗa, sau da yawa kuma a tare da amshi”. Junaidu da ‘Yar’aduwa
(2007:131) sun ce, “Waƙa magana ce
aunanniya, kuma abin rerawa”.
1.2 Taƙaitaccen Tarihin Samuwar Waƙar Baka ta Hausa
Masana sun yi ƙoƙarin bayyana
asalin samuwar waƙar baka a ƙasar Hausa, daga ciki akwai ra’ayin Satatima (1999:30) inda ya bayyana cewa, “Al'ummar ƙasar Hausa sun sami basirar kiɗa
da waƙa daga tsofaffin
daulolin Ghana da Mali da Songhai wanda wasu sassa na ƙasar Hausa suka kasance ƙarƙashin mulkinsu
kafin ƙarni na sha tara.
Masu wannan ra'ayi har sun kai ga cewa daga waɗannan
tsofaffin dauloli Hausawa suka samu kayan kiɗa
irinsu kakaki wanda aka samu daga Songhai cikin ƙarni na sha shida. Algaita kuwa an samo ta ne daga Songhai
da Mali”.
A wurin Gusau (2003:5-6) kuwa, ya kawo
hasashe guda uku waɗanda yake ganin su ne asalin waƙar baka, waɗannan hasashe kuwa
su ne: Ra’ayi na farko, suna ganin ana jin ɗan’adam
ya ƙagi waƙa ne tun lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta,
daga nan ya gano noma sai waƙa
ta ƙara haɓaka.
Ra’ayi na biyu kuwa, an nuna cewa, ana ganin waƙa ta samo asali ne daga wani maroƙi ‘Sasana[1]’ domin haka a wannan ra’ayi ana jin makaɗan Hausa jikokin wannan mutum ne. A ra’ayi na uku kuwa, ana
ganin waƙa ta samo asali ne
daga bautar iskokai.
1.3 Wane Ne Makaɗa Sa’idu Faru?
An haifi Sa'idu Faru a garin Faru ta cikin ƙasar Maradun, Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a wajajen shekara ta 1932.
Sunan mahaifin Sa'idu Faru shi ne Makaɗa
Abubakar dan Abdu, shi kuwa Makaɗa
Abdu, Alu mai Kurya ne ya haife shi, yayin da ita kuwa mahaifiyar Sa'idu Faru
mutuniyar Banga ta cikin ƙasar Ƙaura-Namoda ce, wanda duk a yanzu suke cikin Jihar Zamfara.
Sa'idu Faru ya yi yawancin ƙuruciyarsa ce a garin Banga ta Ƙaura-Namoda, wato inda aka haifi Mahaifiyarsa, amma kafin ya
girma sai ya koma wurin Mahaifinsa Makaɗa
Abubakar a Faru.Makaɗa Sa'idu bai samu ilimin Muhammadiya da yawa ba, sai dai an
sa shi makarantar allo inda ya yi zurfi ga Alƙur'ani mai tsarki.
Makaɗa Sa'idu Faru ya koyi waƙa wurin mahaifinsa Makaɗa
Abubakar, domin tun Sa'idu yana da shekara goma aka fara zuwa yawon kiɗa da shi gari-gari. Bayan da ya cimma shekaru goma sha
shida, ya soma karɓi, a wannan lokaci ne kuma aka haɗa su tare da ƙanensa Mu'azu wanda shi ne Ɗangaladimansa. Baya ga Mahaifinsa Makaɗa Abubakar, Sa'idu Faru bai koyi kiɗa ga kowane makaɗi ba,
dukkan salo iri-iri da yake sakawa a waƙoƙinsa tushensu
mahaifinsa da baiwar da Allah ya ba shi ta gane fasalin waƙa ne. Da Sa'idu Faru ya samu cin gashin kansa, ya fara da
wata waƙa wadda ya yi wa
tsohon sarkin Yamma Faru Ibrahim. Ga kaɗan
daga cikinta:
Jagora: Bi da maza Dan Jodi na Iro, Iro
magajin Shehu da Bello,
: Hasken hitila ba dai da wata ba,
: Tauraro haskenka subahin,
: Dawaya kora ɗimau na wakili,
: Uban Sarkin Zagi Bello na Yari,
: Ruwa da kada ɗibgau na Magaji
: Sai tsohon wawa ka shigarsu.
Dangane da yawan waƙoƙinsa da ya yi, shi
kansa ba zai iya ƙididdige yawansu
ba. Ta fuskar yara kuwa, Sa’idu Faru na da yara uku, wato Mu'azu Daudun Kiɗa (Ɗangaladima) da
kuma Ali.
Makaɗa
Sa'idu Faru yana da matan aure guda uku da 'ya'ya ashirin da shida (26) maza da
mata, inda a cikinsu guda goma sha ɗaya
sun rasu, saura sha biyar (15), sannan yana da jikoki kimamin guda ashirin (20)
(Gusau, 1996:117-125).
1.4 Dabaru
da Hanyoyin Bincike
Kasancewar kowane bincike dole sai an
bi wasu hanyoyi kafin aiwatar da shi, wannan ya sanya a yayin gudanar da wannan
bincike an duƙufa wajen lalubo
wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru,
sannan aka saurara tare da fito da turakun da aka yi zuga a ciki, sannan suka
rubuce su. Har wa yau, an yi ƙoƙarin bibiyar wasu ayyuka na masana masu kamanceceniya ko
kusanci da wannan aiki, sannan aka tuntuɓi wasu
cikin masana da masu bincike ‘yan’uwansu.
1.6 Ra’in
Bincike
Wannann binciken an ɗora shi a kan ra’in Mazahabar Waƙar Baka Bahaushiya (WBB), wanda ra’i ne da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya ƙirƙire shi domin auna
waƙar baka, kuma ra’in ya sami ɗimbin mabiya musamman masu nazarin Waƙar Baka Bahaushiya. Daga cikin manyan mabiya wannan Mazhaba
akwai: Abdullahi Buba da Ibrahim Baba da sauransu.
2.0
Ma’anar Kalmar Zuga da Asalinta
Masana da dama sun tofa albarkacin
bakinsu wajen bayyana ma’anar zuga, misai Bargery (1934) da Oxford Dictionary
(9th edition) da Bunza (2009) sun yi ittafaƙi wajen bayyana ma’anar wannan kalma da cewa, zuga wata magana ce da ake
furtawa domin a harzuƙa ko a kambama
wani mutum ya aikata wani abu da ba zai iya aikatawa ba idan yana cikin
hayyacinsa.
Bunza (2009) ya ƙara da cewa, zuga
da kirari tamkar ɗanjuma ne da ɗanjummai
wajen taka muhimmiyar rawa a fagen isar da saƙo. Ya ƙara da cewa, idan
zuga ya amshi sunansa, dole ne a ji amon kalmomin yabo a cikinsa, domin zuga
wata dabara ce da mawaƙa suke amfani da
ita ta hanyar ambaton kyawawan ɗabi’u da ayyukan
bajinta da iyaye da kakanni suka aikata domin su isar da saƙo ga masu sauraren waƙoƙinsu.
Ita wannan kalma ta zuga, ta samo asali
ne daga zuga-zugi da maƙeran gargajiya
suke amfani da su wajen hura wuta a maƙera, domin su gasa ƙarfe ya yi ja da laushi kafin a sarrafa shi zuwa wani abin
amfani. Yadda ake amfani da zuga-zugi wajen hura huta a maƙera har ta ruru ta gasa ƙarfe ya yi ja, haka zuga da ake yi wa mutum kan harzuƙa wanda aka yi wa, ya kumbura ya aikata wani abin bajinta ko
akasin haka.
2.1 Zuga
a Waƙoƙin Baka
Kamar yadda ma’anarta ta nuna, zuga
wata magana ce wadda mawaƙan Hausa na baka
ko rubutacciya suke amfani da shi domin su ingiza ko harzuƙa wani mutum ya aikata wani abu wanda ba zai iya yin sa ba
idan yana cikin hankalinsa. Wani lokacin kuma, kambama wani mutum ya ji cewa ba
wani mutum da ya kai shi ƙarfi ko hazaƙa ko dukiya ko daraja ko kyauta a duniya.
Ana amfani da zuga da nufin sa wanda
ake wa ya aikata wani abin mamaki, wanda ya wuce abin da aka san ya saba
aikatawa, irin wannan abu kuwa na iya zama na alheri ko na ɓarna (Yakawada, 2013).
2.2
Ma’anar Tubali
Yahaya (1979) a cikin Gusau (1995) ya
bayyana tubalan ginin waƙa a matsayin ɗaya daga cikin matakan da ake la’akari da su wajen feɗe adabin baka; har ila yau, ya bayyana tubala da wasu
muhimman abubuwa kamar haka: mutane da dabbobi da tsuntsaye da aljannu da ƙwari da Annabawa da mala’iku da rauhanai da sauransu. Har
ila yau, Abba da Zulyadaini (2000), sun bayyana cewa mawaƙa kan yi amfani da tubala daban-daban domin gina waƙa ko jigo. Masanan sun sake bayyana cewa akwai jigon kishin ƙasa wanda shi ma yana da tubalan gina shi wasu daga cikin
ire-iren waɗannan tubala sun haɗa da:
gargaɗi da faɗakarwa da
tunatarwa da kuma wayar da kai da dai sauransu.
Bisa ga la’akari da abin da Yahaya
(1979), ya kawo a cikin Gusau (1993) da Abba da Zulyadain (2000), zamu iya
cewa/tubala na nufin dukkanin abubuwa da mawaƙiya yi amfani da su a matsayin matallafa ko ‘yan rakiya wajen isar da muhimman saƙonnin da ake son isar wa waɗanda
kan iya zama: mutane ko aljannu ko dabbobi ko duwatsu ko ababen tsoro. Har ila
yau, faɗakarwa da tunatarwa da ilmintarwa da jajircewa da wayar da
kai da dai sauransu duk sukan iya zama tubala sai dai sukan bambanta da juna
gwargwadon irin saƙon da ake son
isarwa.
2.3
Matsayin Tubalai a Waƙar Baka
Yawancin waƙoƙin baka da ma rubutattu idan mai
nazari ya duba zai tarar an jajjefa wasu muhimman abubuwa na daban a cikinsu
baya ga ainihin sakonnin da suke magana a kai,waɗannan abubuwa da makaɗa/mawaƙa ke sanyawa ƙari ne ga babbar manufar (turken)
waƙar su, su ake kira “tubalan ginin jigo/turke”. Tubala ke
nan suna nufin wasu maganganu da aka bi aka ƙuƙƙulla waƙa da su don ta ƙara tsawo tare da armashi amma ba lallai su ne babbar manufar waƙar ba. Misali: idan jigon waƙar na “yabo” ne, a cikin
waƙar za a iya kawo wasu abubuwa na daban waɗanda ba
lallai sai akan yabo za su yi magana ba, amma za su iya ƙarawa waƙar kyau da armashi. Kowane ’turke’ da irin tubalan gina shi da suka fi dacewa da shi, misali a turken ‘Kishin ƙasa’ an fi amfani da abubuwa da suka danganci ko suke da
nasaba da gargaɗi ko faɗakarwa ko tunatarwa ko jajircewa ko wayar da kai da dai sauransu.
3.0 Nazarin
Tubalan Zuga a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru
Kamar yadda wannan bincike ya nuna tun
a farkonsa, za a yi ƙoƙarin fito da tubalan zuga ne daga cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru, sannan a yi ƙoƙarin fayyace kalmomin da aka yi amfani
da su wajen ƙulla zaren wannan
zuga da ya yi a wannan ɗiya. Don haka a nan, za a kawo su tare da bayani daidai
gwargwado, inda za a bayyana wannan tubali na zuga ko dai ta hanyar yabo ne ko
kuma ta hanyar kambame ko zambo.
3.1
Tubalin Zuga a Waƙar Sarkin Kiyawa
Abubakar Ƙaura-Namoda
Jagora: Gwabron giwa na shamaki Baba Uban Gandu,
: Abu gogarman magaji mai kamsakalin daga.
Har wa yau, a wani ɗa, ga abin da ya ce:
Jagora: Ni kiɗin yaƙi na yi wa Abu na
Isau,
: Ba ni son kana zaunawa banza,
: Ka
ɗauki takobi da bindigogi da bakunkuna,
: Ka sa sirdi,
: Ba mu sansani sai bakin Tsabre,
: Kano da Katsina, Kwantagora hak
Kazaure,
: Riƙon Namoda na, shi
na ac can,
:
Garba ka amshe riƙon duk da Umaru,
: Umaru yab bam ma
A wannan ɗa, ya yi ƙoƙarin zuga ta
hanyar da amfani da kalmomin ‘gwabon giwa’ da kuma ‘gogarma’.
Kalmar ‘gwabro’ a daidaitacciyar
Hausa na nufin ‘gwauro’ wanda yake da
ma’anoni guda uku, wato ko dai ‘mutum da ba shi da aure bayan ya taɓa yi’ ko ‘turken da masaƙa ke tariyar zare daga gare shi’ ko ‘fitaccen abu’ (C.N.H.N, 2006:184). To a nan za a iya kallon wannan zugar
ta fuskar ma’anoni
guda biyu, ko turken, sai ya ba da ma’anar ya zuga shi ta fuskar tsayawar sa kan duk wani abu da
ya sa a gaba, ta yadda ba za a cim masa ba, tunda ya kafu, makamanciyar kafuwar
da turken can na masaƙa ya yi, ko a
kalli zugar ta fuskar fice da ya yi, ta yadda kowa ya san shi a fagen iya mulki
da sarauta da jarunta da sauran abubuwan da ake son a san duk wani jarumin
shugaba da su.
Game da zuga da kalmar ‘gogarma’
kuwa, wannan na nufin ‘mutum jarumi mai ƙarfi zuciya’. Ke nan a nan, ya zuga shi ta fuskar jarunta da ƙarfin zuciya. Don haka wannan zuga, an yi ta ne ta fuskar
yabo da kuma kambamawa.
3.2 Tubalin Zuga a
Waƙar Sarkin Yamman
Faru Ibrahim
Jagora: Bi da maza Ɗan Joɗi na Iro,
: Iro magajin Shehu na Bello.
Jagora: Hasken hitila ba ɗai da wata ba,
: Tauraro
haskenka subahi,
: Dawaya kora ɗimau na Wakili,
: Uban Sarkin Zagi Bello na Yari.
Jagora: Ruwa da kada ɗibgau na Magaji,
: Sai tsohon wawa
ka shigarsu.
A wannan ɗa, ya yi zuga da
kalmomin ‘hasken hitila’ da kuma ‘tauraro’, waɗanda suke da kusan ma’anoni guda, domin ‘tauraro’ yana ba da
haske ne, kamar yadda ‘fitila’ ma take ba da haske, duk da dai hasken ya
bambanta. Shi ‘tauraro’ in dai har ya fito, to dole a gan shi, yayin da shi
kuma hasken fitila yake haskaka wurin da aka kunna ta. Don haka dai a nan, ya
yi masa zuga da waɗannan kalmomi domin ya fito da buwayarsa sarari.
A ci gaba da zugar kuwa, sai ya kawo wani ɗa, wanda a dunƙule jumlar na nuni da yadda ake samun tsoron shiga ruwan da
a cikinsa akwai kada[2] wanda ba mai shigar wannan ruwa face wawa, domin duk wanda
ya shiga, mutuwarsa ce ta zo. To a nan, sai ya yi wannan zuga ta hanyar
mutuntawa, wato ya ɗauko siffar wancan ruwan mai ɗauke
da kada a ciki, ya siffanta Sarkin Yamman Faru; da ma’anar babu wanda ya isa ya
ja da shi, sai wawa wanda bai san abin da yake yi ba.
3.3 Tubalin Zuga a
Waƙar Sarkin Kiyawa
Abubakar Ƙaura-Namoda
Jagora: Gwabron giwa uban Galadima,
: Ɗan Sambo gimshimi,
: Gamshiƙan Amadu na mai Gandi,
: Kai a uban zagi,
: Gogarman,
: Namoda bai magana wani ya walwalad.
Jagora: Ban da gudu ban da razana,
: Ka san sarki ba shi waiwaya,
: Ko da jan D.O yag gani,
: Ka san sarki,
: Ba shi waiwaya, ko da jan Gwamna yag gani.
Idan aka lura a wannan ɗiya da
suka gabata, za a ga ya yi zuga ta amfani da wasu kalmomi da kuma jumloli,
misali ya ambace shi da kalmar ‘gamshiƙan’ wadda
a daidaitacciyar Hausa ake cewa, ‘ginshiƙi’, ma’ana ‘wani
abu da ake ginawa don ɗaukar ɗaki ko soro ko rumfa’ (C.N.H.N, 2006: 166). To shi ma a nan,
ya yi wannan zuga ne ta hanyar nuna yadda Sarkin Kiyawa yake ɗaukar nauyin al’umma ba tare da gajiyawa ba. Sannan ya masa
zuga ta hanyar kore masa baki biyu, ko sauya magana bayan ya yi, ma’ana idan
yace ‘e’, to ba zai dawo yace ‘a’a’ ba, a ƙarshe kuma ya kore masa tsoro, har ya nuna cewar sarki ba ya
waiwaye, ma’ana ko
dai idan ya sa gabansa, to ba zai waigo baya ba, ko kuma idan ya wuce abu da ƙarfin mulki, ko da jarumta, to fa ya wuce ba zai dawo ta
kansa ba.
3.4 Tubalin Zuga a
Waƙar Marigayi Mai
Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III
Jagora: Kai aka saurare kuma
: Kai
a ka wa ɗa'a
: Kai
an kace Musulmi su yi ma sujada Garba,
‘Y/Amshi: Don ba ka gaida kowa,
: Sai
Halikul Adati,
: Don ba ka gaida kowa,
: Sai Halikul Adati.
Jagora: Namun daji suna da dama,
: Ga
Giwa ga Zaki,
: Ga Ɓauna ga Musshe,
: Da
kuma irin sauransu,
‘Y/Amshi: Ban ga wanda yak kai,
: Ga
mu'ijjizag Giwa ba,
: Ban
ga wanda yak kai ga,
: Mu'ijjizag Giwa
ba.
A waɗannan ɗiya kuwa, za a ga ya bi wani salo ta hanyar amfani
kururutawa, da kaɗaita Mai Alfarma Sarkin Musulmai wajen ɗa’a, da jin maganarsa ga kowa. Salon da ya yi amfani da shi
a nan, shi ne abin da aka umarta na yi wa shugaba biyayya a addinin Musulunci,
don haka sai ya yi amfani da wannan salon wajen zuga shi, domin shi ba zai yi
gaisuwa ga kowa ba, sai dai shi za a gaishe kasancewarsa Sarki, shi kam sai dai
ya gai da Allah, wato ya yi sallah. Sannan sai ya sake amfani da dabbantarwa
wajen yi masa zuga; ta yadda ya jero sunayen namun daji manya irinsu giwa da
zaki da ɓauna, sannan sai ya kawo musshe[3], wanda shi dabbar gida ce, amma yana da faɗa da rigima, musamman idan ya riƙa, yakan cinye kajin mutane da sauransu, to yadda waɗannan nau’o’in namun dawa suke da ƙarfi da rashin tsoro da rikici, haka musshe ma yake da su.
Bayan ya zayyano su duka, sai ya keɓe giwa wajen mu’ujiza, wato bayyanuwar wata ɗabi’a wadda ta saɓa wa ɗabi’a ta abin ko jinsinsa. To a nan, sai ya siffanta shi da
giwa, domin yanayin ƙarfinta, da ɗabi’ar da ta sha bamban da sauran dabbobin dawa, da kuma
buwayar ƙarfinta.
3.5 Tubalin Zuga a
Waƙar Sarkin Kudu
Muhammad Macciɗo Abubakar III
G/Waqa: Kana shire Baban ‘yan ruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
Jagora: Mamman haraka sai yaj jiya,
: Yac ce kai ko ƙarya kakai,
: Ƙaura da Gusau da Kwatarkwashi,
: Ɗangulbi da Bunguɗu ham
Maru,
: Dud ɗai
na ga Mamman Sarkin Kudu,
: Ɗan Dikko yana can yaj jiya,
: Wannan magana ta tabbata,
: Da inda rana ka fita gabas,
: Har inda rana taka faɗuwa,
: Dud
ɗai na ga jikan Ɗanhodiyo,
: Babu
wurin da mulki nai yatc tcaya,
‘Y/Amshi: Dud ɗai na ga jikan Ɗanhodiyo,
: Babu
wurin da mulki nai yatc tcaya,
: Kana shire Baban Yan Ruwa,
: Na Bello jikan Ɗanfodiyo,
Jagora: Maganag ga da zani hwaɗa maka,
‘Y/Amshi: Gagarauɗan Alu kai min gahwara,
Jagora: Maganag ga da zani hwaɗa maka,
‘Y/Amshi: Gagarau ɗan Alu kai man gahwara,
: Wada dud aka gado ɗaukaka,
: Wada dud aka gado ƙasura,
: Wada dud aka gadon ci gaba,
: Mamman
ka gadi Abubakar,
: Ko
da sayen halin nan akai,
: Baba halin da
kakai kuɗɗi shi kai,
Idan aka lura da tubala na waɗannan
ɗiya, za a ga yadda Makaɗa
Sa’idu Faru ya yi amfani da zubin kalmomi wajen zuga ta hanyar kambame da
kirari ga Sarkin Kudu Muhammad Macciɗo. A ɗa na farko, bayan na zayyano wasu garuruwan da ke
yankunansu, sai ya nuna har ma duk inda rana ke fitowa da faɗuwa, wato mafita da mafaɗar
rana, to fa mulkin Sarkin Kudu Muhammad Macciɗo
ya kai, wato mulkinsa ya shahara, kuma ya buwaya, an san shi a ko’ina.
A bayanin ‘yan amshi kuwa, sai suka ambace shi da kalmar
‘gagarau’, wadda ke da ma’anar ‘laƙabin da ake yi wa mai suna Abubakar ko wani jarumi ko wani
abu mawuyaci’. To a
nan, domin sununa jaruntar Sarkin Kudu, sai suka ambace shi da wannan kalma ta ‘gagarau’ da nufin jarumi.
3.6 Tubalin Zuga a
Waƙar Marigayi Mai
Girma Dagacin Banga;
Sarkin Yaƙi Sale Abubakar
Jagora: Gurnanin Damisa ka sa mahwarauta sun ɗora
ɗemuwa,
‘Y/Amshi: Ga wani ya yi kokuwa da wan ƙarfi nai,
: Ya hwaɗi
ya kare,
: Tun ba a tantance ba shi na nishi ya lanƙwanshe tsara.
Kalmar ‘gurnani’ na nufin ‘wani irin sauti da kare ko zaki
ko damisa ke yi lokacin da yake shirin faɗa’
(C.N.H.N, 2006). Irin wannan sauti, yana da ban tsoro da sanya firgici da sanya
fargaba, wanda idan damisa ce ta yi a dawa, to sanin faɗanta kan sanya mafarauta shiga ruɗani da firgici. Domin ya sake fito da buwayarsa, da ƙarfinsa, sai ya yi masa zuga ta hanyar dabbantawa, wato ya
ba shi siffar dabba.
3.7 Tubalin Zuga a Waƙar Sarkin Kudun Sakkwato Muhammadu
Macciɗo Abubakar III
Jagora: Bajinin gidan
Bello Mamman na Yari,
: Sarkin Kudu Macciɗo ci
maraya.
Y/Amshi: Bajinin gidan Bello Mamman na Yari,
: Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya,
Jagora /Y/Amshi: Na Marafa D/babamai tura haushi,
: Na Safun Gabas duniya hori
wawa.
Jagora /Y/Amshi: Toron Giwa Uban Bello Mato,
: Duh Hausa ba mai irin hanƙuri
nai,
: Bajinin gidan Bello Mamman Na Yari,
: Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya.
Jagora: Babban dutci a hange
ka nesa,
Y/Amshi: A ishe ka tsoronka ya tcarma kowa,
Jagora: Babban dutci a hange ka nesa,
Y/Amshi: A ishe ka tsoronka ya tcarma kowa,
Y/Amshi: Ka gadi Moyi,
: Saura ka kai inda mai
Hausa yak kai.
Idan aka duba waɗannan ɗiya, za a ga ya yi zuga ta fuskoki biyu, fuska
ta farko ya yi amfani da kalmar ‘Bajini’ wadda ke da ma’ana guda da ‘Bajimi’ a
daidaitacciyar Hausa. Kalmar, na da ma’anoni guda uku kamar haka: ‘riƙaƙƙen sa’ ko ‘ƙasaitaccen mutum’ ko kuma ‘mutum
mai sunan sarkin da ke kan gadon sarauta’ (C.N.H.N, 2006).
To a nan, da yake a lokacin Sarkin Kudu ne, sai
ya zuga sarauta inda ya kambama ta sosai, ta yadda za ta iya bayar da ma’anar ƙasaitaccen sarki, kuma riƙaƙƙe wanda ke kan gadon mulki.
Har wa yau, ya sake ambatar sa da ‘ci maraya’, wato
sarki ne wanda jarumtakarsa ta sanya ya cinye wata maraya wadda ko dai daidai
suke da tasa, ko kuma ta tsere wa tasa, amma ya cinye su a yaƙi.
Bayan nan, sai ya yi masa zuga ta hanyar kirari
har guda uku, ‘Na Safun Gabas duniya hori
wawa’, wato ita duniya tana yi wa wawa horo, wawa shi ne wanda bai san abin
da yake yi ba, kuma bai ma san inda ke masa ciwo ba, don haka rayuwarsa a wauta
take; ta yadda duniya ce za ta masa wa’azi. To a nan, sai ya abuntar da shi,
inda ya nuna cewa Sarkin Kudu daidai yake da duniya wajen horas da wawa. Sannan
ya sake yi masa kirari da haƙuri, inda ya nuna ya kai matuqa wajen haƙuri, sannan ya masa kirari
da ‘babban dutsi’ wanda shi dutse na da ma’anoni
da yawa, sai dai mun ɗauki wadda ta fi dacewa da
a yi kirari da ita, wato tsauni. To a nan, shi tsauni akan iya hango shi daga
nesa, sai ya yi ƙoƙarin abuntar da shi ta hanyar amfani da kalmar ‘babban
dutse’ ta yadda za a iya hango shi daga nesa, imma don
ƙasaitar sa ce, ko don iya
kyalliya da ado, ko domin ƙarfi da jaruntarsa.
4.0 Sakamakon
Bincike
Idan mai bibiyar wannan maƙala ya nutsu, zai iske cewa an yi ƙoƙarin tattauna wasu
muhimman gaɓoɓi tare da fito da wasu ginshiƙan batutuwa game da batun da aka yi magana a kai, waɗannan muhimman abubuwan da aka fito da su kuwa, su ne
tubalan zuga a cikin wasu waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru,
wannan ya sanya a binciken aka sami sakamakon kamar haka:
a. Ƙara fito da
hikimar makaɗa, ta yadda suke sarƙa zuga a cikin waƙoƙinsu.
b. Gano cewa ana yin zuga ta hanyoyin
kirari da yabo da kambame.
c. Yadda ake ɗaukar zantukan azancin magana domin ƙulla tubalin zuga a waƙoƙin baka na Hausa,
misali dabbantawa, mutuntawa da siffantawa da abuntarwa da sauransu.
d. Fahimtar kyakkyawar alaƙa tsakanin makaɗi da wanda yake yi wa kiɗi, domin akan fahimci haka a yayin zugarsa.
e. An fahimci tasirin zuga a waƙoƙin baka na Hausa, da
yadda za a iske kusan duk wata waƙar sarauta ko ta jarumta ko ma sana’a, za a sami kalmomin
zuga a ciki.
f.
Fahimtar
yadda makaɗa ke hura wa wanda suke yi wa kiɗi da waƙa
kai, har ya ji ya zarce inda yake.
4.1 Kammalawa
Kamar yadda wannan bincike ya amsa sunansa, wato Zuga Gishirin Waƙa: Nazarin Tubalan Zuga a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru an yi ƙoƙarin yi masa matashiya da kan bayyana zuga ta zama muhimmin
abu a waƙar baka, sannan
aka je ga ma’anar
waƙar baka, da kuma taƙaitaccen tarihinta, sannan da tarihin Makaɗa Sa’idu Faru, sai aka je kan dabaru da hanyoyin bincike, da
kuma ra’i. Binciken ya zo da ma’anar zuga da asalin kalmar, sannan da taƙaitaccen bayani kan zuga a waƙoƙin baka, sannan
aka zo da bayani a kan ma’anar
tubali, da kuma matsayinsa a waƙar
baka. An ci gaba da batu a gava ta gaba a kan nazarin wasu waƙoƙi, inda aka nan
aka ciro tubalan zuga ɗin, an taƙaita
a kan waƙoƙi guda bakwai kacal, tare da kawo ɗiya da bayanin abin da ya sauwaƙa. Bayan nan, sai aka fito da sakamakon bincike, sai aka
kammalawa.
Manazarta
Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000) Nazari kan Waƙar Baka ta Hausa.
Zaria: Gaskiya Cooperation Limited.
Bargery, G. P. (1934). Hausa-English Dictionary and English-Hausa
Vocabulary. London: Oxford University Press.
Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.
CNHN. (2006). Ƙamusun Hausa na Jami'ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar Baka.Kaduna: Fisbas Media Services Limited.
Gusau, S. M. (1996). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa. Kano: Benchmark PublishingLimited.
Gusau, S.M. (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano:
Benchmark Publishers.
Gusau, S.M. (2014). Waƙar Baka Bahaushiya. Kano:
Bayero University.
Junaidu, I da ‘Yar’adua, T. M. (2007). Harshe da Adabin Hausa a Kammale Don Makarantun
Sakandare. Ibadan: Spectrum Books Ltd.
Sa’id, B. (1981). “Bambancin Waƙar Baka Da Rubutacciya”. A Cikin Yahaya, I.Y. Rufa’i, A. & Abu-Manga, A. (ed) Studies in Hausa Language, Literature and
Culture: The Second Hausa International Conference. Kano: Centre for Study
of Nigerian Languages, Bayero University.
Satatima, I.G. (1999). Tarsashin Adabin Baka a Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Kundin digiri na biyu. Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeirya, Jami’ar Bayero.
Umar, M.B. (1987). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph
Publishers.
Yahaya, I. Y. da ‘Yar Aduwa, T. M. da Gusau, S. M. (1992). Darussan Hausa Don Makarantun Sakandare.
Ibadan: University Press PLC.
Yahaya, A. B. (1995) “Ƙawancen Jigo Tsakanin Waƙoƙin Sarauta na Baka
daRubutattu” In Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Yahaya, I. Y. (1983/85) “Tsarin Kayan
Kiɗa da Muhallan Kaɗa su”
InHarsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar
Bayero.
Yakawada, M.T.S. (2013). “Nazarin Jigon
Yabo da Zuga a Kirarin Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina”. In Himma Journal. Department of Nigerian
Languages, UMYUK Katsina.
[1]Tarihi bai bayyana
takamaiman garin da Sasana ya fito ba, sai dai ana da'awar cewa ya fito daga
nahiyar Asiya ne. Masu wannan da'awa suna ambata Sasana shi ne makaɗi wanda ya
fara kiɗa da waƙa a duniya" (Gusau (2008:III).
[2]Wata halitta ce dangin ƙadangare ƙatuwar da ke zaune a
cikin ruwa, yana da ɓawo-ɓawo mai ƙarfi a bayansa (C.N.H.N, 2006:222).
[3] Namijin kyanwa,
wato daidai yake da muzuru (C.N.H.N, 2006: 353).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.