𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Tambayata ita ce; Zan iya kai karar mahaifina ga magabatansa? Sakamakon duk Wanda yazo neman aurena wajen shi sai ya ce mishi ya bada ni. Kuma wllh masu zuwa da gaske suke, amma bansan menene dalilin shi ba, kuma kafin haka wllh kusa shekarata 22 bawanda yake zuwa wajena, da aka dage da addu'a sai Allah ya fara kawo masu neman auren toh mukuma bamusan dalilin shi ba, da mahaifiyata tai mishi magana me ya sa yake haka ko yabada nine? Sai ya ce shi bai bada niba, kuma ba Wanda ya zo neman aure wajen shi, ya ce kar asake mai maganar. Shine nake so naji zan iya kai kararsa wajen "yan'uwansa?.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis salaam; Toh sai dai mu ce Allah ya
tsare, Allah ya sa ya gane cewa yin hakan Kuskure ne ya sauko da ra'ayin sa na ƙin rashin Aurar da ke a
lokacin da kike so.
Mace tana da Haƙƙoƙin ta a gurin Iyayen ta, kamar yadda su ma iyayen ki suke da Haƙƙi a kanki, Haƙƙin Iyayen ki ne su kula
da lafiyar ki, su nema ilmin Addini idan ta kama sai a haɗa da na Boko, Haƙƙin Iyayen ki ne su ba ki Ci da Sha, idan kin yi rashin lafiya su ɗauke ki zuwa Asibitin, Haƙƙin Iyayen ki ne su kula da Tarbiyar ki sosai har
zuwa ga lokacin da za ki zama Cikakkiyar Mace, Ma'ana lokacin da za ki Balaga
ki Kai ga son yin Aure sai su Aurar da ke.
Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam yana
cewa, da ace Uba zai haifi Yaran Mata guda 3 ya kula da su sosai, ya ba su
Tarbiya, ya ba su ilmin Addini, cin su Shan su, rashin lafiyar su Tufafin sawan
su komai na rayuwar su wannan Uban yana yi iya Karfin sa, Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce har wannan Uban ya Aurar da su ba su taɓa aikata Zina ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa
Sallam ya ce wannan Uban a dalilin Yaran sa matan nan zai shiga Aljannah sai ma
ya zaɓi ta wanne kofa zai bi ya shiga wannan Aljannahn. A wani
ruyawar ko da Mace 1 ne ko 2.
Dalilin me zai shiga Aljannah? Sabida duk wasu Haƙƙoƙin ki ya sauke su sa'annan ya Aurar da ke ga Mijin
da ya dace da ke, Kuma ya mutu baya shirka ga Allah, ko ya mutu bai bar Addinin
Musulunci ba, sa'annan sabida irin sauke Haƙƙoƙin ku da yayi a kanku, ya tsare rayuwar ku ko Zina ba ku taɓa aikatawa ba sai Allah ya ce zai shiga Aljannah sai ya
zaɓi wanne kofa zai bi a gurin shigar Aljannahn.
Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam yana
cewa idan an zo neman ɗiyar ku da Aure,
toh ku bincika idan Kun yarda da Addinin sa Tarbiyar sa Dabi'un sa da halayyen
sa, Sana'ar sa da sauran su kab na kwaira ne, Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam ya ce toh ku ba shi Auren ɗiyar ku, ya ce
Amma idan Kun ƙi toh shakka
babu zaku haddasa fitina a bayan ƙasa, fitinar shine Zina Madigo a yanzu menene Yan Mata ba su aikatawa
dalilin iyayen su sun takure su sun Hana su yin Auren? Wallahi iyaye a ji
tsoron Allah akwai amsa tambaya a ranar Alƙimaya ko ba a so dole sai an amsa tambayoyin.
Sabida haka kina da Haƙƙi a gurin Mahaifin ki, idan kin Kai yin Aure ya
tashi ya Aurar da ke ga wadda kika dace da shi, ya zaba miki Mijin da za ki
Aura wadda ba zai taɓa cutar da
rayuwar ki ba, ya zaba miki Mijin da idan kin Aure shi mutuwa ce kaɗai zata raba ku, Haƙƙin sa ne dole ne ya Aurar da ke ga mutumin Kirki, matukar kin Kai yin Auren
kuma kina son yin Auren toh abun yi shi ne ya Aurar da ke idan Miji ya zo.
Sai dai idan har bai da hujjojin sa na ƙin Aurar da ke, kamar
misalin ace ai Duk Mazajen da suke zuwa Neman Auren ki ba su dace a ba su Auren
Mace a ko Ina ba, wato suna da Matsala a fannin Addinin su, ko halayyen su da
dabi'un su duk ba masu kyau bane, toh indai waɗanda suke zuwa gurin ki ba mutanen Kirki bane akan wannan
ne yake cewa ya bayar da ke don ya kore su, toh wannan babu komai daidai ne,
domin yana duba miki halin da za ki shiga ne bayan kin Aure su, babu Uban da za
a ce zai so wani ya Auri Yar sa ya je Yana Gallazawa rayuwar ta, yana cutar da
ita tana cikin matsala da tashin hankali a kullum, babu iyayen da za su Yar su
ta yi irin wannan Rayuwar, domin halin wasu Mazan a yanzu ki kalle su kawai ki
bar su a gurin duk tunanin ki sun wuce nan, ko misalin ai kina karatu a Jami'a
ba zai so ya haɗa karatun ki da
yin Aure ba, wata kila a ra'ayin sa sai kin gama karatun ki kafin ya Aurar da
ke, don kada ya Aurar da ke Mijin ki ya ce babu karatun ba za ki yi ba, toh
indai domin waɗanda suke zuwa gurin ki
ba su cancanci a ba su Auren Mace ba a ko ina ne ba, ko kuma ke a yanzu karatun
Jami'a kike yi shiyasa ya ce ba za kiyi Aure ba, toh yayi gaskiya, abun yi
kawai ki ci gaba da yin hakuri da juriya kina yin Addu'a har Allah ya kawo miki
irin wadda yake so ma rayuwar ki, kar kiyi gaggawa domin komai lokaci ne idan
lokacin ki yayi za ki yi Auren ki in Sha Allah.
Idan kuma waɗanda suke zuwa
Neman Auren ki mutanen Kirki ne sun cancanci a ba su Auren Mace duk inda suka
je, sa'annan kina karatun Jami'a sun yarda akan cewa za ki ci gaba da yin
karatun ki babu komai, amma ya ce a'a ya bayar da ke alhalin babu wadda ya ba
wa, toh gaskiya wannan Zalunci ne da cutarwa, domin babu irin waɗancan dalilan da zai sa ya hana ki yin Aure, kuma ba
karatu kike yi ba misali, kawai dai shi baya Jin cewa zai Aurar da ke a yanzu
ne, sa'annan Bai kawo hujjojin sa wadda ya dace da hankali ko Shari'ar
Musulunci ba, toh gaskiyar magana wannan Zalunci ne da cutarwa sosai ga rayuwar
ki. Irin hakane Mace tun tana hakuri daga karshe ta bijerewa iyayen ta ko sun
yi magana a banza take ɗaukar su domin
sun ki cika Mata burin ta na son yin Aure.
Irin hakane wasu Yan Mata dayawa suke zuwa ana
Zina da su wallahi zamanin babbar waya Mace ta gama shirya komai da Namiji
iyaye ba ku San komai ba, domin mace ta tabbatar da cewa iyayen su ba Aurar da
su za suyi a yanzu ba, sa'annan ga su Bukatu ga Sha'awa a tare da su, sai su ji
cewa Namiji ya ce ko nawa kike so zai kashe miki kawai ki zo ki Rika ba shi
kanki Yana Zina da ke, ko Mota kike so zai Siya mata, duk abun da kike so na
rayuwa zai yi miki, a rinjayi wasu akan cewa, toh menene a yin Auren ban da tashin
hankali? Ace miki ai abun da ake yi a Auren ai Jima'i ne da Mace ce, toh kin ga
duk zata samu yanzu anan, sa'annan ace idan kin yi Auren ban da masifar Miji ga
Yara za ki Haihu ki shiga cikin tashin hankalin Miji da na Yara da dangin Mijin
ki, amma anan babu abun da za ki ji ba za ki Haihu ba ma, amma bukatun ki suna
samuwa kullum yadda kike so a rude ki, ko Kuma Yan Madigo, duk haka za suke
rinjayi Yarinya da irin wannan a lalata rayuwar ta, iyayen ta ma ba su San
komai ba, dalilin cewa Mahaifin ya ƙi Aurar da ke. Toh rashin Aurar da ke Zalunci ne da cutarwa sosai wallahi.
Sabida haka indai kin San Manyan Mahaifin ki, ko
Mahaifiyar sa tana Raye ko Mahaifin sa yana Raye, ko Yayun sa Maza ko Mata, ko
Baffanun ki ko abokan sa, a cikin Waɗannan mutanen
indai kin san wadda idan sun gaya masa magana ba zai taɓa ketare maganar su ba dolen sa yayi aiki da abun da suka
gaya masa, toh ki bi kansu ɗaya bayan ɗaya da wannan maganar, kiyi musu Cikakken bayani sosai
yadda za su fahimci ki, sai ki ce toh a taimaka a tunatar da shi sa'annan don
Allah su roke shi ya bar ki kiyi Auren ki domin ga irin matsalolin da kike
Fuskanta.
Zuwa gurin su ki sanar da su abun da yake tafiya
kiyi musu bayanin halin da kike Ciki, wannan bawai kin Kai Karar sa bane, kin
je ne kiyi musu bayani a matsayin su na waɗanda suke gaba da shi ko abokan sa amma bawai karar sa
kika Kai ba, kuma inda ace karar sa kika Kai a hukuma za ki Kai shi a zo a kama
shi, sabida haka wannan shi ne karar mutum, amma wannan bawai Kara bane kawai
kina son ne a fahimtar da shi cewa Hakan da yake yi, ya take haƙƙin ki ne bai kamata ace
kin Kai yin Aure kina son kiyi Auren amma ya ƙi barin ki kiyi Auren ki ba, duniya ma ai sai ta
zarge shi.
Wasu iyayen suna da irin wannan ra'ayi na iska
wadda wannan ba daidai bane illa ce sosai ga rayuwar Mace a wannan zamanin,
idan ya bar ki bai Aurar da ke ba, ko duniya zata haɗe shi dai ba zai taɓa Auren ki ba,
toh menene amfanin ajiye ki alhalin kina son Auren, kuma a tambaye shi menene
dalilin sa ya ce kada a sake kawo masa wannan maganar, ba daidai bane wannan,
shi haka iyayen sa suka yi masa a lokacin da ya ce Yana son Mahaifiyar ki da
Aure ne? duk abun da ba a yi ma ba, toh bai kamata ace iyaye suna Hana Yaran su
yin Aure ba, a wannan zamanin ka samu fa wani ya zo gurin ka ya ce yana son Yar
ka da Aure, wannan abun Farin ciki ne da murna, kawai Bincike za a yi ya dace a
ba shi Auren ta? Eh! Shikenan ko tana karatu ko ba ta yi kawai a Aurar da ita
idan tana son yin Auren, shikenan.
Amma wai sai iyaye su sa Ra'ayi a Zuciyar su na
iska wai sai ta gama Jami'a, sai yar ka ta gama Jami'ar tafi shekara 3 ta
gamawa ga shi babu aikin yi Kuma Mijin ya ƙi zuwa neman Auren ta, kuma ga shi tana da Sha'awa
tana son Namiji a kusa da ita, ko kuma ai ba yanzu za ta yi Aure ba sai Nan
gaba, iyaye wannan bai daidai bane wallahi domin kuna jefa Yaran ku cikin
Hatsari da Masifa ba su fitowa su gaya muku ne, don Allah Iyaye a ji tsoron
Allah a yi abun da ya dace da Shari'ar Musulunci, kiwo ne Allah ya ba ka a
kansu, kuma sai Ka je gaban Allah ka amsa tambayoyi akan Yaran ka, haƙƙin su na kanka dole ne
sai ka sauke Haƙƙoƙin su a kanka. Allah ya
shirya, Allah ya sa ya gane, kuma Allah ya kawo miki Miji me tsoron Allah me
Addini nagari Ameen Ya Yayyu Ya Ƙayyum. Dafatan kin gane ko??
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.