𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum. barka da warhaka. ya ƙoƙari. Allah ya biya. Na kasance Ina fama da matsala kamar haka : nakan ji ana amfani dani azahiri ban taɓa mafarki ba. Dana fara ji nake Addu'o'i sai in Dena ji. Farkon lokacin da Abun ya same ni wajan asuba haka nakeji Kuma a duk sanda hakan ta kasance bayan wasu Yan awowi sai period Ɗina yazo. a lokacin dai baifi sai uku zuwa huɗu a shekara ba, ba Wani discharge dai. To Dana chanza environment sai Abun yayi worst sai ya zamana every month kamar sau uku ga matsalar dannau shima kusan ko yaushe sai Kuma na dinga Jin Abu na yawo akaina, su goshi na, Wani lokacin ina Jin ɗan radadu haka a ribs ɗina (wato hakarkari) ko hannu ko kafana Ina yin addu'a sai in Daina ji. Idan Ramadan yazo Kuma sai Abun da yake yawo ya ƙaru kullun sai naji abun. Ina nufi Kai komo ɗin kaina sai naji fuska na yayi nauyi. In Kuma ba Ramadan bane Wani lokacin idan Ina karanta ALƘUR'ANI ko sauraro ko su zikiri nakeji Abun na yawo. Wajen sau uku haka sai naji mutun a kusa Dani. A kwai sanda dama dannau ya danneni Ina addu'a naji an toshe min Baki. In nazo zan yi alwala da sallah in ta wasi wasi. idan ina zaune normal da zaran na tashi zan yi sallah in taji kamar na yi Hutu. Tunda danaji faidar kwanciya da alwala Dana fara sai alwalar ya karye ko Kuma Dana gama. Tun kan waɗannan matsalolin ma da zaran namiji yayi min magana sau ɗaya fa shikenan fa ko in mutun ya ce mun zaizo fa Bai zuwa . Amma Alhamdulillah matsalar dai ta ragu sakamakon bin shawarwari masana da ƙara dagewa da Addu'o'i. Dama Kuma bana wasa dusu azkar sai dai yawan ibaduna sun ragu. Dan Allah mene ne mafita. Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.
Mafita anan ita ce kici gaba da yin duk wani abin
da zai Ƙara miki kusanci da
Allah. Ina nufin kamar yawan Karatun Alƙur'ani da zikirin Allah safiya da maraice, da yawaita sadaƙah da nafilolin dare da
rana.
Hakika wannan abin dake damun ki shafar wani baƙin aljani ne wanda ake
kiransa JINNUL ASHIƘ. Kuma babbar manufarsa ita ce yin kokari wajen nesantaki da Allah ta
hanyar sanyaki ayyukan saɓo, wasa da
sallah, yawan jin waƙa, kallo ko sauraron abin da zai motsa miki sha'awa, yawan fushi, da dai
sauransu.
Abin da yake so ya cimma shine, ya aureki
amafarki, yana zuwa yana saduwa dake amafarki ko azahiri (kamar yadda ke kanki
kika shaida hakan). Daga karshe ya rika shiga cikin lamuranki na aure, ya rika
shiga zukatan samarinki yana korarsu ta hanyar sanya mummunan waswasi ko saɓani atsakaninku, da sauransu.
Game da waswasin alwala da yake sanya miki, ki
rika tureshi daga zuciyarki ki dena la'akari dashi. Kada ki rika biyewa abin da
kikaji azuciyarki. Mutukar kin san kinyi alwala har kin fara sallah, to koda
zuciyarki ta raya miki cewa alwalarki ta karye kada ki fita daga sallar. Sai
dai idan kinji wari ko Ƙarar fitar iskar daga jikinki.
Ki samu ruwa a cikin kofi (anfi son ruwan sama ko
zamzam) kullum ki rika tofa fatiha 7 ayatul kursiyyi 11, laƙad ja'akum 7, falaƙi da Nasi 3, kisha rabi,
sauran kuma ki shafe jikinki baki ɗaya. Safe da
dare.
Ki rika turara HABBATUS SAUDA kina tsugunnawa bisa
hayakin kullum kafin ki kwanta. Kuma ki shafe jikinki da MUHRIKUL JINN.
In sha Allahu zaki dena jin waswasin da abin da ke
yawo ajikinki ɗin. Har dannau dinma
bazai sake zuwa miki ba.
Domin samun Ƙarin wasu shawarwarin ko magani kina iya tuntubar ZAUREN FIƘHU akan wannan lambar
CALL : 07064213990 ko WHATSAPP : 08157968686.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.