Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Matsa Min Sai Mun Yi Jima'i Ina Jinin Al'ada

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhu malam ina kwana ant ashi lafiya ya sanyi to Masha Allah malam don Allah ka ba ni shawara me gidana ne malam bai da hankuri gameda kwanciya nikuma inafama da wata irin Al'ada idan yadauke idan nafara sallah zuwa anjima sai yadawo toyanzu megidana haryafara gajiya to yanzu jinin ya dauke sai ruwa Mai surki Dajini ne kuma yamatsa sai yakwantadani to malam yaya zan yi ne Allah ya rasa ni Amin.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam Wa Rahmatullah wa Barakatuhu:-

Mun Sha amsa irin wannan Tambayar Bai kamata ace kullum muna maimata Abu Ɗaya ba, Sa'annan Kuma idan hakane Babu amfanin Zaman ku a cikin group, Haka zalika Babu Amfanin tura Amsar mu a cikin group ɗin da muke yi. Shi neman ilmi bawai sai a lokacin da ke kike Bukatar sanin abu ne za ki nema sanin sa ba, duk abun da kika gani indai akan Addinin ki ne kamata yayi ki tsaya ki karanta shi yadda za ki fahimta sosai, wadda a gaba ke kanki za ki iya gayawa wasu amsar bawai kene za ki sake yin tambayar ba, amma ana tura Abu kina ciki kina gani ba ki karanta ba, sa'annan idan abu ya same ki irin sa ke kina son a ba ki amsa, ai hakan bai yi ba, masu tsayawa su bayar da amsar har a tura a group su kuma su ce me? balle ke da za ki tsaya kawai ki karanta ki wuce. yakamata mu gyara don Allah.

Mun Sha bada Amsa akan wannan tambayar Cewa idan Jinin Hailar ki, kin Gama yin sa wato kin cika iya Adadin kwanakin ki da Kika Saba Yi na kowanne wata, toh a Lokacin sai kiyi Wanka ki kama ibadar ki, Kuma Mijin ki zai iya Saduwa da ke.

Sa'annan bayan kin Yi wanka sai Kika ga wannan ruwan toh bawai Jinin Hailar ki bane, Alama ce ta Cewa kin Tsarkaka don Haka wannan Ruwan da kike gani bai hana yin Jima'i da Mace ko yin ibadar ki, domin jinin ki ya ɗauke kin Cika adadin kwanakin ki na kowanne Kuma kin Yi wanka. Duk abun da zai biyo baya na Ruwa Alamar Tsarkaka ne.

Sai dai idan Jinin yana rikici ne, ko kuma ke a dabi'ar ki sai kin ga irin wannan ruwan ne yake nuna cewa kin samu tsarki toh dole ne ki Jira shi sai ya zo ya ɗauke kafin nan kiyi wanka, ko Kuma jinin yana miki wasa, misalin ya zo yau gobe ya Ɗauke, toh Nan Kuma duk Lokacin da ya zo sai ki dakatar da ibadar ki, idan ya ɗauke sai kiyi Wanka indai a tsakanin ɗaukewar sa da dawowan sa akwai Sallah toh za ki yi wanka ki kama yin Sallah Kuma Mijin ki na iya sadu da ke, idan Jinin ya sake dawowa sai ki sake Dakatar da yin ibadar ki Sa'annan Mijin ki ba zai Sadu da ke ba har sai ya Ɗauke.

Kuma a Rikicewar Jinin ya zo yau, gobe ya Ɗauke sitta ya dawo a Haka Zaki irga iya kwanakin ki da Kika sabayi a kowanne wata, idan ya Cika sai kiyi Wanka ki kama yin ibadar ki Kuma Mijin ki zai iya Saduwa da ke, Haka zalika idan wani Jinin ya sake dawowa, toh ba jinin Hailar ki bane kin Zama Mai jinin Istihala kenan wato Jinin Ciwo, Nan Kuma Mijin ki zai iya Saduwa da ke a hakan domin ba Jinin Hailar ki bane.

Sa'annan Yakamata Maza Su ji tsoron Allah, Shi Jinin Haila bawai Yin Mace ba ce da har wai Namiji zai iya yayi ta yin Fushi da Hukuncin Allah akan Matar sa tana Jinin haila, sabida haka idan Matar ka tana cikin Jinin Haila, toh wajibi ne ka Saurara Mata har Lokacin da za ta yi tsarki ta yi wanka Haka Allah ya ce, Amma kuskure ne Wai tana Jinin Haila ka yi ta matsa Mata kana takura ta, idan har kana son ka ji Daɗi ai akwai yadda Shari'a ya ce ka yi sai kuyi irin Hakan, Amma bawai ka yi ta matsa mata har Kuna ɓatawa ba, Shin Lokacin da ba ka da Matar Kuma ya kake yi? Don Zama da za ka yi na Kwanaki 5 kawai shine zai zama aiki? Sa'annan Kai da kake matsawa Matar ka, me yasa kuma kuke takura Ɗiyar ku, Ku Hana ta yin Aure, Wai sai ta yi Karatu Shin ita Bata da Sha'awa ne? Kai ma ka gagara samun Natsuwa Dole Sai ka yi Jima'i da Matar ka, toh Shin Ina Kuma ga ita Ɗiyar ka da take tare da Sabon Balaga? Don Haka mu rika sa tsoron Allah a Cikin Zukanmu. Allah ya tsare ya Shirya.

Don Allah Ku Rika Karatun posting ɗin da muke yi Bai kamata ace wata za ta yi ta Tambaya mu amsa mata sa'annan mu tura a cikin group domin a Karanta a karu, Amma ba za a Karanta ba sai daga baya Kuma ku dawo kuna yin tambaya irin wadda Muka amsa sa'annan an tura a group, kenan Babu Amfanin tura Amsar Tambayar da muke yi. Dafatan kin gane Koh??

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments