Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Ka Karanta Qulhuwallahu Sau 10 A Jere Za A Gina Maka Gidan Bene A Cikin Aljannah Idan Ka Karanta A Daren Laylatul Qadari Fa?

TAMBAYA (72)

Hadisi ya tabbata cewar duk sanda musulmi ya karanta Qulhuwallahu ahad sau 10 a jere za a gina masa gidan bene a Aljannah, idan kuma na dace da daren Laylatul Qadari, kenan Allah SWT zai ninninka min ginin gidaje a cikin Aljannah sannan kuma shin zan iya karanta sama da sau 10 don samun gidajen da yawa

AMSA

Alhamdulillah

Shahararren Tabi'in nan Sa'id ibnul Musayyab (Rahimahullah) ya karbo hadisi mursal cewar Annabi SAW ya ce: "Duk wanda ya karanta Qulhuwallahu ahad sau 10 a jere, Allah SWT zai gina masa katafaren gidan bene a cikin Aljannah. Idan ka karanta 20, gidaje 2, ka karanta 30 gidaje 3

Sayyadina Umar RA ya ce: "Na rantse da Allah ! In dai hakane to zamu samu gidajen bene da yawa tunda zamu yawaita karantawa

Sai Annabi SAW ya ce: "Fallahu akhsar" ma'ana: "Allah shi ne mai yawaitawa"

Abin nufi shi ne Allah SWT ba zai gaji da gina muku gidajen ba matuqar zaku yawaita karantawa

(Sunan Darimi hadisi mai lambata 3429)

Hafizh Ibn Khathir (Rahimahullah) ya ce: wannan hadisi ne mursalin jayyid (mai kyau)

(Duba Suratul Ikhas a cikin Tafsir na Ibn Khathir)

(Muhammad Abusoomar ya taba amsa makamanciyar wannan tambayar)

Haka kuma an karbo hadisi daga Abu Hurairah RA ya ce: Annabi SAW yaji wani mutum yana karanta Qulhuwallahu ahad sai ya ce: "gaskiyar sa ce"

Sahabbai suka ce: Ya ma'aikin Allah, mene ne gaskiyar ta sa ?

Sai yace (SAW): "Aljannah ce gaskiyar ta sa"

(Musnad Imam Ahmad 7669)

Annabi SAW ya ce: "Duk wanda ya karanta Qulhuwallahu ahad sau 10 a jere, Allah SWT zai gina masa katafaren gidan bene a cikin Aljannah"

(Sahih al-Jami' al-Saghir, 6472 na Muhammad Nasiriddin albany)

A shawarce, duk wanda ya karanta wannan hadisi to ya dinga aiki dashi musamman ma a cikin goman karshen nan don samun yawan dubunnan gidajen saboda daren Laylatul Qadari - idan kai malami ne to sai ka tara dalibanka ka ce su dinga karantawa sau 10 a jere, idan mahaifiyace to sai itama ta tara yayanta waje guda su karanta a tare kuma a jere, hakama mahaifi. Gidan haya kuke zama a matsayin mata da miji to ku lizamci wannan bonanza don samun babban rabo, kada ayi biyu babu

Wannan bonanza za ta fara ne daga lokacin da rana ta fadi har zuwa ketowar alfijir din daren LAYLATUL QADARI

Kuma duk wanda ya koyawa wani to yana da ladan wani gidan daban ba tareda an tauyewa wanda aka koyawa haqqinsa ba kamar yanda ya tabbata a cikin sahihin hadisi. Allahu Akbar ! Wallahi babu wani Attajiri a duniyarnan da ya isa ya baka wani abu kwatankwacin wannan

Aljannnah gaskiya ce. Tananan yanzu haka, an tanade ta ga masu rabo. Mu'ujizozin Qur'ani kadai sun isa sun tabbatar mana samuwar Aljannah

A shekarun baya akwai wani lokacin da muna muna zaune tareda yan uwa a makarantar Nurul Islam litahfizul Qur'an dake anguwanmu, ina cikin karatun Qur'ani ina karanta daidai ayata 26 cikin Suratu Yunus inda Allah SWT yake cewa;

( لِّلَّذِينَ أَحْسَنُوا الْحُسْنَىٰ وَزِيَادَةٌ ۖ وَلَا يَرْهَقُ وُجُوهَهُمْ قَتَرٌ وَلَا ذِلَّةٌ ۚ أُولَٰئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ )

يونس (26) Yunus

Waɗanda suka kyautata yi, sunã da abu mai kyãwo kuma da ƙari, wata ƙũra bã ta rufe fuskõkinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, sunã madawwama a cikinta.

Anan take sai qurar iska ta taso ta lullube fuskokinmu gaba daya, kasa ta shigarwa wasunmu ido, masu furzar da kasar nayi, tuf ! tuf ! mutane na ta kakkabe fuskokinsu

Nace Allahu Akbar ! Sadaqallahul Azim

Anan naga mu'ujizar Qur'ani qarara, na nunawa yan uwa da muke tare daidai wannan ayar, mukaita fata da roqon Allah Azzawajallah ya sakamu cikin Aljannah gidan dawwama inda qura bata rufe fuskoki wadda fadin Aljannar musulmi daya tak yakai girman sammai bakwai da kassai bakwai kamar yanda Allah SWT ya fada;

( وَسَارِعُوا إِلَىٰ مَغْفِرَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ وَجَنَّةٍ عَرْضُهَا السَّمَاوَاتُ وَالْأَرْضُ أُعِدَّتْ لِلْمُتَّقِينَ )

آل عمران (133) Aal-Imran

Kuma ku yi gaugawa zuwa ga nman gãfara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda fãɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta dõmin mãsu taƙawa.

Allahu Akbar ! A dan karamin sanin da Allah SWT ya ba ni na bangaren ilimin kimiyyar sararin samaniya (Astronomy) wannan ayar ita ce tafi kowacce dauremin kai la'akari da ana auna girman sama ne da gudun haske wanda a kowanne second daya haske yana gudun kilometers 300,000 ne kuma akwai inda kafin haske yaje sai ya share sama da shekaru trillions, quadrillions, octillions ko zillions ko ma sama da haka kuma duk magana ake ta lebatun sama ta farko ballantana ta biyu har zuwa ta bakwai. To in dai har fadin gidan mutum daya a Aljannah zaiyi daidai da sammai bakwai da kassai bakwai to ina kuma ga tsayin gidan, tunda a al'adance tsayi yafi fadi

Wallahu ta'ala a'alam

Ya Allah ka sakamu a cikin Aljannatil Firdous don rahamarka ba don halayenmu ba

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments