DUK WADDA TA ƘARA SAKA DOGON WANDO A CIKIN GIDANA A BAKIN AURENTA
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salamu alaikum warahmatullah mallam brk da asuba ya ƙoƙari'ubangiji ya ƙara imani da lfy amin. Mallam tambaya gareni mata da mijine suka samu sabani harta basa shiga harkar juna na kusan wata huɗu to dama wata rana ya taɓa cewa da duka matansa duk wadda ta ƙara saka dogon wando (trouser) a cikin gidansa abakin aurenta ita kuma wannan mata dataga halin da suke ciki da mijin bayan ya dawo wata rana sai ta saka wando tazo gabanshi tana gaya mishi gashi tasa wando yana ganin haka sai ya fita daga gidan shidai baice mata komaiba tana ganin ya fita sai ta tafi gidansu ta ce ya saketa mallam ƙarshe dai har ta yi zaman idda ta yi aure ta haihu baizo gidansu ba amma agefe yana fadar shi bai saki matarsaba amma ta yi aure kuma yana gayawa 'ya'yansu ma bansaki mamankuba amma gashi ta yi aure to mallam menene hukuncin wannan aure? ubangiji ya kara imani da basira
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam Wa Ramatullahi:-
Toh Abin da Ya ce idan har ta Aikata a Bakin Auren
ta. sai kuma ta aikata shi toh ta Saku, Koda kuwa bayan Shekara Duba ne indai
bai ce ya warware Kalmar sa ba, sai kuma ta aikata wannan abun da ya ce in ta
yi a Bakin Auren ta sai kuma ga shi ta yi shi. toh Saki ya Afku.
Sabida haka Kenan, Wannan Matar bata da wani Lefi.
Don ta yi Idda, sake Auren wani Namijin daban. Domin ita ɗin din Sakakkiya ce. Kuma Auren da tayi, ta yi sa ne a
Bisa Ka'ida. Tinda bata Ɗaura Aure ba, har sai da ta yi Idda. wannan yayi babu komai a gurin Auren
ta yayi.
Sai dai na sha yin Magana akan Wannan Mas'alar.
Cewar duk Namijin da ya Sake ya gayawa Matar sa cewar idan kika yi Abu Kaza a
Bakin Auren ki. Wallahi Komin daren-dadewa, Sai Shaiɗanin ta ya sa ta aikata Wancan Abin da mijin ya ce kada
ta yi toh sai ta yi sa. Kamar yadda ita kanta wannan matar ta Tuno da Abin da
ya fadi. Kuma tana Neman Saki, Sai Ta Aikata Hakan. Wallahi Mata Ba a yi musu
Haka. Shaiɗanin su yafi duk inda
kake Tunani, Sabida Haka Muna Kiyayewa.
Kuma Ni Banga Lefi ba ma dan Mace ta sa Wando a
Gidan Mijin ta ba. Ae ina ga Kamar Burgewa Ne ma Wannan. Indai ba Maza bane
suke Shiga Cikin Wannan gidan ba. su mata duk lokacin Mijin su ya ce wacce idan
kin fita a Bakin Auren ki ko kuma idan kin aikata wannan abun toh a Bakin Auren
ki, za ka ga sheɗan yana ta
rinjayar ta a ƙarshe kawai sai
dai ka ji cewa ta je, Kuma idan ta je sakin ya tabbata ko ba ka so wlh.
Sabida haka Kenan. Ya Kamata Muna Duba abin da zai
sa Muke san Saki a Aure. Sakin nan Barkatai ba tare da an kai Ruwa Rana ba, Ba
shi da wani Amfani. Akan Abin da bai kai ya kawo ba kawai a yi saki. musamman
ga Samari masu yin Aure a yanzu ba su san komai ba akan saki sai Jima'i ba
hakuri babu juriya babu tausayawa Mace sai a yi ta furtawa Mace saki har Auren
ya zo ya haramta a tsakanin su, a dawo ana ta yin Karya ana neman Fatawa me
Sauki don Matar da ta dawo, Kuskure ne wlh Muna kai Zuciya Nesa bai kamata daga
Mace ta yi Kuskure kaɗan ka ce ka Sake
ta ba.
Sabida Mutuwar Aure, tana Sanya Yara shi Shiga
wani hali. Su sami Tabarbarewar Tarbiyya sakamakon Rashin Kyakykyawar Kulawa
daga Ɓangaren Mahaifiya ko
Mahaifi. Toh menene amfanin yin gaggawar sake Mace? ka yi saki ka dawo kana yin
Karya akan cewa Kai ba ma sakin ka yi ba alhalin sakin ne.
Haka zalika Kema da kika Nemi Saki. Baki san Irin
Namijin da Za ki sake Aura ba a rayuwar ki Ba Mamaki ki Auri Namijin da Za ki
yi Da Na sanin Rabuwar ki da shi fiye da wadda kike tare da shi. Ko kuma ma Har
ki Koma ga Allah ba wanda zai zo ya Aure ki. Tin Kina da Sauran Kuruciyar ki,
har ki Tsufa Ba Mijin Auren da zai sake zuwa gurin ki.
Mutuwar Aure bata da Amfani Gaskiya. Sai idan da
Dalilai Masu Karfi. Wanda Ake ganin Mutuwar Wannan Auren Shine Zai fi kawo
Maslaha. Ma'ana idan har Akwai Cutarwa a Tsakanin waɗannan Ma'auratan. Allah ya Zaunar Da Auren Mu Lafiya.
idan kuma akwai cutarwa ko kuma hakan zai Kai ki ga Saɓawa Allah toh gara a raba Auren shi ne yafi dacewa akan
ci gaba da zama da shi, domin mata dayawa a yanzu sun koma Zina da Madigo akan
dalilin gidan Miji kaɗai.
Sa'annan Daman an ce ba ki shi yake yanka Wuya, In
dai a bayanin da Kika fada shima Mijin Haka ya furtawa Matan sa, misali ya ce
idan kun saka Dogon Wando a Cikin Gidan nan, toh a Bakin Auren ku Kuma kowacce
ta ji da Kunnen ta ya Furta hakan, Kuma sai ga shi ita wannan ta Saka wandon da
aka ce musu idan sun saka a Bakin Auren su Kuma ta zo da shi har gaban sa ya
gani.
Toh ta Saku, saki 1 sai dai idan a Lokacin ya ce
ya dawo da ita, wato yayi kome kamar yadda kuke Cewa, toh Nan kam tana zamar
Matan sa, da Asara ai gara gidadanci, Amma in dai tunda Suka Yi hakan har ta
kama Hanya ta je gidan su ta zauna har na wata 3 Bai ce ya dawo da ita ba. Toh
ta Saku Kuma ta fita daga Matar sa. Idan Daman ya taɓa Yi mata Saki 1 a baya toh ga 1 yanzu, ya zama 2 kenan,
idan Kuma daman yayi 2 a baya toh yanzu ga 1 ya zama ukku shi Kuma Daman Saki
ukku Babu kome har sai ta yi Sahihin Aure ga wani Namijin daban. Kuma yanzu ta
yi don haka Kalmar da ya fada Kalmar Saki ne ko Ina Suka je ta fi sa Gaskiya.
Idan Yana ganin Bai yarda ba, Yana Cewa shi Bai
sake ta ba, toh sai ya Kai su kotu gurin Alkali Mai Shari'ar Musulunci shi ya
San me Hukuncin Auren su. Ai shiyasa Miji ba zai kafawa Matar sa wani doka Kuma
ya ce wai idan kin Yi a Bakin Auren ki ba!! Ita Mace a ko da yaushe tana tare
da sheɗan ne, Miji na Cewa idan kin Yi wannan abun a Bakin Auren
ki, toh shi Sheɗan sai ya bi duk
hanyar da zai bi sai ya Saka ki kin Yi wannan Abun Kuma sai kin aikata abun.
Don Haka ne a kullum malamai suke Jan Kunnen Maza
Musamman samari da Babu ilmin Saki a kansu su Dena sake bakin su komai ka ce za
ka gayawa Matar ka ba daidai wannan bane. In da a lokacin ya gane ai sai ya ce
toh ya dawo da ita Nan kam ko tana so ko ba ta so ta dawo idan ta ɗaura wani Auren toh ta yi Aure akan nashi Auren, Amma a
yanzu Kalmar da ya ce idan kin Yi Abu Kaza a bakin Auren ki Kuma ta yi abun,
toh ta Saku Kuma Saki 1 ce sai dai idan ya Kara.
Amma akwai Kalmar da zai yi ba zai zama saki ba ko
ace ta aikata shi, misalin ace ko kafar gidan ku Biyu ne sai ya ce Idan kin
fita ta wannan Kofar a Bakin Auren ki ya nuna miki Kofar, sai kuma kika fita ta
ɗayan kofar da bai nuna miki ba toh ba ki saku ba, amma
muddin kin fita ta inda ya gaya miki Kuma bai warware bayanin sa ba, toh ko
shekara nawa za ki yi indai kin bi ta gurin fa Auren ya Mutu, Allah ya tsare ya
Shirya. Dafatan kin gane Koh????
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.