YAN'UWANA SUN CE IDAN NA KOMA GIDAN MIJINA ZA SU YANKE ALAƘA DA NI HAR ABADA:
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam dan Allah inaso ne a ba ni shawari. Mijina ne ya sake ni , saki ɗaya to kafin ya sakeni dama yasha faɗin zai sakeni akan kowani irin kankanin laifi na mishi. Sannan ya kasance yana da wadata amma kuma baya biya min dukkanin bukatu na ba ma ni kaɗai ba har iyayen shi ma ba jin daɗin shi sukeyi ba, amma iyayenan nashi da yan uwan shi har sun fara zargin cewa ni kaɗai nike moran shi kuma wallahi bana wani moranshi. Bugu da kari ya kasance mutum ne shi marar tsafta ga rashin hakuri wanda har yayi saurin furta cewan ya sake ni akan abin da bai taka kara ya karya ba. To shine yanzu kuma ya dawo wai yana so na koma duk da na haihu 1 dashi amma wallahi ni bana jin zan iya komawa. Besides yan uwana kuma suma sun dage wai babu inda zani muddun kuma na koma to za su yanke alaka dani har abada. Ni marainya ce ban da uwa ban da uba Malam dan Allah abani shawari akan wannan alamari nina kasa sanin yadda zan yi gashi ba wata babba bace ni. Aure na dashi shekara biyu ne ya sakeni. Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam:- Toh ai Halin Mazan Yanzu kenan
sai a Hankali, mafi Yawancin Mazan yanzu Musamman Samari Halin su kenan soyayya
a waje kamar za su hadiye ki kyautawa a waje kamar yaya Ramadan Basket wani
tsiyar duk za a miki domin kawai a samu karbuwa bayan Aure Kuna masifa da
Bala'i kullum kina cikin tashin hankali.
Su Iyayen ki ko Yan uwan ki Suna da Gaskiyar su,
domin duk Mutumin da Za a Ce wai Bai San Mutuncin Mutane ba, Bai San Darajar
mutane ba, Bai San Kimar Mutane ba Uwa Uba don Yana da Dukiya Yana yiwa kowa
Kallon Kashi, ke kanki Bai San Darajar ki da Qimar ki ba, toh me Amfanin Zama
da shi? Sa'annan Duk wadda za a wai bai San Haqqin Allah akan Sa ba ko kuma ya
sani amma ya take sanin sa, Musamman na Iyalin sa, shin menene Amfanin Zama da
shi? Kin ga kenan abun da Yan uwan ki Suka Hanga miki kenan, suka ga ba ki Dace
ki koma wannan gidan sa ba, Kuma Sun Yi gaskiya.
Irin wannan ne ya sa Shari'a ta ce a yi Bincike
sosai, waye Mijin da Za a Aura dakyau kafin nan a yi Auren, toh Amma ba a yin
binciken yadda yakamata, kawai sai a yi bincike Sama-sama, a Bincika Fuskar da
Mijin ya zo da shi bayyane, Amma ba a bincika Boyayyen Fuskar sa na asali ba,
Nan da Nan Wai har an Gama bincike wani kawai yana cikin gidan sa ne zai yi
kira a waya wai Kun San wane? Eh mun San shi kaza ne ah shikenan mutumin Kirki
ne zai iya rike ta, Sai a yi Auren daga baya a zo a samu Halin Mijin kab Bai
dace ma a ba shi Auren Mace a ko Ina ba, a dawo ana ta Neman Mafita, Alhalin ko
an samu mafitar ke Matar an Gama da ke, domin Budurcin ki ba zai dawo yadda
yake da ba, Idan ma kin hakura za ki zauna da shi, Kullum kina Cutuwa ne, Idan
ko ya Sake ki Kin Rabu da Shi, yayi Riba da ke, Domin Kin haihu masa, ke kin
dawo Bazauwara, Kuma idan Za ki Sake yin Aure a Wannan Zamanin Daker Za ki Samu
Namijin da zai So ki ya So Ɗan ki.
Shi Kuma idan ya tashi Kara Auren sa Kowacce Mace
yake so zai Aure ta. Kin ga kenan an Yi Riba da ke. Toh idan an Gaya muku
Shawara kafin ku Auri Namiji ku tsaya dakyau kuyi Bincike sosai kafin ki Aure
shi sai ku ce ai mutumin Kirki ne Jama'a suna Yabon sa, Bincike sama-sama wai
har an gama idan an ba ku Jin Shawarar ba a ɗauka sai an Yi auren a dawo ana yin Nadama.
Ai Shi Bincike indai Auren Za a Yi Kuma a zauna na
Har Abada, toh ko Shekara Za a Yi ana yin Binciken, toh gara a yi Shekara Ɗayan ana Bincike, Kai ko
Shekara 2 ne Za a Yi ana Binciken Halin Mijin da ya zo neman Auren Ɗiyar ku, wallahi gara ku
yi Shekara 2 Kuna Binciken sa, ku gane Gaskiya da Gaskiyar sa yin Haka shine ya
fi dacewa, akan ku yi Binciken Wata 1 ko Sati 1 Nan ma Binciken a Waya Za a Yi
Wai an Yi bincike Sai a sa Ranar Aure, ana yin Auren a dawo ana Neman Mafita ko
Shekara 1 Auren ba zai Yi ba Har an Sake Ɗiyar mutane ta dawo gida. Yau ko Akuya ce zaku siyar dole ne a duba waye za
a siyarwa balle Mace za a ɗauka a Aurarwa
Namiji ace wai an yi Bincike a Kiran waya Kaɗai wannan ai wasan Yara ne Aure ya wuce nan Darajar Mace
ya wuce kiran waya ana Binciken mutum wai za a ba shi Auren ta ne shiyasa ake
Bincike.
Idan an tambayi Ma'auratan Shin ba kuyi bincike
bane kafin Auren ku? Sai su ce Wallahi Malam mun Yi, Alhalin ba su Yi ba, a iya
Waya kawai Iyayen su, suke Kira a Waya a gari kaza ko Anguwa, wai kun San wane?
Eh mun san shi, toh me Halin sa? ai Mai Kyau ne, daman muna son mu ba shi Auren
wacce ne ai mutumin Kirki ne wlh, Shikenan wai har an gama Binciken fa, idan an
ji Haka Wai a hakan ne har an Yi Bincike an gama, Aure fa aka ce muku! Aure
abun wasa bane kamar yadda Yan Films suke yi wallahi. Mace za ka Bayar ma wani Ɗan Adam na Uwan ta,
bawai Ɗan AKUYA Ko Tunkiya ba.
Ko ma wannan ne yakamata ka yi Bincike me zurfi kafin ka Siyar da shi.
Amma Wai Ɗiyar ka za ka Aurar ma wani sai a Gama bincike a Waya haba don Allah, idan
yana Kano ne Mijin da zai Aure ta ita Kuma tana Jalingo, Sai Uban Yarinya ya
Fara kiran Waya a Kano Wai Kun San wane kuwa? Ba tare da An Wakilta wani ko shi
Uban ya je har gurin da yake da sunan zai gudanar da Bincike ba. Idan ma Za a
tura wani zuwa gurin sai ya je yayi Kwana biyu ko sati Wai har an Gama Bincike,
Alhalin ko Rabin Binciken Halin sa ba a Yi ba, ko Halin sa na Kashi 1 ba a
bincika ba.
Ai kamata yayi a yi bincike na Shekara 1 ko 2 ana
Bincike kawai gaggawar me ake yi? domin Allah ya kawo mu Zamanin da Sai a
Hankali Mazan yanzu, kenan idan ana son Auren ya zauna na Har Abada Wajibi ne a
gudunar da Bincike na Shekara 1 ko 2 yin Gaggawan Aurar da Mace hatsari ne
babba ga rayuwar ta, gaggawa ba shi ne Aure ba, a yi sa a natse a zauna har
Abada shine Mai Kyau kowanne Ɓangare zai Fi Jin daɗin Zama da Ɗan uwan sa.
Shawarar da Zan ba ki shine, idan har Mijin ki
Yana ba ki Ci da Sha, Yana Kula da Lafiiyar Ki daidai Ikon sa, Yana Sauke
Haqqin Aure akan Sa, Yana Ɗinka Miki Suturar Sawa. Ɓangaren Jima'i Yana gamsar da ke Yana sauke Haqqoqin ki a kansa, toh Ki yi
Hakuri ki Koma Gidan Sa. Abun da Kika Sani na Munmunan Halin sa ko na Rashin
Tsafta ko Rashin yin kyauta da Sauran Su, Ki bar sa da Halin sa ki Sha maganin
zama da shi a hakan sa'annan ki dage gurin ba shi shawara me kyau da kuma yayi
masa Addu'oi Allah ya sa ya gane gaskiya.
Idan Kuma Bai yin Duk abun da na Lissafa miki a
Sama, Kuma Yana da shi bawai Babu ba, toh Shawarar kenan kada ki koma gidan sa
tunda Allah ya raba ku, domin ko kin koma a yadda Kika San shi a baya, Haka
Zaki sake komawa ki same shi ba zai taɓa Chanjawa ba ko
ya ce ya chanja kawai ya fada ne domin yayi kwana biyu bai yi Jima'i da ke bane
kina komawa idan yayi Jima'i da ke na kwana biyu halin sa zai dawo kab. Amma
muddin Yana yin abun da na lissafa miki a sama, toh Kiyi Hakuri ki Koma Gidan
Mijin ki Yan Uwan ki da duk Waɗanda ba su son
ki koma gidan sa, ki nemi Manya ko wani Malami a Unguwar ku ki haɗa su da shi, zai nemi Su a Yi musu Nasiha da tunatarwa In
Sha Allah Su ma Zaku Goyi Bayan ki koma ba tare da wani Abu ba.
Komawar ki gidan Mijin ki matukar Yana yin waɗancan abubuwan da na ce Miki toh shine ya fi dacewa,
domin Aure a Yanzu idan mace ta samu Damar yin Aure ta shiga gidan Miji, toh ba
karamin Ƙyauta ba ce Allah ya ba
ki, matukar kin Yi watsi da Wannan Damar naki, toh a gaba abun zai zo ya dame
ki Sosai, ki Zauna Babu Auren kuma Gidan ku su Rika matsa Miki kullum Suna
musguna miki da ke da Ɗan ki kullum kina Cikin Tashin hankali na Rana daban na Dare daban, Matukar
ba kiyi Sa'ar Gidan ku ba, toh tashin hankali da za ki Shiga sai kin Gwanmaci
gara Zaman ki a gidan Mijin ki Akan gidan ku.
Domin za su Rika Saka ki a gaba ne kullum ke da Ɗan ki, Amma idan kina
gidan Mijin ki Waye zai saka ki a gaba Sai shi Mijin naki, shi Kuma idan ba ki
da Haqqin Sa, toh Yana Daukawa Kansa Zunubin da idan yayi Wasa Makomar sa ba
zai taɓa Yi Masa Daɗi ba.
Sa'annan idan ba ki koma ba, Kamar yadda na bada
Misalin Cewa a yanzu Maza ba kowa ne yake son ya zauna da Mace Wadda take da Ɗa ko Yarinya ba, Shin
kina ganin idan ba ki koma ba Waye zai Zo Neman Auren ki akan Lokaci? An San
Cewa kowa da rabon sa, Amma yaushe za ki yi? Zaman Watanni nawa za ki yi ko
Shekara nawa za ki yi? Kuma ga shi dai kina da bukatu da na Yaron ki, ga shi
Kuma kin ce Mijin naki a gidan sa ma ba ya Miki, toh yanzu waye zai Rika ba ki
Koda na Sabulu ne? Idan ma Yan uwan ki ne za su Rika ba ki, toh yau da Gobe ya
wuce Wasa dolen su za su gaji, su Fara musguna miki kamar yadda na yi bayani a
baya, shin wani Hali za ki shiga toh?
Kina da Sha'awa kin San Jima'i, Shin Yaya za ki yi
da Sha'awar ki idan ba ki samu Mijin Aure akan Lokaci ba? Sa'annan idan kin
samu Mijin Aure ya zo zai Aure ki, Shin kin San Halin Sa ne? Kin tabbatar Cewa
zai rike riko na Amana, So na Gaskiya Halin sa ba Ɗaya yake da Mijin naki na Farko ba? Domin Mazan
Yanzu Fuska biyu ne da su Za su ɓoye Ainin Fuskar
su, sai Su Bayyanawa Mace abun da ba ta sani ba, sai an Yi Auren Ainin Fuskar
su za ta Bayyana, daga Lokacin Kuma sai a Fara samun matsala sosai har ta Kai
ga Kun rabu. Shin kin San Halin Wadda zai zo ya Aure ki? Gara Mijin ki na Gida
a yanzu kin San gaban sa kin San bayan sa, toh Wadda zai ya nemi Auren ki a
gaba fah?
Shin a yanzu a unguwar ku Yan Mata da Zaurawa Nawa
Kika sani Cewa Suna zaune Suna neman Mazan da za su Aure su kamar Yaya, Amma
har gobe Allah Bai ba su ba? bawai Kuma Ubangiji Bai son su bane ya Hana su
Mazan Auren, Shin ke da Kika samu wannan ƙyautar me yakamata kiyi?
Don Haka Shawara ta shine, matukar Mijin ki Yana
Sauke Haqqin Allah a Kansa, Yana Ciyar da ke, Yana Shayar da Ke, Yana Ɗinka Miki Tufafin sawa, Yana kula da Lafiyar ki Yana Sauke Haqqin
Jima'i a kanki, Amma Kyauta Ce da wasu Biyan bukatar ne Bai Miki, toh Ina ba ki
Shawarar da Kiyi Hakuri ki jure ki koma gidan sa, ki ci gaba da Kai kukan ki ga
Allah, ki bar sa da Halin sa. Ki Koma Gidan sa ki Ci gaba da Yi Masa Ladabi da
Biyayya kina sauke duk wani Haqqin Sa a kanki kina bin Dokokin Allah iya Karfin
ki Allah ya ɗauki Rayuwar ki a gidan
Mijin ki Ki Samu Aljannahn ki, shi Kuma da baya Kyautata Miki ya je a Ranar
Alkiyama zai ga Samakon sa. Yan uwan ki, ki nemi wani babba ko Malami ko Malama
a same su a ba su Hakuri kada su ce za su ɗauki Matakin da Suka Ce za su ɗauka, a yi musu Nasiha a tunatar da su In Sha Allah Suma za
su bar ki ki koma.
Amma idan baya yin abun da na Gaya Miki, Bai Ciyar
da ke, Kuma Yana da shi, Bai Kula da Lafiiyar ki, Kuma Yana da Halin Yi, Bai
Sauke Haqqin Jima'i ba ki Gamsuwa da shi, toh Koda Za ki koma gidan sa ku je
Gaban Alkali Masanin Shari'ar Musulunci a yi sa a Rubuce ya sa hannu ki sa
hannu, kin ga idan ya dawo Bai Ciyar da ke Bai kula da Lafiyar ki, toh Alkali
ya San wanne Hukunci zai masa. Ina ga iya abun da Zan iya Cewa kenan. Allah ya
tsare ya Shiryar da Maza masu yin Haka. Dafatan kin gane Koh?
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.