HUKUNCIN FYAƊE MUSULUNCI
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum waramatullah malam menene hukuncin yin FYAƊE a musulunci, (Rape) ko "AL-AGHTISAAB" da larabci. Na gode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam Wa Ramatullahi:
Hukuncin Yin Fyaɗe a Musulunci, Malamai Suka Ce Hukuncin Wanda Yayi Fyaɗe yana Ɗaukar Ɗayan Huɗun nan ne:
1. Idan ya Taɓa Yin Aure toh a Kashe Shi Kawai, ((Amma Sai da Izinin
Hukuma da Kuma Kotu)). Sabida Hukuncin Sa iri ɗaya ne da Wanda Yayi Zina tare da Amincewar Mace, Matar
Aure Su Ko Budurwa Bayan yana da Aure Ko ya taɓa yin Auren a Baya, ko ita Matar Aure, ko wadda ta Taɓa yin Aure tana Bazauwara tana Zina itama Hukuncin ta
Kenan Kashewa.
2. Idan Bai Taɓa yin Aure ba, toh Za a yi Masa Bula (100) Sannan a Kulle
Shi a Gidan ƴari na Shekara
Guda.
3. Duk Wanda Yayi fyaɗewa Mace Sai a Biyata Sadakin ta, Sai ya Bayar da Kuɗin da idan Za a Aurar da ita Haka Za a Karɓa a Wurin Wanda Zai Aure ta ba tare da An Rage mata Wani
abu ba. Kuma Zai Ɗauki Nauyin Jinyar ta, da Magungunan ta da Abincin ta har ta Warke daga
Raunin da Yayi mata. Domin Neman Karin Bayani Duba Cikin ((Muwaddah ta Imamu
Malik 2/734)).
4. Ana iya Ƙashe Mutum Sabida Fyaɗe idan ya Ji
Mata Rauni, Kuma Ya zo da Wani Makami da ya Tsoratar da ita, Malamai Suka Ce
Wannan Fashi ne da Makami yayi mata, Alkali Ko Hukuma Za Su iya Bayar da
Umarnin a Ƙashe Shi. Domin
Ayar nan da take Magana a Cikin (Suratul Maa'idah Surah ta 5 ayata 33):
إِنَّمَا جَزَاءُ الَّذِينَ يُحَارِبُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ
وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوا أَوْ يُصَلَّبُوا أَوْ تُقَطَّعَ
أَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلَافٍ أَوْ يُنفَوْا مِنَ الْأَرْضِ ذَٰلِكَ لَهُمْ
خِزْيٌ فِي الدُّنْيَا وَلَهُمْ فِي الْآخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Abin sani kawai sakamakon waɗanda suke Yaƙin Allah da Manzonsa, kuma suna aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna a kashe su
ko kuwa a ƙere su, kõ kuwa a kakkatse hannuwansu
da ƙafafunsu daga saɓani, ko kuwa a kõre su daga ƙasa. Sannan gare su wulakanci ne a cikin rayuwar
duniya, kuma a Lahira suna da wata azaba mai girma. (Suratul Maa'idah ayata
33).
Sannan a Duba Cikin Littafin Al-Istizkaar na Ibnu
Addul-Barri 7/146)). Allah ya Kiyaye ya Tsare Mu daga Wannan Mummunar Aikin, ya
Kara Tsare Ƴan Uwan Mu Mata
Musulmai daga Shiga Hannun Masu Wannan ta'addancin.
Yadda Matan Banza suke tallata kansu ma wani Fyaɗe ne mutum zai yi? bawai ina nufin yana dakyau bane,
dukkanin su Haramun ne, toh amma tunda mutum baya Jin tsoron Allah baya tuna
makomar sa da rayuwar iyalan sa, toh akan ka yi Fyaɗen ai gara ka tafi can.
Sannan Ka Sani Cewa fah Idan fah Ba a yi Maka
Wannan Hukuncin a Nan Duniya ba, sai Ka bada Cin Hanci ma Alkali ko Hukuma aka
Sake ka, toh a Ranan Alkiyama ba Ka Tsira ba, idan Kai Kana Ganin Cewa ai Ka
Tsira a Duniyar, toh a Alkiyama babu Tsira. Sa'annan wai me ya sa wasu Mazan
babu tsoron Allah a ransu ne? Namiji da Matan sa da Yaran sa har sun kai Aure,
Amma wai sai ya je yana Zina da matan banza a waje?
Namiji wai har akan shimfidar Matar sa zai ɗauko Mace ya kawo ta yayi Zina da ita don Allah wanne
irin rayuwa ce Musulmai suke jefa kansu a wannan Zamanin namu? Namiji Matar sa
zata tambaye shi kuɗi abun da Haqqin
sa ne yayi ko da ace ba ta tambaye shi ba, Amma zai qi kuɗin da ko 10k bai Kai ba, amma haka zai biyawa Karuwa Kuɗi daga wani state ya kashe Mata kuɗi Sama da 150k ta zo kawai yayi Zina da ita ko da na Yini
1.
Iyayen sa bai taimaka musu ba Matar sa da yaran sa
kab bai wadatar da su ba, amma ya je yana Zina da matan banza duk abun da suke
so zai musu a cikin gaggawa, Shi Musulmi ne itama Karuwar da zai ɗauko daga wani garin ko a garin Musulma ce, iyayen su ma
duk Musulmai ne, don Allah Ina za mu sa kan mu? wanne irin Bala'i ne da Masifa
ne wannan? Menene kake nema a jikin Mace karuwa wadda take ɗauke da Cututtuka? ga Matar ka wadda babu komai a jikin
ta, menene kake nema a jikin Mace wadda Matar ka ba ta da shi a jikin ta? Haba
Maza wanne irin rayuwa ce aka koma yanzu? rayuwar da zai jefa ka cikin halaka
daga nan duniya har zuwa Lahirar ka, ku ji tsoron Allah masu yin Zina da Fyaɗa ma Mata wallahi Rayuwar ku na cikin Hatsari.
Iyaye Mata da Maza Ku Kula da Irin Waɗannan Abubuwa Guda Biyar Waɗanda Kuke Yin Sakaci akan su Har Ake Yin fyaɗe ga Yaran Ku, Waɗannan Abubuwan
Sune Suke Jawo Yin fyaɗewa Mata a
Wannan Zamanin, Daga Cikin Dalilan da Suke Sabbaba fyaɗe Akwai:
1. Tsafi Da Bin Umarnin Bokaye. Wannan Shine
Babbar Dalilin da ya Saka Ake Yin fyaɗe da Yara Ƴan Shekara 3 Ko 6 Ko 8
Domin a yi Kuɗi, Wannan Umarni ne daga
Wurin Matsafa, Bokaye, Domin Abin da Suke Nema ba Zai Yiwu ba Sai An yi Zina da
Mace Mai Shekaru 3 Ko 4 ko 8. Allah Wadaran mu da Wannan Dukiyar. Idan Bahaka
ba Hankalin Zai Gagara Fahimta yaya Za a yi Babban Mutum, Mai Shekaru 25 ko 45
Ko 50, Sai Ka ga ya danne Mace Ƴar Karamar Yarinya Da Ko Magana ba ta iya yin sa da kyau ba, Me yake Nema a
Jikin ta? Babu Abunda yake Nema, Umarni aka Ba Shi daga Wurin Matsafa Cewa yayi
haka, babu Abunda yake So ya Ji a Jikin ta, Kawai tsafi ne da Sihiri.
2. Abu na Biyu da ke Sabbaba yin fyaɗewa Mata a Yanzu Shine, sanya burin a zuciyar Mace ita
damuwar ta kawai ta yi kuɗi ko ta rike
katon waya Iphone 16 pro max da gida me kyau da kuma Buguwa da Samari Suke yi
na Shan Giya Ko Ƙwaya, Ko Wani Abu me Bugarwa, Duk Wanda ya Sha Irin waɗannan Abubuwan Zai Aikata fyaɗe da Kisan Kai, Sabida Duk Wanda Zai Iya Yin fyaɗe, toh Zai Iya Ƙashe Mutum, Don Haka Idan Kuka Bar Ƴa'ƴan Ku Maza Suna
Shaye-Shaye a kusa da su, toh Ku ne First Victim Idan Sun Bugu, Domin Za Su
Fara da Iyayen Su Mata da Kannen Su, Kuma Ku Iyayen Su Kuna Ji Kuna Ganin Su
Tarbiyyan da Kuka Ba su Kenan. Don Haka Iyaye Ku Ɗena Sakaci da Butun Shaye-Shayen nan Har Kuna
Barin Yaran Ku Suna yi Amma Babu Matakin da Ke uwa ko Uba Za ku Ɗauka.
3. Abu na uku Shine Mace ta Rika tafiya Zuwa Wani
Wuri Babu Muharramin ta a Tare da ita, yanzu Yan Mata nawa ne suke shiga Jami'a
su tafi Amma babu kowa nata a garin, Mahaifin ta ko Mahaifiyar ta wata ba su taɓa zuwa garin da ta ke karatu don su duba ta ba, su kawai
damuwar su Yar su ta zo musu da First Class, Mace tana gari tare da iyayen ta
wata za ta yi wanka ta fita amma iyayen ba za su ce Ina za ki je ba, idan kin
jima a can ko kin kwana a can ko a jikin su? za a ga Manyan kuɗa-kuɗe a hannun
Yarinya Budurwa da Katon waya Iphone 16 pro amma ba zata a tambaye ta Ina ta
samu ba? karshe murna za a Taya ta har ma ace gaskiya Yarinyar nan akwai Farin
Jini taurarin ta na haskawa a gurin maza, don Allah me aka Koya mata a yanzu?
Mace zata kama hanya daga Kano zuwa Taraba ko Kaduna Babu Wani Namiji Ɗan Uwan ta da ta ke tare
da shi a kusa da ita, Koda Wani Gida Zata je a Cikin Unguwar Su da Daddare Wani
yayi Mata Rakiya a Matsayin Kariya babu shi. Kun Ƙyale ta a Haka ita ta je Ko Oho, Ke Uwa Kina Ji
Kina Gani ba Dole a Wulakanta ta ba, Har a yi Musu fyaɗen har ta sa burin duniya a zuciyar ta ta je tana yin
Zina ku iyayen ta ba ku sani ba, Mace karama ta San duk hanyar da za a bi Ciki
ba zai taɓa shigar ta ba wadda ke
Uwa ba ki Sani ba domin suna kallo a Fina-Finan Hausa suna karantawa a Littafin
novels ta yaya Yar ki ba za ta yi Zina ba?, Ita Mace Kamar Gold ne Suke, Kula
da su Ake yi ba dare ba rana yadda ki kula Kwai haka yakamata ki kula da Yar
ki, ga Duk Wani Motsin Su da Ba su Kariya, bawai Yin Hakan Takura ba ce, ba
irin Yadda Kake tafiya kai Kaɗai a matsayin
Namiji, ba Haka ya Kamata Mace ta Rika tafiya ba. Amma Sai Iyaye Mata da Maza
Sai Kuka Ce ai Yanzu Kai ya Waye ko Ina Ɗiyar ki Zata Iya Shiga ba tare da Kin ba ta Kariya ba domin ai ba Yarinya
ba Mace ita, kin manta cewa Mace mai rauni ce? Shin idan Wani abu ya Same ta Laifin
Waye ne? Naki ne Ko nata? Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasallama yayiwa
Matan Sa Irin Wannan Rakiyar da Ba Su Kariya, ko ya Saka Wani ya Zamo Musu
Bodyguard, Sabida a Lokacin sa an Samu Cases na fyaɗe da yawa. Duba Cikin (Sahihul Bukhari da Muslim da
Sauran Su).
Toh Sai Ke Kika Ce A'a Ba Za Kiyi Haka ba kawai Za
ki Tura Ɗiyar Ki Har Jami'a ba
tare da Kowa ba domin ita ba Yarinya ba ce, Za ki Aiketa ko Ina ba tare da Kowa
ba ai tana da iKon kare kanta, Uwa uba ma ba Za ta yi fita Irin Wanda Ranta
Yake so ba dole ne Duk Wani Sassan Jikin ta a Waje yake ta Yadda babu Wanda Zai
Ganta ba tare da Yayi Sha'awar ta ba har ya Neme ta da Iskanci ko yin fyaɗe da ita, Shin Yanzu Laifin ta ne ko naki ne ko Kuma na
Wanda yayi mata fyaɗen? Iyaye Mata
da Maza Kuna daga Cikin Masu Taimakawa Yaran Ku mata Wajen Yi Musu fyaɗen Nan.
4. Abu na huɗu Shine Shigar
Banza da Ɗiyar Ku Suke yi
a wannan zamanin suna tallata kansu a duk wasu social media Mace Budurwa kuma
Musulma ta fito tana rawa ta yi kwalliyar da idan Namiji ya kalle ta dole ne
sai yayi Sha'awar Jima'i da ita yayi duk yadda zai yi sai yayi mata magana ko
nawa ta ke so zai kashe Mata domin yayi Zina da ita kawai, ta Sanya Ƙayan da Suke Bayyana Gaɓoɓin Jikin ta
Nonon ta duwawun ta kana ganin pant nata a zata ɗauki kanta a video ta yaɗa a duniya ko Kuma ta tafi Unguwa Ko School iyayen ta na
Kallon ta, Wai Mace ta Saka Tufafi Duk Inda ta Wuce Ana Kallon ta, Wai Shine ɗaiɗai Kuma Ke Uwa
Kina Ganin ta Ko Faɗa ba Za kiyi
Mata ba, Kai Uba Kana Ganin ta ko Sannu ba Za ka yi mata ba ai kanta ya waye,
ga Samari Matasa Suna Zuba mata ido kamar Su Haɗiye ta, ita ba ta San Suna Biyayyar ta ba, Za Su iya Kai
Shekara Guda Suna Tsara Wurin da Za Su Yi Attacking Ɗin ta, Ke Kina Ganin Kamar idan ta yi Hakan
Burgewa Ce, Domin kai Ya Waye Yaya Zata Rika Sanya Tufafin irin na Mutanen da
Yan kauye, Kina Jawo ma Kanki Hatsari ne Ke ba Ki Sani ba, Hatta Hijabi a Yau,
wallahi Wasu Hijaban Sun Zamo Na Rashin Mutunci, Ba Su tsare Musu Jikin Su da
Komai Nasu ba, Don Allah a Matsayin ki Na Uwa Ɗiyar Ki da ta ke Yin Irin Wannan Fitar Yaya Za ki
Ce Wai Kada a yi fyaɗe da ita? Shin
Laifin ta ne idan An yi fyaɗe da ita Ko Naki
Ko na Wanda Yayi mata? Kenan da Taimakon iyaye ne ya sa ake yi Musu fyaɗen. Wallahi iyaye Ku tashi Ku Gyara. Sannan Galiban Waɗanda ake yiwa fyaɗen Suna Samin
Heart Attack, Bayan Lokacin Sai Ace ta Mutu da Bugun Zuciya Duk Wannan Laifin
Ku ne Iyaye Mata da Maza.
5. Na Karshe, Hand Shaking, Musafaha da Maza, Zama
Kusa da Maza, Jikin ta yana Taɓa Jikin Namiji,
Ko a Class ko a Kasuwa ko a Wurin Yin Zance duk waɗannan abubuwan a wannan zamanin ba komai bane a gurin
Mace Budurwa Kuma Musulma, Saurayi zai zo zance gurin ta damuwar sa kullum idan
ya zo taɓa duk inda yake so a jikin ta da kiss nata domin ai hakan
shi ne soyayya me kyau in ji sa kin sake jikin ki, ba Tare da Ke Kin tsaya kin
ba ta Tarbiyyan da ba zata iya Aikata Waɗannan Abubuwan
ba koda ta yi Sabbin Qawaye ne ko Saurayi. Shin Don Allah Laifin ku ne Iyaye
Mata da Maza Ko Kuma Laifin ta ne Budurwa Ko Karamar Yarinyar? Domin Wata
Karamar Yarinyar ma daga Ita Sai Pants babu Riga Babu Komai a Jikin ta, Me Kike
Nufi da Hakan toh??
Don Haka Duk Yadda Za a yi, Ki tashi ki Ba wa Ɗiyar Ki Tarbiyya Ki Ce
mata Kar Ki Yarda Ace Yau Jikin ta Yana Taɓa Jikin Namiji ko a Wajen Zance ne Ko a Cikin Class ko
Yin Musafaha kada ta Taɓa nashi, shima
kada ya Taɓa nata idan ma Zai Taɓa ta, toh ta yi Gaggawan Rabuwa da shi Sannan take Sanya
Suturar da Addinin ku ya Yarda da shi take tafiya da Muharramin ta duk inda za
ta je Domin ba ta Kariya, Shine na Farko idan Za a Miki zai Ba ki Kariya daga
fyaɗe ko Zina amma an bar na ce Budurwa ko ina tana iya zuwa
ita kaɗai ta yaya ba a yi Zina ba?. Allah ya Tsare ya Kare
Ameen.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.