WACCE ADDU'A ZAN YI ABIN DA ZAN HAIFA ƊAN YA ZAMA NAGARI?
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam alaikum yan'uwana musulmi Dan Allah inada tambaya ne karku shareni Dan Allah Na kasance ina da ciki ne, kuma ina so abunda Zan Haifa ya kasance nagari Kuma Wanda yakeda ilimin addini ina so ya kasance me tarbiya da tsoron Allah meya kamata na rikayi kafin na haihu saboda yanzu inada ciki wata biyu. Dan Girman Allah Karku Shareni
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumusalam warahmatallahi wabarakatuh.
Allah Ya Baki Lafiya Dake Da Abin da Yake Cikinki.
Sababin Farko Shine Kisamu Keda Megidanki Duk Abin da Zakici Ko Sha Ya Baki
Halak, Shiyasa Akeso Mace Tagari A Kullin Ko a Sati Sau 2 Tana Tinatarda
Mijinta Yaji Tsoron Allah A Wajen Nemansa, Hakan Ba Karamin Tasiri Yake A
Zuciyar Namiji ba, Wannan Shine Babban Abu Daza Kiwa Kanki Domin Ittifaqan Duk
Mutumin Da aka Gina Jikinsa Da Haram Baya Albarka, Saboda Faɗin Ma'aikin Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Mutumin Da
Abincinsa Haram Ruwan Shansa Haram Tufafinsa Haram Yakoshi (Yagirma Da Haram)
Tayaya Zaiyi Addu'a Ta Karɓu? (Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallam) neYa Fadi Haka, Dan Haka Saimu Kula Kwarai, Sannan
Kofar Tuba Kullin Buɗe Take.
Da Hakane Malamai Suke Ganin Cewa Basai Mutum Ya
Fito Duniya ba Za a Fara Masa Tarbiya Tin Yana Cikima Za a yi Masa, Haɗe da Kiyaye Addu'o'i Kafin Fara Saduwa.
Sannan Kema Kiyi Kokari Ki Kusanci Allah Sosai, Ki
Hakura Kirage Jin Kade-Kade Da Waqe-waqe, Ki yawaita Ibada, Karatun Alkur'ani,
Sallah, Zikirai Da Sauransu, Kina Addu'a, Akan Allah Ya Raya Miki Abin Cikinki
Yayi Masa Albarka, Yabaki Lafiya Ki Haifeshi Kalau.
Ranar Da aka Haifeshi Malamai Masana Dubbun Nabawi
Sukace A Samu Dabino Irin Ajwad, Sai A Tauna A Samu A Fara Bashi Yawun Ruwan
Dabinon Nan Yashiga Cikinsa Koda Kaɗan ne, In sha
Allah, Allah Zai Bashi Fahimta Da Kaifin Basira. Bayan Wannan Bayani Ba Wata
Kebantacciyar Addu'a Da aka Rawaito, Babban Abu Shine Idan Kin Gyara Tsakaninki
Da Allah To Tabbas Addu'arki Ga Ɗanki Kowace Iri Kikayi Masa Da Kowane Yare To Batada Hijabi Wurin Allah.
Allah Ya Baki Lafiya Dakeda Abin da Ke Cikinki. Allah yasa ki sauka lafiya.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Fadakarwa, Ilimantarwa da tunatarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.