Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta’addanci Da Rayuwar Bahaushe: Gargadi Daga Wakar Diyan Jemage Ta Mamman Shata Katsina

Citation: Nalado, N., Rabe, H. and  Hassan, S. (2024). Ta’addanci Da Rayuwar Bahaushe: Gargaɗi Daga Waƙar Ɗiyan Jemage ta Mamman Shata Katsina. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 440-447. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.055.

TA’ADDANCI DA RAYUWAR BAHAUSHE: GARGAƊI DAGA WAƘAR ƊIYAN JEMAGE TA MAMMAN SHATA KATSINA

Nuhu Nalado

Hassan Rabe

Sani Hassan

Sashen Nazarin Harshen Hausa, Tsangayar Nazarin Ilimin Sakandare, Ɓangaren Harsuna, Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita

Tsakure:

Aikin ya himimmantu ne wajen nazarin gudummawar waƙar baka ta Dr. Mamman Shata Katsina ɗauke da taken ‘Ta’addanci A Rayuwar Bahaushe: Gargaɗi daga“Waƙar Ɗiyan Jemage”Ta Mamman Shata Katsina. Manufar aikin ita ce nazartar Jigon Gargaɗi dake a cikin waƙar. Aikin bincike ne na bayani a ɓangaren ayyukan Adabin Hausawa a gurbin waƙar Baka. Haka kuma aikin ya gudana ne ta hanyar nazartarwasu ayyukan masana da manazarta a wannan fanni.Tare da sauraron waƙar ta yin amfani da Na’urar wayar Salula, a inda aka yi amfani da abubuwan da aka saurara daga waƙar aka rubuta su domin samun damar yin Nazari. Duk dai a wannan gaɓa, an ɗora Binciken a bisa ra’in Bincike na Mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya. Daga bisani, nazarin ya gano tare da tabbatar da cewa waƙoƙin baka na Hausa wani babban kamdami ne na ilimi da ke taimakawa wajen tafiyar da rayuwar al’umma a halin da ake ciki da kuma maizuwa. Haka kuma, waƙar na ɗauke da wannan jigo na gargaɗia kan illar gudanar da ayyukan ta’addanci a rayuwar Bahaushe.

Fitilun Kalmomi: Ta’addanci, Rayuwar Bahaushe, Gargaɗi, Waƙar Baka, Mamman Shata Katsina

Gabatarwa

Waƙar baka, wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da daidaituwa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da amshi (Gusau, 2023:ɗiɓ). Haka kuma, dangane da siga da zubi da tsarin aiwatarwa, Bahaushiyar waƙar baka ba ta zuwa a shimfiɗe ko ta zo gaba ɗaya, a’a, tana zuwa ne gutsure-gutsure tare da maimaita gindinta a tsakaninsu. Gutsure shi ne ‘ɗa’. A waƙar baka ba a ƙayyade yawan layuka a ɗan waƙa, musamman ga makaɗan da suke cikin ƙungiya, suna maimaita gindin waƙa a ƙarshen kowane ɗan waƙa.

Samun asalin yadda aka fara waƙar baka a kowace al’umma yana da wuya da kuma neman bincike mai zurfi. Akwai saɓanin ra’ayoyi game da asalin waƙar baka a rayuwar Hausawa. Ana jin Ɗan’adam ya ƙagi waƙa ne tun lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar ‘farauta’. Daga bisani da mutane suka sami fasahar noma sai waƙa ta ƙara haɓaka. Wasu kuma na ganin hanyar bauta ta gargajiya ta daɗa bayar da haske wajen kyautata sha’anin waƙa (Gusau, 2023:7).

Daga cikin ra’ayoyin da ake bayarwa dangane da asalin waƙa a ƙasar Hausa, akwai inda ake ganin waƙa ta samo tushe ne daga wajen wani maroƙi ‘Sasana’. Domin haka , a wannan ra’ayi ana jin makaɗan Hausa jikokin wannan mutum ne da ake kira Sasana wanda ya rayu a ɓangaren Asiya. Daga baya wasu daga cikin ‘ya’yansa suka yiwo ƙaura zuwa ƙasashen Hausa. Kalmar ‘Sasana’ tana nufin ‘maroƙi’ da harshen Faransanci (Gusau, 2023:7). Duk dai a wannan gaɓa masanin ya habarto Sasana a matsayin maroƙi na farko da aka yi tun a lokacin Jahiliyyar duniya. Ta fuskar maroƙan na harshen Hausa kuwa ba a barsu a bayaba ta wannan fuska. Kasancewar nazarin ya habarto Bature maroƙin Dr. Mamman Shata na danganta uban kiɗinsa da cewa:

Duna na Bilkin Sambo;

Kafiri ƙanen Sasana.

Mai tada ta aljannu da mutane” (Gusau, 2023:8 da Nalado, 2019: 2).

Ko shakka babu,wannan nazari na ganin waƙa a matsayin wani tsararren zance ne na hikima, wanda kan kasance a tsare kuma a shirye da ke zuwaa lafazance.Da kan gudana da taimakon wasu mutane  ko ƙugiya a sigar amshi ko kiɗa a wani keɓantaccen lokaci domin cimma wata manufa da aka gina waƙar a kai.

Manufar aikin ya taƙaita ne ga nazarin ilimantarwa a cikin sigar gargaɗida ke a cikin wannan waƙa ta Dr. Mamman shata mai taken:‘Ɗiyan Jemage’,da ya gabatar akan wani mutum a lokacin rayyuwarsa. Akanillar ayyukan ta’addanci a rayuwar Hausawa.

 Waƙar an yi ta ne a shekarar ‘1969’ a matsayin kashin farko na samuwar waƙar. Mutuen da aka yi wa waƙar kuwa shi ne Mati ɗan ‘Yarbanye da ke a garin ‘Yamma,Ƙaramar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina,Tarayyar Najeriya. Waƙar ta gudana a cikin sigar yabo da salon kambamawa.

Yana daga cikin muhimmancin wannan bincike na ƙara samun bunƙasa nau’oin saƙonnin da waƙa ke ɗauke su da kuma ciyar da fagen bincike a wannan fanni gaba. Duk a cikin wannan gaɓa za a kawo jerin wasu muhimman kalmomi da suka shafi binciken tare da bayanansu a taƙaice. Domin ƙara samar da fahimta a lamarin. Haka kuma,an kawo ratayen waƙar da nazarin ya ginu akai a ƙarshen Manazarta.

Muhimman Kalmomi: Ta’addanci darayuwar Bahaushe da gargaɗi da ɗiyan jemage dauwa da mugu da kalmar kunya.

Ta’addanci: Sa’id (2006:416), ya bayyana cewa kalmar na nufin ɓarna ta ganganci da ta shafi aikata mugun aiki a tsakanin al’umma. Shi kuwa Nalado (2015:3), bayyana ma’anar ta’addanci da cewar wasu munanan ɗabi’u ne da suka zamanto daga cikin baƙin al’adun Hausawa ko kuma mummunar tada da ta shafi aikata wasu al’amurra na rashin sanin ya kamata da ke salwantar da dukiya da rayukan al’umma a rayuwar yau da kullum. A ɓangare ɗaya, Maƙalarna ganin tsari ne na aikata rashin daidai a zamantakewar al’umma da ya shafi duk wani nau’in sata da aikata miyagun laifuka a tsakanin al’umma. Kamar yadda ya faru a tsarin ɗiyan waƙar da nazarin ya ginu akai.

Rayuwar Bahaushe: Tsarin rayuwace managarciya da ke gudana a wasu muhimman turaku ko sigogi guda goma sha huɗu da suka shafigurbin hankali da gurbin wayo da gurbin gaskiya da kunya da kamun-kai da nuna halin kirki da son zumunci da taimakon juna da ƙoƙarin haɗiye kwaɗayi da guje wa nuna son kai. Sauran sun haɗa da mora wa kai da kishin ƙasa da mutanenta da sadaukar da kai da kuma hangen nesa a kan lamurran rayuwa Bunza (2013: 2). A nasa ɓangaren, Sallau (2000:27). Ya furta cewa, “Bahaushe mutum ne da Allah Subhanahu Wata’ala ya kimtsawa tunaninsa a turba ko bagiren gudanar da rayuwa a bayan ƙasa. Da yake rayuwarsa a farfajiyar ƙasar Hausa gabanin wannan zamani.” Duba da waɗancan ma’anoni na masana, aikin na ganin rayuwar Bahaushe wata rayuwace da ake gudanarwa a bisa tsari da kiyaye haƙƙoƙin al’umma. Tayadda akasin hakan ba ya daga cikin ayyukan al’adunsa.

Gargaɗi: Kalmar na nufin jan kunne ko yin kashedi ko horo Sa’id (2006:156). Duba da wannan ma’ana, nazarin ke ganin kalmar a matsayin al’amari ne da ya shafi nusar da mutum ko wasu mutane a game da illar aikata wani aiki. Ko ƙoƙarin nisantar da al’umma ne ga dakatar dasu a wajen aikata wani abu da ake ganin yana da matsala a rayuwa.

Onle: Kalmar na nufin ɓarawo da harshen Yarabanci.

Enyusi: Na nufin ɓarawo da harshen Inyamuranci.

 (Ɗan baiti na biyar a waƙar ɗiyanjemage ta Mamman Shata).

Mugu: Bunza (2014:iɗ) da Said (2006:348). Sun yi tarayya a wajen ayyana kalmar a matsayin ɓarawo. Binciken na ganin ma’anar ta shafi duk wani mutum mai mummunan hali da yake cutar da al’umma.

Ɗiyan jemage: Sa’id (2006:156). Ya nuna cewa kalmarna nufin “Ɗanjaura, ma’ana mutumin da yake yawo kasuwa-kasuwa yana baza tarkacensa domin sayarwa”. Tayadda binciken yake ganin ɗan waƙar na uku na a matsayin jigon gargaɗi ga mutane. A inda aka danganta halayyar tauraron da ta Ɗanjaura.

Kunya: Bunza (2006:249).Ya bayyana kunya da cewar, “Wata magana ce ko wani aiki da ya saɓa wa tsarin kamun kai na al’ada, kuma al’ada ta zarge shi da muni na zubar da girma da mutunci”. Binciken na ganin al’amari ne da yake tattare da damuwa da samar da ɓacin rai ga mutum ko danginsa a tsarin zamantakewar Bahaushe,wanda kan haifar da zubewar ƙima da mutunci acikin al’umma.

2.0 Tarihin Mawaƙi a Taƙaice

Mamman Shata na ɗaya daga cikin al’ummar Hausawa mazauna ƙasar Hausa, wanda aka haifa a garin Musawa, a gidan wani mutum da ake kira da suna Ibrahim Yaro. Mahaifiyarsa ta kasance Bafillata mutuniyar Tofa ta ƙasar Kano mai suna Lariya. Mahaifinsa mutum ne mai nasaba da mutanen Sanyinna da ke a ƙasar Sakkwato. A na hasashen haihuwarsa a shekarar ‘1922’. Ya kuma rasu a ranar Juma’a ‘8/06/1999 ‘ a wani asibiti da ke Kano. An kuma rufe shi a garin Daura a ƙarƙashin jagorancin ubangidansa tsohon Sarkin Daura, watau Sarki Muhammadu Bashar. Mawaƙin ya rayu da mata huɗu na aure a garin Funtuwa. Yana da ‘ya’ya da dama. Daga cikinsu akwai Lawal da Sanusi waɗanda ke ƙoƙarin aiwatar da waƙa bayan rasuwar mawaƙin. A lokacin rayuwarsa ya yi fice a sana’arsa ta kiɗa da waƙa a duk faɗin ƙasar Hausawa (Nalado da wasu, 2018:3). 

 3.0  Bitar Ayyukan da Suka Gabata

Masana da manazarta a mabambanta lokutta sun tofa albarlacin bakunansu a game da wannan maudu’i na waƙar bakar Bahaushiya. A fannonin daban daban. Gusau, (2008: 1-150) da Gusau(2023:1-119).Ya nazarci waƙar baka a duniyar adabin Hausawa ta fuskar yanaye yanayenta da hanyoyi ko matakan da za a yi amfani da su a matsayin jagora ta fuskar gudanar da nazarin waƙa Bahaushiya. A inda ya yi bitar ma’ana da asalin samuwar waƙar baka ga Bahaushe da muhimmancin waƙoƙin tare da nau’oinsu. A wata mai kama da wannan, Nalado da wasu, (2018:1-14) da Nalado(2019:1-12 da Rabeh, (2010: 1-12). Sun yi tarayya wajen nazartar muhimmancin waƙar baka Bahaushiya wajen ilimantarwa a tsakanin al’umma a fannoni daban daban.

4.0 Hanyar Gudanar Da Bincike

Duba da cewa bincike ne na nazari da ya shafi bayyanawa a turbar ilimantarwa. Tsarin ya gudana ne ta fuskar bitar wasu ayyukan masana da manazarta a ɓangaren littafai da muƙalu da kundayen bincike. Lamarin bai wanzu ba face sai da aka yi nazarin waƙar da ta jagoranci aikin ta hanyar sauraro. Tayadda daga bisani aka rubata baitukan da nazarin ya shafa.

4.1. Ra’in Bincike

An ɗora aikin a bisa Ra’in Mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya. Ra’ai ne da ya wanzu a shekarun ‘1993’, a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau.

Manufar ra’in ya shafi bayyana tarihi da asali da salsalar waƙar baka ta Hausa. Da kuma zurfafa bayani a kan turke da abubuwan da waƙa ta ƙunsa. Ita wannan mazhaba ta tarken waƙar baka Bahaushiya ta jinginu da wasu ra’oi na wasu Mazhabobin ra’i da suka haɗa da Mazhabar Gargajiya. Ayyukan da aka samu nada suka yi amfani da wannanMazhaba suna da yawa. Kaɗan daga cikinsu akwai aikin Garba, 1998 da Satatima, 2008 da Abubakar 2011 Gusau, (2023:23). Dangantakar Ra’in da aikin da ake gudanarwa shi ne, aikin ya ginu ne a kan nazarin gudummuwar waƙar baka ta Dr. Mamman Shata Katsinaa gurfin Ilimantarwa ta fuskar illar ayyukan ta’addanci a tsakanin al’umma. Shi kuma ra’in yana magana ne a kan nazarin waƙar baka Bahaushiya. Duba da wannan dalili ne aka zaɓi ɗora aikin a bisa wannan ra’in bincike.

5.0 Waƙar Ɗiyan Jemage ta Dr. Alhaji Mamman Shata Katsina

Waƙar na daga cikin rukunin waƙoƙin Dr. Mamman Shata na biyu da ta kasance daga shekarun alif ɗari tara da sitti zuwa alif ɗari tara da tamanin (1960-1980) Nalado, (2018: 10). An fara aiwatar da waƙar a garin Funtuwa a shekarar 1969. Wanda aka yi wa waƙar wani mutumen garin ‘Yammama ne kamar yadda bayani ya gabata. Jigon waƙar ya shafi bayani a kan illar da ke tare da gudanar da ayyukan ta’addanci a cikin al’umma domin kada a yi, sannan a yi hattara da masu yi.

Waƙar na ɗauke da salon aiwatarwa mai armashi da kuma kambamawa da ta zarta tunanin mai tunani (Kambamar zulaƙi). Wani abin sha’awa a game da waƙar shi ne, an kawo wasu ɗiyan waƙa da suke yin nusarwa ga al’umma, dangane da yadda ɓarayi ke tafiyar da al’amurransu a yayin da suka yi sata. Musamman ta fuskar yin satar da sigar satar da kuma bin sawu. Nazarin ya fahimci waƙar ta halarto da wasu ayyuka da tadoji na ta’addanci da ke faruwa a wannan lokaci. Duk da cewar a lokacin da aka yi waƙar ba bu wannan matsala a cikin rayuwar al’ummar, kamar yadda take faruwa a yau. Ko ba komai a iya yin itifaƙin cewa ayyukan adabin harshen Hausa a fagen waƙar baka muhimmin ɓangare ne da ya ƙunshi hasashe da hangen nesa. Kamar yadda ya faru a wannan gaɓa da aka samu tsawon shekaru hamsin da huɗu. A tsakanin wanzuwar waƙar da faruwar ayyukan ƙunshiyar waƙar a rayuwa ta zahiri. Kasancewar a yau al’ummar Arewacin ƙasar nan na fama da matsalolin da suka shafi tsaro da ta’addanci da ya samo asali daga waccan satar shanu da dabbobi na Makiyaya,(Nalado, 2019:10).

5.1  Dangantakar Waƙar Ɗiyan Jemage da Ayyukan Ta’addanci

Maƙalar na ganin ta’addanci a matsayin wani al’amari da ya shafi aikata rashin daidai a zamantakewar al’umma, wanda ya haɗa da dukkan wani nau’in sata da aikata miyagun laifuka a tsakanin al’umma. Duba da hakan, an yi tsokacin dangantakar waƙar da ayyukan na ta’addanci a matakai guda huɗu.

5.1.1 Bayyana Suna da Tadar Masu Aikata Ta’addanci

Tada wasu ayyukan al’ada ne da suka shafi gudanarwa da sassan jiki da kuma wadda ta shafi ƙudurtawa a zuciya a fagen wasu ayyuka,(Bunza, 2006:75). Waƙar ta halarto da sunan da ake kiran mutumin da ke aikata wannan laifi a cikin harsuna da ke da maƙwabtaka da harshen Hausa a ƙoƙarin wayar da kan al’umma. Hakan ya bayyana ne a ɗiyan waƙa na ɗaya da na biyu da ɗanwaƙa na takwas da na tara. Ga abin da Mamman Shata ya faɗa,

Jagora: Na Abdu Ɗanjemage a gaba ake goyonka ɗan-ɗan Mani.

Jagora: Gata mai ɓarna baban ‘Yarbanye.

Jagora: Tafiyata Kurmi ga ɗiyan Yarabawa.

 Na ji sun ce Ole.

 Na biyo ‘Yan Hausa, Mamman suna kiran ka ɓarawo.

 Inyamurai kau sun ce ma Anyusi.

Jagora: Wai duk ɓarawon ne ke nan ‘yan Hausa.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa’.

Ɗiyan waƙar sun halarto da Tadar masu aikata wannan nau’in aiki ta amfani da Tauraronsa. In da aka bayyana su da cewar mutane ne maɓarnata da ke buƙatar a rinƙa kulawa ta hanyar lura da al’amurransu domin kar su sami damar cutar da al’umma. Lamarin bai tsaya a nan ba, face sai da aka kawo sunan da ake kiran mutumin da abun ya shafa acikin yaren wasu daga cikin al’ummomi masu maƙwabtaka da Hausawa domin ƙara faɗakarwa da gargaɗi ga al’umma.

5.1.2  Faɗakarwa a Game da Tsarin Gudanar da Aikin Ta’addanci

Muƙalar ta fahimci hakan ya faru ne a cikinɗiyan waƙa na uku da na huɗu da kuma na biyar daidai inda Mamman Shata ya ce:

Jagora: A faɗa wa Mamman, matuƙar ka ɗauko sa’a.

 Sa’ar tai sa’a.

 Idan ka je gun ƙofa, har in ka buɗe ƙofa.

 Mamman in ka shiga ɗakin, harka iske kaya.

 To zari akwatin tsakiya shi ya fi kaya.

Jagora: In dai ka buɗe ɗakin ka ishe shi a shirye.

 To zari akwatin tsakiya shi ya fi kaya.

Jagora:  Nasaman hoto ne.

 Na ƙasa maganin ƙwari ne.

 Zo zari akwatin tsakiya shi ya fi kaya.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Duba da waɗannan ɗiyan waƙa, ya nuna cewar waƙar na faɗakar da al’umma a game da tsarin yadda masu aikata wannan mummunan hali suke bi wajen gudanar da aikinsu. Duba da yadda suke neman sa’a daga ayyukan addininsu da kuma yadda suke amfani da tunani a wajen ɗaukar kayan da za su sata. Hakan wata dama ce da za ta faɗakar da al’umma a game da wannan matsala domin su kiyaye kuma su sake tsarin ajiye dukiyarsu daga fasalin sa ta a cikin akwatin tsakiya.

5.1.3  Hoton Ayyukan Ta’addanci a Harshen Waƙa

A wannan gaɓa mawaƙin ya yi amfani da hikimarsa inda ya habarto wannan jigo a cikin jerin ɗiyan waƙa naGoma har zuwa ɗanwaƙa na Goma Sha Biyar. Ga yadda abin ya kasance:

Jagora: Ka ga yana yankan Aljihu birni’

Jagora: Na Audu ya ɓalle ƙofa in ambarci.

Jagora: Ba yash shiga banki baƙon Ɗammani.

Jagora: In ya shiga daji ya ishe Hillani,

 Mamman Na Audu kore dut baƙon Ɗammani.

Jagora: Ka kore dut baƙon Ɗammani ko jaki kore Ɗanshata.

Jagora: Bari bar masu ko jaki kore Ɗanshata.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa’.

Waɗannan ɗiyan waƙa da suka gabata na a matsayin dangantakar waƙar da ayyukan ta’addanci. Kasantuwar waƙar ta fito da hoton nau’ukan ayyukan ta’addanci a bayyane domin a kula a kuma kiyaye aikatasu. Sannan mawaƙin yana nuna wa al’ummace irin yadda waɗannan miyagun mutane suke korewa tare da kwashe dukiya da kuma dabbobin al’umma.

5.1.4 Dabarun ‘Yanta’adda a Ayyukan Ta’addanci

Har ila yau, wannan mawaƙi a waƙar tasa ya nuna wasu daga cikin dabarun da ‘yanta’adda suke amfani da su wajen ɓatar da kayan da suka sata. Don a wannan gaɓa muƙalar ta habarto Mamman Shata a ɗanwaƙa na goma sha shida zuwa na ashirin da biyar yana cewa:

Jagora:In ya kori bisashe, sawu sun Yamma.

 Shi Gabas baƙon Ɗammani.

Jagora: Yi Gwambe da su baƙon ‘Yarbanye.

Jagora:Ko ko ka yi Bauci da su baƙon Ɗammani.

Jagora: Ko ko ka yi Barno da su baban ‘Yammani.

Jagora: Ko ka tsallake Kamaru Baƙan ‘Yarbanye.

Jagora: Ko ka laɓe Baga baƙon Ɗammani.

Jagora: A nan babu mai zuwa cigiya domin shanunai.

Jagora: A nan wani daji!

 Nan babu mai zuwa cigiya domin shanunai!

Jagora: A nan ba bu mai zuwa cigiya domin shanunai!

Jagora: Da ka tahi Baga.

 Ko ko ka tahi Barno!

In ka laɓe wani daji, anan babu mai zuwa cigiya domin shanunai.

Jagora: Wa za ya gane Mamman ɗan-ɗan Mani?

Jagora: Yi hannun riga tafi ɗauki abin ɗauka baƙon Ɗammani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa’.

Waɗannan ɗiyan waƙa sun ƙara tabbatar da cewar akwai dangantaka a tsakanin waƙar da nazarin ya ginu a kai da ayyukan ta’addanci. Ganin cewa halayar da ke faruwa a halin yanzu a cikin wannan al’umma ke nan. A inda za a aikata wani ta’addanci a Katsina sai a tsinci mutumin da aka yi garkuwa da shi a Zamfara ko dajin Kaduna ko na neja ko ma Sakkwato. A game da abin da ya shafi satar bisashe kuwa, ba wani bambanci da bayanan da waƙar ta zo da su.

5.2.  Gargaɗi a kan Illar Ayyukan Ta’addanci

Sani, (2017:10). Ya bayyana ta’addanci da cewar “Al’amari ne na aikata ba daidaiba a tsakanin al’umma. Mai nasaba da sata da cutarwa, da ƙoƙarin salwantar da rayuka da dukiyoyin al’umma”. A wannan nazari, ana kallonta’addantanci da cewa al’amari ne da ya shafi aiwatar da rashin daidai da saɓawa managartan al’adun zamantakewa a tsakanin al’umma. A waƙar Makaɗa Dr. Mamman Shata bai yi ƙasa a guiwa ba wajen bijiro da wannan jigo a wasu jagororin ɗiyan waƙarsa kamar haka:

Jagora: A faɗa maka Mamman.

 Na kau hore ka!

 Duk wanda bai ajiye ba.

 Idan ya ce zai ɗauka!

 Mamman ka tabbatar kau kunya sai ta kammai.

 

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

(Mamman Shata: Waƙar Ɗiyan-jemage).

A cikin Sa’id, (2006:255),an bayyana kalmarkunya na nufin nuna kawaici da jin nauyi da rusunawa saboda wata dangantaka a rayuwa. A gefe guda makaɗa Dr. Mamman Shata ya yi amfani da wannan mizani na tantance Bahaushe a adabinsa domin samun cimma wata manufarsa kamar haka:

Jagora: Haka niggan shi ba kunya,

 Yac ce da rabo a tsakanin ‘yar nan.

 Da mijinta na can baya.

(Mamman Shata: Waƙar Alƙali Maɗanɗani).

A wata faɗar jaddadawa Makaɗa Mamman Shata ya ƙara cewa,

Jagora: Baya sarkin rashin kunya.

 Su kare ba a san harara ba

 Mai gidan shi ya ce abokinai.

(Mamman Shata: W.aƙar Bala Gaye Balan Barde).

Duba da Ɗiyan waƙarda suka gabata, binciken ya yi itifaƙin cewa kunya a rayuwar Bahaushe aba ce mai matuƙar muhimmanci. Ganin yadda addinin Musulunci har ma rayuwar maguzanci suka jaddada amfaninta. A rayuwar Bahaushe a ce wa mutum ba ya da kunya tamkar zagi ne. Wasu waƙoƙin Mamman shata sun samu daidaito a wannan gaɓa.

Bunza (2013:8), ya kawo wasu matakai guda goma sha huɗu da suka kasance mizanin da Bahaushe yake amfani da su wajen tantance sahihanci ko nagartar kowane ɗan ƙabilarsa.  Ya ƙara da cewa rasa ɗaya daga cikin waɗannan sifffofi a tsarin zamantakewa da tarbiyyar al’ummar na iya canza matsayi a falsafar mutuntakar Bahaushe. A inda wannan nazari ke tabbabatar da cewa,nuna halin kunya da nisanta daga duk wani aiki da zai sajin kunya na a matsayin muhimmin al’amari ga rayuwar Bahaushe.

A tsarin rayuwar Gargajiyar Bahaushe, yin abin kunya nasa mutum ya bar garinsu ko karkararsu har abada. Maƙalarna ganin wannan dalili ne ya taimaka wa mawaƙin ya cimma manufa ko saƙon da yake ƙoƙarin isarwa ga al’umma ta wannan fuska. Samuwar hakan ya kasance hanyar da mawaƙin ya yi amfani da ita wajen gargaɗi ga al’ummar a kan wannan mas’ala cikin salo mai armashi.  

6.0  Shawarwari

Al’amarin waƙar baka Bahauhiya, abu ne mai girma da faɗi a fagen koyar da darussa masu alfanu ga rayuwar al’umma. Lamarin bai keɓanta ga iyakacin al’ummar Hausawa kaɗai ba, face sai da ya shafi kowace irin al’umma da take rayuwa a doron ƙasa. Matuƙar dai za ta fahimci ƙunshiyar saƙoni ko darussan da waƙoƙin suke ɗauke da su. Ganin an iya fahimtar cewa wasu waƙoƙin na halarto da hasashen ayyukan rayuwa wadda za ta faru a sakamakon aiwatar da waɗansu ayyuka da suka saɓa wa al’adu managarta na tsarin zamantakewar al’umma.

Hakan ne yasa Muƙalar ke kira tare da bayar da shawara musammam ga matasan Hausawa da basu da sha’awa ko ɗabi’ar nazari da kuma sauraron waƙoƙin Gargajiya. Da su lazimci amfani da su domin suna ɗauke da muhimman darussa a fagen rayuwa.

7.0 Kammalawa

Waƙar baka daɗaɗɗiya ce wadda aka fara ta tun lokaci mai nisa da ya shuɗe.  A inda ta ci gaba da bunƙasa har zuwa yau. Nazarin ya fahimci cewa waƙar baka Bahaushiya na gudana ne ta amfani da wasu matakai wato a yayin aiwatarwa da suka haɗa da Jagora da ‘Yan amshi da kiɗa da mabanci tare da sarrafa hikima da amfani da fasaha da murya da rerawa a yayin aiwatarwa. Haka kuma, wannan nazari ya gano cewa waƙoƙin baka na Hausa wani babban kamdami ne na ilimi da suke taimakawa a wajen tafiyar da rayuwar al’umma a halin da ake ciki da kuma hali ko yanayi maizuwa.

Kamar yadda sauran al’ummomin da suke rayuwa a doron ƙasa suke fama da miyagun ayyuka daga wasu ɓaragurbi a cikinsu, wannan al’umma ta Hausawa ba a barta a bayaba ta wannan fuska.A inda suke aiwatar da mabambanta ayyukan ta’addanci a tsakanin al’umma. Hakan ya samo asali da bunƙasa a sanadiyar cakuɗuwa da baƙin al’adun al’umma daban-daban. Musamman ta sanannen tsarinnan na Game-duniya (Globlisation).

Waccan matsala ta cakuɗuwa da baƙin al’adun al’ummu ta kasance babban dalilin faruwar matsalolin ayyukan ta’addanci da al’ummar Arewacin ƙasar nan ke fama da shi a yau.Waɗandasuka haɗa da satar dukiya da dabbobi da garkuwa da mutane da ma ayyukan kisan kan mai-uwa-da-wabi a tsakanin al’umma. Wanda ke ci gaba da haifar da matsaloli a rayuwar Hausawa da sauran al’ummomin cikin ƙasa.

Duba da haka ne ake ganin waƙar Mamman Shata Katsina ta zama cibiyar gargaɗi da hana mutane ko jawo hankalinsu a game da barin aikata ayyukan ta’addanci a tsakanin al’umma da kuma sa mutane su yi hattara ko hankali da aikata hakan.

Manazarta

Bunza, A. M. (2013). “Hutawa ka Alewa, Mangyaɗa ka Tuyar Ƙosai: Barazanar Yanayi da Lokaci a kan Al’adun Hausawa”. Takardar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna sani na Ƙasa da Ƙasa a kan Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa, Katsina: Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua.

Bunza (2014). In Ba Kasan Gari ba Saurari Daka: Muryar Nazari A Tafashen Muhammadu Gambo. Kano: Darul Ummati Publishers.

 Bunza, A .M. (2006), Gadon Feɗe Al’ada. Jerin Littattafan Cibiyar Nazarin Al’adun Hausa. Lagos: Tiwal. Nigeria Limited.

Ɗagoro, A. S. (2017). “Nazarin Tsaro na Gargajiya na Jihar Katsina Jiya Da Yau”. Kundin Digiri na Biyu. Katsina: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua. 

Gusau, S. M. (2008). “Tarihi da Hanyar Nazarin Waƙar Baka Bahaushiya a Taƙaice”. A cikin Waƙoƙin Baka Na Hausa.  Katsina: Department of Hausa, Federal College of Education.

Gusau, S. M. (2023).  Mazhabobin Ra’i da Tarke A Adabi da Al’adu na Hausawa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Gusau, S. M. (2023). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: WT Press, Printing and Publition.

Nalado, N. (2019). “Shata Mawaƙi ko Ɗansiyasa”. Muƙalar da aka Gabatar a Taron Ƙasa da Ƙasa a kan Mamman Shata Katsina, Kano: Center for Nigerian Languages, Bayero University.

Nalado, N, Da wasu. (2018). “Shata A Fagen Wa’azi: Waiwaye a kan Wasu Daga Cikin Waƙoƙinsa. Muƙalar da aka Gabatara a Taron Ƙasa da Ƙasa a kan Mamman Shata Katsina. Kano: Center for Nigerian Languages, Bayero University.

Nalado, N. Da wasu. (2015). “Muguwar Makaranta Maituƙa da Warwara:Barazanar Ayyukan Ta’addanci a Falsafar Gambo”. Muƙalar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna sani, Dutsinma: IKCOE.

Sa’id, B. (2006). Ƙamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.

Sallau, B. A (2000). “Wanzanci: Matsayinsa Na Al’ada da Sana’a A Ƙasar Hausa”.Kundin Digiri na Biyu. Kano: Jami’ar Bayero.

RATAYE

 

Waƙar Ɗiyan Jemage ta Dr. Mamman Shata Katsina

 

Jagora: Na Abdu ɗanjemage a gaba ake goyonka Ɗanɗan Mani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Gata mai ɓarna baban ‘Yarbanye.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: A faɗa wa Mamman, matuƙar ka ɗauko sa’a.

 Sa’ar tai sa’a.

 Idan ka je gun ƙofa, har in ka buɗe ƙofa.

 Mamman in ka shiga ɗakin, harka iske kaya.

  To zari akwatin tsakiya shi ya fi kaya.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: In dai ka buɗe ɗakin ka ishe shi a shirye.

 To zari akwatin tsakiya shi ya fi kaya.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora:  Nasaman hoto ne.

 Na ƙasa maganin ƙwari ne.

 Zo zari akwatin tsakiyashi ya fi kaya.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Ka ga yana yankar aljihu birni.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Na Audu shege sai uwatai.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Tafiyata Kurmi ga ɗiyan Yarabawa.

 Na ji sun ce Ole.

 Na biyo ‘Yan Hausa, Mamman suna kiran ka ɓarawo.

 Inyamurai kau sun ce ma Anyusi.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Wai duk ɓarawon ne ke nan ‘yan Hausa.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Ka ga yana yankan aljihu birni.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora:Na Audu ya ɓalle ƙofa in ambarci.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Ba yash shiga banki baƙon Ɗammani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: In ya shiga daji ya ishe Hillani,

  Mamman Na Audu kore dut baƙon Ɗammani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Ka kore dut baƙon Ɗammani ko jaki kore Ɗanshata.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Bari bar masu ko jaki kore Ɗanshata.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: In ya kori bisashe, sawu sun Yamma.

  Shi Gabas baƙon Ɗammani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Yi Gwambe da su baƙon ‘Yarbanye.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Ko ko ka yi Bauci da su baƙon Ɗammani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Ko ko ka yi Barno da su baban ‘Yammani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Ko ka tsallake Kamaru baƙon ‘Yarbanye.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Ko ka laɓe Baga baƙon Ɗammani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: A nan babu mai zuwa cigiya domin shanunai.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: A nan wani daji!

 Nan ba mai zuwa cigiya domin shanunai!

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: A nanbabu mai zuwa cigiya domin shanunai!

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Da ka tahi Baga.

 Ko ko ka tahi Barno!

 In ka laɓe wani daji, anan babu maizuwa cigiya domin shanunai.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Wa za ya gane Mamman ɗan-ɗan Mani?

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Yi hannun riga tafi ɗauki abin ɗauka baƙon Ɗammani.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa.

Jagora: Na dai hwaɗa maka Mamman.

 Na kau hore ka.

 Wanda duk bai ajiye ba, matuƙar yanaso zai ɗauka.

  Mamman ka tabbatar kau kunya sai ta kammai.

Amshi: Haka nan ne Mamman ƙanen Idi wan Yalwa

Mamman Shata

Post a Comment

0 Comments