Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayyanar Izzar So A Tarbi`in Wakar Zuwana Jami`a Ta Alkali Halliru Wurno Sakkwato

Citation: Sulaiman, M.S. (2024). Bayyanar Izzar So A Tarbi`in Waƙar, "Zuwana Jami`a."Ta Alƙali Halliru Wurno Sakkwato. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 423-431. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.053.

BAYYANAR IZZAR SO A TARBI`IN WAƘAR, "ZUWANA JAMI`A."TA ALƘALI HALLIRU WURNO SAKKWATO

Muhammad Salisu Sulaiman

Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe, Tsangayar Fasaha Jami`ar Jihar Kaduna

Tsakure:

Wannan maƙala ƙunshe take da sharhin wata waƙa wadda Alƙali Halliru Wurno ya rubuta mana a lokacin muna ɗalibta digirin farko a Jami`ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, a shekarar 1994. Halliru Wurno ya ziyarce mu ne sakamakon gayyatar da malaminmu Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya yi masa. A yayin ziyarar ya gabatar mana da wasu daga cikin waƙoƙinsa. Bayan ya kammala gabatar da waƙoƙin, mun yi masa tambayoyi game da rayuwarsa da waƙoƙin da ya gabatar. A lokacin da zai tafi, sai ya karɓi sunayen ɗaliban ajin domin ya rubuta masu waƙa. Sai aka yi rashin sa`a sunayen wasu ɗaliban bai fito a cikin waƙar ba. Wannan ya kawo `yan gunaguni a tsakanin ɗalibai. Sannan a cikin waƙar sai ɗaliban suka lura cewa an fifita ambaton sunan wata ɗaliba Binta. Saboda an ambaci sunayen ɗalibai kowa sau ɗaya, ita kuwa an ambace ta har waje takwas. Waɗannan abubuwa guda biyu, su ne suka haifar da tambayoyi kamar haka: Me ya sa sunayen wasu ɗaliban bai fito ba? Sannan mece ce alaƙar Halliru Wurno da Binta? Waɗannan tambayoyi su ne aka yi sharhi a kansu a cikin wannan maƙala.

Fitilun Kalmomi: Izzar So, Tarbi`i, Waƙa, Alƙali Halliru Wurno

Gabatarwa

A lokacin muna ɗalibta a matakin digirin farko a Jami`ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, malaminmu Farfesa Abdullahi Bayero Yahya, yana da wani tsari da yake gabatarwa ga ɗalibansa: "Waƙa A Bakin Mai Ita." Yakan gayyaci marubuta waƙoƙi cikin aji, mawaƙi ya gabatar da waƙarsa, ɗalibai su yi masa tambayoyi. A irin wannan tsari Malam ya taɓa gayyato mana Malam Sambo Wali da Malam Garba Gwandu da Alhaji Alƙali Halliru Wurno.

Maƙasudin wannan tsari shi ne domin ɗalibai su sami ƙaruwar ilimi daga bakin mawaƙa kai tsaye. Game da gayyatar da ya yi wa Halliru Wurno, ga abin da Farfesa Abdullahi Bayaro Yahya ya ce:

"Saduwar Halliru Wurno da ɗaliban aji uku na ALH. 312: Rubutattun Waƙoƙin Hausa, na gayyaci Alhaji Halliru da ya zo cikin wannan aji a ranar 08-01-1994 domin ɗalibaina suna buƙatar su yi hira da shi. Ya kuwa karɓi wannan gayyata. Mun yi hira da shi mai amfani kuma na naɗe hirar a cikin faifan rikoda."

Ina iya tunawa a cikin godiyar da Farfesa Abdullahi Bayaro Yahya ya yi ga Halliru Wurno, bayan an gama hirar, ya yaba mana sosai, a taƙaice ga abin da ya ce:

"Bisa al`ada ta zamantakewa, idan ɗalibanka suka yi abin yabo, kakan jira ne wani ya yaba masu. To amma waɗannan ɗalibai ba zan jira yabon wani ba, ni da kaina zan yaba masu. Wato zan yi koyi da sunnar ƙadangare. A lokacin da ya faɗo daga sama, ya duba dama da hagu, ya ga ba wanda ya jinjina masa, sai ya jinjina wa kansa. Alal haƙiƙa na yaye ɗalibai da dama, amma waɗannan ɗalibai na musamman ne, ba zan taɓa mantawa da su ba."

A lokacin da Halliru Wurno zai tafi, sai ya karɓi sunayen wasu daga cikin ɗaliban. An karɓi sunayen ne a gurguje, saboda haka sunayen wasu bai fito a cikin waƙar ba.

Asalin waƙar ƙwar biyu ce, sai na yi mata tarbi`i, wato na ƙara ɗangwaye biyu a kan kowane baiti. Saboda akwai ƙorafi na rashin fitowar sunayen wasu ɗaliban ajin, sai aka ƙoƙarta aka kawo su cikin waƙar. Waƙar Halliru Wurno ta tsaya ne a baiti na 51. Daga nan sai na ɗora har zuwa baiti na 80, wato kusan dukkan ɗalibai na B.A.Hausa 1995 sun fito a cikin waƙar. Sannan aka yi godiya ga wasu daga cikin malaman da suka koyar da mu a shekarar.

Ma`anar Waƙa

“Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba, wadda ke ƙunshe da wani saƙo a cikin zaɓaɓɓun kalmomi waɗanda aka auna domin furucinsu ya yiwu ba tare da tuntuɓe ba." (A.B.Yahya:199: 3)

"Rubutacciyar waƙa, aunanniyar maganar hikima ce wadda ake rerawa a cikin tsarin daidaitattun ɗangwaye da baitoci da tsayayyun ƙafiyoyi a rubuce ko a haddace ba tare da kiɗa ba." (Sulaiman S.M. 2019)

Zubi Da Tsarin Waƙar

Asalin wannan waƙa ta Halliru Wurno ya rubuta ta ne da haruffan Ajami. Farfesa Abdullahi Bayero Yahya, ya juya ta zuwa haruffan Ingilishi, sannan waƙar `yar tagwai ce, tana da ƙanana da babban amsa-amon (na)

Daga baya ɗaya daga cikin ɗaliban ajin Sulaiman Salisu Muhammad Mai Bazazzagiya ya yi mata tarbi`i. Wato ya ƙara ɗangwaye bibbiyu a bisa kowane baitin waƙar. Sannan ya ƙara wasu baitoci a cikin waƙar, domin sunayen duka ɗaliban ajin ya fito. Halliru Wurno ya tsaya a baiti na 51, shi kuma Sulaiman ya ƙara har zuwa baiti na 80.

Amsuwar Waƙar Ga Ɗalibai

Bayan Halliru Wurno ya kammala wallafa waƙar, an gabatar da ita ga ɗalibai, maimakon ɗaukacin ɗalibai su nuna gamsuwarsu da waƙar, sai wasu ɗalibai suka fara gunaguni. A lokacin sai tunanin ɗalibai ya kasu zuwa gida huɗu:

Waɗanda sunayensu ya fito a cikin waƙar suna murna, saboda tarihi ba zai mance da su ba. Wannan ya sa sun yaba sun yi godiya matuƙa ga Halliru Wurno.

Waɗanda sunayensu bai fito ba, duk da cewa suna cikin ajin a lokacin da aka yi hirar, suna gunaguni mene ne ya haifar da haka? Duk da yake a cikin waƙar Halliru Wurno ya amsa wannan tambaya kamar haka:

Ina zuba godiyata na yaba ku,
Rashin sunanku shi at tarnaƙina.
Zama sunan waɗansu da ban sani ba,
A nan su nis sani ga irin sanina.

Wasu daga cikin ɗalibai mata sun nuna kishi, me ya sa aka ambaci sunan Binta fiye da su, tana ɗaliba suna ɗaliba, kuma haɗuwar farko a cikin aji?

A bisa al`adar zamantakewar ɗalibai a cikin aji, za ka ga akwai ƙauna, ko so, ko soyayya da ke gudana a tsakanin ɗalibai. Akwai masu son Binta a cikin aji, wasu sun nuna jin daɗi wasu kuwa damuwa suka nuna.

2.1 Mece ce Izzar So?

2.1.1 Izza

Asalin kalmar izza Balarabiyar kalma ce. A cikin Alƙur`ani mai girma Allah SWT ya ce: "Duk wanda ya kasance yana neman wata izza, to Allah shi ne mai izza gaba ɗaya."   (Sura: Faɗir, Aya ta 10 )

Bargery (1934) a cikin ƙamus ɗinsa ya bayyana ma`anar izza da, 'Girman kai.'

Kalmar izza na iya ɗaukar ma`anar ƙuwwa ko shauƙi ko ƙarfi ko ɗaukaka, musamman abin da ya shafi mulki.

2.1.2 Ma`anar So

So, shi ne sosuwar ko ƙawazucin zuciya na kusantar, ko mallakar, ko ganin, ko jin labarin wani abu mai rai ko maras rai, da nufin biyan wata buƙata domin sanyayar zuciya.

2.2. Yadda Ake Kamuwa Da So

Kamuwa da so wanda ya shafi mu`amala tsakanin mace da namiji, ba abu ne wanda ake shirya masa ba. Haka kwatsam mutum kan sami kansa cikin tarkon so, ya cukuikuye shi. Kamar yadda hatsarin mota kan zo ba shiri, wani ya ji ciwo, wani ya fita lafiya, wani ma har ya mutu, to haka shi ma shiga tarkon so yake. Babu wani wuri takamaimai inda so ke ɗana tarkonsa. Tarkon so na nan a kakkafe a ko`ina, ana iya faɗa masa ba dare ba rana. Mutum na iya aukawa a tarkon so a kasuwa ko a mota ko a filin wasa ko a wurin biki ko asibiti ko makaranta da sauransu.

2.3. Mabuɗan Kamuwa Da So

Mabuɗi shi ne abin da ake amfani da shi wajen buɗe rufaffiyar jaka ko akwati, ko ƙofa domin a samu a shiga ciki. Kamar yadda kullalliyar ƙofa take, haka nan zuciyar ɗan Adam ke a kulle. Akwai mabuɗai guda uku waɗanda ke buɗe zuciyar ɗan Adam. Da zarar sun buɗe ta, sai so ya sami damar cusa kansa ciki. Wani kan tsaya a bakin ƙofa, wani kan tsaya a tsakiya, wani kan kai ƙarshen zuciyar wanda ya kamu da shi. Waɗannan mabuɗai na so ga su kamar haka:

2.3.1 Gani: Yana ɗaya daga cikin abubuwan da ke haifar da kamuwa da so a tsakanin `yan Adam. Namiji na iya kamuwa da so, da zarar ya ga wata mace, ba sai ya yi magana da ita ba, haka nan abin yake ga mace. Wannan ganin na iya kasancewa ganin fuska da fuska, ko gani a hoto, ko kuma gani ta talbijin. Sannan mutum na iya kamuwa da son wani ko wata da zarar ya gan shi, ko bai san shi ba.

3.1.2 Magana: Magana kan taka muhimmiyar rawa a wajen buɗe ƙofar so a cikin zukata. Wani da ya ji maganar mace zai kamu da son ta. Haka ita ma wata macen da ta ji maganar wani, sai ta kamu da son sa. Wannan maganar tana iya kasancewa ta baka da baka ce ta gudana a tsakanin mai son da wadda ake son. Ko kuma ta kafafen yaɗa labarai kamar: Rediyo ko Talbijin ko Jarida. Wani kuma ta jin waƙa ko kuma karatun Al`ƙur`ani ko wa`azi. So na iya sarƙuwa ta kowanne ɗaya daga cikin waɗannan nau`o`in magana.

3.1.3 Labari: Jin labari na ɗaya daga cikin hanyoyin da kan sa mutum ya kamu da son wani ko wata ko wani abu ba tare da ya gan shi ba, bai kuma ji maganarsa ko maganarta ba. Sai dai kawai ya ji labarinsa ko labarinta ne. Tana iya kasancewa wannan labarin an ji shi baki da baki ne, ko a gidan Radiyo, ko a Talbijin. Ko kuma a rubuce a Mujalla ko a Jarida. Labarin da aka ji yana iya kasancewa ta wata jarumta ce, a fannin sana`arsa, ko a makaranta, ko dukiyarsa ko ɗabi`unsa da sauransu.

3.2 So Ba Shi Da Bare

Ɗabi`ar so, kamar jini ne a jikin ɗan Adam, ba wanda ba shi da shi. Ko kuma kamar iska ce, ba wani abu mai rai wanda ba ya shaƙar sa. Ba wani abu mai rai, mutum ne ko dabba ce, tsuntsu ne ko ƙwaro ne, ko shuka da zai ce ba ya shaƙar iska. To haka shi ma so yake, duk wata halitta mai rai tana da nata hanyoyin aiwatar da so. Mutum ba ya gushewa da son wani abu, sai ranar da aka ce ya bar duniya.

Sai dai ɗabi`ar so, kowace ƙwarya akwai abokiyar burminta. Yara da matasa, da tsofaffi, malamai da ɗalibai, masu arziki da talakawa duk suna da shi a cikin zukatansu. Haka dabbobi da tsuntsaye da ƙwari da shukoki, duk akwai irin nasu nau`in son.

3.3. Wace ce Binta?

Asalin Binta Bakatsiniya ce tana cikin ɗalibai waɗanda ba su yi aure ba a lokacin, wato budurwa ce. kamar yadda Alƙali Hilliru ya kawo bayaninta a cikin waƙar.

6. Garinta na Dikko can Katsinanssu,

Haƙiƙan Binta ta tsere ka juna.

Akwai baitoci guda takwas da aka ambaci Binta, waɗannan baitoci ga su kamar haka: 6, 8, 9, 17, 19, 23, 27, 47. Haka nan akwai wata Binta Chinoko, wadda aka ambata sau ɗaya. A gaskiya an shaidi Binta da kyawawan ɗabi`u. Hannayenta a buɗe suke ga duk wani ɗalibi da ya nemi agajinta, musamman kuɗi ko abinci idan ALUTA ta ratsa.

A wajen siffar jiki ba a bar ta a baya ba, irin siffar Katsinawa ke gare ta. Ita ba ƙatuwa ba, ba kuma lange-lange ba. Ita ba fara ba ce, amma kuma ba baƙa ba. Wato siffar wankan tarwaɗa ke gare ta. Ga ta kyakkyawa ga fuska da sauran sassan jikinta. Duk wanda ya yi wata hulɗa da Binta, tabbas zai ce ta cancanci wancan yabo da Halliru Wurno ya yi mata. Gamayyar kyawawan ɗabi`u na iya mu`amala, da kyawun siffar diri, da iya magana, waɗannan su ne tarkon da ke ribatar zukatan masu mu`amala da Binta har su ƙaunace ta.

3.4. Bayyanar Izzar So

A sakamakon gabatar da waƙar da Halliru Wurno ya yi Izzar So ta bayyana a waɗannan a tsakanin waɗannan kason mutane:

Yawaita ambaton sunan Binta a cikin waƙar, akwai alamun Halliru Wurno ya kamu da son Binta. Ba komi ya haifar da haka ba illa Izzar so. Ƙila ita ce ta ingiza shi ya yi wannan yabo, ba tare da la`akari da me zai biyo baya ba.

ii. Halliru Wurno a matsayinsa na babban malami, Alƙali, mawaƙi, ba zai rasa wasu daga cikin ɗalibai mata masu son sa ba. Tunda kowa yana son nagari. To sai ga shi ƙarara ya karkata yabonsa zuwa ga Binta. Wannan ya haifar da kishin so a tsakanin wasu ɗaliban masu ƙauna ko son Halliru Wurno. Misali dubi yadda yake umurtar sauran matan da su kai caffa zuwa ga Binta.

Garinta na Dikko can Katsinanssu,
Haƙiƙan Binta ta tsere ku juna.
Ku saurara ɗiya mata ku ji ni,
Ku kai caffa ga Binta tana da rana.
Halinta kama da Binta ta Dikko waccan,
Da nic ce tai kama da wata da rana.

Waɗannan baitoci sun fifita Binta a kan sauran ɗalibai mata. Abu ne sananne ga mata cewa ba kasafai mata ke yarda wata ta fi su ba. Wannan ya haifar da kushewa da tsangwama a tsakanin Binta da sauran ƙawayenta. Ba komi ya haifar da haka ba, illa izzar so da ke cikin zukatansu.

Waɗanda ke son Binta izzar so ta bayyana a gare su ta fuska biyu:

Kaso na farko, suna jin daɗi an kwarzanta masoyiyarsu. Saboda haka zaɓinsu ga Binta ba su yi zaɓin tumun dare ba. Saboda haka sonsu zuwa ga Binta ya ƙaru matuƙa, haka nan ƙaunarsu ga Halliru Wurno ta ƙaru, saboda ya yabi tasu.

Kaso na biyu, suna ganin wannan yawan yabo, da walakin, goro a cikin miya. Sawun giwa ne ke son take na raƙumi. Misali a baiti na 11 ga abin da ya ce:

Karatu tat taho ba son maza ba,

Akwai su garinsu mai wargi ka daina.

Wannan baitin kamar yana yi wa masoyan Binta shaguɓe ne, cewa su daina damun ta da batun neman soyayya. Ba abin da ya kawo ta Jami`a ke nan ba, karatu ta zo yi. Idan maza take so, ai akwai su a garinsu. Wannan ya sa izzar so da ke cikin zuciyarsu ya sa sun ƙara ƙaunatar Binta saboda a bisa alamu ana so a ture su gefe. A gefe ɗaya kuma, a dalilin izzar so, suna yi wa Halliru Wurno kallon hadarin kaji, saboda abin da ya faɗi gare su, kamar yana kashe masu kasuwa ne.

4.1 Kammalawa

A bisa bayanai da suka gabata, an yi bayani game So da yadda ake kamuwa da So. Sannan mun ga bayyanar izzar So daga ɓangarori mabambanta. Wadda izzar So ta ja Halliru Wurno yawaita yabon Binta a cikin waƙarsa, ba tare da la`akari da me haka zai haifar ba, a tsakanin ɗaliabai. Izzar So ce ta haifar da kishi a tsakanin ƙawayen Binta, saboda an fifita ta a kansu. Haka nan izzar So ta sake bayyana a tsakanin masoyan Binta maza, wasu na yabon Halliru Wurno saboda ya wasa gwanarsu. Wasu kuwa na kushe masa saboda suna da tunanin cewa, in ka ga kare yana sunsunar takalmi, ƙila ɗauka zai yi.

Daga ƙarshe a cikin wannan maƙala an kawo tarbi`in 'Waƙar Zuwana Jami`a,' sannan an ga yadda aka ƙara sunayen ɗaliban da Halliru Wurno bai sanya su a cikin waƙarsa ba. Aka rufe waƙar da godiya ga wasu malamai da suka koyar da ɗaliban shekarar 1995.

TARBI`IN WAƘAR ZUWANA JAMI`A TA ALƘALI HALLIRU WURNO

Sulaiman Salisu Muhammad (Mai Bazazzagiya)

08067917740  30-08-2023

Zuwana Jami`a nis san ka Dabo,
Zuwana Jami`a dai mun yi sabo,
Zuwana Jami`a na sami tarbo,
Ga manyan ɗalibai manyan ɗiyana.

Maza mata ina ƙaunar ku sosai,
Maza mata fa ga tsaraba ta ƙosai,
Maza mata fa na same su sosai,
Akwai ladabi gare su suna da rana.

Da duba na ga fuskokin ƙawaye,
Da ƙauna tas shige ni ina hawaye,
Da duba na ga fuskokin su waye,
Kamar dai safiyar sallah ganina.

Da mata har mazansu nake ta ƙauna,
Da mata har mazansu irin ganina,
Da mata har mazan nan salihina,
Sakin fuska mutumci sun yi suna.

Akwai wata malama ba ta bilayi,
Akwai ladabi na ce ba kauce layi,
Akwai wata malama dubin da na yi,
Akwai natsuwa ga Binta irin ganina.

Garinta na Dikko ga kara gare su,
Garinta na Dikko kunya ce gare su,
Garinta na Dikko can Katsinanssu,
Haƙiƙan Binta ta tsere ku juna.

Akwai kyawo akwai natsuwa gare ta,
Akwai kyawon ɗabi`a ba mugunta,
Akwai ladabi akwai hange gare ta,
Daɗai ba ta ya da kai ba ku ɗau batuna.

Kwaɗai ke sa ake dai raina mata,
Kwaɗai sam babu shi a wajenta Binta,
Kwaɗai dai ba ta yi ta kama kanta,
Faɗin baba ga Binta abin musu na.

Ɗiyata tabbaci kin zarce mata,
Ɗiyata kin yi tsatsa zuciyata,
Ɗiyata na jiya kumya ke gare ta,
Yawan ladabi ga Binta abin yabo na.

Da ɗai ba a ce taho domin kira ba,
Da ɗai ba a ce taho ba ta sunkuya ba,
Da ɗai ba a ce taho ki jiya ta zo ba,
Ajin nan dole dai taka amsa suna.

Karatu tat taho ba shirbici ba,
Karatu tat taho ba gulmace ba,
Karatu tat taho ba son maza ba,
Akwai su garinsu mai wargi ka daina.

Zama ba don ana ce ɗaliba ba,
Zama ba don ina guje kuskure ba,
Zama ba don ganin ta cikin aji ba,
Walicci zan kirai mata ni ganina.

Zama Binta a ilmi zaruma ta,
Zama azumi da salllah ta naƙalta,
Zama ita saliha ta mumina ta,
Na Allah ɗai take shagali mu`ina.

Akwai wata salaha yanzun tana nan,
Akwai wata mai himma tana nan,
Akwai wata Hanne `yar Kawoje na nan,
Akwai lura da himma lalabena.

Haƙiƙa zubinta yai siffar madubi,
Haƙiƙa halinta kullum kama carbi,
Haƙiƙa halinta Hannatu ko ga dubi,
Fulanin Yamma kumya sun yi suna.

Ɗiyar nan yanzu kaya za ni sauke,
Ɗiyar ɗakinta kullum ga shi wanke,
Ɗiyar Kangiwa na ga Amina yanke,
Ga boko ko gurama ta yi suna.

Halinsu guda da manya masu ilmi,
Halinsu guda da waye mai muƙami?
Halinsu guda da Binta zuwa ga ilmi,
Ta Birnin Dikko ƙusa ba ta kwana.

Da himma tat tafo kwa daina ƙyashi,
Da himma tat tafo hannu da mashi,
Da himma tat tafo digiri ta yo shi,
Garat `yan si, e, wannan ƙanƙane na.

Ba`a kam Binta sam ba ta kula sa,
Ba`a kam Binta ba mata na gasa,
Ba`a kam Binta ba ta kula da wasa,
Sani taz zo biɗa wasa buzaina.

Ba`a ab ba ta yi ko ɗai ƙazamat,
Ba`a sai sokuwa waina ku sammat,
Ba`a ab ba ta yi don kar a rammat,
A maisat shawarakanya faɗina.

Da Maryam Tambuwal kar dai ku manta,
Da Maryam tabbaci ta ɗarma mata,
Da Mairamu Tambuwal huska akwai ta,
Mutunci ta fake ni kam ganina.

Da mata masu halaye karimi,
Da matayen Riɓa mata na Zurmi,
Da Binta Chinoko mata masu ilmi,
Gurama Ingilishi godabe na.

Halinta muna yabawa ni da waccan,
Halinta ku tabbata ta zarce waccan,
Halinta kama da Binta ta Dikko waccan,
Da nic ce tai kama da wata da rana.

Da kamun kai na ce maku ta yi suna,
Da yin ladabi biyayya ba hiyana,
Da kamun kai da ɗa`a ga amana,
Da tsoron Jalla ba su kama da arna.

Da mataye karimai kun ga na san,
Da kyau Safiya ɗiyar Kyaftin ku dai san,
Da kyau Safiya ɗiyar Abdallah na san,
Da alhairinsu sun wanke zufana.

Hijabi sun ka sa sun kauce jifa,
Hijabi kariya tamkar fa rumfa,
Hijabi sunka sa sun ɓoye siffa,
Kamar Jarwal da Hausawan Madina.

Ku dai kula yanzu dai zan gargaɗe ku,
Ku gane Yarima bai daidai da Kuku,
Ku dai kula kar ku sa haɗama a ranku,
Kamar wada Binta taz zama ni ganina.

Ana ƙamfarku can daji su ƙwanso,
Ana wanka da kyau an sanya soso,
Ana ƙamfarku har ku ma kuna so,
Katangar hanƙuri ku yi an nufina.

Maza gumba ta dutse zan faɗe ku,
Maza zan waiwaye ku ina tuna ku,
Maza zan waiwayo ku ina yaba ku,
Yawan ladabinku tare da tanadina.

Sulaiman yanzu kai ne zan wa ƙaimi,
Sulaiman nai du`a`i sam muƙami,
Sulaiman bin Bawa Digi Karimi,
Kwaleji idekeshi mai murnar ganina.

Da Adamu Ila yau zan je gare shi,
Da Adamu Ila tilas zan kire shi,
Da Adamu Ila na Tsafe fa sa shi,
Hussaini Umar Ruwan-daɗi Aminna.

Uzairu Haruna wa yas san ƙasarsu,
Uzairu na ce Bayajidda ƙasarsu,
Uzairu Haruna Daura ak ƙasarsu,
Biɗar digirinsa yaz zaka mahiri na.

Da kau Idrisu yanzu ku zam tunawa,
Da kau noma gari nasu ba gazawa,
Da kau Idrisu Yusufu ɗan Jigawa,
Sa`idu na Bangi Ali muzakkari na.

Mu zo wani jarumi zan ambace shi,
Mu zo mu gani a yau dai zan yabe shi,
Mu zo Ɗangulbi Ali muna ishe shi,
Da Ibrahim na es-es zarumi na.

Mutanen Kwantagora irin ganina,
Mutane ne na Gwamatse zarumai na,
Mutanen Kwantagora akwai amana,
Dalilin Abdu nis san ɗalibina.

Aminu karamci kun ga ya min,
Aminu garinsu ku zan tuna min,
Aminun Es Fada ba zai ɓace min,
Dalilin Abdu Bayaro ɗan uwana.

Ina zuba godiya domin tuna ku,
Ina waƙe ɗiyana malamanku,
Ina zuba godiyata na yaba ku,
Rashin sunanku shi at tarnaƙina.

Zama sunan wasunku da ban gani ba,
Zama tilas na bar wasu ban faɗi ba,
Zama sunan waɗansu da ban sani ba,
A nan su nis sani ga irin sanina.

Akwai Sarki na Hausa na ce Kabiru,
Akwai zikiri akwai natsuwa Kabiru,
Akwai Abdulkarim Kano Kabiru,
Fasaha ag garai da mutumta juna.

Ga fuska sai ka ce Hillo na Mubi,
Ga fuska in yana duban madubi,
Ga fuska sai ka ce Liman ga dubi,
Wurin cika alƙawal shi yai suna.

Da Ya`u na Shehu tabbas na gidan nan,
Da Ya`u na Shehu Zariya jarumi nan.
Da Ya`u na Shaihu Zariya wa mutum nan,
Shi far mai kan sani faɗi ɗalibina.

Da wannan ɗalibin bai son husuma,
Da Adam Zariya zan sa shi, shi ma,
Da Adamu wanga Abdullahi shi ma,
Tsayayye na ga ilmin zamanina.

Abubakari na ce maku ɗan ina ne,
Abubakari ganina salihi ne,
Abubakari na Ummaru Dange ɗa ne,
Da yas san Jabru babban haziƙi na.

Sulaiman Zariya yau zo mu gaisa,
Sulaiman Salihu ilimi gare sa,
Sulaiman Salihu shi bai da wasa,
Wurin tsare gaskiya in dai faɗi na.

Aliyu Kajuru ya zarce wa sako,
Aliyu Kajuru Sadauki na kadarko,
Aliyu Kajuru ɗan Abdallah shi ko,
Halinsa ga ƙoƙari babban mutum na.

Zuwana Jami`a Allah Tabara,
Zuwana Jami`a na sami kara,
Zuwana Jami`a na iske yara,
Ɗiyan manyan mutane ɗalibaina.

Ku saurara maza mata ku ji ni,
Ku saurara aron kunne ku ba ni,
Ku saurara ɗiya mata ku ji ni,
Ku kai caffa ga Binta tana da rana.

Kwaɗai ab ta yi nono ga rugga,
Kwaɗai ab ta yi gun ɗinka riga,
Kwaɗai ab ba ta yi ba ƙalla yanga,
Da jin izza gare ta abin gudu na.

Kamar wada an ka ce in Binta na nan,
Kamar wata Gimbiyar Sarki tana nan,
Kamar wada an ka ce kul Binta na nan,
Ga kamun kanta wane fasiƙina.

Ku bi ta a sannu ƙawaye kui abota,
Ku bi ta ku ɗauki halayenta mata,
Ku bi ta ku ɗauki halayenta kyauta,
Da sakarci da roƙo tasari na.

Ji Alhaji Haliru yau dai nai batuna,
Ji Alƙali ina yaba ɗalibaina,
Ji Alhaji Wurno Alƙali Halir na,
A can dai dauri yau kam mallamina.

Waɗanda Alƙali Hilliru Wurno Bai Ambace Su A Cikin Waƙar ba.

Sulaiman yanzu lissafo wasunsu,
Sulaiman yunƙura don ambato su,
Sulaiman gaisuwa kai ta gare su,
Dalili yanzu ai ba ni da suna.

Muna yin godiya Allah ya saka,
Muna yin godiya Allah ji ƙan ka,
Muna murna dalilin wagga waƙa,
Na Wurno karimi malamina.

Da juyawa a yanzu na ga waye,
Da waigawa a baya fa na kiyaye?
Abokai ne a can gefe ƙawaye,
Suna nan jere dukkan `yan ajina.

Na Katurunmu na ce Adamu Sani,
Na Katuru biɗo mani ka ji Mani,
Na yo masa gaisuwa ya zam kula ni,
Mutum mai dariya mai kama kaina.

Sa`idu na Bangi yau na waiwaye ka,
Sa`idu na Bangi Allah dai ya saka,
Sa`idu na Bangi dole in yabe ka,
Mutum ne kamili tabbas in nuna. 

Ina Bello na Bandiya yau ka gane,
Ina Bello na Bandi na ce mutum ne,
Ina Bello na Bandi muzakkari ne,
Mutum ne salihi a irin ganina.

Ina Sani na Yakubu ɗan Bicin nan,
Ina Sani na Yakubu jarumin nan,
Ina Sani ku nemo min garin nan,
Farar fuska iwa huda ta rana.

Mu dai gaisa Muhammadu Namadina,
Mu je Anka mu gaisai ɗalibina,
Mu dai koyi ga Manzo ɗan Amina,
Mutum ne salihi tabbas ganina.

Ina Yarawal fa Umaru dai karimi,
Ina roƙo ga Rabbi ka sam muƙami,
Ina ƙaunar sa tabbas bai da ɗumi,
Mutum ne kamili na so da ƙauna.

Muhammadu Altine na Maru Sahihi,
Muhammadu Altine jika ga Shehi,
Muhammadu tabbaci shi kam madihi,
Akwai ladabi akwai natsuwa ganina.

A ƙofar mata nemo Mustafa ne,
A ƙofar mata can ne za mu zaune,
A can ne Mustafa ya tafo ku gane,
Kanawan Dabo mun sabo da juna.

Akwai Bello na Wamba muzakkari ne,
Akwai Bello na Wamba yana ina ne?
Akwai shi ajin ga saurara ka gane,
Akwai ƙwazo karamci ɗalibi na.

A Bakori Abubakari na san shi,
A nan ya taho fa ilmi zai biɗe shi,
A can Katsina yake zaune gidanshi,
Ina Umar mutumin can Katsina.

Abubakari Mafara kana ina ne?
Abubakari fa babban ɗalibi ne,
Abubakari cikakken ɗalibi ne,
Ku nemo min Sama`ila jarumina.

Mutanen Zuru nai cigiya gare ku,
Mutanen Zuru ga saƙo gare ku,
Mutanen Zuru wa gwarzon cikin ku,
Ina Umar fa Yakubu sahibina.

Madomawa Ƙwazo ina ka je ne?
Madomawa garinsu fa jarimi ne,
Madomawa Muhammadu ɗalibi ne,
Na ce Sani karimin jarimina.

Sulaimanu na Kumbashi karimi,
Sulaimanu mutum ne mai muƙami,
Sulaimanu mutum ne shi salami,
Akwai haƙuri da dattaku ganina.

Abubakari na Rabi`u ba ya wasa,
Abubakari a yanzu ina biɗar sa,
Abubakari mu bi shi zuwa gidansa,
Garinsu ka bincika can ne Gumina.

Ina Mai Shehi Gayari kana ina ne?
Ina kake ne mu zauna salihi ne,
Ina Mai Shehi babban ɗalibi ne,
Abubakari a yau ga gaisuwana.


Ina tuna Malami Sani na Jega,
Ina kake ɗalibi mai kyau da riga,
Ina kai gaisuwa can ne fa Jega,
Ina yin godiya kai malamina.

Ina Lamiɗo Dada na can Kanon nan?
Ina ne zan gano shi cikin ajin nan?
Ina adu`a da yaz zam ba shi dai nan,
Mutum ne haziƙi shi ɗalibina.

A ƙarshe Ummaru namu na Bunza,
A ƙarshe dole mai tauna ya furza,
A ƙarshe Umaru ya kai ga mazza,
Mutum ne jarimi a irin ganina.

Sulaiman na yi tarbi`i na waƙa,
Sulaiman na yi ƙari baiti waƙa,
Sulaiman Halliru Wurno na saƙa,
Muna yin godiya Hallir gwanina.

Muna yin godiya gun malaminmu,
Na Bayero Abdu Farfesa a ilmu,
Yahya tabbaci ya taimake mu,
Asiri gun salon waƙa gwanina.

Akwai wasu malamanmu ina yabawa,
Akwai Dunfawa malam bai gazawa,
Akwai malam fa Yakasan Kanawa,
Akwai Amfani Farfesan garina.

Akwai Iron Malumfashi ku duba,
Akwai Sa`adiyya Umar can ka duba,
Akwai Muhabub fa Alƙali na duba,
Gafuru ka gafarta masa nai addu`ana.

Akwai Ɗantumbushi zan so ganin ka,
Akwai ma Ɗahiru Arugungu naka,
Akwai saƙo na ce Allah ya saka,
Gare ku muna yin godiya duk malamaina.

Muna roƙon ka ya Allah ji ƙan mu,
Muna roƙon ka Aljanna ka ba mu,
Muna roƙo maza mata ɗiyanmu,
Mu san tsira Gafuru Ubangijina.

A yau dai sha tara na kammala ta,
A wanga wata na ce maku dai Agusta,
A yau dai shekara ta dubu biyunta,
A sa ashirin da ukku shekara na.

Manazarta

Abdullahi, B. (1983) “A Critical Anthology Of The Ɓerse Of Alhaji Bello Giɗaɗawa.” Kano: Department Of Nigerian Languages, Bayero Uniɓersity. Unpublished M.A.Thesis.

Adamu A.U. (2007) Manuscript Learning Ability And Indegenous Knowledge For Deɓt. Hausa Ajami In Historical Conteɗt. Nigerian Interlectual Heritage Proceeding Of An Internal Conference On Preserɓing Nigerian Scholar And Literary Traditional And Arabic Ajami Manuscript Heritage. Arewa House, Ahmadu Bello Uniɓersity, Kaduna. Kaduna: Prime Publicity Nig. Ltd

Bargery, G.P (1934) A Hausa-English Dictionary And English-Hausa Ɓocabulary. Zaria: Jami`ar Ahmadu Bello Press Ltd

Bello, G. (1993) “Baje Kolin Hajar Tunani.” Sokoto: Giɗaɗawa Press.

Bello, S. (2002) Rubutattun Waƙoƙin Hausa Na Ƙarni Na Ashirin A Jihohin Sokoto Da Zamfara Da Kabi. Unpublished Ph.D Bayero Uniɓersity Kano

Bosso, M.A. (2010) Nazarin Ajami Cikin Hausa Don Makarantu Manya Da Ƙanana. Minna: Hasbunallah Printers

Birniwa, A.H. (1981) “The Imfiraji 1 And 4 Of Aliyu Namangi.” London: Soas. Uniɓersity Of London. Unpublished M.A Thesis.

Bugaje, M.H. (2011) Wa`Azi A Rubutattun Waƙoƙin Mata Na Ƙarni Na Ashirin. Zariya: Sashen Harsuna Da Al`Adun Afrika Tsangayar Fasaha Jami`Ar Ahmadu Bello: M.A. Thesis

Bunza A.M. (2002) Rubutun Hausa Yadda Yake Da Yadda Ake Yinsa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre Ltd

Dangambo, A. (2007 ) Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Zaria: Amana Publishers.

Garba, S. (2011) Salon Sarrafa Harshe A Waƙoƙin Aƙilu Aliyu: Zariya: Sashen Harsuna Da Al`Adun Afrika Tsangayar Fasaha Jami`Ar Ahmadu Bello: Ph.D Thesis

Idris Y. (2016) Bijirewa A Waƙoƙin Siyasa: Bincike Kan Waƙoƙin 1903-2015: Zariya: Sashen Harsunan Afrika Da Al`Adu Jami`Ar Ahmadu Bello.

Malumfashi, A.I. (2010) Wa`azi A Rubutattun Waƙoƙin Ƙarni Na Ashirin. Harshe 4 Jounal Of African Languages Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Da Na Afrika Jami`Ar Ahmadu Bello, Zariya

Malumfashi, A.I. (2019) Ɗanbuzuwar Akuya, Ko Bai Yi Gashin Ko`ina Ba, Ya Yin A Katara: Aƙilu Aliyu Da Waƙoƙin Bijirewa Sashen Harsuna Da Al`Adun Afrika Tsangayar Fasaha Jami`ar Ahmadu Bello Zariya

Malumfashi, I. (2019) Labarin Hausa A Rubuce: Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press

Maniya, M.S. (2004) “Tarihin Sahabban Shehu. Sokoto: Al-Amen Printing Press

Muhammad, D. (1985) “Ɓisual Imagery In Blind Poetry Illustration From Namangi`s Imfiraji And Audu Makaho`s Tabuka.” Lagos: Nigeria Magazine

Muhammad S.S (2011) Kwatancin Waƙar Jiddul Ajizi Ta Shitu Ɗan Abdurra`uf Da Kanzil Azimi Ta Aliyu Namangi. .”Zariya: Department Of African And Nigerian Languages. Unpublished M.A. Thesis

Muhammad, S.S (2018) Gudummuwar Marubuta Waƙoƙi Wajen Yaƙar Talauci A Ƙasa. Nazari Daga Waƙar Gangar Wa`Azu Ta Malam Muhammadu Na Birnin Gwari. First International Conference, Faculty Of Arts Kaduna State Uniɓersity, Nigeria

Mukhtar, I. ( 2005 ) Bayanin Rubutacciyar Waƙar Hausa. Abuja: Countryside Publishers

Namangi, A. (1972) Waƙoƙin Imfiraji Juzu`I 1-4 Zaria:Northern Nigeria Publ. Company.

Sarɓi A.S. (2007) Nazarin Waƙen Hausa. Kano: Samarib Publishers.

Skinner, A.N. (1969 ) “A Hausa Poet In Lighter Ɓein’ African Language.” African: Language Reɓiew, Ɓol. 8.

Sulaiman, S.M. ( 2010) Bazazzagiya. Zaria: Maigwado Multi-Media

Sulaiman S.M. (2019) Matakan Nazarin Rubutacciyar Waƙa. Zariya: Ahmadu Uniɓersity. Press Limited

Tahir R.M. (2012) Ajamin Hausa. Don Ƙananan Makarantu. Zariya: Yahaya Ɓentures General Printers And Publishers

Yakawada, M.T (1983) “Waƙeƙeniya” Zaria: Department Of Nigerian And African Languages, Ahmadu Bello Uniɓersity. Unpublished B.A. Project.

Yakawada, M.T. (1987). “Tarkakken Matanin Waƙar Kanzil Azimi Ta Aliyu Namangi.”

Zariya: Dept. Of Nigerian And African Languages, Ahmadu Bello University. Unpublished M.A. Thesis

Yahaya. I.Y ( 1988 ) Hausa A Rubuce. Zariya: Northern Nigeria Publishing Company.

Yahya.A.B. (2016 ) Salo Asirin Waƙa. Sokoto: Guaranty Printers Sokoto

Zaruk, R.M. Da Wasu (2006) ‘Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa’ University Preess PLC, Ibadan.

Amsoshi Hausa Materials

Post a Comment

0 Comments