Ticker

6/recent/ticker-posts

Balbela Ba Ta Bin Kare Sai Shanu: Al’adar Roko Da Kunshiyarsa A Bakin Mawakan Baka Na Hausa

Citation: Umar, H.A. and Ɗalha, I. (2024). Balbela ba ta Bin Kare Sai Shanu: Al’adar Roƙo da Ƙunshiyarsa a Bakin Mawaƙan Baka na Hausa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 384-396. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.049.

BALBELA BA TA BIN KARE SAI SHANU: AL’ADAR ROƘO DA ƘUNSHIYARSA A BAKIN MAWAƘAN BAKA NA HAUSA

Halima Ahmad Umar
Department of Nigerian Languages
Sokoto State University, Sokoto

Ibrahim Ɗalha
Government Day Senior Secondary School Birnin Kudu
Jigawa State

Tsakure:

Wannan bincike mai taken: “Balbela Ba Ta Bin Kare Sai Shanu: Al’adar Roƙo da Ƙunshiyarta a Bakin Mawaƙan Baka na Hausa.” An gina shi da manufar laluben ƙunshiyar al’adar roƙo a bakunan mawaƙan baka na Hausa. Binciken ya yi ƙoƙarin waiwayar ayyukan da magabata suka gudanar masu alaƙa da roƙo, domin ganin inda suka tsaya, saboda a san inda za a tunkara. Wasu daga cikin hanyoyin da binciken ya yi amfani da su sun haɗa da: Sauraren waƙoƙin Hausa na baka daga bakin maƙagansu, waɗanda aka taskance su a na’urar adana bayanai ta memori. Haka kuma, nazarin ya bibiyi wasu daga cikin waƙoƙin baka da aka rubuta a wallafaffun littattafai domin daidaita abin da aka saurara na muryoyin mawaƙan da kuma abin da yake a rubuce. Har wa yau, an tuntuɓi wasu ɗaiɗaikun manazarta da suke da masaniya a kan batun da ake bincike a kan sa, saboda buƙatar da ake da ita ta samun hasken da zai ƙara wa maƙalar tagomashi. An yi amfani da Bahaushiyar hanyar ɗora aiki wadda ke cewa: “Kowace Ƙwarya Tana da Abokiyar Burminta.” Binciken ya yi garkuwa da ɗiyan waƙoƙi 26 daga bakunan mawaƙa daban-daban guda 12 a matsayin misalai. A ƙarshe, takardar ta gano cewa, akwai hanyoyi da yawa da mawaƙan baka na Hausa suke amfani da su domin bayyana abin da suke roƙo a wurin waɗanda suke wa waƙa. Kamar yadda nazari ya ƙyallaro cewa, mawaƙan sun fi roƙon abubuwan da suka shafi abin hawa (mota ko doki) da kuɗi da hajji da sutura (tufafi) da gida da gona da abinci da kuma sauran abubuwan da rayuwar ɗan’adam ke buƙata.

Fitilun Kalmomi: Balbela, kare, shanu, al’ada, roƙo, da mawaƙan baka

Gabatarwa

Alfanun da ke ƙunshe a cikin waƙoƙin baka na Hausa masu nazarin al’adun Hausawa ba za su iya kawar da kai daga gare su ba. Wannan ta sanya tuni masana da ɗalibai suka fahimci haka, inda suka himmatu ga laluben abubuwan da suka shafi fannonin karatun Harshe da adabi da kuma al’adun Hausawa a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Sakamakon haka, sai fagen nazarin waƙa ya samu armashi a wurin ɗalibai da manazarta, wannan sai ta ba shi tagomashin samun ayyuka mabambanta, Bunza (2012) a cikin Sifawa, (2019:58). Duk da haka, giɓin da wannan takarda ta iya ƙyallarowa, bai wuce na wata ƙaramar kafa da ya kamata a cike ba. Hango giɓin ya bijiro ne saboda ganin ayyukan da aka gudanar a kan kyauta, sai ya haska ƙamfar da ake da ita na nazarce-nazarcen da suka tunkari roƙo.Wannan shi ne dalilin da ya sa aka ga dacewar wannan bincike, saboda a toshe wannan kafa. Wani abin armashi ga wannan bincike, takardar kan iya zama wata matashiya ga mai laluben al’adar Hausawa ta zaɓen kalmomin girmama gabaci, musamman a lokacin da ake neman wani abu a wurin wani, duba da yadda tarbiyar matasa a kullum take komawa gara jiya da yau. Ke nan, wannan aiki kan iya zama wata matakala da za ta gwada wa masu tasowa ladabin zaɓen kalmomin girmamawa a lokacin da ake tare da magabata ko kuma ake neman sahalewar su kan neman wata buƙata.

1.1 Farfajiyar Bincike

 A ƙoƙarin gudanar da wannan bincike, an samu damar leƙa wasu ayyuka da aka gudanar masu alaƙa da roƙo. Wasu daga cikin waɗannan ayyuka da aka samu zarafin kaiwa gare su sun haɗa da na: Shinkafi (2003) da na Ahmad da Isma’il (2023) waɗanda suka karkata a kan nazarin roƙo a matsayin wani salo daga cikin salailan nazarin adabin waƙoƙin baka. Hassan (2013) da Ibrahim (2015) da kuma Daura (2023) sun yi garkuwa da al’adar kyauta a tunanin mawaƙan baka. Shi kuwa Bunza (2009) ya ƙyallaro wani abu na al’ada ta fuskar yanayin nau’o’in roƙo a tunanin mawaƙan baka na fada. Wannan ya tabbatar da cewa, akwai buƙatar a ƙara fito da wani keɓantaccen abu da ya shafi al’adar roƙo a tunanin mawaƙan baka domin cike giɓin da ke tsakaninsa da ayyukan da aka gabatar a kan kyauta. Kasancewar binciken wani ɗan yunƙuri ne na cike wannan giɓi na ilimi, shi ne ya sa aka taƙaita shi ga laluben ɗabi’un mawaƙa na ƙulla dabarar roƙo a ɗiyan waƙoƙinsu. An lura da rabe-raben mawaƙan baka da magabata suka samar; inda aka lalubo ɗiyan waƙoƙin da suka ƙunshi roƙo a rukunonin mawaƙan baka guda biyar (mawaƙan fada da na jama’a da na maza da na sana’a da kuma na ban-dariya).

2.0 Fashin Baƙin Kalmomin Tubalan Take

 A wannan mahalli, an mayar da hankali kan bayyana ma’anar kalmomin da aka yi amfani da su wajen samar da taken takardar, saboda saƙon da muƙalar take ɗauke da shi ya isa ba tare da gargada ba . Kalmomin da aka bayyana ma’anarsu sun haɗa da:

Ø    Balbela: Wata irin tsuntsuwa fara fat mai yawan bin shanu, CNHN (2006:33). Sai dai Mustapha, (2016:104) ya bayyana balbela da cewa: “Wata tsuntsuwa ce fara da ba ta cika girma sosai ba. Tana rayuwa a kusa da bakin ruwa kuma tana kiwo a jikin shanu, saboda kaska da take samu a jikinsu.” Kasancewar balbela a ɗaya daga cikin tsuntsayen da ke rayuwa a wuraren da ke da dausayi a ƙasar Hausa, shi ya ba ta damar ma’amala da shanu, saboda amfanuwa da take da kaskar da ke jikinsu. Wannan ya sanya Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya buga misali da ita a lokacin da yake yabon Alhaji Usman Shehu Shagari (Tsohon shugaban ƙasar Nijeriya).

 Jagora : Alhaji Musa na ci dariya,

 : Na koma na yi mamaki,

 : Sannan kuma na ga tausan maza,

 : Siyasag ga wadda taz zarce,

 : Don ga wasu sun ci zaɓen ƙwarai,

 : Don ga wasu sun ci ƙubeji,

 : Wasu kau tunku sunka ci,

 : Don ba su da daɗin rai daji,

 : Kuma ba su da daɗin rai birni,

 : Shi yaz zama hasken balbela,

 : Balbela idan tat taho.

 Yara : Sai ka ga jikinta zah hwari,

 : Amma cikin naman nan nata zab baƙi.

 Gindi : Baban Habibu Shugaban Ƙasa,

 : Alhaji Shehu ka buwai maza.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Alhaji Shehu Aliyu Shagari).

Ø    Kare: Wata dabba mai ɗamammen ciki wadda girmanta ya yi na akuya; tana da yawan faɗa da haushi; akan yi farauta ko zuwa kiwo ko tsaron gida da ita; haka kuma Musulmi ba sa cin namanta, yana da sunaye daban-daban dangane da launi kamar su: Dirwa ko bule ko jatau ko bare ko duna, da sauransu, CNHN (2006: 234). Muhammad, (2015: 33) ya nuna rungumar addinin Musulunci da Hausawa suka yi ta taimaka saboda ƙa’idojin da Addinin ya tanada ga masu yin ma’amala da kare. Wannan ya sa wasu ba su ɗauki kare da wani mahimmanci ba. Makaɗa Ɗanƙwairo yana cewa:

 Jagora : Da kare da agola da karuwa,

 : Duc ci da su ba ya da lada.

 Gindi: Jikan Mamman na Ɗanzagi,

 :Mai Tcahe sannu da rana.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Sarki Tsafe).

Ø    Shanu: Jam’in wata dabbar gida mai ƙahonni da tozo da jela mai gashi; ana cin namanta a kuma sha nononta; kuma ana amfani da ita wajen noma,CNHN (2006:379). Newman (2020:219) ya yi la’akari da kashe-kashen dabbobi, inda ya bayyana shanu a matsayin jam’i na sa wanda kuma suke cikin rukunin dabbabin gida wato, “Cattle pl. of sa anda saniya.” Kodayake, Muhammad (2015:25), ya lissafa shanu a cikin dabbobin gida, saboda tarayyarsu da Bahaushe a gidansa.

Ø    Al’ada: Masana da manazarta sun fassara ma’anar kalmar al’ada gwargwadon ikonsu. CNHN (2006:9) ya fassara ma’anar al’ada da hanyar rayuwar al’umma.” Bunza (2006:xxxii) ya bayyana cikakkiyar ma’anar al’da da cewa: “Al’ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗan’adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. A ko’ina mutum ya samu kansa duk wata ɗabi’a da ya tashi da ita tun farkon rayuwa ya tarar a wurin da ya rayu, ko yake rayuwa, ita ce al’adarsa da za a yi masa hukunci a kai. Babu wata al’umma da za ta rayu a doron ƙasa face tana da al’adar da take bi, kuma da ita ake iya rarrabe ta da wata da ba ita ba.” Bisa fahimtar waɗannan ma’anoni, wannan maƙala tana da ra’ayin al’ada ita ce, gangar jikin dukkanin rayuwar ɗan’adam.

Ø    Roƙo: CNHN (2006:374) ya fassara ta da: “Sana’ar maroƙa ta yi wa mutane kirari ko yabo a yi musu kyauta, ko kuma nenan kyauta daga wani. A wannan takarda, kalmar roƙo tana da ma’anar neman wata kyautar biyan buƙatar rayuwa ta wani abu da za a iya ganinsa ƙarara daga wajen wani wanda yake da damar bayarwa a dalilin wata waƙa da wani mawaƙi ya rera masa.

Ø    Mawaƙan Baka: La’akari da yadda manazarta da su kansu mawaƙan sukan ambaci mai gudanar da kiɗa da waƙa da sunan makaɗi ko kuma mawaƙi[1]; wannan takarda ita ma ta bi sahun wannan tunanin duba da kalmomin guda biyu duka dodo ɗaya suke wa tsafi. Sakamakon haka, Gusau (2008:110) ya bayyana ma’anar kiɗa da: “Yin waƙa tare da kaɗa ko buga wani abu mai ba da amo ko sauti. Ashe ke nan, makaɗan baka, mutane ne waɗanda suke yin kiɗa da waƙa da fatar baki.” Duk da yake wannan ma’anar ba ta fito da ƙudurin takardar sosai ba, amma ma’anar da binciken Daura (2023:148) ya bayar shi ne ya dace da ƙudurin wannan takarda. Binciken yana da ra’ayin: “Waƙa hanya ce ta isar da saƙo cikin nishaɗi/raha da ake rerawa domin ƙara wa saƙo armashi.” Gwargwaddon bayanin ma’anonin da suka gabata, wannan takarda tana da ra’ayin mawaƙan baka su ne mutanen da suke isar da saƙonsu ga al’umma ta hanyar zaɓen kalmomi da sarrafa su cikin azanci da hikima da kuma raujin murya tare da amfani da wani nau’i na kayan kiɗa domin samun nishaɗin waɗanda ake isar wa saƙonnin.

3.0 Hanyar Ɗora Bincike

Kasancewar hanyar ɗora aiki a matsayin wani tunani na masana da aka gina shi a kan ilimi da ke da manufar yin jagora game da yadda za a jingina aiki daidai da fahimtar magabata. Wannan bincike an ɗora shi a kan tunanin Bahaushe da ke cewa: “Kowace ƙwarya tana da abokiyar burminta.” Sakamakon kowane abu da mawaƙi yake buƙata akwai nau’in dabarar da yake amfani da ita domin daidaita kalmomin ɗiyan waƙoƙinsa su dace da abin da yake nema. Idan an lura, dabarar da mawaƙa suke amfani da ita wajen ƙulla ɗiyan waƙoƙinsu ta fuskar roƙon wani abu a wajen Sarki ko mai riƙe da muƙamin sarauta, sun bambanta da yadda suke amfani da su ga masu sana’a ko attajirai ko malamai. Hakan ya nuna a wurin mawaƙan baka na Hausa, kowane mutum yana da nau’o’in kalmomin da suke amfani da su a lokacin da suke roƙonsa. Ke nan, gaskiyar Hausawa da sukan ce: “Wurin da fata ta fi taushi nan akan mayar da gaban jima.”

3.1 Hanyoyin Bincike

A ƙa’idar ilimi, akan bayyana wurin da aka naƙalto shi domin kauce wa abin da Hausawa ke cewa: “Jita-jita hadisin Bamaguje.” Sakamakon haka, hanyoyin da wannan bincike ya yi amfani da su domin farauto bayanai sun haɗa da:

a. Sauraren waƙoƙin mawaƙan baka daga bakin maƙagansu waɗanda aka taskance su a cikin ma’adanar tattara bayanai ta memori.

b. Nazarin ayyukan da aka taskance na waƙoƙin baka waɗanda suka haɗa da na: Gusau (2002, 2008, 2009, da kuma 2019) da Bunza (2009) da kuma Bunguɗu (2020). An yi haka ne domin a ƙara daidaita akalar abin da ke rubuce da kuma abin da mawaƙan suka rera. Bugu da ƙari, wannan dabarar, ta haska wa binciken fahimtar yanayin al’adun da mawaƙan suke amfani da su a lokacin da suke roƙon wani abu. Haka kuma, an samu damar yin ido biyu da wasu ayyuka da aka gudanar a matakai daban-daban waɗanda suka haɗa da na digiri na ɗaya da na biyu da kuma na uku. Wasu daga cikin waɗannan ayyuka sun haɗa da: Hassan (2013) da Dunfawa (2015) da kuma Daura (2023) Haka kuma an samu damar kaiwa ga wasu mujallu da muƙalun da suka haɗa da na: Shinkafi, (2003) Muhammd, (2015) Ibrahim, (2015) Mustapha, (2016) da kuma Sifawa, (2019).

c. Bugu da ƙari, an samu zarafin leƙa wasu littattafai wallafaffu masu alaƙa da binciken da aka gudanar. An samu waɗannan kayan aiki ne a ɗakunan karatun Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato da kuma wurin wasu ɗaiɗaikun mutane.

d. Binciken bai yi ƙasa a guiwa ba wajen tuntuɓar masana waƙoƙin baka da masana al’ada da kuma wasu makusantan mawaƙan baka ta hanyar amfani da wayar hannu, domin daidaita akalar aikin.

4.0 Waiwayen Tarihin Samuwar Waƙa da Rabe-raben Mawaƙan Baka na Hausa

 Gano asalin abu ko tushensa wanda musamman aka ce ba a san lokacin da aka fara shi ba, abu ne mai matuƙar wuya, sai dai a yi hasashe a bayyana abin da ya sauƙaƙa. Ayyukan masana irin su Yahaya da wasu (1992:22) da Gusau (2003:1 da 2008) sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen lalubo wani abu game da tarihin samuwwar waƙar baka a wurin Hausawa. Wasu daga cikin waɗannan hasashe nasu ya haɗa da:

Hasashe na farko da ke cewa, waƙa ta faro ne daga hasken da aka samu na tsarin tsofin daulolin Afrika ta yamma, wato, Mali da Songhai. An danganta wannan zance ne da faruwar waƙa a ƙasar Hausa saboda ganin cuɗanyar da aka samu tsakanin sarakunan ƙasashen, musamman lokacin mulkin Sarki Askiya Muhammadu Ture (1493-1508) na Songhai. Sannan da ganin yadda wasu kayan kiɗan na waɗannan daulolin suka yi kama da na ƙasar Hausa, kamar su taushi da tambari da dundufa.

 Hasashe na biyu kuwa cewa ya yi, waƙa ta samu ne saboda ƙangin bautar iskoki da dodanni, musamman ta hanyar kiraye-kirayen da ake yi musu. Hasashe na uku kuwa, wanda shi ne aka fi yarda da shi cewa ya yi, waƙa ta faro ne sakamakon hasken kirare-kiraren da ake na farauta da na noma da kuma na yaƙe-yaƙen da suka haddasu a tsakanin ƙabilun Hausawa. A ƙauli na huɗu kuma ana ganin, waƙa ta samu ne daga wani mutum “Banu Sasana” wanda a wata fassara ana cewa, shi ne Hassanu ɗan Sabitu, mawaƙin jahiliyyar Larabawa, wanda daga bisani ya musulunta bayan bayyanar Annabi Muhammadu (S.A.W.).

 Ta fuskar kashe-kashen mawaƙa kuwa, Junaidu da ‘Yar’aduwa (2007:92) suna da ra’ayin gida biyar suka kasu[2]. Amma Dunfawa (2015:258) ya gano kason makaɗa ya tashi daga guda shida zuwa bakwai. Kodayake, Bunza (2013:41) ya tabbatar da cewa, masana sun karkasa mawaƙan baka bisa ga tsari uku:

a. Na farko, wasu suna kallon mawaƙa ta fuskar kayan kiɗansu.

b. Na biyu, wasu suna kallonsu ta fuskar abubuwan da suke yi wa waƙa.

c. Na uku, wasu suna kallonsu ta fuskar jigogin waƙaoƙinsu.

Bayan wannan rabe-rabe, sai suka sake karkasa mawaƙan zuwa:

a. Makaɗan maza

b. Makaɗan sarauta

c. Makaɗan jama’a

d. Makaɗan sha’awa

e. Makaɗan ban-dariya

f. Makaɗan sana’a

g. Makaɗan tankiya

h. Makaɗan gayya

i. Makaɗan buki

j. Makaɗan zamani[3]

5.0 Roƙo da Ƙunshiyarsa a Waƙoƙin Baka na Hausa

Ga al’adar Hausawa, suna kallon roƙo a matsayin gazawa. Haka kuma, rungumar Musulunci da Hausawa suka yi, ya ƙara sanya ƙyamar roƙo a gare su saboda faɗakarwar da addinin ya yi dangane da makomar mai gudanar da shi. Wanda hakan bai hana samun waɗanda ya zama hanyar neman abincinsu ba, saboda gadarsa da suka yi ko kuma a dalilin sha’awa. Don haka, wasu mawaƙan baka na Hausa suke haɗa roƙo da wasu sana’o’i kamar noma da kiwo da sauransu. Sai dai wasu mawaƙan baka na Hausa sukan yi fatan jingine waƙa (roƙo) kafin ƙarshen rayuwarsu. Hakan ya sa (Dr.) Mamman Shata Katsina yake cewa:

 Jagora: In ba ya da kai Bashar Ɗansanda,

 : Da na daina ɗan-ɗan-ɗan.

 Gindi: Kwana lahiya mai Daura,

 Jikan Audu gwauran giwa.

(Mamman Shata Katsina: Waƙar Sarkin Daura).

Ƙyamar roƙo da Hausawa ke yi, shi ya sa suke da maganganun azancin da ke nuna irin kallon da al’ada ke yi masa. Wasu daga cikinsu sun haɗa da:

a. Guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni.

b. Kowa da haɓarsa yake tagumi.

c. Idan da kwaɗayi da wulaƙanci.

d. Kowa ya hau motar kwaɗayi, za ta sauke shi a tashar wulakanci,

e. Zakaranka raƙuminka.

f. Kowa ya yi salla da karatunsa. d.s.

A tunanuin Bunza (2009:123), sunan kowane irin makaɗi maroƙi, idan kuwa maroƙi bai yi roƙo ba me zai ci? Su kansu makiɗan sukan kira kiɗa roƙo, kuma suna gudanar da shi ne saboda su samu wani abin biyan buƙatar rayuwa. Hakan ta sa Makaɗa Aliyu Ɗandawo Shuni yake cewa:

 Jagora: Ni roƙo yak kawo ni,

 : Ba zama makaranta ba,

 : Ba riƙon birni ba,

 : Ba ni dillanci,

 : Ban taho hito jirgi ba.

 Yara : Abin da ya kawo ni,

 Dag gabas shi niy yi.

 Gindi : Gadan-gadan yay yi dawo uban Hassan mahawayi,

 : Muhammadu Abdullahi danni mai ƙarhi.

(Aliyu Ɗandawo Shuni: Waƙar Sarkin Yawuri Muhammadu Tukur).

Wannan ya nuna ga al’adar mawaƙa, sukan kira waƙa roƙo, wani lokaci sukan ambaci kiɗa roƙo. Makaɗi na da damar kai-tsaye ya ce, a ba ni abu kaza, ko kuma ya yi nune a kan haka domin a gane roƙo yake yi. Hakan ta sanya Makaɗa Nabuddigau yake tabbatar da kiɗa shi ne roƙo, a inda yake cewa:

 Jagora : Ka bi sannu,

 : Na gaya ma tun ɗazu,

 : Na ce garin neman kwalliya idanu ya makance,

 : Ni na ce, da allo na wuce gabas,

 : Ina tabka karatu ban ga mai ba ni kwabo ba,

 : In ka lura faskaren ne na fasa,

 : Kawai na sai gangar roƙo.

Jagora : Ka ganni tun ina yawo kasuwa,

 : Ana ba ni kashin gyaɗa su rogo,

: Masa karen rake na tara su.

(Abdu Nabuddigau: Waƙar Gambara).

A nan makaɗa ya nuna ƙarara kiɗa shi ne roƙo. Hakan ya sa ya jingine allonsa na karatu saboda ba ya iya roƙo da shi, sai sayi gangar kiɗa domin ya sami kuɗi. Ke nan ya tabbatar da irin tagomashin da yake samu na kyauta a kasuwa saboda roƙon da ya fara. A wani hanzari ba gudu ba, Abubakar, (2015:365) yana da ra’ayin akwai maroƙa iri biyu: Masu yin roƙo da kayan kiɗa da kuma masu yin roƙo da baki kawai. Fahimtarsa ta yi daidai da ta Makaɗa Ɗanƙwairo Maradun inda shi ma ya raba maroƙa zuwa gida biyu, wato masu kiɗa da waƙa da kuma masu roƙon baki (waɗanda ba sa roƙo da kiɗa ko waƙa, sai dai da baki). Ga abin da yake cewa:

 Jagora : Ku masu kiɗa da waƙa,

 : To har da ku masu roƙon baki,

 : Da nit tambaye su Ɗanƙwairo,

 : Ga Sardauna Amadu ya hurce,

 : Shin yanzu wa za a yi wa sardauna?

 Yara : Sun ce a bai wa Bello ad daidai.

 Gindi : Sardauna Bello,

: Mai sulken yaƙi ya hi gaban wargi.

 (Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Bello Maitama Yusuf).

Dangane da kashe-kashen roƙo ta fuskar masu nazarin salon adabi kuwa, Ahmad da Isma’il, (2023:300) suna ganin roƙo yana da sigogi guda biyu da suka haɗa da: Siga ta kai-tsaye da kuma siga ta kaikaice. Bunza (2009:123) ya klli roƙo a farfajiyar al’ada, inda ya yi la’akari da yanayin yadda makaɗan fada suke aiwatar da shi. Hakan ya sanya ya raba shi zuwa nau’o’i huɗu. Duk da haka, wannan takarda tana ganin akwai buƙatar a ƙara duban nau’o’in roƙo a bakin mawaƙan baka, inda ya yi la’akari da yanayin halayyarsu a lokacin da suke gudanar da waƙa. Sakamakon haka take ganin kamata ya yi rabe-raben roƙo ya zama zuwa nau’o’i biyar kamar haka:

i. Roƙo kai-tsaye

ii. Nune ga abin da ake so

iii. Zugar roƙo

iv. Godiyar gabanin kyauta

v. Roƙon huce takaicin kyauta

Domin gano wurin da salka take yin tsatsa, sai a biyo bayanan da aka tanada na fashin baƙin waɗannan nau’o’i na roƙo.

5.1              Roƙo Kai-tsaye

 Wannan nau’i na roƙo mawaƙan baka sukan yi shi ne ta hanyar bayyana abin da suke nema ɓaro-ɓaro ba tare da jin tsoro ko kunya ba. Bunza (2009:124), ya nuna a wannan nau’i, makaɗin kai-tsaye zai ce a ba ni abu kaza, kamar ya ce a ba shi mota ko doki. Irin wannan nau’in roƙo, makaɗan kan ambaci abin da suke nema ƙarara ba tare da wata dabarar da ba kowa ne zai iya ganewa ba. Misalin ɗiyan waƙoƙin da ke ɗauke da wannan dabarar al’adar roƙo sun haɗa da:

 Jagora : E.O na taho kiɗi,

 : An ce ka yi sabuwar mota,

 Yara : Ba ni tsohuwa tun ba ka saisuwa ba,

: In ka saisuwa Baba ɗebo min rabona.

 Gindi : Bai ɗau wargi ba Audu,

: Ku zo mu ga Madawaki

 (Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Madawaki Abdu).

A wannan muhalli, makaɗa ya nuna kai-tsaye ya taho roƙo ne saboda buƙatarsa ta samun kyautar mota ko kuma wani abu daga cikin kuɗin da aka sayar da ita. Idan an lura, a wannan nau’in roƙo makaɗa Sani Ɗandawo ya bayyana abin da yakawo shi ƙarara. Haka abin yake a lokacin da Makaɗa Salihu Jankiɗi yake buƙatar a biya masa kuɗin kujerar zuwa aikin Haji, kamar yadda ya ce:

 Jagora : Alu Makaman Bida da Isa Kaita.

 Yara : Da Sarkin Gwamba ku taimaka,

 : Ku kai ni can Hajji in yo salla.

 Gindi : Ga darajja Amadu Bello,

 : Da arzuƙi na mazan jiya yay yi.

 (Salihu Jankiɗi: Waƙar Sardaunan Sakkwato).

A wannan nau’in dabarar roƙo, makaɗa kai-tsaye ya nemi a biya masa kuɗin tafiya Makka domin ya je ya sauke farali (aikin Hajji). Haka kuma, Makaɗa Kassu Zurmi ya roƙi kayan sawa na sutura kai-tsaye a lokacin da yake yi wa tauraronsa waƙa kamar haka:

 Jagora: Taƙamad da nikai,

 : Sale na da rai na Gidan Goga,

 : In na ga ba ni da riga zuwa nikai,

 : In na rasa wando zuwa nikai,

 : Kyawon makaɗi a ba shi riga,

 : Girken gabas da kufta,

 : Na Amadu Gogan dare,

 : Kana hwasa karnai duguzuma,

 : Sai ka ji ya bugi karanka ya yi “Hai !”

 Jagora: Komi roƙon mutum ana ba shi abin da ba ya so,

 : Mutane komi ƙwacin mutum,

 : Yana cim ma abin da ba ya bi,

 : Abin da nihwa hwaɗa mukai,

 : Da kaina hwa nig gani.

 (Kassu Zurmi: Waƙar Sale na Gidan Goga).

Sabon Makaɗa Kassau Zurmi da tauraronsa da yake wa waƙa ya sa shi roƙon kai-tsaye, inda ya nemi ya ba shi kayan sawa da suka haɗa da nau’o’in kufta da kuma girken gabas, wato babbar riga (girken Nupe ko ta Zazzau). Mamman shata Katsina ya yi amfani da wannan nau’i na roƙo a lokacin da yake yabon Shehu Tijjani, inda yake nuna cewa, yana da masaniyar wasu suna yi masa kyauta ne domin kiɗansa wasu domin waƙa wasu kuma domin yaransa. Duk da haka, shi a lokacin so yake a gaggauta ba shi kyauta saboda wanda yake wa waƙa. Ga abin da yake cewa:

Jagora : Ka san waɗansu sui mani dan waƙata,

 : Waɗansu sui mani don yarana,

 : Waɗansu ko sui mani dan gangata,

 : Wannan duk a aje gangar nan,

 : Ku sammani don darajar Tijjani.

Jagora/Yara : ‘Yan’uwa a sammani dan darajar Tijjani,

Danginmu a sammani dan darajar Tijjani.

 Gindi : Domin Sayyadina Tijjani.

(Dr. Mamman Shata Katsina: Waƙar Shehu Tijjani)

Irin wannan nau’i na roƙo, makaɗa Amali Sububu ya yi wa Musa raƙumin Daji, lokacin da ya kai masa hirar waƙa, inda ya nemi ya ba shi raƙumi ko doki ko kuma abin hawan zamani, wato, honda ko besa. Ga abin da yake cewa:

 

Jagora: Goje raƙumin yaka sai min,

 : Shi nir roƙa.

Yara: Kai a sai ma doki,

 : Shi ad daidai.

Jagora: Ko ya sai man honda,

Yara: In hau daidai.

Jagora: Ko ya saiman besfa,

Yara: In hau da ita.

Gindi: Na taho in gaisai ya aika man,

 Raƙumin daji bai zauna ba.

(Amali Sububu: Waƙar Musa Raƙumin Daji).

Wannan nau’in roƙo da aka tattauna ya nuna mawaƙan baka suna amfani da shi a al’adarsu, saboda roƙon wani abu da suke nema ba tare da ɓata lokaci ba. Kasancewar mawaƙa mutane masu kaifin basira, akwai nau’o’in roƙon da ba sa bayyana abin da suke nema ƙarara, irin wannan roƙo shi ake kira da nune ga abin da ake so. Ga yadda abin yake.

5.2              Nune ga abin da Ake So

A nan kuma, mawaƙan baka sukan sarrafa kalmomin ɗiyan waƙoƙinsu ta yadda ba za su nemi a ba su wani abu ko nuna wa wanda suke wa waƙa ƙarara ga abin da suke nema kai-tsaye ba, sai dai su yi nuni ga abin da suke so, ta yadda daga an ji za a gane su. Hakan ya sa Bunza (2009:124) yake ganin ƙwarewar makaɗi da iya maganarsa ne sukan sa ya sarrafa roƙo ba tare da ya ambaci roƙon ba, amma ya yi abin da za a gane kuma ya burge. Misalin wannan nau’i na roƙo ya haɗa da wanda (Dr.) Mamman Shata ya yi a lokacin da yake yabon Alhaji Wili Jallo, ga yadda ya ce:

Jagora : Ka dai ba ni kuɗi ɗan Shehu,

 : Ka ban sutura ɗan Shehu,

 : ka ban mota ɗan Shehu,

 : Baba ka kai ni ƙasashen Turai!

 : Tun ban tad da iyayena ba.

Jagora : Sha’anin duniya shiga da fita ne,

 : Duk in mun mutu sai tarihi,

 : Sai yara na baya su mai da abin tarihi.

 Jagora : Baba ka kai ni ƙasar Turawa,

 : In je in ga maƙera mota,

 : In tafi in ga maƙera fijo,

 : In ga wurin da ake marsandi,

 : In ga wurin da ake bilhodi,

 : In tad da wurin da ake tayota,

 : In ɗauki guda da ɗumi in ɗauka,

 : Baba in zaɓi guda da ɗumi in ɗauka,

 : Idan na je gaba can ta huta.

 Gindi : Wili Ɗan’usman Salgare.

(Dr. Mamman Shata Waƙar Wili Ɗan’usman Salgare).

Wannan muhalli, makaɗa yana roƙon a saya masa sabuwar mota fil nau’in ƙirar da ake ya yi a zamanin (ƙirar fijo ko marsandi ko bilhodi ko kuma toyota). Hakan ya sa yake neman a kai shi ƙasar Turai domin a sayo masa ita daga kamfanin da ake ƙerawa. Domin kar a ga kwaɗayinsa sai da ya nuna godiyarsa da irin kyautukan da aka yi masa a baya. Sai dai yana buƙatar kyautar da za a yi masa ta gaba ta zama ta kaiwa ƙasar waje ce domin ya samo sabuwar motar da ake yayi. Irin wannan nune ga abin da ake so, shi Makaɗa Sani Sabulu ya yi a lokacin da yake wa karuwai hannunka-mai-sanda, ga abin da ya ce:

Jagora : Karuwai ban hana ku yin dadiro ba,

 : Kun tashi za ku yin dadironku,

 : Na so ku dinga zaɓen na kirki,

 : don ku samu atamfa ta ɗauri,

 : In kun ganen kuna ‘yan min naira.

 Jagora : Kuma karuwa mai dadiro da ƙanƙu kin taɓe,

 : Na tabbatar kina hanƙurin yunwa,

 : Kuma kina da ƙoshin talauci,

 : Ba mai kiɗa ba ko mai alburda,

 : Ya zo wajenki bai amsar naira.

(Sani Sabulu: Waƙar Mai Dadiro).

Ke nan, shi a wurinsa ba dadiro yake ƙyama ba. Babban abin da yake ƙyama ita ce rowa. Don haka yake nuna musu nau’o’in kyautar da yake so (kyautar kuɗi). Ke nan yana nune ga karuwai su riƙa ba shi kuɗi idan yana waƙa. Haka aka yi da Makaɗa (Dr.) Narambaɗa, inda yake yabon irin alfarmar da ya samu a wurin maigidansa Sarkin Gobir na Isa. Duk da godiyar da ya nuna, ya nuna yana buƙatar a ba wa matar ɗansa Kurma saniya, saboda ita kaɗai ce ba ta da ita, amma saboda kunya sai ya ƙi roƙa da kansa, sai ya bar yaransa (masu yi masa karɓi) suka roƙa. Sakamakon maganar Hausawa da ke cewa: “Mai kyauta surukin mai amsa.”

Jagora : Amadu naka lokaci da yawa nai komai.

Yara : Zamanin na aje kuramen saunan gero,

 : Manyan riguna akwwai ƙarfe nai shanu,

 : To bana doki bakwai garan har barga nay yi.

Jagora : Ah duk matan gidanmu sun saye ƙoren tatsa.

Yara : To, kowace na da nata saura matar kurma.

Gindi : Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa,

 : Baban dodo ba a tamma da batun banza.

(Dr. Ibrahim Narambaɗa: Waƙar Bakandamiya).

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi irin wannan roƙo na nune ga abin da ake so a lokacin da yake yabon Ciroman Katsina, inda ya ce:

 Jagora : Ɗanƙwairo na yi mafarki.

 Yara : Ina jin ƙarar injin ko mota za a ba ni,

 : Albarkacin Ciroma Ƙwairo an ba ka mota,

 : An koma an ba ka mota,

 : Sai Alhaji Bukar Mandara,

 : Ya ce ya ba ka mota,

 : A. A. Abubakar Hamza ga naira dubu da yab ban.

 Gindi : Mai ban tsoro sadauki,

 : Hassan ɗan Shehu Malam.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Hassan Usman Katsina).

 Kasancewar mawaƙa mutane masu kaifin basira, a wani lokaci kuma, sukan fake da zuga su shigar da saƙon wani abu da suke roƙa. Irin wannan ɗabi’a ita ta sanya aka tabbtar da wani nau’in roƙo da ake kira da zugar roƙo.

6.0 Zugar Roƙo

Wannan nau’i na roƙo kuma ana kallonsa a wata dabarar da mawaƙi ba ya faɗin abin da yake roƙo kai-tsaye; kuma sannan ba nune zai yi a kan abin da yake roƙo ba. Sai dai, zai dai zuga uban gidansa ta fuskar roƙo, ga haƙiƙani zuga ce, amma kuma ga fashin baƙin manazarci ya san roƙo ake yi. Misalin irin wannan nau’i na roƙo shi ne:

Jagora : Mai kyautar manyan riguna,

 : Mai kyauta da dawakin Azbin,

 : Amma lokaci ya canza.

 Yara : An koma ga kyautar mota,

 : In Allah ya ce a yi min x 2.

Jagora/Yara : Mota abin hawan zamani,

 : Allas sa Mamman ya yi min.

 Gindi : Muhammadu Cindo bi da maza,

: Malam ɗan Mamman bajimi.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Sarkin Keffi).

A wannan ɗiyan waƙa, makaɗa yana roƙon mota ne, amma sai da ya zuga Sarki a kan cewa, kyauta tana daga cikin al’adarsa. Sakamakon haka sai yake nuna shi dai ba zai iya cewa Sarki ya ba shi mota ba, amma tun da al’adarsa ce kyauta, saboda haka yake roƙon Ubangiji ya sa a irin kyautar da Sarkin zai ba shi a ce mota ce. Haka a bin yake a lokacin da (Dr.) Narambaɗa ya je gidan Alƙali Abu neman abin da zai yi larurar bukin salla. shi ne yake nuna girman gidan ya wuce a ce ka tafi, a aiko maka, shi ya sa ya ce ya san ba zai tafi daban kayan da ya roƙa daban ba.

 Jagora : Abin salla shi nab biɗa,

 : Da abin yanka da abin miya.

 Yara : Alƙali in kau ya jiya,

 : na bar tahiya bamban da su.

 Gindi : Ya ɗau girma ya ɗau yabo,

: Mu zo mu ga Alƙali Abu.

(Dr. Narambaɗa: Waƙar Alƙali Abu).

Irin wannan zugar roƙo Ɗanƙwairo Maradun ya yi wa Sarkin Kano Alhaji ado Bayero inda ya ce:

 Jagora : Sarki mai kyautar doki,

 : sarki mai kyautar riguna,

 : Sarki mai kyautar wanduna,

 : Sarki mai kyautar kuftoci,

 : Sarki mai kyautar alkyabba,

 : Sarki mai kyautar rawunna,

 : In dai yai maka kayan ƙawa,

 : Ya miƙa ma kuɗɗi fam ɗari,

 Yara : Abin shagali ya samu.

 Gindi : Ba ta kura kaurin gaba,

 : Na yarda da Sarki Ado.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Sakin Kano).

6.1              Godiyar Gabanin Kyauta

Ga al’adar wasu mawaƙan baka, sukan gabatar da godiya gabanin a ba su kyautar da suke roƙo. Suna yin haka ne domin su ƙara wa wanda suke roƙon ƙaimi wajen yi musu kyauta. Wannan dalili ya sa sukan ƙulla kalmomin yabo tare da neman agajin yaransu kan su taya su godiya dangane da kyautar da aka yi musu, tare da cewa kyautar ba ta zo ba. Misalin wannan a ɗiyan waƙoƙi sun haƙa da:

 Jagora : Ɗanƙwairo na yi mafarki.

 Yara : Ina jin ƙarar injin ko mota za a ba ni,

 : Albarkacin Ciroma Ƙwairo an ba ka mota,

 : An koma an ba ka mota,

 : Sai Alhaji Bukar Mandara,

 : Ya ce ya ba ka mota,

 : A. A. Abubakar Hamza ga naira dubu da yab ban.

 Gindi : Mai ban tsoro sadauki,

 : Hassan ɗan Shehu Malam.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Hassan Usman Katsina).

Bayan da makaɗa ya yi nune ga abin da yake so, inda ya nuna ya yi mafarkin mota, sai kuma ya riƙa bayyana godiyarsa ga wasu mutane saboda kyautar motar da ya tabbata za su yi masa tun kafin su ambata kyautar. Haka makaɗa Ɗanƙwairo ya yi ga sarkin Ƙayan Maradun domin a lokacin da yake roƙon kyautar doki da kuma hatsi.A nan ne makaɗa ya nuna a duk shekara yana ba shi dame dubu. Duka wannan, wani nau’in roƙo ne na nuna godiya tun gabanin a yi kyauta.

Jagora : Ya ban doki huɗu,

Yara : Da manyan riguna,

 : Ƙwairo ka yi godiya,

 : Sannan kowace shekara,

 : Yana ba ni dame dubu.

 Gindi : Ye magai,

  : Ɗangarba na Garkuwa.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Sarkin Ƙayan Maradun).

Irin haka ta kasance da Makaɗa Abdu Wazirin Ɗanduna a lokacin da yake roƙon kayan hidimar bukin hawan salla.

 Jagora: Na Nana hakimi mai kyautad dokuna,

 : Ya ba ni doki ga rigar hawa,

 : In don ta ni ko yau salla ta zo,

 : Sarki ya hau doki ni ma in hau,

 : In ɗan tsaya Sarki ya wuce gaba,

 : Mu ko mu bi shi a baya da tambura

 : Sarki sai tambura.

 Gindi : Sarkin Ƙaraye Abubakar.

(Abdu Wazirin Ɗanduna: Waƙar Sarkin Ƙaraye).

A hannu guda kuma, wasu mawaƙan kan yi amfani da wannan nau’i na roƙo inda sukan bayyana wata kyauta da suke nema cikin sigar da takan nuna an yi. Sai dai lokacin da suke bayyana kyautar, sukan yi ƙarin lamba dangane da abin da aka ba su ɗin. Irin wannan ɗabi’a ta mawaƙa ce Makaɗa (Dr.) Narambaɗa ya nesanta kansa da ita lokacin da yake cewa:

 Jagora: Yanzu na aje ƙarya in ina kiɗi,

 : Na bar wargi in ina kiɗi,

 : Tun da nai sittin saba’in nika hwaɗi,

 : Mai saba’in yai ƙarya.

 Yara : Ana ta zunɗe nai,

 : Ko yaran da ag garai wawwatce mishi sukai,

 :Yana yawo shi ɗai baram-baram.

 Gindi: Ya ci maza yakwan yana shiri,

 : Jan zakara dodo na Umaru.

(Narambaɗa: Waƙar Sarkin Isa).

A wani lokaci kuma, akan samu wani abu ya tusgo, wanda yakan sanya mawaƙa yin roƙo ga wasu iyayen gidansu domin ɗebe takaicin wata damuwwa da suke ciki. Sukan yi haka ne domin ƙara tabbatar wa wanda suke roƙon matsayinsa a wurinsu, dangane da tabbacin da suke da shi na fitar da su kunya. Wannan nau’i na roƙo shi aka raɗa wa suna da:

6.2              Roƙon Huce Takaicin Kyauta

Wannan nau’i na roƙo dai, mawaƙan baka suna yin sa ne domin su bayyana wani abu da yake ci musu tuwo a ƙwarya (ya dame su) da nufin samun ɗaukinsa da gaggawwa daga wurin wanda suke wa waƙa. Sai dai ba kowa suke yi wa wannan roƙo ba sai wanda suke da kusanci da shi matuƙa. Wannan dalili ya sa akan ji kalmomin da suke nuna fushi ko karaya dangane da wani abu maras daɗi da ya bijiro musu. Misali,

 Jagora : Turaki ka ba ni kyautar doki.

 Yara : In za ka ban kuma,

 Jagora : Ihm!

 Yara : Sa a kirawo ni Baba sai na zaɓa.

 Jagora : ‘Yan Sarki sun rena mutane,

 : ‘Yan Sarki sun rena mutane,

 : ‘Yan Sarki sun rena mawaƙa,

 : Sun maishe mu ba mu san komai ba,

 : In za su ba mu kyautar doki,

 : Wai su ramamme suka ba mu.

 Yara : Ko wanda bai gani,

 : Shi ta hawaye ina bugam mai mara.

 Jagora : To in za ka ba ni sai na zaɓa.

 Yara : In na ga bai yi min,

 : Turaki ina ko sakin shi nan garkakka.

 Jagora : Baba idan za ka ba ni sai na duba,

 Yara : In na ga bai yi min,

 : Turaki ina ko sakin shi nan garkakka.

 Gindi : Ni za ni in gano,

 : Turaki Aminu wan maza na Sarkin Zazzau.

(Sani Aliyu Ɗandawo: Waƙar Turakin Zazzau).

Takaicin renin da ake yi masa, shi ya sa makaɗa ya nuna damuwarsa ƙarara ta hanyar maimaita ƙasƙantar da su da ake ta hanyar ba su abubuwwan da dace ba a matsayin kyauta idan sun yi roƙo. Idan an lura, a lokacin da makaɗa yake maimaita wannan ɗan waƙa, za a ji yadda yake nuna fushi saboda renin da ake yi musu. Domin ya nuna takaicinsa ma, shi ne yake cewa, idan dokin da aka ba shi bai yi masa ba, a garkarsa zai bar shi ya yi tafiyarsa. Mawaƙan kan yi haka ne domin huce takaicin damuwar da suke da ita. Irin wannan yanayi ya sa makaɗa Musa Ɗanƙwairo bayyana wa Sarkin Daura takaicin da yake ciki, inda yake neman ya share masa hawaye domin ya ba shi gida da gona saboda yanayin damuwar da ya shiga.

 Jagora : Allah shi ka kawo komi,

 : Yaƙin Dam na Bokolori ya ci mu,

 Jagora/Yara : Sai in hwaɗa ma Mamman,x2

 : Ban da gida yanzu ban da gona.x2

 Jagora/Yara : Yanzu cikin damana muke ta shirin,

 : Gyaran wurin da za ni bacci,

 : Yanzu gidan makaɗa ya zamo gurbi na ƙwarai,

 : Wanda ad da zurhi,

 : Sarkawa su sukai da taru.

 : Sarkin Daura!

 : Ko da damina sai kai ta shirin tariyab baƙinka,

 : Idan wasu sun koro mu mu taso,

 : Ba ni zama inda ban da gona,

 : Ba ni zama inda ba abinci,

 : Kaico! Ashe abin hwaɗi tudu ne,

 : Sai in ka tsallake naka,

 : ka koma hangen na wani,

 : Ai ga wasu nan,

 : Sun hana sata to amma yanzu ga su sun yi.

 Gindi : Babban jigo na Yari uban shamaki,

 : Tura haushi.

(Musa Ɗanƙwairo: Waƙar Sarkin Daura).

Haka Bawa Ɗan’nace ya ji a lokacin da ya so zuwa aikin Hajji amma bai samu wanda zai share masa hawaye ba. Don haka ya ce a faɗa wa Sardauna, yana yi masa kukan takaicin wannan damuwa tasa domin ya share masa hawaye.

 Jagora : Ina Sarkin Fada ko Zagin Sardauna?

 : Kai ka ganin Sardauna,

 : To kuma kai ka jin batun Sardauna,

 : In kaz zo gida ka ce Sardauna,

 : Ga ni inai mashi kuka,

 : Ba a maishe ni Alhajin makiɗa ba.

(Bawa Ɗan’anace: Waƙar Shago).

Haka makaɗa (Dr.) narambaɗa ya koka a lokacin da yake yi wa Alhaji Ɗandurgu waƙa, inda yake cewa:

 Jagora : Ai laihina da kai guda jikan Ila,

 : Ka gano ɗakin Kaba,

 : Ban gano ɗakin Kaba ba,

 : Ba kuɗɗi nah hi so ba,

 : Na hi buƙatar Haji,

 : Ka hau Arhwa da ni.

 Gindi : Alhaji Ɗandurgu taimako Allah ag garai,

 : Na yarda d duniya akwai namijin arziki.

(Dr. Narambaɗa: Waƙar Alhaji Ɗandurgu).

Naɗewa

A ƙarshe, mawaƙan baka a ƙasar Hausa wasu taskoki ne da ke adana al’adun Hausawa ta fuskar amfani da fasahohin bakinsu. Takarda ta mayar da hankali a kan fashin baƙin ƙunshiyar roƙo a al’adar mawaƙan baka na Hausa. Maƙalar ta yi la’akari da wasu rukunonin mawaƙan da ake da su na baka, saboda a nuna yadda suke sarrafa nau’o’in roƙo a waƙoƙinsu. An yi ƙoƙarin fito da misalai a ƙarƙashin kowane daga cikin nau’o’in roƙo guda biyar da aka bayyana. Yanayin yadda mawaƙan suke amfani da dabarar ƙulla ɗan waƙar da ke dacewa da girman wanda aka roƙa ko kuma abin da ake nema, ya tabbatar da maganar Hausawa da ke cewa: “Kowace ƙwarya tana da abokiyar burminta.” Kamar yadda hakan ya nuna, wurin da fata ta fi laushi, nan akan mayar da gaban jima. Kodayake, a ɓangare ɗaya kuma, maganar Hausawa da ke cewa: “Guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni” ta haska irin ƙyamar da al’ada ke yi wa ɗabi’ar roƙo.

Manazarta

Abubakar, A. T. (2015). Ƙamusun Harshen Hausa. Zaria: Northern Nigerian Publication Company.

Ahmad, M. I. da Isma’il, H. (2023). “Salon Roƙo a Zubin Wasu Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo.” Cikin Gusau, S. M da wasu (editoci). Studies of the Poetic Dynasty of Musa Ɗanƙwairo Ƙanen Makaɗa Kurna, Pp.297-306. Kano: WT Press Printing Publishing.

Bunguɗu, H. U. (2020). Waƙoƙin Amali Sububu. Kaduna: Sawaba Press & Publishing Co.

Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Nigeria Limited.

Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Al-Ibrash Publication Plc.

Bunza, A. M. (2012). ‘Lalurar Kixa a Bakin Makaxa: Hasashen Xaliban Al’ada Ga Makomar Waqoqin Baka.” Sakkwato: Maqalar da aka gabatar a sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Xanfodiyo.

Bunza, A. M. (2013). “An Shiga Lafiya An Fita Lafiya (Bitar Tubar Alhaji Muhammadu Gambo Fagada Mai Waƙar |arayi a Ma’aunin Manazarta Al’ada). Cikin Yakasai, S. A da Wasu (editoci), Makaɗi a Mahangar Manazarta. Pp. 35-69. Kano: Gidan Dabino Publishers.

C.N.H.N, (2006). Qamusun Hausa. Kano: Jami’ar Bayero.

Daura, H. K. (2023). “Kyauta Jarumtar Sarki: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Baka.” Cikin Tasambo Journal of Language, Literature and Culture, vol. 2, No. 1, Pp.145-153. Department of Languge and Culture, Federal University Gusau, Zamfara-Nigeria.

Dumfawa, A.A. (2003). Ma’aunin Waƙa. Sakkwato: Garkuwa Media services.

Dunfawa, A.A. (2015). “Makaɗan Zamani: Wani Ƙarin Kaso na Makaɗan Hausa.” Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies (Special Edition) Vol. 1, No.1, Pp.257-266. Department of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Xangambo, A. (1984). Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph.

Gusau, S. M. (1987). Makaxa da Mawaqan Hausa. Kano: Benchmark Publishers.

Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Waqar Baka. Kaduna: FISBAS Media Services.

Gusau, S. M. (2002). Sarkin Taushi Salihu Jankiɗi. Kaduna: Baraka Publishers Limited.

Gusau, S.M. (2008). Waqoqin Baka a Qasar Hausa: Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited

Gusau, S. M. (2019). Diwanin Waqoqin Baka Juzu’i na Huxu. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Hassan, S. (2013). “Hikimar Yaba Kyauta a Waƙoƙin Sarkin Taushi Salihu Jankiɗi.” Mujallar Zauren Waƙa (Journal of Hausa Poetry Studies) Vol. 1, No. 1, Pp.46-61. Sokoto: Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University.

Ibrahim, A. A. (2015). “Kyauta Ma’aunin Yabo a Waƙoƙin Fada na Hausa.” Kundin Digiri na Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Junaidu, I. da ‘Yar’aduwa, T. M. (2007). Harshe da Adabin Hausa a Kammale (Don Manyan Makarantun Sakandare). Ibadan: Spectrum Book Ltd.

Magaji, A. (2016). Kassu Zurmi da Waƙoƙinsa. Ibadan: Spectrum Books Limited.

Muhammd, M.S. (2015). Dabbobi a Tunanin Bahaushe.” Kundin Digiri na Uku (Ph.D). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Mustapha, B. (2016). “Adon Harshe a Adabin Baka: Nazari a Kan Amfani da Tsuntsaye a Wasu Waƙoƙin Ɗanƙwairo.” Kudin Digiri na Biyu (M.A). Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Newman, P. & Newman R. M. (2020). Hausa Dictionary( Hausa-English & English-Hausa). Kano: Bayero University Press.

Sifawa, M. B.(2019). “Malami da Malunta a Wasu Waƙoƙin Baka na Hausa” Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Shinkafi, R. H. (2003). Nazarin Jigon Roƙo Cikin Waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa.” Kundin Digiri na Ɗaya (B.A), Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Yahya, A. B. (1992). Jigon Nazarin Waqa. Kaduna: Fisbas Service.

Yahaya, I. Y., Zariya, M. S., Gusau, S. M. da ‘Yar’adua, T. M. (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare 1-3. Ibadan: University press.

Waƙoƙin da Aka Saurara

1.                  Waƙoƙin Makaɗa Salihu Jankiɗi.

2.                  Waƙoƙin Makaɗa (Dr.) Ibrahin Narambaɗa.

3.                  Waƙoƙin Makaɗa (Dr,) Mamman Shata

4.                  Waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo.

5.                  Waƙoƙin Makaɗa Sani Aliyu Ɗandawo.

6.                  Waƙoƙin Sani Sabulu Kanoma.

7.                  Waƙoƙin Abdu Wazirin Ɗanduna.

8.                  Waƙoƙin Makaɗa Bawa Ɗan’anace

9.                  Waƙoƙin Abdu Nabiddigau

Waɗanda Aka Tattauna da Su

1.                  Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, a ofishinsa da ke Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Tsangayar Fasaha, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ranar Alhamis, 10/08/2023 da misalin ƙarfe 2:30 na rana.

2. Ɗanmincika Mai gado da katifa, ranar 25/07/2023 a bakin tashar Birnin Kudu da misalin ƙarfe 5:15 na yamma.



[1] Jagora : Ku masu ki]a da wa}a,

 : To har da ku masu ro}on baki,

 : Da nit tambaye su [an}wairo,

 : Ga Sardauna Amadu ya hurce,

 : Shin yanzu wa za a yi wa sardauna?

 Yara : Sun ce a bai wa Bello ad daidai.

 Gindi : Sardauna Bello,

 : Mai sulken ya}i ya hi gaban wargi.

(Musa [an}wairo: Wa}ar Bello Maitama Yusuf).

[2] Sun nuna akwai maka]an fada da na jama’a da na maza da na mata da kuma na ban-dariya.

[3] Dunfawa (2015:258) ya tabbatar da samuwar }arin kaso na rukunin maka]an Hausa wanda ya kira shi da maka]an zamani.

Amsoshi

Post a Comment

0 Comments