Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Awon Baka a Wakar Annobar Korona Ta Khalid Imam

Citation: Rabeh, H. and Karofi, I.A. (2024). Nazarin Awon Baka a Waƙar ‘Annobar Korona’ ta Khalid Imam. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 373-377. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.047.

NAZARIN AWON BAKA A WAƘAR ‘ANNOBAR KORONA’ TA KHALID IMAM

Hassan Rabeh 1

Isah Abubakar Karofi 1

1 Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita, Dutsinma, Jihar Katsina

Tsakure

Cutar Korona cuta ce da ta girgiza duniya baki ɗaya wadda har ya zuwa yau mutane ba su gama warwarewa daga tasirin irin ɓarnar da ta haddasa masu ba. Daga cikin hanyoyin faɗakar da al’umma a kan wannan cuta ita ce amfani da hanyar adabi, musamman waƙoƙi don wayar da kai da kuma faɗakar da al’umma a game da yadda za a kare kai daga kamuwa da wannan cuta. Ɗaya daga cikin mawaƙan da suka bayar da gudummuwa ta wannan fanni shi ne Khalid Imam da waƙarsa ta Cutar Korona. An yi nazarin wannan waƙa ta hanyar yin nazarin awon baka. An yi haka ne ta hanyar feɗe waƙar da nuna karin da ta hau da kuma bayyana naƙasu ko larurorin da suka wanzu a cikin waƙar. An yi amfani da ra’i Khalili a yayin aiwatar da wannan takarda. A ƙarshe takardar ta gano larurori uku da suka wanzu a cikin waƙar; biyu daga cikinsu zihaffai ne, ɗaya kuwa illa ce.

Fitilun Kalmomi: Awo, Baka, Waƙa, Annobar Korona, Khalid Imam

Gabatarwa

Cutar korona cuta ce wadda ƙwayar cutar coronaɓirus da ake wa laƙabi da SARS-CoV 2 takan haddasa. An fara jin ɗuriyar wannan cuta a ranar 31 ga wata Disambar shekarar 2019 bayan wani rahoton kamuwar rukunin wasu mutane a Wuhan ta ƙasar Sin (China). Wannan cuta ta zamo annoba ga duk faɗin duniya. Cuta ce wadda ta haddasa rasa rayuka masu yawa da haifar da taɓarɓarewar arzikin ƙasashe da dama baya ga haddasa fargaba da kuma yin barazana ga zamantakewar al’umma a duk faɗin duniya. An yi ta samun bayanai da gargaɗi daga ɓangarori da dama na rayuwar al’umma a ciki har da ɓangaren adabin Hausawa inda mawaƙa ma ba a bar su a baya ba wajen faɗakarwa da kuma ilimantar da jama’a a kan wannan cuta. Ɗaya daga cikin mawaƙan da suka bayar da gudummuwarsu ta wannan fanni shi ne Imam Khalid.

Waƙar cutar korona waƙa ce da Imam Khalid ya rubuta domin faɗakarwa da nusar da al’umma da mu koma ga Allah maɗaukakin sarki. Waƙa ce ‘yar ƙwar biyu wadda ba ta ɗauke da amsa-amo. Waƙar tana ɗauke da baiti talatin da shida (36) waɗanda suke ɗauke da sauƙaƙan kalmomi na harshen Hausa da kuma wasu da aka yi aro daga harsunan Larabci da kuma Ingilishi.

Ganin irin muhimmanci da kuma gudummuwa da wannan waƙa ta bayar a fagen adabi ya sanya aka yi nazarin arulinta inda aka feɗe waƙar tare da yin nazarin ƙafafuwa da zihaffan da waƙar take ɗauke da su tare kuma da bayyana Karin waƙar.

2.0 Manufar Bincike

Manufar wannan takarda ita ce yin nazarin arulin waƙar ‘Cutar Korona’ ta Imam Khalid. Za a yi nazarin waƙar ne ta hanyar feɗe waƙar tare da gano karinta wato gano a bisa wane kogi aka gina waƙar. Za a yi haka ne ta hanyar gano ƙafar waƙar. Za a kuma bayyana irin illoli ko zihaffan da suka yi tasiri a ƙafar waƙar.

3.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike

Daga cikin hanyoyin da aka bi wajen aiwatar da wannan takarda akwai ta karanta waƙar tare kuma da yin fiɗar ta da kuma yin nazarin ƙafafuwa don gano karinta, sannan kuma da bayanin irin larurorin da suka wanzu a cikinta. Sannan kuma za a karanta littattafai domin samun wasu muhimman abubuwa da takardar ta ƙunsa.

4.0 Aruli

Ita dai kalmar aruli kalma ce da ta samo asali daga kalmar ‘Arudh’ ta Larabci. Wannan kalma tana nufin ilimin da ake sanin karin waƙa da shi. Da wannan ilimi ne ake tabbatar da daidaituwar karin ko akasin haka da kuma dalili ko dalilan da suka sanya karin ya fanɗare (wato ya ƙi daidaituwa). A wannan fanni ana amfani da alamomi da nufin fayyace karuruwa a cikin rubutattun waƙoƙi na Hausa. Ta wannan hanya ce ake gane waƙoƙi masu kyau da masu naƙasu.

Bello da Sheshe (2013:5) suna da da’awar cewa, “A Hausa Aruli ilimi ne wanda yake nuna hanyoyin da za a fahimci kari a waƙoƙin Hausa bisa wani ƙayyadajjen tsari, tare da irin abubuwan da ke sa wannan tsari, wani lokaci ya fanɗare”.

5.0 Ra’i

Akwai ra’o’in da ake amfani da su domin fayyace karin waƙa. Ra’in da aka yi amfani da shi a yayin wannan nazari shi ne ra’i Khalili wato yadda ake bayyana karin Bahaushiyar waƙa ta amfani da Balarabiyar hanya. Wannan ra’i Al-Khalil bn Ahmad AlFarahidhi wanda ya rayu a 706-791 CE ya samar da shi.Wannan ra’i yana danganta karin waƙar Larabci da na Hausa ta yin amfani da ƙafafuwa/sawaye masu ɗauke da gaɓoɓi, domin bayar da karin waƙa (Bello, 2015:2). 

6.0 Awon Waƙar

Dangane da awon waƙoƙin Hausa suna hawa kan karin waƙoƙin Larabci. Sanin karuruwa shi ne babban jigon awon baka. Karin kuwa, sun ƙunshi Basid, Hafif, Hajaz, Kamal, Madid, Mutadarik, Mutaƙarib, Rajaz,Ramal, Ɗawil da kuma Wafir  (Auta, 2017 sh. 151).

 

baitin waƙa

tsarin ƙafafuwa/sawaye

1

Masu gaɗa suna ta shewa,

'Yan caca da masu karta.

 

– v – v v + –  v –  –

- v +v –  v –  –

2

'Yan daudu da ma kilaki,

Sun tsere babu kowa.

 

– –vv + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

3

Tituna leƙa ka duba,

Kasuwanni har mashaya.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

4

Makarantu har sinima,

'Yan ƙwallo da masu dambe.

 

v  v –  – + –  v –  –

–  –  v v + –  v –  –

5

Sun ɓace duk don Korona,

Ko'ina duka tsit kake ji.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  v –  v v + –  v –  –

6

Ta bi Gwamna har gidansa,

Ta shaƙi wuyan Minista.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  –  v v + –  v –  –

7

Can a Ladan ga Yarima,

Ta bi shi cikin turaka.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  –  v v + –  v –  –

8

A Abuja har a Billa,

Ta shige ciki ta yi sheƙa.

 

v  v –  – + –  v –  –

–  v –  v v + –  v –  –

9

Tai ƙwayaye ta yi 'ya'ya,

Ta miƙe ƙafa a fada.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  –  v v + –  v –  –

10

Tabbas cutar Korona,

Annoba ce ta gaske.

 

–  –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

11

A masallatai da coci,

Duk an koma ga Allah.

 

v  v –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

12

Sarki mai shirya komai,

Dole ne bauta gare shi.

 

–  –  – + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

13

Ba tsumi kuma ba dabara,

Duniya yau an bi Allah.

 

–  v –  v v + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

14

Masu sheƙe aya su more,

A Italiya ko Amurka.

 

–  v –  v v + –  v –  –

v  v –  v v + –  v –  –

15

Har ƙasar Sin can a Chana,

Ta kai da yawa kushewa.

Ko Farisa har Faransa,

Ba kowa yau a titi.

–  v –  – + –  v –  –

–  –  v v + –  v –  –

–  –  v v + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

16

Kufai a kira yi Turai,

Champions League an tsaya cik.

 

–  v –  v v + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

17

Ba a yin zancen Ronaldo,

Har Messi ba batunsa.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

18

Ita annobar Korona,

Cuta ce babu shakka.

 

v  v –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

19

Ba ta kunya ba ta tsoro,

Ba ta sabo ba sanayya.

 

–  –  –  + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

20

Yau mutum ya gane cewa,

Bai da ƙarfi sai na Allah.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

21

Bai da sauran duk dabara,

Kariyarsa tana ga Rabbu.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  v –  – v + –  v –  –

22

Gatan kowa Ilahu,

Mui ta bauta mai da ɗa'a.

 

–  –  – + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

23

Ma rabauata a yau da gobe,

Don ko dai cutar Korona.

 

–  v –  v v + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

24

Wa'azi ce babu shakka,

Me je shi ke asara.

 

v  v –  – + –  v –  –

–  – –  + –  v –  –

25

Kurciya in ta yi kuka,

Saƙo nata ban da wawa,

 

–  v –  – + –  v –  –

–  v –  v v + –  v –  –

26

Bare gaula da soko.

Masu shashanci a hanya.

 

v –  – + –  v –  –

–  v –  – + –  v –  –

27

Hankali kura kira shi,

Ta yin zabari na guga.

 

–  v –  – + –  v –  –

v –  v v + –  v –  –

28

Mai rabo shi ke rabauta,

In an wa'azi ya ɗauka.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  –  v v + –  v –  –

29

Zunubansa ya nemi tuba,

Kan ya ji shi cikin kushewa.

 

v v – v v + –  v –  –

–  v –  v v + –  v –  –

30

Ni Khalid bani shakka,

Tabbas cutar Korona.

Jan kunne ce gare mu.

Mu bar saɓo da sharri.

–  –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

v  –  – + –  v –  –

31

Mu so junanmu gaske,

Hakan zai taimake mu.

 

v –  – + –  v –  –

v –  – + –  v –  –

32

Ni Imam Khalid na Indo,

Jikan Hauwa’u tabbas.

 

–  v –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

33

Na san cutar Korona,

Ƙanwa ce gun talauci.

 

–  –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

34

Wajen ƙeta da sharri,

Har ma yawo a dangi.

 

v –  – + –  v –  –

–  –  – + –  v –  –

35

Ni nan zan sanya aya,

Cikin waƙar Korana.

 

–  –  – + –  v –  –

v –  – + –  v –  –

36

Allahu kasa mu gane,

Mu tuba zuwa gare Ka.

–  –  v v + –  v –  –

v –  v v + –  v –  –

 

6.1 Bayanin Kari

A dukkan baitocin talatin da shida (36) na waƙar an samu maimaicin ƙafa ta bakwai (7) mai suna fa’ilatun (faa-i-laa-tun–  v –  –) wato:

a –  v –  – / –  v –  –

 –  v –  – / –  v –  –

b 7+7

 7+7

c faa-i-laa-tun / faa-i-laa-tun

 faa-i-laa-tun / faa-i-laa-tun

d Karin Ramal

6.2 Bayanin Larurori

An samu bayyanar wasu zihaffai waɗanda suka sauya tsarin wasu ƙafa a cikin wasu baituka na waƙar. Dukkan zihaffan sun bayyana ne a ɓangaren farko na ɗangon waƙar. Zihaffan da aka samu a wannan waƙar sun haɗa da:

6.2.1 Habni: Wannan zihafi yana ɗaya daga cikin zihaffan da suka yi tasiri a ƙafar da ta samar da karin wannan waƙar. Wannan zihafi yakan sauya doguwar da’ira ta farkon ƙafa zuwa gajera, muddin dai ba turke ne a farkon ƙafar ba. 

fa-i-laa-tun  oo o oo oo  oo o oo oo    o o oo oo  v v –  –

An sami wannan zihafi a ɗango na biyu (baiti na 1) da ɗango na ɗaya (baiti na 2 da 4 da 8 da 11 da 18 da 24) inda aka sami v v –  – a maimakon –  v –  –

6.2.2     Kaɗa’i: Ana samun wannan illa ne a lokacin da aka soke da’ira ta 3 a turke, sannan aka haɗe gajera mai zaman kanta, suka haɗu suka zama doguwar da’ira. Ana samun wannan illa ne a inda turke ya fara da gajerar gaɓa sannan doguwar gaɓa ta biyo baya. Misali: 

faa-i-laa-tun  oo o oo oo      oo o oo oo      oo o o  oo    oo oo oo. An samu wannan illa a ɗango na biyu (baiti na 2 da 11 da 17 da 18 da 24 da 32 da 34) da ɗango na ɗaya (baiti na 10 da 12 da 19 da 22 da 35) da ɗango na huɗu (baiti na 15) da ɗango na 1 da 2 da na 3 (baiti na 30) ɗango na 1 da na 2 (baiti na 33) inda aka sami  –  –  –a maimakon –  v –  –.

6.2.3    Shakali: Ana samun wannan zihafi ta dalilin haɗuwar zihafi habni da kaffi a ƙafa ta 7  oo o oo oo      oo o oo oo      o o oo oo   Habni    o o oo oo      o o oo oo    o o oo  o   Kaffi    o o oo o     v v – v     Shakali.

7.0 Sakamakon Bincike

A ƙarshen wannan nazari binciken ya nuna cewar waƙar Cutar Korona waƙa ce mai baitoci 36, ‘yar ƙwar biyu , babu amsa amon ƙarshen baiti a cikinta. Waƙa ce da ta hau Karin Ramal, wato wadda aka samu maimaituwar ƙafa ta bakwai (7) a cikinta. Haka nan kuma, an samu wanzuwar illa kaɗa’i da zihaffan habni da shakali.

8.0 Kammalawa

Wannan takarda ta yi nazarin awo ko arulin waƙar Cutar Korona ta Khalid Imam a inda aka gabatar da manufa da hanyoyin gudanar da bincike da ra’in da aka gudanar da binciken a kansa. An kuma feɗe waƙar tare da gano karinta da kuma larurorin da suka wanzu a cikinta.

Manazarta

Auta, A.L. (2017).  Faɗakarwa a rubutattun waƙoƙin Hausa. Bayero University, Press.

Bala, I. da Imam. K. (2020). Corona Blues (A Bilingual Anthology of Poetry). Whetstone Publishers.

Bello, A.(2014).Poetry, Prosody and Prosodic Analyses of Hausa Poems. Ahmadu Bello University, Printing Press.

Bello, A. (2015). Arulin Hausa a Faɗaɗe. Ahmadu Bello University, Printing Press.

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon tsari). Amana Publishers.

Yahya, A.B. (2014). Gudale Waƙar soyayya: Misalin Gazl (Ghazal) Cikin Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Garkuwan Adabin Hausa A Festschrift In Tribute To Abdulƙadir Ɗangambo. Department of Nigerian Languages, Bayero University. pp125-138.

Zaria, A.B. da Sheshe, N.I.  (2013). Arulin Hausa a Sauƙaƙe. SM Graphics Printers.

 

Ratayen Waƙar

1. Masu gaɗa suna ta shewa,

'Yan caca da masu karta.

 

2. 'Yan daudu da ma kilaki,

Sun tsere babu kowa.

 

3.Tituna leƙa ka duba,

Kasuwanni har mashaya.

 

4. Makarantu har sinima,

'Yan ƙwallo da masu dambe.

 

5. Sun ɓace duk don Korona,

Ko'ina duka tsit kake ji.

 

6. Ta bi Gwamna har gidansa,

Ta shaƙi wuyan Minista.

 

7. Can a Landan ga Yarima,

Ta bi shi cikin turaka.

 

8. A Abuja har a Billa,

Ta shige ciki ta yi sheƙa.

 

9. Tai ƙwayaye ta yi 'ya'ya,

Ta miƙe ƙafa a fada.

 

10. Tabbas cutar Korona,

Annoba ce ta gaske.

 

11. A masallatai da coci,

Duk an koma ga Allah.

 

12. Sarki mai shirya komai,

Dole ne bauta gare shi.

 

13. Ba tsumi kuma ba dabara,

Duniya yau an bi Allah.

 

14. Masu sheƙe aya su more,

A Italiya ko Amurka.

 

15. Har ƙasar Sin can a Chana,

Ta kai da yawa kushewa.

Ko Farisa har Faransa,

Ba kowa yau a titi.

 

16. Kufai a kira yi Turai,

Champions League an tsaya cik.

 

17. Ba a yin zancen Ronaldo,

Har Messi ba batunsa.

 

18. Ita annobar Korona,

Cuta ce babu shakka.

 

19. Ba ta kunya ba ta tsoro,

Ba ta sabo ba sanayya.

 

20. Yau mutum ya gane cewa,

Bai da ƙarfi sai na Allah.

 

21. Bai da sauran duk dabara,

Kariyarsa tana ga Rabbu.

 

22. Gatan kowa Ilahu,

Mui ta bauta mai da ɗa'a.

 

23. Ma rabauata a yau da gobe,

Don ko dai cutar Korona.

 

24. Wa'azi ce babu shakka,

Me je shi ke asara.

 

25. Kurciya in ta yi kuka,

Saƙo nata ban da wawa,

 

26. Bare gaula da soko.

Masu shashanci a hanya.

 

 

27. Hankali kura kira shi,

Ta yin zabari na guga.

 

28. Mai rabo shi ke rabauta,

In an wa'azi ya ɗauka.

 

29. Zunubansa ya nemi tuba,

Kan ya ji shi cikin kushewa.

 

30. Ni Khalid bani shakka,

Tabbas cutar Korona.

Jan kunne ce gare mu.

Mu bar saɓo da sharri.

 

31. Mu so junanmu gaske,

Hakan zai taimake mu.

 

32. Ni Imam Khalid na Indo,

Jikan Hauwa’u tabbas.

 

33. Na san cutar Korona,

Ƙanwa ce gun talauci.

 

34. Wajen ƙeta da sharri,

Har ma yawo a dangi.

 

35. Ni nan zan sanya aya,

Cikin waƙar Korana.

 

36. Allahu kasa mu gane,

Mu tuba zuwa gare Ka.

Amsoshi

Post a Comment

0 Comments