Daga cikin manyan shubuhohin 'Yan Bidi'a da masu inkarin Sunna (Aqlaniyyun), da kuma wasu masu dangantuwa ga Sunna masu inkarin wasu Hadisai da ba su kwanta musu a rai ba, akwai fadinsu cewa; HADISI AHAAD ZATO NE.
To abin da ya kamata a sani shi ne; wannan ra'ayi ne na wasu Malaman "Usulul Fiqh". Kuma kar ka manta, galibinsu Mabiya "Ilmul Kalam" ne, sun gina fahimtarsu ga mas'aloli masu yawa na "Usul" bisa Akidunsu na Bidi'a. Kuma wannar mas'ala tana cikinsu.
Alhali abin
da Salaf suke kai, tun daga kan Sahabbai da Tabi'ai da A'imma, irin su Malik da
sauransu, kuma shi ne Mazhabar Jamhurin Malaman Hadisi, shi ne cewa; Hadisi
Ahaad yana fa'idantar da ilimi. Ma'ana; tabbatuwarsa da ingancinsa ta fiskar
riwaya "Qat'iy" ne Yaqini ne, babu shakka a cikin haka. Wannan shi ne
abin da aka ruwaito daga su Imamu Malik da sauran A'imma, kamar yadda Ibnu Hazm
ya hakaito daga gare su. Ibnul Qayyim ya ce:
((الذي اعتمده نفاة
العلم عن أخبار رسول الله خرقوا به إجماع الصحابة المعلوم بالضرورة وإجماع
التابعين وإجماع أئمة الإسلام، ووافقوا به المعتزلة والجهمية والرافضة والخوارج
الذين انتهكوا هذه الحرمة، وتبعهم بعض الأصوليين والفقهاء، وإلا فلا يعرف لهم سلف
من الأئمة بذلك بل صرح الأئمة بخلاف قولهم.
فممن نص على أن خبر الواحد يفيد العلم مالك والشافعي وأصحاب
أبي حنيفة وداود بن علي وأصحابه كأبي محمد بن حزم ونص عليه الحسين بن علي
الكرابيسي والحارث بن أسد المحاسبي.
قال ابن خواز منداد في كتاب أصول الفقه، وقد ذكر خبر الواحد
الذي لم يروه إلا الواحد والاثنان، ويقع بهذا الضرب أيضا العلم الضروري نص على ذلك
مالك، وقال أحمد في حديث الرؤية: نعلم أنها حق، ونقطع على العلم بها، وكذلك روى
المروذي قال: قلت لأبي عبد الله: هاهنا اثنان يقولان إن الخبر يوجب عملا ولا يوجب
علما فعابه، وقال: لا أدري ما هذا)).
مختصر الصواعق المرسلة على الجهمية والمعطلة (ص: 553)
Ma'ana;
wadanda suka ce; Hadisi Ahaad zato ne, ba ya fa'idantar da "Yaqini"
sun saba Ijma'in Sahabbai da Tabi'ai da Limaman Muslunci. Asali sun dauko
ra'ayin ne daga 'Yan Bidi'a; Jahamiyya, Rafidha, Khawarij da Mu'utazila d.s.
Kuma hatta
cikin Malaman "Usul" din akwai wadanda suka ce: Hadisi Ahaad
"Yaqini" ne idan ya hadu da Qarinoni. Wannan shi ne ra'ayin su
Amidiy, Ibnul Hajib, Juwainiy, Baidhawiy da wasunsu. Al-Amidiy ya ce:
((اختلفوا في الواحد
العدل، إذا أخبر بخبر، هل يفيد خبره العلم، فذهب قوم إلى أنه يفيد العلم ثم اختلف
هؤلاء.
فمنهم من قال: إنه يفيد العلم بمعنى الظن لا بمعنى اليقين،
فإن العلم قد يطلق ويراد به الظن كما في قوله تعالى: {فإن علمتموهن مؤمنات} أي:
ظننتموهن.
ومنهم من قال: إنه يفيد العلم اليقيني من غير قرينة، لكن من
هؤلاء من قال ذلك مطرد في خبر كل واحد، كبعض أهل الظاهر وهو مذهب أحمد بن حنبل في
إحدى الروايتين عنه.
ومنهم من قال: إنما يوجد ذلك في بعض أخبار الآحاد لا في
الكل، وإليه ذهب بعض أصحاب الحديث.
ومنهم من قال: إنه يفيد العلم، إذا اقترنت به قرينة،
كالنظام، ومن تابعه في مقالته.
وذهب الباقون إلى أنه لا يفيد العلم اليقيني مطلقا، لا
بقرينة ولا بغير قرينة.
والمختار حصول العلم بخبره، إذا احتفت به القرائن، ويمتنع
ذلك عادة دون القرائن)).
الإحكام في أصول الأحكام للآمدي
(2/ 32)
Ka ga bayan
ya hakaito ra'ayoyin Malamai a kan mas'alar, karshe sai ya ce:
((والمختار حصول العلم
بخبره، إذا احتفت به القرائن)).
((Zababben
ra'ayi (a wajensa) ana samun yakini a Hadisin mutum daya adali, idan Qarinoni
suka kewaye shi)).
Ibnu Hajar
ya ce:
((الخبر المحتف
بالقرائن يفيد العلم النظري وممن صرح به إمام الحرمين والغزالي والرازي، والسيف
الآمدي وابن الحاجب ومن تبعهم)).
النكت على كتاب ابن الصلاح لابن حجر (1/ 377)
((Hadisi
Ahaad wanda Qarinoni suka kewaye shi, yana fa'idantar da Yaqini na nazari, daga
cikin wadanda suka tabbatar da haka akwai Juwainiy, Gazzaliy, Raziy, Amidiy da
Ibnu al-Hajib da wadanda suka bi su)).
Daga cikin
Hadisan da Qarinoni suka kewaye su akwai Hadisan Bukhari da Muslim, Ibnu Hajar
ya ce:
((والخبر المحتف
بالقرائن أنواع:
أ - منها: ما أخرجه الشيخان في صحيحيهما، مما لم يبلغ
التواتر، فإنه احتفت به قرائن، منها:
- جلالتهما في هذا
الشأن.
- وتقدمهما في تمييز
الصحيح على غيرهما.
- وتلقي العلماء
لكتابيهما بالقبول، وهذا التلقي وحده أقوى في إفادة العلم من مجرد كثرة الطرق
القاصرة عن التواتر.
إلا أن هذا يختص:
1) بما لم ينتقده أحد من
الحفاظ مما في الكتابين.
2) وبما لم يقع التخالف
بين مدلوليه مما وقع في الكتابين، حيث لا ترجيح؛ لاستحالة أن يفيد المتناقضان
العلم بصدقهما من غير ترجيح لأحدهما على الآخر، وما عدا ذلك فالإجماع حاصل على
تسليم صحته)).
نزهة النظر في توضيح نخبة الفكر ت الرحيلي (ص: 60 - 61)
Ka ga sai ya
nuna cewa; Hadisan Bukhari da Muslim suna cikin Hadisan da Qarinoni suka kewaye
su. Daga cikin Qarinonin akwai:
- Girman
matsayinsu a Ilimin Hadisi.
- Sun yi
fice wajen tace ingantattun Hadisai.
- Malaman
Muslunci sun karbi littatafansu biyu sun yarda da su. Wato kamar Ijma'i ne a
kan haka.
Kai, hasali
ma Abu Ishaq al-Isfirayiniy ya hakaito Ijma'in Malaman Hadisi a kan cewa;
Hadisan Bukhari da Muslim A YANKE BABU SHAKKA A KAN TABBACINSU ZUWA GA ANNABI
(SAW) (riwayarsu "Qat'iyya" ce). Ibnu Hajar ne ya nakalto maganarsa
kamar haka:
((الأستاذ أبو إسحاق
الإسفرائيني فإنه قال: "أهل الصنعة مجمعون على أن الأخبار التي اشتمل عليها
الصحيحان مقطوع بها عن صاحب الشرع وإن حصل الخلاف في بعضها فذلك خلاف في طرقها
ورواتها)).
النكت على كتاب ابن الصلاح لابن حجر (1/ 377)
((Malaman
Hadisi sun yi Ijma'i a kan cewa: Hadisan Sahihul Bukhari da Muslim yanke babu shakka
wajen tabbacinsu daga Annabi (saw), ko da an samu sabani a wasu daga ciki, to
kawai sabani ne a hanyoyinsu da maruwaitansu)).
Kuma fa kar
ka manta, Ijma'i abin lura a wannan babi shi ne Ijma'in Malaman Hadisi, kamar
yadda al-Isfirayiniy ya fada a maganarsa. Shi ya sa Ibnu Taimiyya ya ce:
((وإذا كان الإجماع على
تصديق الخبر موجبا للقطع به فالاعتبار في ذلك بإجماع أهل العلم بالحديث كما أن
الاعتبار في الإجماع على الأحكام بإجماع أهل العلم بالأمر والنهي والإباحة)).
مجموع الفتاوى
(13/ 352)
((Idan
Ijma'i a kan gaskata Hadisi ya kasance zai wajabta samun Yakini, to Ijma'i abin
lura shi ne Ijma'in Malaman Hadisi, kamar yadda Ijma'in Malaman Fiqhu shi ne
abin lura a Babin Hukunce-hukuncen Shari'a)).
Wannan
gaskiya ne, ai ba za a zo ana maganar kiwon lafiya amma a gabatar da ra'ayin
Injiniyoyi a kan na Likitoci ba.
Saboda haka
wannan shi ne Manhajin Malaman Sunna, babu wadanda suka saba sai 'Yan Bidi'a
makiya Hadisi.
Don haka ya
kai Dalibin Ilimi wanda yake kan gwadaben Ahlus Sunna, ya kamata ka shiga
taitayinka, kar ka yarda wani ya zo ya yi amfani da Sonka ga Annabi (saw), ya
rusa maka asalin Addininka, tushen Sunna, ya raba ka da Manhajin Ahlus Sunna, a
zo ana ce maka Hadisin da Bukhari ko Muslim suka ruwaito ai Hadisi ne Ahaad,
Hadisi ne zato, don haka idan ya saba Alkur'ani dole a jefar da shi, kamar
Hadisan Makomar Iyayen Annabi (saw). Alhali mun yi bayani a baya, hasali ma
babu "Ta'arudh" (cin karo) a tsakanin Ayoyi da Hadisan, kamar yadda
bayani ya gabata.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.