Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Akwai Banbanci Tsakanin Hoto (Photograph) Da Bidiyo (Video)?

Abu ne sananne a wajen ma'abota ilimi (malamai da dalibai) cewa; wajen yanke hukunci a kan abu a Shari'a ana lura ne da abubuwa guda biyu:

Na Farko: ayyana hakikanin abun, wato sanin asalin yadda yake, da sanin cikakkiyar ma'anarsa, saboda dole ya dace da sunan da ya zo a cikin dalilin hukuncin, bisa ma'anarsa da hakikaninsa ta Shari'a. Shi ya sa ka'ida shahararriya take cewa:

"الحكم على الشيء فرع عن تصوره".

Na biyu:  Dole a samu illar hukuncin (hikimar hukunci) a cikin wannan abun, idan hukuncin da mu bayi zamu iya sanin illarsa ne, ko idan ta zo a cikin Nassi.

Don haka idan aka ce asalin bidiyo tarin hotuna ne, to bayanin hakikaninsa ba zai cika ba, dole sai an kara da cewa; hotunan masu motsi, har ana iya jin sauti.

Don haka sai a ce: Bidiyo hoto ne mai motsi, har da sauti.

Amma shi kuma hoto (photograph) kowa ya san ba ya motsi, balle ya yi sauti.

Don haka sun banbanta a hakikani.

Don haka tarin hotuna masu yawa ba sa zama bidiyo har sai an sanya su sun zama masu motsi, har ma ana iya sa musu sauti.

Don haka bidiyo hoto ne da kari. Wato hoto kadai (ba motsi) bai zama bidiyo ba.

Ba na zaton akwai mai jayayya a kan haka.

Wannan ya sa ake banbance hoto (photograph) da vedio. Hatta a wajen suna da mu'amala ba abu daya ake daukarsu ba, saboda sun banbanta a hakika. Duk hoton da ba ya motsi ba za a taba kiransa da sunan bidiyo ba.

Ko za a kira shi?!

Don haka ita Shari'a hakikanin abu take dubawa, ba mujarradin suna kadai ba, ko kuma tarayya a cikin abu daya ban da saura ba. Tana duba cikakken ma'anar abu ne. In an samu banbanci a cikakkiyar ma'anar to za a iya samun banbanci a hukunci.

Kuma idan mun kalli mas'alar bisa mahanga irin ta 'yan Falsafa, za mu iya cewa: shi hoto (photograph) idan aka dora shi a kan takarda, to ya zama "Jauhari" (الجوهر), wato zaunanne abu dindindin.

Amma shi kuma bidiyo "Aradhi" (العرض) ne, wato abin da ba zai zauna dindindin ba. Wato ba za ka gan shi ba sai ka kunna shi, kuma idan ka kunna, hotunan ba za su zauna ba, tafiya za suna yi, har su kare gaba daya, saboda suna motsi. Don haka ba sa zama dindindin.

To wannan ma wani abu ne da zai tabbatar mana da banbancin hakikanin hoto (photograph) da bidiyo.

Saboda banbanci a hakika ne ya sa aka samu wasu Malamai sun haramta daukar hoto (photograph), amma sun halasta daukar bidiyo, kamar yadda Shaikh Ibnu Uthaimeen ya tabbatar da haka, inda ya ce:

"وأما الصور بالطرق الحديثة فهي قسمان:

القسم الأول: ما لا يكون له منظر ولا مشهد ولا مظهر، كما ذكر لي عن التصوير بأشرطة «الفيديو»، فهذا لا حكم له إطلاقا، ولا يدخل في التحريم مطلقا، ولهذا أجازه أهل العلم الذين يمنعون التصوير بالآلة «الفتوغرافية» على الورق، وقالوا: إن هذا لا بأس به...

القسم الثاني: التصوير الثابت على الورق. وهذا إذا كان بآلة «فوتوغرافية» فورية، فلا يدخل في التصوير، ولا يستطيع الإنسان أن يقول: إن فاعله ملعون؛ لأنه لم يصور في الواقع...".

الشرح الممتع على زاد المستقنع (2/ 201 - 201)

Ka ga sai ya ce:

"ولهذا أجازه أهل العلم الذين يمنعون التصوير بالآلة «الفتوغرافية» على الورق، وقالوا: إن هذا لا بأس به...".

"Saboda haka ne Malaman da suke haramta daukar hoto a kan takarda (photograph) suka halasta shi (daukar bidiyo), suka ce babu laifi da shi (saboda bidiyo ba hoto ne tabbatacce zaunanne ba)...".

To ka ga akwai Malaman da suka haramta hoto (photograph), amma ba su haramta bidiyo ba, saboda suna ganin hakikaninsu ba daya ba ne.

Misali a kan haka shi ne: Abu ne sananne Shaikh Ibnu Baaz yana haramta hoto (photograph), amma a kan bidiyo na aikin da'awa, da karantar da Addini yana da ra'ayoyi guda uku:

1- Yana da fatawa da take nuni a kan rashin halasci.

2- Yana da fatawa da ya yi "tawaqqufi".

3- Amma a karshe ya yi "taraju'i" daga "tawaqqufin", ya koma bayar da fatawa ta halastawa, saboda girman Maslahar hakan. Amma almajirinsa Ibnu Maani'i ya hakaito halastawa daga gare shi, saboda banbancin hakikanin bidiyo, da hakikanin hoto, kamar yadda ya kawo a littafinsa:

62 - سئل شيخنا عن كاميرا الفيديو مرارًا؟

فلم يمنع منها؛ وعلّل ذلك بأنها ليست ثابتة في ورق أو جدار.

قال شيخنا: الصور في التلفزيون مثل الصور في المرآة؛ لا بأس".

مسائل الإمام ابن باز (ص: 45 - 46)

Ka ga sai Shaikh Ibnu Baaz ya halasta bidiyo, bisa hujjan cewa: ba hoto ne tabbatacce kamar hoton takarda (photograph) ba.

A daya maganar kuma ya ce: bidiyo ba laifi, saboda kamar madubi yake.

Abun nufi a nan, Malamai irin su Shaikh Ibnu Baaz ba su yi tufka da warwara ba, saboda hakikanin hoto da bidiyo ba daya ba ne.

Saboda haka, ni sai nake ganin babu bukatar sai mutum ya yi nazari kafin ya san akwai banbanci tsakanin hoto (photograph) da bidiyo wajen hakikaninsu. Hakikaninsu ba daya ba ne. Don haka hukuncinsu zai iya banbanta.

Shi ya sa a post na baya na ce: a Fiqhance ba mamaki idan Malami ya haramta daukar hoto (photograph), amma kuma ya halasta daukar bidiyo. Saboda hakikarsu ba daya ba ce.

Don haka ni dai fadakarwata ita ce: mas'alar hoto mas'ala ce ta Ijtihadi, ba a tsanantawa a kanta. Shi ya sa ba mu taba jin labarin Shaikh Ibnu Baaz ya soki Shaikh Ibnu Uthaimeen don ya halasta hoto ba.

Saboda haka nake nasiha wa duka bangarorin guda biyu, masu halastawa da masu haramtawa; don Allah su ji tsoron Allah, su dena ta da jijiyar wuya a kan daukar hoto, har a kai ga zagin juna. Saboda mas'ala ce ta Ijtihadi, kuma bai halasta a yi zargi a mas'alar Ijtihadi ba.

Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments