Ticker

6/recent/ticker-posts

Sabani A Kan Mas'alar Hoto

Mutane da yawa suna tambayoyin da suka haɗa da:

Mene ne hukuncin ɗaukar hoto a Musulunci?

Shin hoto halas ne ko haram?

Shin ya halatta in dauki hoto?

Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

 ya yi bayani taƙaitacce mai gamsarwa dangane da wannan matsalar. Yana cewa:

Babban abin da ya shafa bakin fenti wa Da'awar Salafiyya a Nigeria shi ne tsanantawa a kan mas'alolin da ba su kai a tsananta a kansu ba. A kan haka - a shekarun baya - wasu matasa suka bayyana da sunan Salafiyya, suka yi ta rigima da sauran Ahlus Sunna - musamman kungiyar Izala - a kan Sunnonin Sallah da mas'alolin Ijtihadi, alhali bai halasta a yi rigima a kansu ba, tun da ba mu ji labarin Imamu Malik da Shafi'iy, ko Imamu Shafi'iy da Imam Ahmad sun yi rigima a tsakaninsu ba, alhali sun yi sabani a kan irin wadannan mas'alolin, alhali kuma su ne A'imma a Salafiyyar.

Asali ana tsanantawa ne a kan manyan mas'alolin Addini, su ne "Mas'alolin Usuluddeen", wato galibin mas'alolin Akida da Mas'alolin Ijma'i, sai kuma mas'alolin Halal da Haram, amma idan akwai NASSI a kansu. Saboda wanda ya saba a Akida ya zama dan bidi'a, wanda kuma yake aikata ayyukan haramun ya zama fasiki. Don haka ake tsanantawa a kansu.

To amma idan ka dauki mas'alar hoton da ake dauka da na'ura (photograph da bidiyo) babu NASSI KARARA a kanta, saboda babu irin wannan nau'in hoto a zamanin Annabi (saw). Shi ya sa Malamai suka yi sabani a kan hukuncinta. A lokacin da wasu suke ganin cewa: hoton na'ura ya amsa sunan hoton da Annabi (saw) yake nufi a cikin Hadisan haramta hoto, don haka suka haramta, wasu Malaman kuma suna ganin hoton na'uran bai amsa sunan hoton da Annabi (saw) yake nufi ba, sai suka halasta.

To ka ga asali abin ya ginu ne a kan Ijtihadi, ba a kan son zuciya ba. Mas'ala ce ta Ijtihadi, saboda rashin Nassi karara a kanta.

Saboda haka ne ya sa - duk da ni na fi ganin cewa: dalilan masu haramtawa sun fi karfi - ni ban gamsu da yin zargi a kan hoto ba. Don ba a zargi a mas'ala ta Ijtihadi.

Kuma a Fiqhance abu ne wanda yake normal a samu Malami yana haramta hoto (photograph), amma kuma yana halasta hoton bidiyo. Saboda ba nau'i daya suke ba, akwai banbanci a tsakaninsu. Shi ya sa duk Malamai da Manazarta da suka yi magana da rubuce-rubuce a kan hukuncin hoto, za ka samu cewa; suna banbanta tsakaninsu. Suna bayanin hukuncin kowane nau'i daban. Saboda haka, ga wanda ya san Fiqhu ba zai yi mamaki ba, don an samu wani Malami ya ce hoto (photograph) haramun ne, amma hoton bidiyo halas ne. Babu maganar tufka da warwara a cikin maganarsa, balle a yi masa ilzami!

Ala ayyi halin, mas'alar hoto mas'ala ce ta Ijtihadi, don haka babu laifi mu yi sabani a kanta. Kai ka fahimci cewa hukuncin hoto (photograph) haram ne, ni kuma na fahimci halas ne. Ba tare da kowane bangare ya zargi daya bangaren ba.

Amma abin da yake faruwa, na zage-zagen juna tsakanin masu haramta hoto da masu halastawa ba dadai ba ne. Mai laifi a mas'alolin Ijtihadi shi ne wanda ya zargi abokan sabaninsa, ya zage su, ya kaurace musu. Saboda ya zama mai raba kan al'umma.

Allah ya shirya.

Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments