"Hakimiyya" wani suna ne da ya bayyana daga Abul A'ala al-Maududiy, Sayyid Qutub kuma ya yada shi, wanda yake nufin wata ma'ana; wacce ta ginu bisa Akidar Khawarijawa, ta kafirta al'umma, wacce Kungiyoyin Ta'addanci irin su Boko Haram suka dauka daga gare su, suna yakar al'ummar Musulmi.
To kasancewar ya bayyana wa mutane cewa; wannar Akida ta "Hakimiyya" tushenta Akidar Khawarijawa ne, shi ya sa wasu suke ta kokarin lullube ta, da nema mata goyon baya daga maganganun Malaman al'umma, Ahlus Sunna, wadanda aka sansu da yakar Akidun Khawarijawa.
Bayyanan wannan sabon salo, na cakuda tsakanin
karya da gaskiya, shi yake lazimta raddi don bayani wa mutane, da barrantar da
Malaman da aka jingina musu wannar Bidi'a da barna ta Khawarijawa. Saboda haka
wannan rubutu nawa raddi ne ga masu danganta"Hakimiyya" ga Shaikh
Muh'd bn Ibrahim Alu-Shaikh, Muftin Saudiyya kafin Shaikh Ibnu Baaz.
Don haka raddin zai zo ne kashi biyu; a dunkule da
kuma a fassale gaba – gaba da iznin Allah.
RADDIN A DUNKULE: ya kunshi bayanin wasu abubuwa
kamar haka:
- Asalin lafazin "Hakimiyya" da matsayin
amfani da shi.
- Mecece Akidar Sayyid Qutub?
- Mecece Akidar Shaikh Muh'd bn Ibrahim?
- "Hakimiyya" a wajen Sayyid Qutub.
Mutum ba zai fahimci gaskiyar danganta
"Hakimiyya" Akidar Khawarijanci ma Shaikh Muh'd bn Ibrahim ba har sai
ya san Asalin "Hakimiyya", da kuma Akidar Shaikh Muh'd bn Ibrahim, da
Akidar Sayyid Qutub. Idan mutum ya san haka a nan zai fahimci kowanne a cikinsu
a bisa wace Akida ya gina maganarsa. A cikinsu wanda muka same shi bisa Akidar
Ahlus Sunna to mun san maganganunsa zai gina su kan Manhajin Sunna. Wanda kuma
muka samu Akidarsa ta Khawarijawa ce, to maganganunsa dole zai zama bisa Akida
da Manhajin Khwarijawa ne.
1- BAYANIN LAFAZIN "HAKIMIYYA":
Lafazin "Hakimiyya" (حاكمية) Masdari ne "Sina'iy" (صناعي), wanda
aka kirkire shi daga lafazin "Hukm" (حكم), wato
hukunci. Wannan lafazi na "Hakimiyya" ba za ka same shi a cikin
littatafan Luga da ake dogaro da su ba, balle littatafan Shari'a.
Haka wannan lafazi bai zo cikin Alkur'ani ko Sunna
ba. Kuma babu wannan lafazi a cikin littatafan Shaikh Muh'd bn Ibrahim, saboda
haka ta yaya za a yi a jingina ma Shaikh Muh'd bn Ibrahim Hakimiyya?!
Wannan lafazi na "Hakimiyya" lafazi ne
"Mujmali" dunkulalle, wanda ya kunshi karya da gaskiya. Wato irin
lafuzan da mabarnata suke fakewa da su suna shigar da bidi'o'insu cikin
al'umma, kamar yadda da ma Manhaji ne na 'Yan Bidi'a, kunshe bidi'o'insu a
cikin dunkulallun lafuza:
((الألفاظ المجملة عرضة للمحق والمبطل)).
شرح الطحاوية ت الأرناؤوط (1/ 266)
((Su lafuza dunkulallu abin amfani ne ga mai
gaskiya da mabarnaci)).
Don haka a ka'ida ta Ahlus Sunna ba sa amfani da
lafuza "Mujmalai" dunkulallu wajen bayanin gaskiya, kawai suna
takaita ne a kan lafuza na Shari'a, ko lafuzan da gaskiya kawai suka kunsa.
Ibnu Abil Izz ya ce:
((التعبير عن الحق بالألفاظ الشرعية النبوية الإلهية هو سبيل أهل
السنة والجماعة)).
شرح الطحاوية ت الأرناؤوط (1/ 70)
((Bayanin gaskiya da lafuzan Shari'ar Annabi ta
Allah shi ne hanyar Ahlus Sunna wal Jama'a)).
Don haka hanya ce ta 'yan bidi'a su dauko wani
lafazi da bai zo a Shari'a ba, kuma wanda ya kunshi karya da gaskiya, sai su
dora masa bidi'arsu, sai kuma su cuso cikin Addini, suna kafirta mutane da shi,
kamar yadda muka gani a wajen Ustaz Sayyid Qutub a wannan lafazi na
"Hakimiyya".
Manhajin Ahlus Sunna a irin wadannan lafuza sai a
nemi bayani daga wanda ya yi amfani da su. Idan yana nufin ma'ana mai kyau
wacce ta dace da Alkur'ani da Sunna sai a karbi ma'anar, amma idan kuma
mummunar ma'ana yake nufi sai a yi watsi da ita.
Saboda haka, idan suna nufin Allah shi ne mai
hukunci, kuma hukunci nasa ne, da wajabcin yin hukunci da Abin da Allah ya
saukar, kuma hakan yana karkashin kadaita Allah da bauta, to wannan ma'ana ce
mai kyau, wacce ta zo a Shari'a.
Amma idan suna nufin "Hakimiyya" bisa
ma'anarta a wajen Sayyid Qutub, to sai mu yi watsi da ita, don ma'ana ce ta
Khawarijawan farko, "Muhakkima", wadanda suka kafirta Sayyidina Aliyu
(ra), suka yake shi, kuma daga karshe suka kashe shi.
Saboda haka akwai babban kuskure a cikin jingina
ma Shaikh Shaikh Muh'd bn Ibrahim da Jami'ar Madina wannan kirkirarren lafazi,
wanda yake dauke da mummunan ma'ana a wajen wadanda suka kirkire shi.
2- AKIDAR SAYYID QUTUB:
Akwai bukatar mu san Akidar Sayyid Qutub don sanin
tushen da a kansa ya gina ma'anar "Hakimiyya". Saboda abu ne sananne
cewa: Musulmai sun yi Ijma'i a kan wajabcin yin hukunci da abin da Allah ya
saukar. Amma sai Khawarijawa suka saba, suka kara bidi'o'i masu hatsari a kan
haka, wanda ya kai su ga fita daga al'umma da halasta jinanenta, da daukar
makami a kanta. Wannan ya sa har aka kira Khawarijawan farko da sunan:
"Muhakkimah", saboda sabawarsu ga Musulmai a kan wannar mas'ala.
A wannar mas'ala dole ne mu san Akidar Sayyid
Qutub, don mu san shi Akidarsa irin ta Khawarijawa ce ko kuma irin ta Ahlus
Sunna ce?
To idan muna so mu san Akidar Sayyid Qutub, shin
irin ta Khawarijawa ce ko a'a, sai mun san Akidarsa a "MAS'ALAR HAKIKANIN
IMANI DA MUSLUNCI", da abin da ke da alaka da su na Hakikanin Kafirci. Don
haka idan muka duba za mu ga cewa: Ma'anar Imani da Muslunci a wajen Sayyid
Qutub irin ma'anarsu ce a wajen Khawarijawa, Akidarsu ita ce Akidarsa. Abin da
zai tabbatar mana da haka shi ne; Sayyid ya tabbatar da cewa; Imani da Muslunci
abu ne guda daya a dunkule, wanda ba ya rarrabuwa, ta yadda idan an rasa wani sashe
nasa to an rasa shi gaba daya. Don haka a wajen Sayyid; idan mutum ya rasa wani
bangare na Imani ko Muslunci (wato ya bar wani aikin imani), to ya fita daga
Muslunci gaba daya, ya zama kafiri. Wannan kuwa ita ce: Akidar Khawarijawa,
kamar yadda Ibnu Taimiyya ya ce:
((أصل نزاع هذه الفرق في الإيمان من الخوارج والمرجئة والمعتزلة
والجهمية وغيرهم أنهم جعلوا الإيمان شيئا واحدا إذا زال بعضه زال جميعه وإذا ثبت بعضه
ثبت جميعه فلم يقولوا بذهاب بعضه وبقاء بعضه كما قال النبي صلى الله عليه وسلم {يخرج
من النار من كان في قلبه مثقال حبة من الإيمان}.
ثم قالت "الخوارج والمعتزلة": الطاعات كلها من الإيمان
فإذا ذهب بعضها ذهب بعض الإيمان فذهب سائره فحكموا بأن صاحب الكبيرة ليس معه شيء من
الإيمان)).
مجموع الفتاوى (7/ 510)
Sai Ibnu Taimiyya ya bayyana cewa; Khawarijawa ma
– kamar sauran 'yan bidi'a – duka sun tafi ne a kan cewa; Imani abu daya ne ba
ya rarrabuwa, ta yadda idan sashensa ya gushe to gaba daya imanin zai gushe
mutum ya fita daga Muslunci. Sai ya ambaci ra'ayin Khawarijawan ya ce:
((Khawarijawa da Mu'utazila suka ce: aiyukan da'a
ma Allah gaba dayansu suna cikin Imani, idan sashen aiyukan da'an ya tafi ya
gushe, sashen imanin ya tafi, to sauran imanin ma zai tafi ya gushe daga daya,
wannan ya sa suka yi hukunci ma wanda ya aikata babban sabo to zai zama ba shi
da sauran imani (ya kafirta))).
Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya ce:
((المعتزلة والخوارج قالوا: إن الإيمان قول وعمل لكن لا يتبعض
ولا يتجزأ، قالوا: إن ترك المعصية وفعل الطاعة إيمان، فإذا فعل الموحد المعصية، أو
ترك الطاعة زال عنه الإيمان بالكلية. ثم الخوارج تكفره، والمعتزلة تجعل له منزلة بين
منزلتين. وافقوا أهل السنة في أصل الإيمان أنه قول وعمل، لكن خالفوهم فقالوا: لا يتبعض
ولا يتجزأ)).
شرح العقيدة الواسطية (ص: 128)
Sayyid Qutub kuwa wannar Akida ta Khawarijawa ita
ce Akidarsa, ya tabbatar da ita a wurare masu yawa a cikin "Fi Zilalil
Qur'an", daga ciki ya ce:
((وهو اطراد يوجه النظر إلى حقيقة هذا الدين.. إنه وحدة لا تتجزأ))
في ظلال القرآن (1/ 164)
Ka ga a nan sai Sayyid Qutub ya nuna cewa;
hakikanin Addini abu guda ne, ba ya rarrabuwa.
Ya ce:
((يصبح المنهج الإلهي وحدة واحدة. لا تتجزأ ولا تتفرق. ويصبح ترك
جانب منه وإعمال جانب، إيماناً ببعض الكتاب وكفراً ببعض.. فهو الكفر في النهاية)).
في ظلال القرآن (1/ 177)
Ka ga a nan ma sai Sayyid Qutub ya nuna cewa;
Manhajin Allah, wato Addini kenan, abu ne guda daya, ba ya rarrabuwa. Idan
mutum ya bar wani bangare nasa to karshensa kafirci ne.
Ya ce:
((إن الإيمان وحدة لا تتجزأ.. الإيمان بالله إيمان بوحدانيته-
سبحانه- ووحدانيته تقتضي وحدة الدين الذي ارتضاه للناس لتقوم حياتهم كلها- كوحدة- على
أساسه. ويقتضي وحدة الرسل الذين جاءوا بهذا الدين من عنده- لا من عند أنفسهم ولا في
معزل عن إرادته ووحيه- ووحدة الموقف تجاههم جميعاً.. ولا سبيل إلى تفكيك هذه الوحدة.
إلا بالكفر المطلق وإن حسب أهله أنهم يؤمنون ببعض ويكفرون ببعض! وكان جزاؤهم عند الله
أن أعد لهم العذاب المهين.. أجمعين..))
في ظلال القرآن (2/ 798)
Ka ga a nan kuma sai Sayyid Qutub ya nuna cewa;
hakikanin Imani abu ne guda daya, ba ya rarrabuwa.
Ya ce:
((والإسلام منهج للحياة كلها. من اتبعه كله فهو مؤمن وفي دين الله.
ومن اتبع غيره ولو في حكم واحد فقد رفض الإيمان واعتدى على ألوهية الله، وخرج من دين
الله. مهما أعلن أنه يحترم العقيدة وأنه مسلم. فاتباعه شريعة غير شريعة الله، يكذب
زعمه ويدمغه بالخروج من دين الله.))
في ظلال القرآن (2/ 972)
A nan ma sai Sayyid Qutub ya nuna cewa; Muslunci
tsarin rayuwa ne gaba dayanta, sai wanda ya bi shi gaba daya ne zai zama
Mumini. Wanda kuma ya bi wani abu ba Muslunci ba a rayuwarsa, ko da a hukunci
ne guda daya to ya yi watsi da imanin, kuma ya fita daga Addinin Muslunci, ko
da ya ce: shi Musulmi ne, kuma yana girmama Akidar Muslunci.
Wannan shi yake tabbatar mana cewa; Akidar Sayyid
Qutub a Babin Hakikanin Muslunci da Imani iri daya ne da na Khawarijawa, wannan
ya sa kafirta Musulmai da yake yi, iri daya ne da na Khawarijawa.
Saboda haka maganar da zai yi a kan mas'alar
"Hukunci da abin da Allah ya saukar", iri daya ne da na Khawarijawa,
irin ra'ayin Khawarijawan Farko, wadanda aka kira su da sunan
"Muhakkima", wadanda suka kafirta Sayyidina Aliyu (ra), kuma suka
kashe shi.
Saboda haka "Hakimiyyar" da Sayyid Qutub
ya yada, wacce ya dauko daga Maududiy, matsayinta shi ne "كلمة حق أريد بها الباطل", ma'ana; kura ce da fatar
Akuya, kamar yadda za mu ga hakan a nan gaba.
3- AKIDAR SHAIKH MUHAMMAD BN IBRAHIM:
Shi kuma Shaikh Muhammad bn Ibrahim wanda wasu
suke danganta masa "Hakimiyya" Akidar Khawarijawa, - duk da cewa;
asali bai taba ambaton kalmar ba – mecece Akidarsa a Babin Hakikanin Muslunci
da Imani?
Shin Akidarsa irin ta Khawarijawa ce da har za a
danganta masa "Hakimiyyarsu", ko irin ta Ahlus Sunna ce?
To ga nan inda Shaikh Ibnu Ibrahim ya tabbatar da
Akidarsa a kan haka kamar haka:
((إن الإسلام والإيمان والإحسان دوائر، أوسعها دائرة الإسلام،
ثم يليها في السعة الإيمان، ثم أضيقها الإحسان، وهكذا، مثل الدوائر التي كل واحدة محيطة
بالأخرى. فمن المعلوم أن من كان في الدائرة الوسطى – وهي دائرة الإحسان – فهو داخل
في الإسلام والإيمان، وإذا خرج عن الوسطى فهو داخل في الثانية وهي الإيمان، وإذا خرج
عنهما فهو داخل في الثالثة، وهي الإسلام، وإذا خرج عن هذه الدوائر الثلاث فهو خارج
إلى غضب الله وعقابه، وداخل في دوائر الشيطان والعياذ بالله. فنعرف بالتمثيل بهذه الدوائر
صحة قول من قال: كل محسن مؤمن مسلم وليس كل مسلم مؤمنا محسنا، فلا يلزم من دخوله في
الإسلام أن يكون داخلا في الإحسان والإيمان. وليس المراد أن من لم يكن في الإحسان والإيمان
أنه يكون كافرا، فإنه مسلم، لكن لا يكون مؤمنا الإيمان الكامل الذي يستحق أن يثنى عليه
به)).
شرح الأصول الثلاثة (ص: 213 - 214)
To ka ga sai Shaikh Muhammad bn Ibrahim ya bayyana
mana cewa; Addini ba abu daya ne a dunkule ba - kamar yadda Sayyid Qutub ya
fada -, ta yadda idan an rasa sashe an rasa shi gaba daya. A'a, Addini matakai
ne guda uku, kuma kowane mataki yana da asali da kuma kamala. Akwai matakin
Muslunci, Imani da Ihsani. Sai ya misalta mana su da misalin da wani cikin
Salaf ya yi, inda ya nuna Addini da'irori (circle) ne guda uku, sun kewaye
juna. Da'irar Muslunci ta fi fadi, da'irar Ihsani kuma ita ce mafi karanta.
Ga nan da'irar Ihsani 'yar karama, sai da'irar
Imani ya kewaye ta. Ita kuma da'irar Imani, sai da'irar Muslunci ya kewaye ta.
Don haka da'irar Ihsani tana cikin da'irar Imani, da'irar Imani kuma tana cikin
da'irar Muslunci.
Idan mutum ya fita daga Ihsani, ya aikata abubuwa
da za su fitar da shi daga Ihsanin, ba zai fita daga Muslunci ba, a'a, zai koma
cikin da'irar Imani ne. Idan kuma ya fita daga da'irar Imani (ya aikata
abubuwan da suka fitar da shi daga Imani), ba zai fita daga Muslunci ba, a'a,
zai koma da'irar Muslunci ne. Har sai idan ya aikata abin da zai warware masa
Muslunci shi ne zai fitar da shi daga Muslunci gaba daya. Shi ya sa a karshen
maganarsa Ibnu Ibrahim din ya ce:
((وليس المراد أن من لم يكن في الإحسان والإيمان أنه يكون كافرا،
فإنه مسلم، لكن لا يكون مؤمنا الإيمان الكامل الذي يستحق أن يثنى عليه به)).
((Ba a nufin cewa; duk wanda ya fita daga da'irar
Ihsani da ta Imani ZAI KASANCE KAFIRI, A'A, LALLAI SHI MUSULMI NE. Sai dai ba
zai zama Mumini mai Imani cikakke ba, wanda za a yabe shi a kansa (Ma'ana; yana
da imanin, amma sai dai ba cikakke ba ne)".
To yanzu ka auna wannar magana ta Shaikh Muhammad
bn Ibrahim da maganar Sayyid Qutub, inda ya ce:
((يصبح المنهج الإلهي وحدة واحدة. لا تتجزأ ولا تتفرق. ويصبح ترك
جانب منه وإعمال جانب، إيماناً ببعض الكتاب وكفراً ببعض.. فهو الكفر في النهاية)).
Ma'ana; Barin wani janibi na Addini kafirci ne.
Za ka ga banbancin Akida a tsakaninsu. Shaikh
Muhammad bn Ibrahim Akidarsa ta Ahlus Sunna ce, amma Sayyid Qutub Akidarsa ta
Khawarijawa ce.
Don haka idan ka karanta wannan za ka san cewa;
Akidar Shaikh Muhammad bn Ibrahim Akidar Ahlus Sunna ce ba ta Khawarijawa kamar
Akidar Sayyid Qutub ba. Sanin wannan da banbance tsakanin mutanen biyu, shi zai
sa mu fahimci banbancin da ke tsakanin maganar Shaikh Muhammad bn Ibrahim a
mas'alar "Hukunci da abin da Allah ya saukar", da maganar Sayyid
Qutub a "Hakimiyyar" da suka kirkira, wacce ta ginu bisa Akidar
Khawarijawa.
4- MA'ANAR "HAKIMIYYA" A WAJEN SAYYID
QUTUB:
Asali Kalmar "Hakimiyya" a wajen
Maududiy ta fara bayyana, sai Sayyid Qutub ya dauke ta ya yi ta yada ta a cikin
littatafansa, yana kirkira mata hukunce – hukunce iri daban – daban, masu girma
masu hatsari, bisa Akidarsa da Manhajinsa na Khawarijawa.
Daga cikin irin wadannan hukunce – hukuncen da ya
kirkira, akwai fadinsa cewa:
1. Ita wannar Hakimiyya ita ce: ma'anar Kalmar
Shahada, ta yadda duk wanda ya yarda da wani tsari ko wata Gomnati a wannan
zamani, balle har ya yi ta'amuli da ita, to lallai ya kafirce ma Kalmar
Shahada, ya zama kafiri. Ga wasu maganganunsa a kan haka. Yana magana game da
Larabawa sai ya ce:
((قد كانوا يعرفون من لغتهم معنى: «إله» ومعنى: «لا إله إلا الله»
.. كانوا يعرفون أن الألوهية تعني الحاكمية العليا.. وكانوا يعرفون أن توحيد الألوهية
وإفراد الله - سبحانه - بها، معناه نزع السلطان الذي يزاوله الكهان ومشيخة القبائل
والأمراء والحكام، ورده كله إلى الله))
في ظلال القرآن (2/ 1005)، معالم في الطريق (ص: 26)
-Wai- Larabawa sun san cewa: Ma'anar
"Uluhiyya" ita ce: "Hakimiyya".
Kuma ya ce:
((«لا إله إلا الله» كما كان يدركها العربي العارف بمدلولات لغته:
لا حاكمية إلا لله، ولا شريعة إلا من الله، ولا سلطان لأحد على أحد، لأن السلطان كله
لله))
في ظلال القرآن (2/ 1006)، معالم في الطريق (ص: 28)
2. A yau mutane sun koma Jahiliyya, saboda sun bar
"Hakimiyya":
((أما اليوم وقد عادت الأرض إلى الجاهلية وارتفع حكم الله- سبحانه-
عن حياة الناس في الأرض، وعادت الحاكمية إلى الطاغوت في الأرض كلها، ودخل الناس في
عبادة العباد بعد إذ أخرجهم الإسلام منها.. الآن تبدأ جولة جديدة أخرى للإسلام- كالجولة
الأولى- تأخذ- في التنظيم- كل أحكامها المرحلية، حتى تنتهي إلى إقامة دار إسلام وهجرة
ثم تمتد ظلال الإسلام مرة أخرى- بإذن الله- فلا تعود هجرة ولكن جهاد وعمل كما حدث في
الجولة الأولى..))
في ظلال القرآن (3/ 1560)
Ya ce:
((إن المجتمع الجاهلي هو كل مجتمع غير المجتمع المسلم! وإذا أردنا
التحديد الموضوعي قلنا: إنه هو كل مجتمع لا يخلص عبوديته لله وحده. . متمثلة هذه العبودية
في التصور الاعتقادي، وفي الشعائر التعبدية، وفي الشرائع القانونية. .
وبهذا التعريف الموضوعي تدخل في إطار " المجتمع الجاهلي
" جميع المجتمعات القائمة اليوم في الأرض فعلا!...
تملك سلطة التشريع دون الرجوع إلى شريعة الله. . أي أن لها الحاكمية
العليا باسم "الشعب" أو باسم "الحزب" أو باسم كائن من كان. . ذلك
ان الحاكمية العليا لا تكون إلا لله سبحانه، ولا تزاول إلا بالطريقة التي بلغها عنه
رسله)).
معالم في الطريق (ص: 86 - 87)
3. Duka Musulmai sun yi Ridda sun fita daga
Muslunci, saboda sun bar "Hakimiyya":
((لقد استدار الزمان كهيئته يوم جاء هذا الدين إلى البشرية بلا
إله إلا الله. فقد ارتدت البشرية إلى عبادة العباد، وإلى جور الأديان ونكصت عن لا إله
إلا الله، وإن ظل فريق منها يردد على المآذن: «لا إله إلا الله» دون أن يدرك مدلولها،
ودون أن يعني هذا المدلول وهو يرددها، ودون أن يرفض شرعية «الحاكمية» التي يدعيها العباد
لأنفسهم- وهي مرادف الألوهية- سواء ادعوها كأفراد، أو كتشكيلات تشريعية، أو كشعوب.
فالأفراد، كالتشكيلات، كالشعوب، ليست آلهة، فليس لها إذن حق الحاكمية.. إلا أن البشرية
عادت إلى الجاهلية، وارتدت عن لا إله إلا الله. فأعطت لهؤلاء العباد خصائص الألوهية.
ولم تعد توحد الله، وتخلص له الولاء))
في ظلال القرآن (2/ 1057)
Wannan shi ne "Mafhumin Hakimiyyar" da
su Sayyid Qutub suka kirkira, kuma ya kafirta al'umma gaba daya da ita. Har
'yan ta'adda suka tasirantu da shi, suke ta kashe al'ummar Musulmi.
A kan haka ya bayyana cewa: hakikanin
"Hakimiyya" a wajen Sayyid Qutub shi ne Akidar Khawarijawan
"Muhakkima", masu kashe mutane, a bisa "shi'ar" na "لا حكم إلا لله". (Babu hukuma sai ta
Allah). Kalmar da Sayyidina Aliyu (ra) ya kira ta da: "كلمة حق أريد بها الباطل".
To ka ga da wannan za mu fahimci banbancin Sayyid
Qutub da Shaikh Muh'd bn Ibrahim Alu-Shaikh, cewa; Sayyid Qutub Akidarsa ta
Khawarijawa ce. Shi kuma Shaikh Muh'd bn Ibrahim Alu-Shaikh Akidarsa ta Ahlus
Sunna ce.
Saboda haka duk maganar da Sayyid Qutub zai yi a
kan mas'alar "Hukunci da abin da Allah ya saukar" to zai yi ne bisa
Akidarsa ta Khawarijanci.
Kamar yadda shi kuma Shaikh Muh'd bn Ibrahim
Alu-Shaikh zai yi ne bisa Akidarsa ta Ahlus Sunna.
Sai ku biyo mu a kashi na 3, inda za mu yi raddi a
fassale da iznin Allah.
Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.