Ticker

6/recent/ticker-posts

Hamayya Ko Adawa a Cikin Wakokin Siyasa a Kasar Hausa

Citation: IIdris, Y. (2024). Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 161-169. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.019.

Hamayya ko Adawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa a Ƙasar Hausa

Yahaya Idris
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu [anfodiyo,
Sakkwato, Nijeriya.
Kibɗau yahayaidris33@gmail.com

Tsakure: Waƙa a siyasa kamar gishiri ne a cikin miya, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba a cikin harkokin siyasa, kusan a iya cewa, siyasa ba ta zama da ƙafafunta ba tare da waƙa ba (Usman 2013:3). Jam’iyyun siyasa sukan yi amfani da waƙoƙi domin yin kamfe, wanda a cikinsu ne suke bayyana manufofinsu da yin suka, da kawo hanyoyin gyara ko yin zambo har ma da zagi ga abokan hamayya ko tsakanin jam’iyyu biyu (Adamu 2003:54). Ta ɗaya hannun kuma akan sami waƙoƙi masu yin ɓatanci ga wata jam’iyya ko magoya bayan jam’iyya wani lokaci har da cin mutunci da zagi da yin fito-na-fito da zambo ta yadda manufar ta kauce hanyar hamayya ta zama adawa. A siyasance kalmar “Hamayya” ya kamata a yi amfani da ita wadda ba ta hana jituwa tsakanin ‘yan siyasa. Ba Kalmar “Adawa” ba mai manufar ƙiyayya ta har abada. Manufar wannan takarda ce, ƙoƙarin kawo manufofi na adawa maimaikon hamayya kamar yadda aka tsinkayi hakan a cikin wasu waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa domin faɗakarwa.

Fitilun Kalmomi: Hamayya, Adawa, Waƙoƙi, Siyasa, Ƙasar Hausa

Gabatarwa

A cikin ɓangarorin adabin baka ko rubutacce wato waƙa da zube da wasan kwaikwayo waƙa ce ƙololuwar magana ta hikima da ɗan Adam ke iya yi, ita ce ta fi ingancin tacewa kuma ita ce mafi tasiri kai tsaye ga zuciyar taliki. Waɗannan siffofi nata ne suka sa ta fi saurin isar da saƙonni da ke ƙunshe da bayanan tarihi da al’adu da addini da siyasa da sauran lamuran rayuwa, Usman (2009:2). Masana da manazarta waƙoƙin Hausa sun yi ayyuka da dama game da waƙoƙi, wasu waƙoƙin kaɗai suka ɗauka don ƙwanƙwancewa, wasu zambo da yabo suka duba Isah (2013:1). Wannan takarda za ta mayar da hankali ne ga irin hanyoyin da ake amfani da su a cikin waƙoƙin siyasa domin nuna adawa. Kamar yadda aka bayyana a cikin tsakure, siyasa hanyar tafiyar da mulkin jama’a ce a zamanance ko a gargajiyance Idris (2010:12). A wajen tafiyar da harkokin siyasa waƙa tana taka muhimmiyar rawa, a cikin waƙoƙin siyasa akan samu jam’iyyu suna hamayya da juna. Wani abun lura, a halin yanzu maimakon jam’iyyun siyasu suke yi hamayya da juna wadda take nufin (kiyayya ta ɗan lokaci) sai ake samun akasi, jam’iyyun siyasa na wannan lokaci adawa da juna suke yi wadda take nufin (ƙiyayya ta har abada) ta yadda abun yake zama da cin mutuncin juna da zage-zage da abubuwa makamantan haka. Yana daga cikin manufar wannan takarda kalato ire-iren abubuwa da ‘yan siyasa suke yin amfani da su a tsakaninsu waɗanda na adawa ne da babu komai a cikinsu sai cin zarafi da cin fuska. Za a nazarci ire-iren waƙoƙin da suke ɗauke da irin wannan badaƙala a kuma yi ƙoƙarin fahimtar abubuwan da suke ɗauke da su.

Ma’anonin Muhimman Kalmomi

A ƙarƙashin wannan yanki za a kalato fashin baƙin dam asana da manazarta suka yi a game da muhimman kalmomin da suke ƙunshe cikin batun wannan takarda. Kalmomin da za a yi fashin baƙinsu sun haɗa da, Adawa da kuma Hamayya. Haka kuma za a dubi ma’anonin Kalmar siyasa da kuma ƙasar Hausa.

Ma’anar Kalmar Adawa da ta Hamayya

Kalmar adawa Balarabiya ce watau “Adawatu” ma’anarta ƙiyayya. Bayan an samar da kalmar aiki sai aka samar da mai yin aiki watau “Adawu” ma’ana maƙiyi.

Ma’anar adawa kamar yadda aka kalato a cikin Ƙamusu Hausa (2006:2) an bayyana ta da cewa, gaba ko hamayya ko ƙiyayya tsakanin mutum biyu ko fiye.

A cikin Wikipedia kuwa ga abin da aka samu a game da adawa.

A siyasa, adawa tana nufin samuwar jama’iyya ko jama’iyu ko waɗansu ƙungiyoyi su haɗu suna sukar gwamnatin da take mulki. Yanayin yin adawa ya danganta ga jama’iya da kuma tsarin gwamnatin da take mulki. Yanayin adawa ga gwamnati mai sassaucin ra’ayi ba zai zama ɗaya ba da gwamnati mai ra’ayin riƙau.

Adawa ta rabu ya zuwa,

·                     Adawar Tankiya

·                     Adawar sa in sa da kuma

·                     Adawar cacar baki

‘Yan siyasa a ƙasar nan suna amfani da wannan kalma (Adawa) tun fil-azal kuma yadda suke amfani da ita haka ma’anarta. Amma a tsarin siyasa kalmar da ta kamata a yi amfani da ita a siyasance ita ce “Hamayya” wadda ba ta hana jituwa tsakanin ‘yan siyasa. Ba kalmar adawa ba mai nufin ƙiyayya.

Bisa fahimta ana iya cewa kalmar adawa tana nufin ƙiyayya kamar yadda ake amfani da ita musamman a fagen siyasa maimakon kalmar hamayya.

Ma’anar Siyasa

 Ƙamusoshin Hausa da masana Harshen Hausa da dama sun ba da ma’anar siyasa. Waɗannan masana ko litattatafai sun haɗa da Bargery (1934) da Abbaraham (1962) da Lawal (1983) da Gusau (1984) da Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ta Kano (2006). Bergery (1934) yana cewa siyasa tana nufin ko dai rangwame a farashin kowane abu ko kuwa tausasawa a cikin al’amura. Wannan ra’ayi ya yi daidai da na Abraham (1962).

 A cikin Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ta Kano kuwa an kawo ma’anonin siyasa har guda huɗu da suka haɗa da:

-Tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu da shawarwari da su.

- Ko kuma rangwame musanman a ciniki.

-Da kuma ma’anar siyasa da ke cewa, dabara ce ko wayo.

-Da kuma ma’anar siyasa ta iya hulɗa da jama’a.

Waɗannan ra’ayoyi sun sha bamban da na Lawal (1983). Domin shi cewa ya yi siyasa, tana nufin halayyar cim ma wani buri dangane da mutane ko kuma gwamnati.

 Shi kuwa Gusau (1984) ya yi tsokaci a kan ma’anonin siyasa har guda biyu inda yake cewa: Ma’anar ta farko ita ce; siyasa tana nufin gudanar da mulki ko tafiyar da mulkin jama’a ta ba wa kowa haƙƙinsa. Ma’ana ta biyu kuwa ita ce; a wajen Bahaushe idan ya ce ya yi min siyasa yana nufin:

-Yaudara ko dabara

-Sauƙi ko rangwame

-Lumana ko lallami

A taƙaice siyasa tana nufin hanya ta tafiyar da mulkin jama’a a zamanance ko a gargajiyance. Kuma dabara ce ta iya jan hankalin mutane ta hanyar karkata inda suka sa gaba, a kowane fage. Misali idan ɗan siyasa ya lura da abin da mutane suke so, shi ma sai ya nuna yana tare da su ko da kuwa ba da gaske yake ba. Ke nan ta haka a iya cewa duk wanda ya iya shan kan mutane ya iya siyasa ko da kuwa hanyar yaudara ce Imam (2002).

 Ƙasar Hausa

Ƙasar Hausa, ƙasa ce mai girman gaske musamman dangane da fili, tsari da kuma irin albarkatun da ke tattare a cikinta. Ƙasar Hausa, tana da girma da faɗin gaske, domin idan muka duba iyaka za mu ga cewa ta yi wani irin zagaye ne mai yawa. Kasancewar ƙasar Hausa ba ƙarƙashin jagorancin shugaba ɗaya take kafin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyoba, shi ya sa masana suke ta mamaren ina ne iyakacin ƙasar take, ta kowane ɓangare. A bayanin wasu masana, sukan shata ƙasar ne ta la’akari da wuraren da masu magana da harshen Hausa suke zaune Gobir (2012:32).

Masana da suka haɗa da Ibrahim (1982) da Zarruƙ da wasu(1986) da Yakasai (1988) da Adamu (1997) da Sarki (2000) da Dunfawa da wasu (2007) da Abdullahi (2008) da Adamu (2010) da kuma Amfani (2011, 2012) sun kawo ra’ayinsu a game da ƙasar Hausa.

An nazarci ma’anonin da waɗannan masana da manazarta suka kawo a game da ko ina ne ƙasar Hausa, kuma bisa fahimta ra’ayoyin da masana suka kawo ya nuna cewa, ƙasar Hausa ita ce yankin arewacin ƙasar Nijeriya da kuma kudancin ƙasar Nijar.

Adawa A Cikin Waƙoƙin Siyasa A Ƙasar Hausa

A ƙarƙashin wannan sashe za a dubi siyasar zuwan Turawan mulkin mallaka ƙasar Hausa, za a kuma kalli zanguna uku na tsarin siyasar Najeriya. Zangunan da za a dubi waƙoƙin siyasa a cikinsu sun haɗa da Jumhuriya ta farko da ta biyu da kuma jumhuriya ta huɗu.

Adawa A Cikin Wasu Waƙoƙin Hausa Lokacin Turawa Mulkin Mallaka

A nan za a dubi yadda zuwan turawa ya gudana a ƙasar Hausa, musamman irin mamayar da suka yi wa ƙasar Hausa wadda ta haifar da rubuce-rubuce daga wajen masana ciki har da waƙoƙi da suka soki zuwan Turawa da dasisarsu. Tun kafin a san komai game da zuwan Turawa a ƙasar nan, mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya faɗa a cikin wasiyyar da ya yi wa jama’ar ƙasar nan, cewa zuwa gaba akwai waɗanda za su zo (Mani 1956:13). Duniyar baƙar fata ta sha yunƙure-yunƙure a kan nuna ƙin amincewarta ga mulkin Nasara da miyagun ɗabi’unsa. A wasu wuraren, yunƙurin akan yi shi da sunan addini wasu wurare da niyyar tunkuɗe baƙin haure ‘yan mu-kaɗai-muka-iya. A wasu wuraren kuwa, akan yi yunƙurin da niyyar kare sarautu da al’adun al’umma. Daular Usmaniyya ta yi yunƙurin kawar da Turawan mulkin mallaka da ƙarfin Allah tare da neman yardarsa da yunƙurinsu na jihadi. Duk da sanin cewa an yi ɗauki-ba-daɗi da gumuzu da accakwama da makafirtan Turai musamman a kwaninkan giginya. Malaman ƙasar Hausa da suka gane bakin zaren addini da sanin makirci da dasisar Yahudu da AnNasara ba su mayar da takobinsu a kube ba (Bunza 2002:2). An yi waƙoƙi a kan wannan manufa a kan Bature wasu kuma suka yi a kan Nasara waɗanda aka tsinkaya tamkar yin adawa da Nasara ne sakamakon zuwansa ƙasra Hausa wanda siyasa tana daga cikin dalilan zuwan.

Da farko za a fara dubin abun da Malam Ibrahim Khalihu Marinar Tsaminya ya faɗa a game da Nasara cikin waƙarsa “Dubu Musulmi” a cikin waƙar yana cewa:

…………..

71 - A’uzu Billahi da yin soyayya,

            Da kafiri mun fi da son ƙiyayya.

(Waƙar Dubi Musulmi: Ibrahim Khalilu Marinar Tsamiya Sakkwato)

A cikin wannan waƙa a fili aka nuna ƙiyayyaya a kan Nasara, babu wani ɓoye-ɓoye babu wani zancen shayi ƙarara aka nuna ba a son Nasara ba a tare da shi kuma ba za a bi shi ba. Da yin soyayya das hi gara a yi ta ƙiyayya har a mutu.

A gaba kuma, an ci karo da waƙar Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ta “Baturen Ingilishi” a cikin waƙar yana cewa:

 ……………

3 - Na roƙi mai girma shi yo mini buɗi,

            In zagi kafirin da ba su biyar da shi.

4 - Don wajibina gun Musulmi duk shi fal-

            Lasa kafiri, har dai Bature, don shi,

Ya ƙara labta wasu kalmomin domin jaddada manufa, a nan sai ya ce:

………..

6 - Don ja’irina, kafiri, kuma makiri,

            Ga halinsa kwas san shi bai ƙaunar shi.

 A gaba kuma sai ya ce:

……….

14 - Mi ag gare shi abin yabo, ba ko guda,

            Ƙarya munafunci da kissa gare shi.

 (Waƙar Baturen Ingilishi: Shehu Shagari)

Yana daga cikin zagi mai nauyi ka ce mutum kafiri ko ja’iri ko kuma makiri, dukkansu kalmomi ne na ɓatanci ga mutum. Ba tare da jin nauyin waɗannan kalmomi ba, Shehu Shagari ya labta su a kan Bature domin tsanin ƙiyayya da shi.

Adawa A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasar Jimhuriya Ta Farko

Akwai ƙungiyoyi da dama musamman na ƙabilun larduna daban-daban da suka rayu kafin da bayan samun ‘yancin kai, amma kusan duk waɗanda suka rayu kafin shekarun 1950, su ne suka narke a matsayin babbar jama’iyyar nan ta mutanen arewa wato NPC. Daga baya kuma wasu suka ɓalle daga NPC suka kafa NEPU.

Jamhuriya ta farko ita ce wadda ‘yan ƙasa suka yi mulkin ƙasa a matsayin gwamnatin farar hula. Ita wannan jamhuriya ta samu sanadiyar haɗuwar jama’iyyun siyasa daban-daban da suka haɗa da NPC wadda ita ce ke da mafi rinjayen kujeru a majalisar ƙoli da ita da jama’iyyar NCNC. Su kuma jama’iyyurn NEPU da AG sun fi rinjaye ne a jihohinsu. Jama’iyyar NPC ita ce ke da firayin minista da ministan harkokin waje da sauransu.

Hassan (2010 : 99-100) a jamhuriya ta farko wato kafin samun ‘yancin kai zuwa 1966 lokacin da aka yi juyin mulki na farko, siyasun da ake da su na yankuna ne. a tsohon yankin arewa akwai manyan siyasu guda biyu wato NPC da NEPU wacce ta zama babbar siyasar adawa a arewa. NPC ta samu rinjaye ta amfani da jami’an gwamnati NA da sarakuna, ita kuma takwararta ta NEPU ta samu goyon bayan talakawa da mata sa da masu aikin gwamnati da ƙananan ƙabilu. A taƙaice ana iya cewa tsakanin NPC da NEPU kamar dangantaka ce ta tsakanin mai mulki da wanda ake mulka.

Tun sanda ƙasar nan ta samu ‘yanci a shekarar 1960, siyasa ta zauna da gindinta. Jama’iyyar NPC ce ta fara kafa gwamnatin tarayya, a lokacin jihohi uku ne rak ake da su a Najeriya, watau jihar arewa da jihar gabas da jihar yamma. Jama’iyyar NPC ta kafa gwamnati ta yin ƙawance da jama’iyyar NCNC. Wannan gwamnati ta kai har shekarar 1966 lokacin da sojoji suka yi juyin mulki. A cikin wasu waƙoƙi na wannan jumhuriya da hannu yakai kansu, an fahimta akwai waɗanda suke ɗauke da adawa kamar haka:

A cikin waƙar Muhammadu Giɗaɗo ya yi wa NPC ya zargi mawaƙin NEPU da bai bayyana sunansa ba da cewa arne ne. ga abun da ya ce;

…………

Na ji wanda ya tsara waƙar NEPUNKA,

Asalinsa arne ne a Jos Sardauna.

Sunan ubansa Avom tsirara ma yake,

            Goyon tsiraici jakunan Sardauna.

(Waƙar NPC ta Yabon Sardauna: Muhammadu Giɗaɗo)

Dubi yadda aka ƙasƙanta wani mutum day a yi wa wata jam’iyya waƙa da cewa arne ne kuma ubansa ma arne. Hasali ma an bayyana cewa das hi da iyayensa rayuwar dabbobi suke yi ta zama tsirara.

A nan kuma ga abun da Aƙilu Aliyu yake faɗa:

A nan kuma NEPU ce ta yi nata habaicin ga takwararta NPC a inda Aƙilu ya yi ‘jifa a kasuwa’ ya ce akwai masu ci da gumin wasu da masu ƙarya da fasiƙai da ɓarayi da maƙaryata har ma da masu cin hanci a cikin NPC. Mawaƙain ya faɗi haka ne tare da cewa, wane da wane yake zargi da waɗannan kalamai na ɓatanci da ya yi, domin haka riga ce ya yanka duk wanda ya gwada ta masa daidai to da shi ake.

  ………….

37 – Ni abin da ya sa na ƙi su,

Yara har manya cikinsu,

So suke su ci ba guminsu,

            Ga munafinci da ƙarya.

38 – Ba su kunyar fasiƙanci,

Ba su aiki don karimci,

Ko suna tsare sa ci hanci,

            Sa yi sata sa yi ƙarya.

(Waƙar NEPU ta Jiya da Yau: Aƙilu Aliyu)

Haka kuma a gaba sai ya ƙara da cewa:

…………

 14 – Mai tumbi da washa,

Da ganin banza kwasa suke,

            Shugaba.

15 – Wasu manyan jakuna,

A cikin gona ɓarna suke,

            Shugaba.

 (Waƙar NEPU ta Maraba Maraba: Aƙilu Aliyu:)

An sakaya da bayyana duk wanda ya shiga NPC a matsayin munafiki kuma jahili a cikin addinin Musulunci. Duk wanda aka ce bai iya fatiya a cikin Musulunci ba, babu jahilin da ya fi shi ga abun da Gambo Hawaja ya faɗa;

 …………

 110 - Wa ke shiga NPC ban da munafiki,

Sai alhajin da ya kasa ƙarasa fatiya.

 (Waƙar NEPU ta ‘Yan Sawaba Gambo Hawaja)

Adawa A Cikin Wasu Waƙoƙin Siyasar Jimhuriya Ta Biyu

A ranar 21-09-1978 aka ɗaga takunkumin yin siyasa a Njeriya. Daga nan sai jam’iyyun siyasa suka fara fitowa. Daga cikin jama’iyyun da suka fara fitowa akwai UPN ta Obafemi Awolowo da NPP wacce daga baya ta koma GNPP ta Waziri Ibrahim sai kuma jama’iyyar NPN da kuma PRP ta Aminu Kano da kuma waɗansu ƙananan Jam’iyyun. Duka-duka an samu jama’iyyun siyasa sama da hamsin (Birniwa 1987:252). Daga cikin waɗannan, jam’iyyun siyasa guda biyar ne kawai suka sami rijista domin su ne suka cika sharuɗɗan da hukumar zaɓe ta ƙasa ta bayar. Jam’iyyun su ne UPN da NPP da GNPP da NPN da kuma PRP.

Ta la’akari da waɗannan jama’iyyu mutum yana iya fahimtar inda aka kwana, domin jama’iyyun suna da nasaba da zamanin jumhuriya ta farko. Jam’iyyar UPN tana da alaƙa da AG haka Jam’iyyar NPP tana da nasaba da NCNC. Ita kuma NPN da NPC yayin da PRP take da NEPU. Jam’iyyar GNPP ce kawai ba za a iya alaƙanta da wata jam’iyya ba a jumhuriya ta farko ba (Birniwa 1987:253).

Sa’id (2002:176-180) ya bayyana cewa jam’iyyar NPN a jumhuriya ta biyu aka kafa ta, ita kuma ta kafa gwamnati a wannan karon. Masu hamayya da ita sun nuna cewa ita gyauron NPC ce a jumhuriya ta farko, domin kusan yanayinsu ɗaya ne, dangane da manufofinta da aƙidarta. ita kuma PRP jam’iyya ce da aka kafa a jumhuriya ta biyu. Manufarta ita ce ƙwato ‘yancin talakawa da kuma kawar da zalunci, ta kuma kafa adalci. Shugabanta shi ne malam Aminu Kano, abin ƙauna mai ƙwato haƙƙin talakawa daga masu mulkin kama-karya, ya warware dukkan ƙangi.

An kalato wasu waƙoƙi daga cikin waƙoƙin siyasun wannan jumhuriya. Da farko ga Musa Madugu:

Musa Madugu ya yi wawar kora ta habaici a kan jam’iyyar PRP. Ya zayyana waɗansu halaye da ɗabi’u na wani mai riƙe da muƙamin siyasa a cikin jam’iyyar PRP. Ya yi bayani ta yadda duk wanda ya san wanda aka yi wa habaicin zai gane ko kuma idan ya san abun da ya faru a Kano a wancan lokacin wannan kuwa ta faru ne saboda rashin yarda da manufofinsu sai ya ce akwai wani mutum uwarsa da ‘ya’yansa suna amfani da guntun zanin ɗaurawa wadda kamar yadda aka sani wannan ba ɗabi’ar Hausawa b ace. Idan Bahaushe ya yi to ta zama wata baƙuwar al’ada a gurinsa domin haka ɗabi’ar wasu ƙabilu ce da ba Hausawa ba, ya kuma kira shi da gwamnan tsiya kuma baƙin azzalumi. A cikin waƙar sai ya ce;

………..

13 – Uwar ta ɗaura gyauto,

Matar ta ɗaura gyauto,

Shi ma ya ɗaura gyauto,

Ɗan banza gwamna ƙato,

            Jatau sarkin butulci.

………..

20 – Da sun jawo jikinsu,

Sai ‘yanfi ‘yan ta ƙi su,

Domin mugun halinsu,

Har Jatau shugabansu,

            Sarkin ‘yan fasiƙanci.

……….

23 – Zato da mumini ne,

Ashe gwamnan tsiya ne,

Jatau mugun kare ne,

Baƙin azzalumi ne,

            Mai zamba cikin aminci.

(Waƙar NPN ta Ya Allah Ka Ba Mu Aminci: Musa Madugu)

A gaba kuma duk da cewa sha’irin ya ambaci sunan wani itace da ake yin laƙabin suna da shi, wannan bai hana abun da ya faɗa ba ya zama habaici. Domin kuwa akwai mutane da yawa da suke amfani da wannan laƙabi. Rimi itace ne da sakkarawa suke yin sassaƙa da shi, haka kuma ana yin katako, amma kusan duk abun da aka yi shi da itacen rimi ba shi da inganci musamman abun da ya shafi aikin gini musamman wajen yin rufin gida. Wannan ta sa sha’irin ya dubi rashin ingancin itacen rimi ya yi habaicin domin nuna rashin amfaninsa da kuma nuna rashin yarda da shi. Ya yi amfani da shi wajen yin habaici ga wani mai riƙe da muƙamin siyasa ɗan jam’iyyar PRP. Duk dai a cikin waƙar ya danganta mutumin da Maitasine.[1] Mutumin da ake zargi da kawo miyagun manufofi domin jirkita addini Musulunci, da zarar an kwatanta mutum da Maitatsine an san ya zama mutumin banza. Baituka na ƙasa sun yi ƙarin haske a kan haka;

 ………..

28 - Rimi gautsi gare shi,

Reshe in ka bi shi,

Sai ya ja ma tsiyarshi,

Ɗa mai zagin ubanshi,

            Ba ɗa ne mai mutunci.

29 – In an ce gwamna wane,

Ta yaya za a gane,

Rimi iccen tsiya ne,

Duk ɗa in Maitatsine,

            Ya goya bai mutunci.

……….

46 – Kanawa kun faɗa ne,

Kun ce ba Maitatsine,

Bayan ga gwamna wane,

Ɗan gatan matatsine,

            Yana da rashin mutunci.

47 – Ɗan gatan Maitatsine,

Mun sheda murtadi ne,

Sannan kuma fasiƙi ne,

Mu shaida munafiki ne,

            Mai zamba cikin aminci.

 (Waƙar NPN ta Ya Allah Ka Ba Mu Aminci: Musa Madugu)

A ƙoƙarinsa na jan hakalin mata da su shiga jam’iyyar NPN Ɗunɗaye ya bayyana matan da suke cikin PRP da karuwai marasa kintsi. Saboda tsananin yawo a dandi har da manajan giya suke bakanta. Sai ya ce;

………

16 – Ku guje wa ɓarayin jama’iyya,

Wata karuwa mai satar miya,

Ita ce farkar manajan giya,

Daga jin reza ba tambaya,

            Sharri bakinta ya ɗamfara.

(Waƙar NPN ta ‘Yan santsi Gammon Sabara: Muhammad Sulaiman Ɗunɗaye:)

Zagi a matsayin hanyar nuna adawa ya faru a tsarin siyasar jumhuriya ta biyu, a inda jam’iyyar NPN ta bayyana adawarta ga PRP ta hanyar zagi kamar yadda aka kalato a cikin waƙar Muhammad Sulaiman Ɗunɗaye ta NPN mai suna ‘Yan Santsi Karnukan Farauta’.

A cikin waƙar ya yi amfani da kalmomi masu nauyi na zagi a kan ‘yan PRP ɓangaren santsi inda ya ce maciya amana ne manufa munafukai tun da akwai hadisi na Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam da yake bayyana alamomin munafuki guda uku, a wajen yin magana zai faɗi ƙarya sai ci amana da kuma karya alƙawari. Ya kuma yi tsinuwa a kansu inda ya ce ‘Allah ya tsine musu.’ Babbar magana da ya kawo ita ce ta komawar wasu ‘yan PRP cikin NPP inda ya bayyana su a matsayin kafirai tun da NPP jam’iyyar waɗanda ba sa yin sallah ce. Bai gushe a kan wannan zagi da ya yi wa abokan adawar siyasa ba sai da ya musu zagin ƙare dangi na shege wanda ya danganta su da rashin iyaye.

Marubucin wannan waƙa ta NPN Sulieman Ɗunɗaye ya jero waɗannan baituka ne ga jam’iyyar adawa ta PRP domin mutane su guje su ƙi ta su bijire mata su finjire su kuma yi tofin alatsine su kuma shiga jam’iyyarsa, dalilinsa kenan na cewa;

………..

21 – Laifinai za mu auna,

Jatau Sarkin hiyana,

Kare maciyin amana,

Allah tsine wa gwamna,

            Da ke yin fasiƙanci.

………..

25 - Tsinanne ɗan kunama,

Sarkin neman husuma,

Wai ‘yanfifi ya koma,

Yana neman muƙami,

            Saboda rashin mutunci.

………

27 – ‘Yan sunna sun guje ta,

Ga Jatau ya shige ta,

Du shegu ne ɗiyanta.

Ɗan sunna kar ka yi ta,

            Don ba ‘yanci cikinta.

 ………..

62 – Du wanda ya ce a canja,

Shege shi za mu canja,

Domin mun sami hujja,

Ga Bawa Rijau a Neja,

            Ya zarce cin mutunci.

 (Waƙar NPN ta ‘Yan santsi Karnukan Farauta: Muhammadu Sulaiman Ɗunɗaye:)

Adawa A Cikin Waƙoƙin Siyasar Jimhuriya Ta Huɗu

Jumhuriya ta huɗu ta fara ne daga shekarar 1999 zuwa wannan lokaci da ake ciki a yanzu. Jumhuriya ta huɗu ta rabu ya zuwa zanguna huɗu ana kuma shirin shiga zango na biyar nan ba da daɗewa ba. Zango na farko ya kama daga watan Mayu 1999 zuwa farkonn shekara ta 2003, zango na biyu kuwa ya fara daga watan Mayu 2003 zuwa farkon shekara ta 2007, a yayin da zango na uku na jumhuriya ta huɗu ya fara daga watan Mayu 2007 zuwa shekara ta 2011, sai kuma zango na huɗu da ya fara daga watan Mayu 2011 ya zuwa wannan lokaci, a yayin da ake shirin yin zaɓe domin shiga zango na biyar a cikin jumhuriya ta huɗu nan ba da daɗewa ba (Ɗan’Illela 2010:32).

Siyasa na da matsayi mai girma ga kowace al’umma, saboda irin wannan matsayi nata, sai mutane suka riƙa yi mata hidima iri-iri. Daga cikin hidimomin da ake mata akwai waƙa, wadda za a iya cewa ta fi alfanu kuma da ake yi da manufofi kala-kala. Waƙa na da muhimmanci sosai a fagen siyasa, don alfanunta da tasirinta ba zai misaltu ba, domin wata hanya ce ta isar da saƙo cikin sauƙi, mutane sukan zaɓe ta domin cimma burinsu na ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa da sauran makamantan haka (Isah 2012:1).

Mawaƙan siyasa na wannan zamani ma ba a bar su a baya ba wajen yin amfani da wannan hanya musamman daga ɓangaren adawa, suna amfani da irin wannan salo suna cin mutuncin abokan adawa musamman waɗanda jam’iyyarsu take kan mulki. An samu misalan irin wannan salo a cikin waƙoƙin siyasa na jumhuriya ta huɗu zango na huɗu kamar haka;

A nan za a farad a tsokaci daga waƙoƙin Aminu Ɗandago:

A cikin Waƙar APC ta ‘Sungumin Bugun Lema’ Ɗandago ya ɗaukko wani ɗan siyasa daga ɓangaren jam’iyyar da take mulki ya wulaƙanta shi, yana cewa a ɗaukko guduma a kashe shi mai hular tsiya, wato hularsa ba ta arziƙi ba ce. Ya kuma kira shi da ɗan giya wato maras mutanci da daraja. Bai tsaya a nan ba sai da ya ce masa jemage ne shi, ya zama shi ba tsuntsu shi kuma ba dabba ba, a ƙarshe dai ya zage shi ya ce uwarsa ƙazama ce, tun da so yake sai ya ga yankin arewa ya mutu murus ‘yan ‘yankin sun koma suna bara. Ga dai abun da ya faɗa nan cikin (bt na 61 da kuma na 62).

 …………….

61.              Hassan ɗau guduma ka wargaje mai malfar tsiya,

Tsohon ɗan kokino uban ‘yan farfaɗiya,

Jemage wanda baya kashinsa ta tsuliya,

Tantiri ɗan gidan ƙazama tantiriya,

            Ya samu a arkane arewa ga baki ɗaya.

62.              Hassan ɗau guduma ka wargaje mai malfar tsiya,

Tsohon ɗan kokino uban ‘yan farfaɗiya,

Jemage wanda baya kashinsa ta tsuliya,

Tantiri ɗan gidan ƙazama tantiriya,

            Gurinsa Arewa mui talauci da baƙar tsiya.

 (Sungumin Bugun Lema APC ta Aminu Ibrahim Ɗandago)

A gaba kuma ga abun da Dauda Kafutu Rarara ya faɗa;

……………..

1.                  Mun ji zancen tsohon Najadu bai duba gida ba,

Mai gudun dangi ko da yaushe zancen ka na duba,

Ba ya gane ƙamshin abinci bai manta kuɗi ba,

Ka yi tsufan ƙoƙon giya batu ya fasu mun ji.

2.                  Na ji Yakasai na faɗin a aiko da magirbi,

Ƙila in ya gani ya tuna ya san …………,

Don muna zaton tsoho ya cika ya gaza tumbi,

An yi tsufan kwando Nalako don ta fasu mun ji.

 (Waƙar APC Tsofan Najadu: Dauda Kafutu Rarara)

A cikin waƙar APC mai suna “Sungumin Bugun Lema” wadda Aminu Ɗandago ya yi, ya bayyana zambo na halayya ga abokan adawa. A cikin waƙar an muzanta ‘yan adawa da cewa shashashu ne kuma ‘yan iska. ya ƙara da cewa, mahaukata ne kuma kataɓarɓaru, manufa waɗanda ba su ds siffa mai kyau da tsari. ya bayyana haka ne a cikin (bt na 80, da kuma na85).                 

……………….

78.              Mai taya kishi ga kishiya shashashan gari,

Mai ba da gudunmuwa ga ‘yan iska shagiri,

An yi butulci a bara aka ɗau makatartari,

Shashashan babu wanda yat tsira da ko ɗari,

Bana ai hatara a duba masa toyayyiya.

……………..

85.              Baƙar motar can ku duba an tara mahaukata,

Sun lamunce da wanda zai ja ta ya sa wuta,

Suna ta faɗa wa direba ka da ma fa ya dakata,

Har ma da waɗanda ke faɗi sun shiga ba fita,

Jalla ka kare mu don saninmu ga baki ɗaya.

 (Sungumin Bugun Lema APC: Aminu Ibrahim Ɗandago)

Kammalawa

A cikin wannan takarda an yi ƙoƙarin tsokaci a kan ababen da ake ganin tamkar na adawa ne a cikin waƙoƙin siyasa kamar yadda aka tsikayo hakan. An yi ƙoƙarin kasa abubuwan gida-gida har huɗu da suka haɗa da zuwan Turawan mulkin mallaka ƙasar Hausa da kuma zamunan siyasar jumhuriya ta farko da ta biyu da kuma jumhuriya ta huɗu. A cikin waƙoƙin da aka nazarta, an yi taliyon abubuwan da ‘yan siyasa suka bayyana waɗanda tamkar na adawa ne. Ire-iren abubuwan da aka tsinkayo sun haɗa da zagi da cin mutunci da kuma abubuwan da ake gani tamkar tonon silili ne. An kawo waɗannan abubuwa ne domin a fahimta cewa, ‘yan siyasa suna amfani da abubuwan adawa a cikin waƙoƙi maimakon abubuwan na hamayya waɗanda su ne ya kamata a ce suna fitowa a cikin waƙoƙI ba zagi da cin mutnci ba.

Manazarta

Abdullahi, I. S. S. (2008) Jiya ba Yau ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa. Kundin Karatun Digiri na Uku, Sashen Harsunan Najeriya. U.D.U Sokoto.

Abraham, R. C. (1962) Dictionary of Hausa Language. London, Hodder and Soughton.

Adamu, M. (2010) Major Landmarks in in the History of Hausaland. The Eleventh Inaugural Lecture. Sokoto, Trans-Akab Printing and Publishing. U.D.U.Sokoto.

Ahmad, A. A. (2003) Nzarin Zambo-Zagi a Adabin Hausa: Tsokaci kan Siyasar Arewacin Nijeriya (1950-1960) Kundin Kammala Karatun Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, U.D.U Sokoto.

Amfani, A. H. (2012). Hausa da Hausawa: Jiya da Yau da Gobe. Festchscript in Honour of Prof. Ɗalhatu Muhammad. Department of African Languages and Cultures. A. B. U. Zaria.

Birniwa, H. A. (1987) Conservatism and Dissent: A Comparative Study on NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse From Circa 1946-1984. PhD Thesis Department of Nigerian Languages U. D. U. Sokto.

Bergery, G. P. (1933)            Hausa-English and English-HausaVocabulary. London, Oxford University Press.

Bunza, A. M. (2002) Gwagwarmayar Malaman Sakkwato da Dasisar Nasara. Yunƙurin bi-ta- da-ƙullin Akirka Cikin Waƙar Osho ta Malam Muhammadu Huci, Tahamisin Malam Mahrazu Barmu Kwasare cikn Juyayin Masana: Muƙalun Binciken Adabi da Harshe da Al’adun Hausawa don Juyayin Malam Habibu Alhassan (1935-1995). Huhkumar Fassara, Ofishin Fassara Jakadiyar UNESCO

CNHN/BUK (2006) Ƙamusun Hausa. Zaria, Ahmadu Bello University Press Limited.

Dunfawa, A. A (2007). Gudummuwar Kano ga Jagorancin Yaɗa Addinin Musulunci a Ƙasar Hausa Kafin Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodoyo. Al-Nahda: A Journal of Islamic Heritage vol 5 no 1&2. Center for Islamic Studies U. D. U. Sokoto.

Gobir, A. Y. (2012). Tasirin Iskoki ga Cututtuka da Magungunan Hausawa. Kundin Karartun Digiri na Uku. Sahen Nazarin Harsunan Nageriya. U. D. U. Sokoto.

Gusau, S. M. (1984) Waƙoin Noma na Baka: Yanaye-yaneyansu da Sigoginsu, Musamman a Sakkwato. Juzu’i na Ɗaya. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, BUK.

Hassan, B. M. (2010). Hausa Political Verse as an Effective Tool for Mobilisation. Ɗagel, Journal of Faculty of Arts and Islamic Studies. Vol IX. UDUSok.

Ibrahim, S. N. (1982). Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci kan Rayuwar Hausawa. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nageriya, B. U. K. Kano.

Idris, Y. (2010). Waƙoƙin Addini na Siyasa: Nazarin Waƙoƙin Emmanuel Wise mai Molo.             Kundin Kammala Karatun Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afirka. A.B.U. Zariya

Imam, A. H. (2002) Waƙoƙin Bijirewa na Tajadidi. Kundin Neman Digiri na Farko, Sashen Harsunan Nijeriya da Afirka. A. B. U. Zariya.

Isa, Z. (2013) Gudummuwar Mawaƙan Hausa ga Ci Gaban Arewacin Nijeriya: Nazarin Waƙar “Ajanda” ta Haruna Aliyu Ningi. 1st National Conference in Language, Lterature and Culture. Center for Study of Nigerian Languages, B. U. K.

Lawal, B. M. (1983) Waƙar “Gagara Ƙarya Sadauki” ta Buda Ɗantanoma. Kundin Digiri na Farko. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya da Afirka. Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Mani, A. (1966) Zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa. N.N.P.C Zaria.

Sarki, H. A. (2000). Tarihin Zuwan Musulunci Afirka da Shigowarsa Ƙasar Hausa. Babu wurin bugu.

Sa’id, B. (2002) Rbutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na Ashirin a Sakkwato, Kabi da Zamfara. Kundin Digiri na Uku. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. B. U. K

Usman, N. A. (2013). Gudummuwar Waƙoƙin Adawar Siyasa Wajen Haɓaka Adabin Hausa: Nazari Kan Waƙoƙin Haruna Aliyu Ningi. Takarda da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sanin a Ƙasa na Farko. C. S. N. L. Bayero University Kano.

Yakasai, A. S. (1988). Tarihin Hausawa da Yanayin Ƙasar Hausa. Department of Nigerian Languages. U D. U. Sokoto

Zarruƙ, R. M. et al (1986). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare. Liitafi na Ɗaya. Zaria, U. P. L. Plc.



[1] Wani mutum ne mai suna Alhaji Muhammadu Marwa Maitatsine da a ranar juma’a 18 -12-1980 da mutanensa suka yi yun}urin }wace masallacin cikin garin Kano da niyyar }wace ragamancin garin gaba ]aya domin ya]a gur~atattun manufofinsu da suke da’awar Musulunci ne. Wikipedia The Free Encyclopedia

Post a Comment

0 Comments