Ticker

6/recent/ticker-posts

Ba Ya Iya Saukewa Matarsa Hakkinta Na Aure Amma Kuma Yana Son Karin Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Menene hukuncin wanda ba ya iya sauke wa matarsa haƙƙinta, amma kuma a hakan yake son ya ƙara aure?

BA YA IYA SAUKEWA MATARSA HAƘƘINTA NA AURE, AMMA KUMA YANA SON KARIN AURE

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Haƙƙoƙin da suka hau kan miji a bayan aure sun haɗa da samar mata da wurin zama, ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, bayar da magani, da saduwa daidai gwargwado iyawarsa da ikonsa. Allaah Ta’aala ya ce:

{وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ}

Kuma ku rayu da su (matan aurenku) yadda aka sani a shari’a. (Surah An-Nisaa’: 19).

Idan dai zai iya bayar da waɗannan abubuwan gwargwadon iyawarsa da ikonsa, to Shari’a ta halatta masa sake yin wani auren, matuƙar dai zai iya yin adalci a tsakanin matan guda biyu ko uku ko huɗu a cikin hakan. Allaah Ta’aala ya ce:

{فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ}

Idan kuma ba za ku iya adalci ba, to ku auri guda ɗaya kawai, ko kuma abin da damarku suka mallaka. (Surah An-Nisaa’: 3).

Ma’anar adalci a nan shi ne: Daidaitawa a wurin rabon kwana da abinci da tufafi da sauran abubuwa makamantan hakan. Amma ba kamar yadda waɗansu mata suke tunani ba ne cewa, ya haɗa da cikin sakin jiki da murmushi da dariya da saduwa da makamantan hakan ba.

Wanda kuwa ya ƙi yin adalci a cikin abubuwan da Shari’a ta ambata, to yana da mummunar azaba a Lahira:

«مَنْ كَانَتْ لَهُ امْرَأَتَانِ فَمَالَ إِلَى إِحْدَاهُمَا، جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَشِقُّهُ مَائِلٌ»

Wanda yake da matan aure biyu sai kuma ya karkata a ɗayarsu, zai zo ranar Ƙiyama a halin gefensa ya shanye! (Sunan Abi-Daawud: 2133, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi).

Don haka duk wanda ya san ba shi da ƙarfin sauke wa matarsa wani abu na waɗannan abubuwan, kamar wanda ba ya iya gamsar da sha’awar iyalinsa, to bai halatta ya je batun ƙara aure ba.

Amma kuma a nan dole ne a san cewa saduwa da mijin aure gaskiya ne, ba drama ne daidai da shirin da ake gani a cikin waɗansu fina-finai ba. Don haka kar wata mace ta yi zargin wai mijinta ya gaza domin bai iya yi mata irin abin da aka nuna a cikin fim iri kaza ba! A Shari’a ana kallon iko da gwargwadon iyawar mijin ne kawai. Shiyasa ba daidai ba ne mace ta takura wa mijinta har sai ya wuce iyawarsa, abin da kan iya cutar da shi ko kuma ya kai shi ga kwanciya a asibiti.

Allaah ya ƙara mana fahimta.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

+2348021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments