Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Amfani Da Sunan Miji A Maimakon Na Mahaifi

TAMBAYA (188)

Assalamualaikum, barka da safiya malam, Allah ya Kara daukaka, nace Dan Allah ni matar aure ce kuma Ina da bukatan asanya ni a class domin in Kara ilimi kan abunda ban saniba.nagode🙏

Mlm inada tambaya, menene sunan da mace ya kamata tayi amfani dashi wajen Bude katin antenatal a asibiti, shin sunan mahaifinta ko na mijinta zata Saka? Nagode mlm.

HUKUNCIN AMFANI DA SUNAN MIJI A MAIMAKON NA MAHAIFI

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Bai halatta mace tayi amfani da sunan Mijinta ba saidai tayi amfani da sunan mahaifinta

Wannan sunan Miji da suke sakawa koyine da Turawan Yamma amman ba Addini baneba

Abinda ya tabbata a Qur'ani da Sunnah shine kowa a kirashi da sunansa da na mahaifinsa

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya dauki Sahabi Zaidu Ibn Harith (Radiyallahu anhu) tun yana yaro, ya taso ya girma a gidansa, lokacin da iyayen Zaidu suka ji labarin yana wajen Ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam sai suka zo don su tafi dashi

Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya bashi zabi kodai ya bi iyayensa ko Kuma ya ci gaba da zama a qarqashinsa

Nan take Zaidu ya zabi ya ci gaba da zama da Annabi Sallallahu alaihi wasallam

A lokacinne Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya kirashi da Zaidu Ibn Muhammad

Daga baya Kuma Allaah Azzawajallah ya saukar da aya akan a dinga Kiran kowa da sunan iyayensa:

( ادْعُوهُمْ لِآبَائِهِمْ هُوَ أَقْسَطُ عِندَ اللَّهِ ۚ

الأحزاب (5) Al-Ahzaab

Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi ãdalci a wurin Allah.

Silar wannan ne sai ya koma Zaidu Ibn Harith

Akwai Kuma inda Allaah Azzawajallah yace:

( مَّا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَا أَحَدٍ مِّن رِّجَالِكُمْ وَلَٰكِن رَّسُولَ اللَّهِ وَخَاتَمَ النَّبِيِّينَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمًا )

الأحزاب (40) Al-Ahzaab

Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme.

To Kinga kenan wannan qalubale ne ga Mata musamman wadanda suke auren hamshaqan masu kudi ko Kuma masu Sarauta ko wani Honorable ta yanda zakiji ana danganta ta da Mijin ta maimakon mahaifin da ya haifeta

Shawarar da Zan baki ko Kuma wadda tasa kiyi Mata Tambayar shine a gaggauta canza wannan sunan daga na Mijin ta ya koma mahaifinta saboda a ranar Lahira zaa Kira mace ne da sunan iyayenta bawai Mijinta Kamar yanda Ibn al-Qayyim Aljauziyya ya kawo cikakkun bayanan a cikin shahararen littafinsa Mai suna: "Tuhfatul Maudu bi Ahkamul Maulud" (Newborn Baby Guide) ma'ana: "Hukunce hukuncen jariri daga Haihuwa zuwa suna"

Gameda batun sabuwar makarantar: "MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI", zan turo miki dokokin sai ki karanta a tsanake

Wallahu taala aalam

Muna muku tallar sabuwar makarantar Online mai suna: "MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI". Wanda yake da ra'ayin shiga yayi magana ta Private hukumar makaranta zata turo masa tsare - tsare da dokokin shiga

(WhatsApp: 07035387476)

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments