𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mahaifina ne ya rasu ana binsa bashi, amma ba a san wanda yake binsa bashin ba. To yaya za a iya biya masa bashin?
YA RASU ANA BIN SA BASHI AMMA
BA A SAN WANDA YAKE BIN SA BASHIN BA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Asali dai wajibi ne kowane mai haƙƙi ya tabbatar da haƙƙoƙin da suke a kansa a
rubuce kafin zuwan mutuwarsa. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya ce:
«مَا حَقُّ امْرِئٍ مُسْلِمٍ لَهُ شَيْءٌ يُوصِي
فِيهِ، يَبِيتُ لَيْلَتَيْنِ إِلَّا وَوَصِيَّتُهُ مَكْتُوبَةٌ عِنْدَهُ»
Ba haƙƙin
wani musulmi ba ne wanda yake da wani abin yin wasiyya, amma ya kwana har
darare biyu face dai wasiyyarsa tana nan a wurinsa a rubuce. (Sahih
Al-Bukhaariy: 2738; Sahih Muslim: 1627).
A irin wannan wasiyyar ce yake rubuta sunaye da lambobin wayar waɗanda suke bin sa bashi, da adadi ko yanayi da
nau’ukan abin da suke bin sa. Ta yadda da zaran ya cika za a yi gaggawan neman
su har kuma a iya sauke masa wannan nauyin tun kafin ma a kai shi makwancinsa.
Amma idan aka samu irin wannan mamacin da ba a san wanda yake bin sa
bashi ba, to babu abin da ya rage sai dai kawai a yi sadaka da wannan abin, da
fatar Allaah ya isar da ladan ga shi mai haƙƙin. Idan kuma daga baya mai haƙƙin ya zo, sai a yi
masa bayanin abin da aka yi da haƙƙinsa. Idan ya yarda shikenan. Idan kuma bai
yarda ba sai magadan mamacin su biya shi daga cikin dukiyarsu. Ladan sadakar ya
komo gare su kenan, in sha’al Laah.
Allaah ya ƙara mana fahimta.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
+2348021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.