𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Wai wanene ya fara yin Tajweedin
Ƙur’ani? Kuma mutum nawa
ne suka yi Tajweedin Ƙur’ani a bayansa?
WANE NE YA FARA YIN TAJWEEDIN AlƘUR’ANI?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Ma’anar At-Tajweed a wurin malamai, wani ilimi ne
wanda da shi ake sanin yadda ake kyautata karatun Alƙur’ani, ta hanyar bai wa kowane harafi daga cikin
haruffan Alƙur’anin haƙƙinsa da duk abin da ya
cancance shi, kamar ta kula da mafitarsa da siffofinsa da hukunce-hukuncensa da
sauransu.
Yin aiki da ƙa’idojin At-Tajweed a wurin karatun Alƙur’ani wajibi ne a kan duk mai karatun Alƙur’ani, kamar yadda malamai suka faɗa:
وَالْأَخْذُ بِالتَّجْوِيدِ حَتْمٌ لَازِمٌ * مَنْ لَمْ يُجَوِّدِ
الْقُرْآنَ آثِــمٌ
لِأَنَّــهُ بِــهِ الْإِلَـــهُ أَنْـــــزَلَا * وَهَكَـذَا
مِنْهُ إِلَيْنَـا وَصَـلَا
Kuma yin aiki da Tajweed dole ne lazimi, duk wanda
ba ya Tajweedin Ƙur’ani mai zunubi ne.
Saboda da shi ne Allaah ya saukar, haka nan daga
gare shi zuwa wurinmu da sadaddun isnadai. (Al-Jazariyyah na Al-Imaam
Al-Jazariy)
Dalilai ko Hujjojin da suka nuna wannan wajibcin
suna da yawa a cikin Alƙur’ani da Hadisi, kamar inda Allaah Ta’aala ya ce:
الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَتْلُونَهُ حَقَّ تِلَاوَتِهِ
أُولَئِكَ يُؤْمِنُونَ بِهِ
Wanda muka ba su Littafi suna karanta shi a bisa
haƙƙin karatunsa, waɗannan su ne suka yi imani da shi. (Surah Al-Baƙarah: 121)
Daga cikin malaman da suka fassara wannan ayar
akwai Sahabi Abdullaah Bn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhu) wanda ya ce:
وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ ، إِنَّ حَقَّ تِلَاوَتِهِ : أَنْ
يَحِلَّ حَلَالَهُ وَيُحَرِّمَ حَرَامَهُ ، وَيَقْرَأَهُ كَمَا أَنْزَلَهُ اللهُ ،
وَلَا يُحَرِّفَ الْكَلِمَ عَنْ مَوَاضِعِهِ ، وَلَا يَتَأَوَّلَ مِنْهُ شَيْئاً عَلَى
غَيْرِ تَأْوِيلِهِ
Na rantse da wanda rai na ke a hannunsa! Haƙiƙa, haƙƙin karatunsa shi ne: Ya halatta abin da Alƙur’ani ya halatta
kuma ya haramta abin da ya haramta, kuma ya karanta shi kamar yadda Allaah ya
saukar da shi, kuma kar ya sauya kalmominsa daga wuraren da aka ajiye su, kuma
kar ya fassara wani abu daga cikinsa ba da irin fassararsa ba.
Karanta shi kamar yadda Allaah ya saukar da shi,
shi ne a karanta shi da Tajweed. Wannan kuwa wajibi ne, tun da dai yin hakan
yana daga cikin siffar masu imani.
Kuma Allaah Ta’aala ya ce:
وَرَتِّلِ الْقُرْآنَ تَرْتِيلًا
Kuma ka jera karatun Alƙur’ani daki-daki. (Surah Al-Muzzammil: 4)
Sannan kuma daga cikin malaman da suka fassara
wannan ayar akwai babban Tabi’in nan Al-Hasan Al-Basariy (Rahimahul Laah).
Al-Imaam Ibn Jareer At-Tabariy ya riwaito da isnadinsa kyakkyawa daga gare shi,
inda ya faɗa a kan ma’anar wannan
ayar cewa:
اقرأه قراءة بينة
Ka karanta shi karatu a fili bayyananne.
Wannan kuma ba ya samuwa sai ga wanda ya bi ƙa’idojin Tajweed a wurin karatunsa. Kuma bin wannan umurnin
na Allaah Ubangijin Halittu wajibi ne, kamar yadda yake a asali.
Yana daga cikin aikin da Tajweed kyautata murya da
karatun, kamar yadda Sahabi Al-Baraa’ Bn Azib (Radiyal Laahu Anhu) ya riwaito
daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
زَيِّنُوا الْقُرْآنَ بِأَصْوَاتِكُمْ
Ku ƙawata Alƙur’ani da muryoyinku. (As-Saheehah: 772)
Kuma Sahabi Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya
riwaito daga gare shi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
لَيْسَ مِنَّا مَنْ لَمْ يَتَغَنَّ بِالْقُرْآن
Wanda ba ya kyautata muryarsa da karatun Alƙur’ani ba ya tare da mu.
(Sahih Al-Bukhaariy: 7527)
Kuma daga cikin waɗanda suka yi fice da zaƙin murya a wurin karatu tun a zamanin farko akwai
sahabi Abu-Musa Al-Ash’ariy (Radiyal
Laahu Anhu), wanda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce masa:
يَا أَبَا مُوسَى ، لَقَدْ أُوتِيتَ مِزْمَاراً مِنْ مَزَامِيرِ
آلِ دَاوُدَ
Abu-Musa, haƙiƙa an ba ka murya mai zaƙin murya irin zaƙin muryar Annabi Daawud
(Alaihis Salaam). (Sahih Al-Bukhaariy: 5048; Sahih Muslim: 793)
Yana daga cikin Tajweed a cikin karatun Alƙur’ani a riƙa yin madda (tsawaita
murya) a wurarensu. Saboda an tambayi Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) a kan
yadda karatun Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ke? Sai ya ce:
كَانَتْ مَدّاً. ثُمَّ قَرَأَ بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
، يَمُدُّ بِبِسْمِ اللهِ ، وَيَمُدُّ بِالرَّحْمَنِ ، وَيَمُدُّ بِالرّحِيمِ
Karatunsa ya kasance mai madda (tsawaitawa) ne:
Sai kuma ya karanta: Bismil Laahir Rahmaanir Raheem. Sai ya tsawaita: Bismil
Laah, kuma ya tsawaita: Ar-Rahmaan, kuma ya tsawaita: Ar-Raheem. (Sahih
Al-Bukhaariy: 5046)
Yana daga cikin kyakkyawan Tajweed a Sunnah a riƙa tsayawa a ƙarshen kowace aya, domin
haka Ummu-Salamah (Radiyal Laahu Anhaa) ta siffata karatun Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), cewa:
يَقْطَعُ قِرَاءَتَهُ آيَةً آيَةً
Yana yanke karatunsa aya-aya. (Sahih At-Tirmiziy:
3/13; 2927)
Sakamakon mai kyautata karatun Alƙur’ani shi ne samun
Gidan Aljannah A Lahira. Sahabi Abdullaah Bn Amr (Radiyal Laahu Abhumaa) ya
riwaito daga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
يُقَالُ لِصَاحِبِ الْقُرْآنِ : اقْرَأْ وَارْتَقِ وَرَتِّلْ
كَمَا كُنْتَ تُرَتِّلُ فِي الدُّنْيَا ، فَإِنَّ مِنْزِلَكَ عِنْدَ أَخِرِ آيَةٍ تَقْرَؤُهَا
Za a ce wa makarancin Alƙur’ani: Karanta ka ƙara hawa, kuma ka kyautata karatun daki-daki kamar
yadda kake yi a duniya. Domin masaukinka yana a aya ta ƙarshe ce da kake iya karantawa. (Sahih
At-Tirmiziy: 2329)
Daga waɗannan bayanan a
taƙaice ya fito fili cewa:
1. Wanda aka saukar masa da Alƙur’ani, watau Manzon
Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) shi ne wanda ya fara yin
Tajweedin Alƙur’ani.
2. Daga bayansa kuma sai Sahabbansa musamman irin
su Abu-Musa Al-Ash’ariy (Radiyal Laahu Anhum). Sai kuma waɗanda suka bi hanyarsu daga cikin Taabi’ai da mabiyansu da
kyautatawa har zuwa yau, kuma har zuwa Tashin Ƙiyama.
Allaah ya datar da mu ga bin hanyarsu har zuwa ƙarshenmu.
WALLAHU A’ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.