Ticker

6/recent/ticker-posts

Barayin Gona

TAMBAYA (170)

Assalamualaikum, Malam dafatan antashi lafiya barka da safiyar Juma a. Don Allah Malam menene maganin matsafa masu dauke kuruwar amfanin gona. Agaskiya da anabani labarin cewa ana dauke kuruwar amfanin gona bana yarda. To amma yanzu gona ta kullum abin sai ƙara raguwa yakeyi.

Dama makwabta na sun camfi wani mutum Wanda keda gona a tsakanin gonakin mu da cewa yakan iya dauke kuruwar amfanin gonar wani zuwa tasa gonar. Abinda na kula shi ne ,gonar shi ko Rabin tawa batayi ba Amma yakan dibi amfanin da ni Mai babban gona bana diba Kuma ba gyara gonna tashi yake yi fiye damu ba. Don Allah Malam in akwai wata addua ta musamman a taimaka mana don kare gonakin mu. Nagode 🙏

Ai ganin wannan labarin ne yasa na tuna da wannan matsalar tawa Malam. Don baka fayyace mana irin addu,o in da kabashi ba. Shi yasa nayi wannan tambayar kozan sami mafita. Don agaskiya abin Yana damu na, har ma Ina tunanin hakura da noma gonar. Duk da cewa gona ce da na gada awajen mahaifina.

ƁARAYIN GONA

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Lahaula wala ƙuwwata illa billah

Shi wancan mutumin indai ya tabbata Haka yake to tabbasfa da akwai taimakon bokaye a lamarinnasa Kuma Duk Wanda ya je wajen Dan duba to sallarsa ta Kwana 40 baa amsarta

Wanda Kuma ya yarda da Dan duba to haƙiƙa ya kafircewa abinda aka saukarwa da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallam

A shawarce kayi masa tsayuwar dare ta hanyar miƙawa Allaah kokenka sannan Kuma Abu na biyu shine kaje ka samu mutumin ka ƙulla alaƙar kasuwanci dashi

Ka biyo Masa ta inda yake da naƙasu (weakness point) ma’ana tunda son abin duniyane a gabansa to ka bincika sana’arsa sannan ka ƙulla alaƙar business dashi ka dinga yi masa ihsani idan kuma wannan abinda yake mara kyau shi ya maida sanaa to dukda haka ka dinga yi masa ihsani

Idan ya gano cewar wannan gonarka ce to tabbas bazai sake ƙoƙarin cutarka ba in Sha Allaah

Kowacce mas’ala tanada mafita saboda dukkan tsanani yana tareda sauƙi kamar yanda Allaah Subhanahu wataala ya fada a Ƙur’ani mai girma

Wallahu taala aalam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments