Ticker

6/recent/ticker-posts

Ban Ga Wani Abin Da Ke Tabbatar Da Samuwar Allah Ba!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Wani farfesa ne a jami’a ya ce, wai a iyakacin bincikensa a cikin ilimi bai ga wani abin da ke tabbatar da samuwar Allaah ba! Wace amsa za a ba shi?

BAN GA WANI ABIN DA KE TABBATAR DA SAMUWAR ALLAH BA!

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Sai a ce masa: Ai wannan maganar da ma ba shi ne farau ba, kuma duk mahankalta sun san ba ta fitowa sai daga nau’uka mutane guda biyu: Ko dai zunzurutun maƙaryaci ko kuma cikakken mahaukaci.

1. Domin abin da shi kansa Allaah (Subhaanahu Wa Ta’aala) ya tabbatar a cikin Alƙur’aninsa a wurare da dama, littafin da a cikinsa ya ƙalubalanci dukkan mutane da aljanun duniya a kan su zo da irinsa, kuma har yau ba su iya kawowa ba, to kuwa idan ba mahaukaci ko maƙaryaci ba waye zai yi musun hakan, ya yi jayayya?

2. Sannan abin da dubunnan Annabawa da Manzannin Allaah (Sallal Laahu Alaihim Wa Alihim Wa Sallam) suka tabbatar da samuwarsa, waɗanda kuma su ke kammalallu, zaɓaɓɓu kuma cikakkun mutane a cikin hankali da ilimi da fahimta, da gogewa a cikin kyawawan ɗabi’u da halaye a tsawon tarihin duniya, to kuwa wanene zai yi musunsa in ba maƙaryaci ko mahaukaci ba?

3. Kuma abin da dubunnan miliyoyin mutane waɗanda suka rayu a baya da waɗanda suke rayuwa a yau a wannan duniyar - daga cikin mabiya addinin Musulunci da Yahudanci da Kiristanci da sauran mabiya addinin da asalinsa saukakke ne - suka tabbatar da samuwarsa, in ba maƙaryaci ko mahaukaci ba wa zai yi musun samuwarsa?

4. Sannan in ba maƙaryaci ko mahaukaci ba wanene zai kalli sama da ƙasa da bubuwan da su ke a tsakaninsu da waɗanda su ke a cikinsu, na rana, da wata, da taurari, da bishiyoyi, da tsire-tsire, da dabbobi, da tsuntsaye, da ‘yan ƙwari manya da kanana, a cikin tudu da ruwa da samaniya, da abubuwan da har yanzu ba a gama bincike an gano su ba, waye zai kalli irin kyakkyawan tsarin da suke gudana a kansa, da yadda suke tafiyar da harkokinsu a cikin rayuwa, sannan ya yi daawar wai babu wanda ya samar da su?

5. Kai ba ma sai an tafi da nisa ba, ko a cikin kira da ginin jikin mutum ma ai akwai hujja. Domin in ba motsattse ko mai ƙaryar tsiya ba wanene zai kalli tsarin injuna ko maaikatun da suke tafiyar da ayyuka a cikin jikinsa, kamar maaikatar numfashi, da abinci, da abin sha, da jini, da kashi da fitsari da zufa da ɗaukar ciki da haihuwa. Ga kuma sashen gani, da ji, da sansano, da ɗanɗano, da ji na shafawa. Ga kuma tsari da yanayin gashin kai da sauran gashin jiki, da yanayin fatun jiki, da tsoka da jijiyoyin jini da na kai saƙonni, ga ƙashi da ɓargo da kuma ƙumbuna da sauransu. Wanene zai kalli waɗannan a yadda suke sannan ya ce wai ba wanda ya samar da su, ko yake tsara musu hanyar gudanar da ayyukansu? Wai haka nan ne kawai suka samu a cikin cin sa’a (coincidence)?

6. Meyasa ba a taɓa cin sa’ar a wurin haihuwa ba, kamar a ga kura ta haifi akuya, ko kyanwa ta haifi ɓera, ko kuma mutum ya haifi kaza ko kifi ko ɗawisu ba? Ko kuma meyasa ba a taɓa cin sa’ar haihuwar wanda bakinsa na cin abinci a tsakanin ƙafafuwansa, kuma mafitsara da duburarsa a goshinsa ne ba? Ko kuma meyasa ba a ci saar haihuwar wanda cikinsa a gadon bayansa ne, idanuwansa kuma a ƙeyarsa ba? Meyasa?!

7. Sai a kwanakin nan ne fa da waɗansu maƙiya cigaban rayuwar mutum a duniya, daga cikin malaman kimiyya suka yi shisshigi wurin sassauya ƙwayoyin halitta a cikin magunguna da abincin (GMD), shi ne irin waɗannan matsalolin suka yawaita a cikin mutane: Inda ake haihuwar yara biyu da kai a haɗe da juna, ko jariri mai ido ɗaya ko mara mafitsara da sauransu! Meyasa a da babu irin waɗannan?

Kuma su da kansu masu irin wannan da’awar ta cewa babu Allaah, ƙarya kawai suke yi, kamar yadda Allaah Taaala ya ce:

 وَجَحَدُوا۟ بِهَا وَٱسۡتَیۡقَنَتۡهَاۤ أَنفُسُهُمۡ ظُلۡمࣰا وَعُلُوࣰّاۚ فَٱنظُرۡ كَیۡفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلۡمُفۡسِدِینَ

Kuma sun yi jayayya da ita (ayoyin gaskiya), alhali rayukansu sun sakankance da ita, domin zalunci da neman ɗaukaka. (Surah An-Naml: 14)

8. Idan kuma ba haka ba, meyasa ƙasashen Turai da suke yayata wannan daawar da tallata ta a duniya, meyasa idan wata masifa ta auka musu kamar iska da gobara da ambaliya saboda irin zaluncinsu kuma suka rasa yadda za su yi, sai shugabanninsu suke neman malaman addini su shigo cikin lamarin, su roƙa musu Allaah domin samun mafita? Sannan kuma ba ga shi nan ƙuru-ƙuru a cikin takardar kuɗin Amirka ba cewa: ‘In God We trust’ (watau, Ga Allaah Kaɗai Muka Dogara)?! Meye wannan, in ba ingiza mai kantu ruwa ba?!

9. Sannan tun da sun gano cewa ɗigon ruwa da ba su suka halitta shi ba, yana ƙunshe ne da hydrogen ɗaya da oɗygen biyu (H2O), me ya hana ba za su zauna su sauya hydrogen da oɗygen ɗin su koma ɗai-ɗai ko kuma biyu-biyu ba? Kuma da suka gano cewa ƙwan maniyin namiji guda ɗaya ne kawai yake iya shigewa a cikin ƙwan haihuwa guda ɗaya na mace a lokaci guda, me ya hana su cusa masa ƙwayayen maniyyi sama da guda ɗayan a lokaci guda?

10. Ko a yanzu ba irin wannan shisshigi da zaluncin ne ya kai su ga samar da kwayoyin cutar korona ba? Kamar yadda suka samar da na HIƁ domin wai su rage yawan jama’ar duniya?! Kuma kodayake manyan ‘yan siyasarsu suna cewa an samo rigakafin cutar ta korona (coɓid-19), ba ga ƙwararrun likitoci da manyan masana a cikinsu suna ta gargaɗin cewa kar wanda ya amince aka yi masa wannan allurar ba? Don me?! Domin suna tsoron cewa sinadaran da aka cusa a cikin allurar suna iya sauya tsarin DNA (ƙwayoyin halittar cikin jikin mutum) na dindindin, ta yadda mutum zai rasa siffa da ɗabi’u da halaye irin na mutum, kuma ba za a iya gyarawa ko a raba shi da wannan matsalar ba!

Iyakan abin da suke iyawa kenan yin shisshigi a cikin halittar da Allaah ya samar a cikin halitta, amma ba za su iya ƙirƙirar ko da wata ƙwayar halitta ta daban a cikin ɗakunan bincikensu, ba tare da kalatowa ko yin amfani da abin da Allaah Mahalicci Mai Girma ne ya halitta ba. Allaah Ta’aala ya ce:

 یَـٰۤأَیُّهَا ٱلنَّاسُ ضُرِبَ مَثَلࣱ فَٱسۡتَمِعُوا۟ لَهُۥۤۚ إِنَّ ٱلَّذِینَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَن یَخۡلُقُوا۟ ذُبَابࣰا وَلَوِ ٱجۡتَمَعُوا۟ لَهُۥۖ وَإِن یَسۡلُبۡهُمُ ٱلذُّبَابُ شَیۡـࣰٔا لَّا یَسۡتَنقِذُوهُ مِنۡهُۚ ضَعُفَ ٱلطَّالِبُ وَٱلۡمَطۡلُوبُ ۝ مَا قَدَرُوا۟ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦۤۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِیٌّ عَزِیزٌ

Ya ku mutane! An buga misali, sai ku saurare shi: Haƙiƙa! Waɗannan da kuke bauta musu ba Allaah ba, ba za su taɓa iya halittan ko ƙuda ba, kuma ko da sun taru sun haɗa-gwiwa a kan hakan. Kuma idan da ƙudan ya ƙwace musu wani abu, ba za su iya karɓo shi daga wurinsa ba. Mai nema da abin neman duk sun raunana. Ba su ƙaddara Allaah yadda ya cancanta a ƙaddara shi ba. Haƙiƙa Allaah, tabbas! Mai Ƙarfi ne, Mabuwayi. (Surah Al-Haajj: 73-74)

Allaah ya shiryar da mu, ya kare mu daga hanyoyin hallaka.

Wal laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments