Ticker

6/recent/ticker-posts

Tuna Ba’adiyyah A Cikin Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya manta da Sujadar Ba’adiyyah bai tuna ba sai a cikin wata sallah, yaya zai yi?

TUNA BA’ADIYYAH A CIKIN SALLAH:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

[1] An shar’anta Sujudar Rafkanuwa ne domin a cike giɓin da ya auku a cikin sallah sakamakon kuskure ko mantuwa. Don haka ba zai yiwu a yi watsi da Sujadar ba kwata-kwata saboda an manta ba a yi ta ba. Shiyasa malamai suka ce, wanda ya manta da Ƙabaliyyah har sai da ya yi Sallama, to sai ya zo da ita a bayan Sallamar. Ta zama Ba’adiyyah kenan. Amma idan Ba’adiyyah ce ya manta sai suka ce, lallai ya zo da ita a duk lokacin da ya tuna, ko da bayan shekara ne!

[2] Amma idan ya tuna da Ba’adiyyar a halin yana cikin wata sallah, to ba zai yiwu ya yi ta a cikin sallar ba, domin yin hakan ya zama ƙari ne da gangar a cikin wannan sallar. Haka kuma ba zai iya yanke wannan sallar domin ya yi sujadar ba. Domin yin hakan ɓata wannan sallar da yake yi ne da gangar, kuma Allaah ya hana hakan, a inda ya ce:

{وَلَا تُبْطِلُوا أَعْمَالَكُمْ}

Kuma kar ku ɓata ayyukanku. (Surah Muhammad: 33).

Don haka babu wurin da ya rage, sai dai ya yi sujadar da ya manta ɗin a bayan ya yi sallama daga wannan sallar da yake ciki.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments