Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Kana Da Hakki A Kan Shugaban Da Baka Zabe Shi Ba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam barka da yini ya kokari Allah yasaka da alkhairinsa Amin, mlm don Allah inada tambaya kamar haka. Jarabawa ce zamuje ta wurin aiki watau promotion eɗam to Kuma harda abokan aikin mu waɗanda ba musulmai ba. Shin ya hallata kayi ma Wanda ba musulmi ba addu’a akan Allah ya Baku nasara tare dashi.? Allah Saka da alkhairinsa Amin.

Sannan wai wajibi ne Idan ka Isa yin zaɓe sai kayi zaɓe dole? wai wasu suka ce idan baka Yi zaɓe ba bakada Wani hakki akan shuwagabanni. Shin yaya abun yake??

SHIN KANA DA HAKKI AKAN SHUGABAN DA BAKA ZAƁESHI BA?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Na’am. Kasan su kansu kafiran nau’i biyu ne. Akwai kafirin amana wanda ake ce masa ‘Dhimmiyyi’ sannan akwai kafirin da ba’a zaman lafiya tsakanin jama’arsa da ta musulmai, shi ana kiransa ‘Harbiyyi’.

Sannan kuma akwai wajibcin hakkin nuna so da kauna da goyon baya wanda ke tsakaninka da duk wani musulmi, mutukar dai babu wani dalili na shari’a wanda zai wajabta maka ka kaurace masa.

To game da tambayarka kuma, idan har akwai musulmai ‘yan uwanka wadanda suke neman wannan muƙamin tare dashi, kuma suma suna da kwarewa irin tasa ko fiye da tasa akan wannan aikin, to ba ya halatta gareka ka taimaka masa wajen samun daukaka akansu domin yin hakan zai iya jefaka cikin irin ayyukan munafukai kamar yadda Allah ya fada acikin Alƙur’ani yayin da yake yin bayani akan siffofi da ayyukan munafukai Yace:

الَّذِينَ يَتَّخِذُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِ الْمُؤْمِنِينَ أَيَبْتَغُونَ عِندَهُمُ الْعِزَّةَ فَإِنَّ الْعِزَّةَ لِلَّهِ جَمِيعًا

"SUNE WAƊANNAN DAKE RIKON KAFIRAI AMATSAYIN MASOYA BANDA MUMINAI, SHIN GIRMA SUKE NEMA AWURINSU?. TO HAKIKA GIRMA YANA GA ALLAH BAKI DAYANSA" (Suratun Nisa’i ayah ta 139).

Acikin wata ayar dake gaba da wannan kuma Allah Yace:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَتَّخِذُوا الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِ الْمُؤْمِنِينَ أَتُرِيدُونَ أَن تَجْعَلُوا لِلَّهِ عَلَيْكُمْ سُلْطَانًا مُّبِينًا

"YAKU MASU IMANI!! KADA KU RIKI KAFIRAI AMATSAYIN MANYAN MASOYANKU BANDA MUMINAI. SHIN KUNA SO KU SANYA WATA HUJJAH BAYANANNA GA ALLAH (DOMIN AZABTAR DAKU?) (Suratun Nisa’i ayah ta 144).

Al Imam Al-Hafiz Ibnu Katheer akan tafseerin wannan ayar cewa yayi : "Acikin wannan ayar Allah Maɗaukakin Sarki ya hana bayinsa muminai ne su riki kafirai amatsayin majibinta, ba muminai ba. Ana nufin yin abota ta kut da kut dasu, da yin aminantaka dasu, da fifita maslaharsu da sirranta musu bayanan sirri, da yin soyayya dasu aɓoye, da sanar dasu boyayyun sirrukan muminai kamar yadda Allah ya faɗa acikin wata ayar, Allah Yace :

"Kada muminai su riki kafirai amatsayin manyan majibintansu koma-bayan muminai, duk wanda ya aikata haka, tofa shi ba komai bane awurin Allah (Ma’ana babu ruwan Allah dashi) sai dai idan kuna tsoron wani abin tsoro ne daga garesu. Kuma Allah yana tsoratar daku game da uƙubarsa (wacce zata sameku idan har kuka aikata haka).

To kaga bisa hujjar wannan ayar bai halatta ka fifita maslahar wannan kafirin akan maslahar ‘yan uwanka muminai ba. Koda kuwa shi kafirin ya fisu kusanci dakai ta fuskar rayuwar yau da kullum, ko dangantakar jini, ko Ƙabila, ko wurin zama.

Sai amsar tambayarka ta biyu da ta uku : Idan mutum ya zama shugaba acikin al’ummah, to wajibi ne ya shugabancesu baki ɗaya bisa adalci ba tare da fifita wani ɓangare akan wasu ba, koda kuwa waɗancan ne suka zaɓeshi ko suka fi kaunarsa banda waɗannan.

Saboda hadithin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam wanda Yace : "DUKKANINKU MASU KIWO NE, KUMA DUKKANKU ZA’A TAMBAYEKU GAME DA KIWON DA AKA BAKU".

Bisa wannan ma’anar kaga duk wani shugaba sai ya amsa tambaya agaban Allah game da dukkan talakawan da suka rayu akarkashin Mulkinsa. Don haka wajibinsa ne ya fifita jin daɗin rayuwarsu da tsaron lafiyarsu fiye da tashi lafiyar ko jin daɗin, idan har yana fatan samun tsira agaban Allah aran Alƙiyamah.

Hakanan kowanne talaka yana da hakkin yin nasiha ga Shugaban dake milkinsa, sai dai ita nasihar tana da lokaci da wuri da yanayin da ya kamata ayita. Kuma wajibi ne mai yin nasihar ya kauce wa bakaken maganganu ko zagi ko cin mutunci acikin duk mahanar da zai yi.

Babu wata doka a addinance da ta wajabta wa dukkan mutane zaɓar Shugabannin da zasu mulkesu, sai dai ana fita ayi zaɓen ne domin kyautata maslahar kai da kai. Amma abinda aka saba gani daga Magabata ma shine kwamitin amintattu ne suke zama suyi shawarwari atsakaninsu su zaɓi wanda sukafi kyautata zaton samun fifikon kwarewarsa wajen gudanar da jagorancin jama’a, su sanyashi amatsayin Khalifah ko Amirul Mu’mineen (kamar yadda ya faru bayan zamanin Sayyiduna Umar lokacin da manyan sahabbai suka zauna sukayi shawara atsakaninsu suka zabi Sayyiduna Uthman ya zama Khalifa).

Shi kansa tsarin wannan siyasar da ake yi azamanin nan namu na cike da ruɗani, mai suna demokuradiyyah asalinsa an kirkireshi ne ba bisa dokokin addinin Musulunci ba. Tsari ne wanda wasu mutane suka kirkireshi bisa tsarin da zai dace da son ransu. wanda kuma idan aka bibiyeshi dalla-dalla za’a tarar da abubuwa masu yawa waɗanda suka ci karo da dokokin Allah (SWT).

Don haka idan lokacin zaɓe yayi, idan kaga kana ra’ayi kuma kana da iko, babu laifi ka fita kaje ka zaɓi duk mutumin da kake kyautata zaton samun adalci gwargwadon iko daga gareshi, ko awacce jam’iyyah ya fito. Kayi zaɓe bisa chanchanta shine yafi.

WALLAHU A’ALAM.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments