Ticker

6/recent/ticker-posts

Ma’anar Sunan Asiya Da Zaliha

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam. Menene Fassara Da Kuma Ma’anar Waɗannan Sunayen. (ÃSIYA DA ZALIHA)

MA’ANAR SUNAN ASIYA DA ZALIHA:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa’alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Yakamata mutum ya zaɓawa ‘ya’yansa sunaye kyawawa masu ma’ana kyakkyawa, ya nisanci zaɓar sunaye munana, Annabi sallallahu Alaihi wasallam yakasance yana duba zuwa ma’anar sunayen mutane, idan yaga ma’anar suna mummunace saiya canzawa mutum da kyakkyawan suna.

Muslim yaruwaito hadisi(2139) daka Abdullahi dan Umar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yacanzawa wata suna wanda ma’anarsa take nufin ( mai saɓo) ya canja mata da jamila.

Sunaye sunada dalilai na ambatarsu suna kuma da alaƙa tsakaninsu.

Ibnul ƙayyeem rahimahullahu Yace: " Allah cikin hikimarsa da hukuntawarsa da kaddarawarsa, yanaiwa rai ilhamar sanya suna abisa yanda za’a kirata dashi danya dace da hikimarsa tsakanin lafazi da ma’anarsa, kamar yanda ake samun dacewa tsakanin sababi da dalilansa.

Halaye da dabi’u da ayyuka munana suna janyo sunan daya dace dasu, kishiyoyinsu suna janyo sunayen daya dace dasu. Kamar yanda hakan yake tabbataccen acikin sunayen sifofi hakama yake asunayen Alam.

Ba’a ambaci Annabi sallallahu Alaihi wasallam da Ahmad da muhammad ba, sai saboda yawan halaye da ababen yabo masu tarin yawa atare dashi, saboda hakane tutar yabo take ahannunsa, al’ummarsa suka zamto masu yawan godiya, shine wanda yafi dukkan halittu girman godiya ga ubangijinsa, saboda haka yai umarni da kyautata sunaye Yace: ( ku kyautata sunayenku) domin mai kyakkyawan suna yana iya rayuwa abisa dabi’unda suka dace da kyakkyawan sunansa, sunansa kyakkyawa yana iya kaishi kyautata ayyukansa, saboda haka nema zakaga mafiya yawa daka cikin magabata sunayensu sun dace dasu, Mafi yawan daukakar dasuka samu tadace da sunayensu. " Tuhfatul maulud ( 146-147).

Sunan ÃÃSIYA yanada ma’anoni masu yawa acikin harshen larabci, daka ciki yana nufin magani, da tushen gini, Dukkan ma’noninsa kyawawane.

Amma kwai (ASIYA) wanda shi kuma yake nufin mai saɓo, wanda shine manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yaji ana kiran wata dashi cikin sahabbai yacanja mata da (JAMILA).

Amma ZALIHA sunane na alam wanda za’a gane cewa sunan watace, amma ma’anarsa tana nufin rauni. Shine bahaushe yake cewa, ZALIHA, ko ZULAI, ya halatta sanyawa mutum shi batare da la’akari da hararo ma’anarsa, lokacin sawa mutum shi.

WALLAHU A’ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments