𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Wani matashin malamin ɗarika ne a cikin ɓideo clip ya yi zargin cewa wai, Ibnul Ƙayyim ya rubuta a cikin littafinsa Al-Waabilus Sayyib cewa: ‘In masifa ta same su… In bala’i ya yi musu tsanani, ba Allaah suke roƙa ba, Ibn Taimiyyah suke zuwa wurinsa! Sai kuma su samu waraka!’ Menene gaskiyar wannan maganar?
NEMAN
TAIMAKON WANIN-ALLAAH:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
[1] Abu na-farko dai shi ne: Ko da hakan ya
tabbata daga gare shi (Rahimahul Laah), ko daga kowane malami ma daga cikin
malaman Ahlus-Sunnah, wannan ba ya zama hujja a kan mabiya tafarkin
Ahlus-Sunnah. Domin a wurin su, Littafin Allaah (Subhaanahu Wa Ta’aala) da
Sunnar Manzonsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) Sahihiya su ne kaɗai abubuwan riƙo da bi a cikin addini. Domin su ne kaɗai tsararru daga samun kuskure ko rashin daidaito a
cikinsu. Kowane malami, duk yadda ya kai da girma a cikin ilimi da fahimta, ba
tsararre ne daga yin kuskure ko mantuwa ko zamiya da sauran irin waɗannan siffofin na mutane ba. Don haka abin da ya fito
daga malami na saɓanin gaskiya ba
ya taɓa zama hujja abin kafawa domin rushe gaskiyar da ta
tabbata a cikin Al-Kitaab Was Sunnah. Al-Imaam Abul-Hajjaaj Mujaahid Bn Jabar
Al-Makkiy (Rahimahul Laah) ya fayyace wannan a cikin maganarsa cewa:
« لَيْسَ أَحَدٌ مِنْ خَلْقِ اللَّهِ إِلَّا وَهُوَ يُؤْخَذُ مِنْ
قَوْلِهِ وَيُتْرَكُ ، إِلَّا النَّبِيَّ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ »
Babu wani ɗaya daga cikin
halittun Allaah face akwai abin karɓa a cikin
maganganunsa akwai kuma na mayarwa, sai dai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam). (Jaami’u Bayaanil Ilmi Wa Fadlih: 2/925 (1762) na Ibn
Abdilbarr An-Numariy Al-Ƙurtubiy, wanda ya rasu: 463H).
[2] Na-biyu: Wannan wata hikima ce ta kafe abokin
magana a matsayin mai bayar da kariya ga kansa kawai, a hana shi ya zama mai ƙoƙarin kai hari ko kai farmaki. Ma’ana: waɗannan ‘yan bidi’a
su suke da abin suka a cikin al’amuransu na aƙeeda da ibada da mu’amalolinsu da shehunansu. Idan
suka bari bayanai da hujjojin malaman Ahlus Sunnah suka yaɗu, sun tabbatar asirinsu ne zai tonu, kuma ba za su kai
labari ba. Don haka sai suke tayar da irin waɗannan matsalolin, don su shagaltar da ɗaliban Ahlus-Sunnah wurin ƙoƙarin warware su. Ta haka sai su hana su yin magana a kan ayyukansu na
shirka da kafirci. Ko ba komai za su yi tunanin cewa, idan suka je magana a kan
hakan za a mayar musu da martanin cewa, ai ku ma kuna da matsala kwatankwacin
hakan!
An sha jin irin wannan maganar daga gare su, kamar
a kan fassarar ma’anar bidi’a, inda suke maimaita faɗin: ‘Ai ku ma ‘yan Izala kuna yin bidi’ar musabaƙa, da ta saukar karatu
ko yayen ɗaliban Islamiyyah, da
sauransu!’ Duk kuwa da sun san cewa, waɗannan abubuwa ne
da suke da alaƙa da tarbiyyar ɗalibai da neman ƙarfafa su ga neman ilimi kawai, irin yadda ake kulawa da irinsu tun tuni a
makarantun allo na gargajiya da makarantun boko na zamani ma. Ba abu ne da ke
da alaƙa da addini kai-tsaye,
irin bidi’o’insu na roƙon waliyyai a cikin ƙabruka da bukukuwan
maulidi da makamantansu ba.
[3] Na-uku: Tushe ko asalin addinin Musulunci ya
ginu ne a kan neman taimakon Allaah shi kaɗai kawai, ban da duk wanda ba shi ba.
1. Shiyasa aka ɗora wa kowane musulmi ya yi ta maimaitawa a kullum a
cikin sallarsa, ƙaranci sau goma sha-bakwai cewa:
{ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ }
Gare ka kaɗai muke bauta,
kuma daga gare ka kaɗai muke neman
taimako. (Surah Al-Faatihah: 5).
Kalmar ‘kaɗai’ da muka
ambata a wurin fassarar ta fito ne daga yadda ginin larabcin ya ke, kamar yadda
malaman Tafsiri suka yi bayani. Wannan tsari da ginin maganar ya fi kamar ya
ce: Na’buduka Wa Nasta’eenuka, wato: (Muna bauta maka, kuma muna neman
taimakonka). Domin wannan ɗin bai kore
bauta da neman taimakon wanda ba Allaah Ta’aala ba, saɓanin wannan maganar da Allaah ya tabbatar a cikin ayar
cewa: Iyyaaka Na’budu Wa Iyyaaka Nasta’een. Ya kore bauta da neman taimakon
kowa sai ga Allaah shi kaɗai kawai, wanda
babu abokin tarayya a gare shi ko da wani mala’ika ne makusanci, ko kuma wani
Annabi Manzo, balle kuma sauran halittu!
2. A kan bayanin wannan ayar ce kuma har shi kansa
Ibnul Ƙayyim ɗin (Rahimahul Laah) ya wallafa littafi guda mai suna:
Madaarijus Saalikeen Baina Manaazili Iyyaaka Na’budu Wa Iyyaaka Nasta’een, mai
shafuka kusan ɗari biyar.
Don haka daga nan, kowane mai hankali da tunani
yana iya tambaya: Ta yaya babban malamin da ya san wannan, kuma har ya yi
rubutu a kan shi zai koma ya saɓa masa?! Sai dai
idan an yi wa maganarsa mummunar fahimta ne, ko kuma wani abin yake nufi ban da
abin da mai magana yake faɗi.
3. Kuma a cikin hadisi Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa wa ɗan baffansa Abdullaah Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa)
cewa:
« يَا غُلَامُ إِنِّي أُعَلِّمُكَ كَلِمَاتٍ، احْفَظِ اللَّهَ
يَحْفَظْكَ، احْفَظِ اللَّهَ تَجِدْهُ تُجَاهَكَ، إِذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلِ اللَّهَ،
وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللَّهِ »
Kai yaro! Haƙiƙa zan karantar da kai waɗansu kalmomi muhimmai: Ka kiyaye dokokin Allaah, sai shi
kuma ya tsare ka. Ka kiyayi dokokin Allaah, sai ka same shi a gabanka. Idan ka
tashi roƙo, to ka roƙi Allaah. Kuma idan ka
tashi neman taimako, to ka nemi taimakon Allaah. (Sahih At-Tirmiziy: 2516).
4. Duk malaman da suka yi sharhin wannan hadisin
sun yarda cewa fassararsa shi ne: Allaah ne kaɗai ake roƙon sa, kuma shi ne kaɗai ake neman
taimakonsa a cikin komai. Ba Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ko wani wanda ke ƙasa da shi daga cikin halittun da su ke a sama da waɗanda su ke a ƙasa ba. Dubi Tuhfatul Ahwaziy: 7/185, da Jaami’ul Uluumi Wal Hikam, shafi: 192, da Sharh Al-Arba’een An-Nawawiyyah, shafi: 202 na Al-Uthaimeen, da kuma
Minhaajul Firƙatin Naajiyah,
shafi: 13 na Shaikh Ibn Jameel Zainu. Wannan shi ya taƙaito fassarar da Al-Imaam An-Nawawiy shi da kansa
ya yi wa hadisin, cewa:
إِذَا طَلَبْتَ الْإِعَانَةَ عَلَى أمْرٍ مِنْ أمُورِ الدُّنْيَا
وَالْآخِرَةِ فَاسْتَعِنْ بِاللهِ ، لَا سِيَّمَا فِي الْأُمُورِ الَّتِي لَا يَقْدِرُ
عَلَيْهَا غَيْرُ اللهِ ، كَشِفَاءِ الْمَرْضِ وَ طَلَبِ الرِّزْقِ وَالْهِدَايَةِ،
فَهِيَ مِمَّا اخْتَصَّ اللهُ بِهَا وَحْدَهُ ، قَالَ تَعَالَى : " و َإنْ يَمْسَسْكَ
اللهُ بِضُرٍّ فَلَا كَاشِفَ لَهُ إلَّا هُوَ".
Ma’ana: Idan ka tashi neman taimako a kan wani al’amari
daga cikin al’amuran duniya da lahira, to ka nemi taimakon daga Allaah ne.
Musamman ma a cikin al’amuran da wanin-Allaah ba shi da iko a kan su, kamar:
Warkar da cuta da neman arziki da shiriya. Duk waɗannan suna daga cikin abubuwan da Allaah ya keɓantu da su ne shi kaɗai kawai. Allaah Ta’aala ya ce: ‘Kuma idan Allaah ya
shafe ka da wata cuta, to babu mai yaye ta sai dai shi kawai.’ (Surah Al-An’am:
17).
7. Daga ƙarshe kuma ya kawo maganar babban shehin sufayen gaskiya, As-Shaikh Abdulƙaadir Al-Jeelaaniy
(Rahimahul Laah) a cikin littafin: Al-Fat-hur Rabbaaniy cewa:
"سَلُوا اللهَ وَ لَا تَسْأَلُوا غَيْرَهُ، اسْتَعِينُوا بِاللهِ
وَ لَا تسْتَعِينُوا بِغَيْرِهِ ، وَيْحَكَ! بِأَيِّ وَجْهٍ تَلْقَاهُ غَدًا ، وَ أَنْتَ
تُنَازِعُهُ فِي الدُّنْيَا ، مُعْرِضٌ عَنْهُ ، مُقْبِلٌ عَلَى خَلْقِهِ، مُشْرِكٌ
بِهِ ، تُنْزِلُ حَوَائِجَكَ بِهِمْ. وَ تَتَّكِلُ بِالْمُهِمَّاتِ عَلَيْهِمْ. ارْفَعُوا
الْوَسَائِطَ بَيْنَكُمْ وَ بَيْنَ اللهِ ، فَإِنَّ وُقُوفَكُمْ مَعَهَا هَوَسٌ، لَا
مُلْكَ وَ لَا سُلْطَانَ وَ لَا غِنىً وَ لَا عِزٌّ إلَّا لِلْحَقِّ عَزَّ وَ جَلَّ
. كُنْ مَعَ الْحَقِّ بِلَا خَلْقِ " (أيْ كُنْ مَعَ اللهِ بِدُعَائِهِ بِلَا
وَاسِطَةٍ مِنْ خَلْقِهِ).
Ma’ana: Ku roƙi Allaah, kar ku roƙi waninsa. Ku nemi taimakon Allaah, kar ku nemi
taimakon waninsa. Kaiconka! Da wace fuska za ka haɗu da shi Gobe Ƙiyama alhali kana jayayya da shi a duniya, kana mai kau-da-kai daga gare
shi, mai fuskantar halittunsa, mai yin shirka (tarayya) da shi, mai saukar da
buƙatunka gare su. Kana mai
dogaro a cikin muhimman al’amuranka gare
su! Jama’a! Ku ɗauke shamaki a
tsakaninku da Allaah, domin tsayuwanku tare da su nau’in hauka ne kawai! Babu
mulki ko sarauta ko wadata ko buwaya sai dai a wurin Allaah Sarkin Gaskiya
Mabuwayi Mai Girma kaɗai. Ka zama tare
da Allaah ba da halitta ba. (Wato: Ka zama tare da Allaah ta hanyar tsarkake
addu’a gare shi, ba tare da shamakin wata halittarsa ba). (Minhaajul Firƙatin Naajiyah, shafi: 13
na As-Shaikh Muhammad Bn Jameel Zainu, malami a Daarul Hadeethil-Khairiyyah da
ke birnin Makkah, ya rasu a ‘yan shekarun baya. (Allaah ya ji ƙan sa)).
[4] Na-huɗu: Su ‘yan ɗariƙa galibinsu suna da wani ra’ayi ne da ya
kafu a kan zaƙewa da
wuce-iyaka game da matsayin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam). Sun saɓa wa
daidaitaccen matsayin da Sahabbai da mabiyansu da kyautatawa su ke a kansa,
kyakkyawan matsayi matsakaici a tsakanin zaƙewa da taƙaitawa a cikin al’amura. Sun ɗaga matsayin Annabin Rahama (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) fiye da inda Ubangiji (Tabaaraka Wa Ta’aala) ya ajiye shi, na cewa
shi: Bawan Allaah ne shi kuma Manzon Allaah kaɗai. Wanda kuma ba shi da wata siffa ta ubangijintaka
(rubuubiyyah) ko kuma allantaka (uluuhiyyah).
(1) Asalin wannan mummunan ra’ayin sun samo shi ne
daga waɗansu da’awoyi guda uku:
1. Da’awar cewa wai, an halicci Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ne daga hasken Allaah Ubangijin Halittu
(Tabaaraka Wa Ta’aala)!
2. Da’awar cewa wai, an samar da Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) tun kafin a halitta Annabi Adam kakan talikai
(Alaihis Salaam)!
3. Da’awar cewa wai, sauran halittu daga gare shi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) aka samar da su!
Su kuma waɗannan da’awoyin
sun gina su ne a kan waɗansu riwayoyi na
ƙarya marasa tushe balle
makama, kamar riwayar da aka jingina wa Jaabir Bn Abdillaah (Radiyal Laahu
Anhumaa) cewa wai ya tambayi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) a kan abu na-farkon da Allaah ya halitta? Shi ne wai, ya bayyana masa cewa:
Abu na-farko da Allaah ya halitta shi ne, hasken
Annabinka (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) wanda ya fitar daga haskensa
(Subhaanahu Wa Ta’aala). Sannan lokacin da ya yi nufin halitta sauran halittu
sai ya raba wannan hasken gida huɗu, ya samar da
abubuwa uku daga cikinsa:
1. Alƙalamin Ƙudura.
2. Allon Lauhul Mahfuz.
3. Al-Arshi.
Ya raba shi gida huɗu.
Daga wannan (4) ɗin kuma ya samar da abubuwa uku:
1. Mala’iku maɗauka Al-Arshi.
2. Al-Kursiyyu.
3. Sauran Mala’iku.
Ya raba shi gida huɗu.
Daga wannan (4) ɗin kuma ya halicci abubuwa uku:
1. Gani na idanun muminai.
2. Hasken zukatansu, shi ne sanin Allaah Ta’aala.
3. Hasken rayukansu, shi ne Tauhidi. (Laa Ilaaha
Illal Laah, Muhammadur Rasuulul Laah).
Wannan riwaya ƙirƙirarriya ce ɓatacciya, domin
ko isnadin da za a dogara a kansa don hukunta ta ma ba ta da shi. Haka Al-Imaam
As-Suyutiy ya faɗa a cikin
Al-Haawiy Lil Fataawiy: 1/325, kamar yadda ya kawo a cikin littafin Huƙuuƙ Annabiy (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
Alaa Ummatihi Fee Dau’il Kitaab Was Sunnah, na As-Shaikh Muhammad Bn Khaleefah
Bn Aliy At-Tameemiy.
(2) Ko ba komai dai wannan aƙida mai cewa wai, Annabi ne farko halitta ta saɓa wa riwayoyi sahihai da suka zo a cikin sanannun
littaffan hadisai, kamar riwayar Ubaadah Bn As-Saamit (Radiyal Laahu Anhu)
wanda ya ji Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cewa:
« إِنَّ أَوَّلَ مَا خَلَقَ
اللَّهُ الْقَلَمَ »
Abu na-farko da Allaah ya halitta shi ne alƙalami. (Abu-Daawud:
4700, At-Tirmiziy: 2155, Ahmad: 22705).
Malamai suka ce: Yana nufin a bayan halittar
Al-Arshi kenan, saboda riwayar Imraan Bn Al-Husayn (Radiyal Laahu Anhu) cewa,
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
«كَانَ اللَّهُ وَلَمْ يَكُنْ شَيْءٌ قَبْلَهُ، وَكَانَ عَرْشُهُ
عَلَى المَاءِ، ثُمَّ خَلَقَ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضَ، وَكَتَبَ فِي الذِّكْرِ كُلَّ
شَيْءٍ»
Allaah yana nan, kuma babu komai kafin shi. Kuma
Al-Arshinsa ya kasance a kan ruwa. Sai ya halicci sammai da ƙasa, kuma ya rubuta
dukkan komai a cikin Littafi. (Sahih Al-Bukhaariy: 7418).
A nan duk babu ambaton halittar Annabi Adam
(Alaihis Salaam) ma, balle kuma halittar Manzon Allaah Annabi Muhammad (Sallal
Laahu Alihi Wa Alihi Wa Sallam).
(3) Amma duk da haka mutanen sun cigaba da yaɗa waɗannan ra’ayoyin
a tsakankaninsu, har abin ya zama musu aƙida tabbatacciya, wacce kuma manyansu suke karantar da ƙananansu. Duk kuwa da
kasantuwar hakan ya saɓa wa nassoshi
ingantattu daga cikin Al-Kitaab Was Sunnah, kamar waɗanda muka ambata ɗazun nan, da
kuma kamar Maganar Allaah Ta’aala Ubangijin Halittu, cewa:
{ خَلَقَ الأِنْسَانَ مِنْ صَلْصَالٍ كَالْفَخَّارِ وَخَلَقَ
الْجَانَّ مِنْ مَارِجٍ مِنْ نَارٍ }
Ya halitta mutum daga gasasshen yumɓu kamar kasko. Kuma ya halitta aljani daga harshen wuta
mai launuka mabambanta. (Surah Ar-Rahmaan: 14-15).
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
kuwa daga cikin jinsin mutane ya ke. Ba mala’ika ba ne, ba aljani ba ne. Allaah
Ta’aala ya ce:
{ قُلْ سُبْحَانَ رَبِّي هَلْ كُنْتُ إِلاَّ بَشَراً رَسُولاً }
Ka ce: Tsarki ya tabbata ga Ubangijina! Ai ni ba
kowa ba ne face dai mutum kawai manzo. (Surah Al-Israa’: 93).
Kuma Allaah (Subhaanahu Wa Ta’aala) ya ce:
{ قُلْ إِنَّمَا أَنَا بَشَرٌ مِثْلُكُمْ يُوحَى إِلَيَّ أَنَّمَا
إِلَهُكُمْ إِلَهٌ وَاحِدٌ }
Ka ce: Ni mutum ne kawai irinku: An yi mini wahayi
cewa, abin bautarku abin bautawa guda ɗaya ne. (Surah
Al-Kahf: 110).
Abu ne sananne kuwa cewa, Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) daga zuriyar Annabi Ismaa’il ne ɗan Annabi Ibrahim (Alaihimas Salaatu Was Salaam) ya ke.
Shi kuwa Annabi Ibrahim daga zuriyar Annabi Adam ne (Alaihimaa Wa Alaa
Nabiyyinaas Salaatu Wa Salaam). Kuma halittar Annabi Adam (Alaihis Salaam) a
matsayinsa na mutum na-farko, ta biyo bayan halittar mala’iku da sammai da ƙasa da dabbobi da sauran
halittu ne, kamar yadda wannan riwayar ta yi bayani:
«خَلَقَ اللَّهُ التُّرْبَةَ يَوْمَ السَّبْتِ ، وَخَلَقَ فِيهَا
الْجِبَالَ يَوْمَ الْأَحَدِ ، وَخَلَقَ الشَّجَرَ يَوْمَ الاثْنَيْنِ ، وَخَلَقَ الْمَكْرُوهَ
يَوْمَ الثُّلَاثَاءِ ، وَخَلَقَ النُّورَ يَوْمَ الْأَرْبِعَاءِ ، وَبَثَّ فِيهَا
الدَّوَابَّ يَوْمَ الْخَمِيسِ، وَخَلَقَ آدَمَ بَعْدَ الْعَصْرِ مِنْ يَوْمِ الْجُمُعَةِ
، آخِرُ الْخَلْقِ مِنْ آخِرِ سَاعَةِ الْجُمُعَةِ فِيمَا بَيْنَ الْعَصْرِ إِلَى اللَّيْلِ»
Allaah ya halitta turɓayar kan ƙasa a ranar Asabar, ya halitta duwatsu a cikinta a ranar Lahadi, ya halitta
bishiyoyi a ranar Litini, ya halitta abubuwan ƙyama a ranar Talata, ya halitta haske a ranar
Laraba, ya yaɗa dabbobi a cikinta a
ranar Alhamis, kuma ya halitta Annabi Adam (Alaihis Salaam) a bayan La’asar na
ranar Jumma’a, a matsayin halitta ta ƙarshe a sa’a ta ƙarshe ta yinin Jumma’a, a tsakanin La’asar zuwa dare. (Silsilah As-Saheehah: 1833).
Don haka dai, Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ba shi ne halittar farko da Allaah (Subhaanahu Wa Ta’aala) ya fara
yi ba.
(4) Haka kuma sun ƙirƙiro riwayoyi da dama domin tabbatar da aƙidar cewa wai, domin Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ne aka halitta duniya da abin da ke cikinta! Riwayoyi kamar
wannan:
أوْحَى اللهُ إلَى عِيسَى: يَا عِيسَى، آمِنْ بِمُحَمَّدٍ وَأْمُرْ
مَنْ أَدْرَكَهُ مِنْ أُمّتِكَ أَنْ يُؤْمِنُوا بِهِ، فَلَوْلَا مُحَمَّدٌ مَا خَلَقْتُ
آدَمَ، وَلَوْ لَا مُحَمَّدٌ مَا خَلَقْتُ جَنَّةً وَلَا نَارًا ...الخ
Allaah ya yi wahayi ga Annabi Isaa cewa: Ya kai
Annabi Isaa! Ka yi imani da Annabi Muhammad, kuma ka umurci wanda ya riske shi
daga cikin al’ummarka cewa, su yi imani da shi. Domin in ba domin Annabi
Muhammad ba da kuwa ban halicci Annabi Adam ba. In ba domin Annabi Muhammad ba
da ban halicci Aljannah ba, haka ma Wuta..!! (Al-Mustadrak: 2/614-615).
Malaman Hadisi suka ce:
Da farko dai wannan riwaya ce mauƙufiya, ba ta kai ga
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba.
Sannan kuma a cikin isnadinta akwai Amr Bn Aus,
wanda malamai suka siffata shi da cewa, majhuul haal ne.
Ita kanta riwayar kuma Al-Haafiz Az-Zahabiy ya ce
munkarah ce. A zatonsa ma yana ganin maudu’iyah ce (ƙirƙirarriya ta ƙarya). (Meezaanul I’itidaal: 3/246).
Sannan kuma shi ma Al-Haafiz Ibn Hajr Al-Asƙalaaniy a cikin
(Lisaanul Meezaan: 4/354) ya dace da shi a kan hakan.
Amma duk wannan ba wani abin kallo ko damuwa ba ne
a wurin mutanen. Su sun doge a kan riƙe irin waɗannan ruɓaɓɓun riwayoyin,
suka manta da abin da Ubangiji Ta’aala ya faɗa a cikin Alƙur’ani cewa:
{ وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالأِنْسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ }
Kuma ban halitta aljanu da mutane ba, sai domin su
bauta mini. (Surah Az-Zaariyaat: 56).
وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ
أَيَّامٍ وَكَانَ عَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا
وَلَئِن قُلْتَ إِنَّكُم مَّبْعُوثُونَ مِن بَعْدِ الْمَوْتِ لَيَقُولَنَّ الَّذِينَ
كَفَرُوا إِنْ هَٰذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ
Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki
shida, kuma Al’arshinSa ya kasance akan ruwa, dõmin Ya jarrabã ku, wannan ne
daga cikinku mafi kyãwon aiki. Kuma
haƙĩƙa idan ka ce: ‘‘Lalle kũ waɗanda ake tãyarwa ne a bãyan mutuwa,’’ haƙĩƙa waɗanda suka kãfirta sunã cẽwa: ‘‘Wannan bai zama ba fãce sihiri bayyananne.’’
(Surah Huud: 7)
إِنَّا جَعَلْنَا مَا عَلَى الْأَرْضِ زِينَةً لَّهَا لِنَبْلُوَهُمْ
أَيُّهُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا
Lalle ne Mũ, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa ce gare ta, dõmin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau
ga aiki. (Surah Al-Kahf: 7)
Da sauran ayoyi makamantan wannan, har ma da
maganarsa (Tabaaraka Wa Ta’aala) da ya siffata kansa da cewa:
{ الَّذِي خَلَقَ الْمَوْتَ وَالْحَيَاةَ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ
أَحْسَنُ عَمَلاً }
Shi ne wanda ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya
jarrabe ku: wanene daga cikinku zai fi kyautata aiki. (Surah Al-Mulk: 2).
Duk waɗannan nassoshi
ne a fili masu nuna hikimar yin halittu kawai ita ce, domin Allaah ya jarraba
bayinsa da umurni da hani a duniya, kuma daga ƙarshe ya yi sakayya gare su a lahira kowanne da
gwargwadon irin aikinsa. Amma sam! Allaah Ta’aala bai halitta duniya da abubuwan da ke cikinta domin
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), ko kuma domin wani daga cikin
halittunsa ba. Sahabbai masu daraja (Radiyal Laahu Anhum) ba su ji wannan
karatun daga gare shi ba (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
Allaah ya ƙara faɗakar da mu.
(5) Kai! Waɗansu daga cikin
masu zaƙewa a cikin mabiya
addinin ɗariƙa suna ganin halaccin yi wa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
wani nau’in ibada ma. Suna roƙon ya ba su irin abin da a ƙa’ida, ba a roƙon kowa sai Allaah a
kansu. Kamar neman saukar da ruwan sama, da gafarar zunubai, da cin nasara a
kan maƙiya, da samun aure ko
samun haihuwa. Haka kuma da neman mulki da shugabanci, da biyan bashi, da
warkar da mara lafiya, da sauran samar da alheri da amfani, da kuma kawar da
damuwa da baƙin-ciki. Duk waɗannan babu wanda ke da iko a kan su a cikin rayuwar
duniya sai Allaah shi kaɗai (Wahdahu Laa
Shareeka Lahu).
{ أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ، وَيَكْشِفُ السُّوءَ،
وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَاءَ الْأَرْضِ، أَإِلَهٌ مَعَ اللَّهِ، قَلِيلًا مَا تَذَكَّرُونَ }
Ko kuwa wanene yake amsa wa mabuƙaci idan ya kira shi,
kuma yake yaye damuwa da baƙin-ciki, kuma yake sanya ku halifofi a doron ƙasa? Shin akwai wani abin bauta tare da Allaah? Kaɗan ne ƙwarai kuke tunawa. (Surah An-Naml: 62).
(6) A taƙaice dai irin waɗannan mutanen
sun mayar da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) kamar yadda
kiristoci suka ɗauki Annabi Isaa
(Alaihis Salaam), sai dai kawai ba su yi furuci da allantakarsa ba ne!
Dubi abin da mai littafin Al-Mawaahibul
Ladunniyyah yake faɗi:
وَيَنْبَغِي لِلزَّائِرِ - لِقَبْرِهِ - أَنْ يَكْثَرَ مِنَ
الدُّعَاءِ وَالتَّضَرُّعِ وَالاسْتِغَاثَةِ وَالتَشَفُّعِ وَالتَّوَسُّلِ بِهِ - صلى
الله عليه وسلم-، فَجَدِيرٌ بِمَنِ اسْتَشْفَعَ بِهِ أَنْ يُشَفِّعَهُ اللهُ تَعَالَى
فِيهِ
Ya dace ƙwarai ga mai ziyara ga ƙabarin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yawaita yin addu’a da ƙanƙan-da-kai da neman agaji
da neman ceto da tawassuli da shi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
Domin ya cancanta ga duk mai neman ceto da shi Allaah Ta’aala ya karɓi cetonsa a gare
shi.
Har zuwa inda ya ce:
ثُمَّ إنَّ كُلًّا مِنَ الاسْتِغَاثَةِ وَالتَّوَسُّلِ وَالتَشَفُّعِ
وَالتَّوَجُّهِ بِالنَّبِىِّ- صلى الله عليه وسلم- كَمَا ذَكَرَهُ فِى «تَحْقِيقُ النُّصْرَة»
وَ «مِصْبَاحُ الظَّلَامِ» - وَاقِعٌ فِى كُلِّ حَالٍ، قَبْلَ خَلْقِهِ وَبَعْدَ خَلْقِهِ،
فِى مُدَّةِ حَيَاتِهِ فِى الدُّنْيَا وَبَعْدَ مَوْتِهِ فِى مُدَّةِ الْبَرْزَخِ،
وَبَعْدَ الْبَعْثِ فِى عَرَصَاتِ الْقِيَامَةِ.
Sannan kuma kowane ɗaya daga cikin neman agajin da tawassulin da neman ceton
da tawajjuhi ga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), kamar yadda ya
ambata a cikin Tahƙeeƙun-Nusrah da
Misbaahuz-Zalaam mai aukuwa ne a cikin kowane irin hali, kafin halittarsa da
bayan halittarsa, da cikin tsawon rayuwarsa a duniya, da bayan rasuwarsa a
tsawon zamansa a barzahu, da kuma bayan tashi a farfajiyar ƙiyama. (Al-Mawwahibul
Ladunniyyah Bil Manhil Muhammadiyyah: 3/604-605 na Abul-Abbaas Shihaabuddeen,
Ahmad Bn Muhammad Bn Abi-Bakrin Bn Abdilmalik Al-Ƙastalaaniy Al-Ƙutaibiy Al-Misriy, wanda ya rasu 923H).
Ka ga waɗannan duk ayyuka
ne waɗanda Allaah Ta’aala kaɗai ake yi wa su. Amma dubi yadda ya mayar da su ga Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Kuma dubi yadda ya mayar da shi mai
ji da gani da biyan buƙatu tun kafin ma a halicce shi, da kuma bayan ya rasu, har zuwa ranar Ƙiyama!
(7) Shiyasa daga cikin mummunar aƙidarsu, kamar yadda mai
littafin Huƙuuƙ An-Nabiyy ya kawo:
Akwai cewa: Neman taimako ko agajin Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fi neman agajin Ubangiji (Tabaaraka Wa Ta’aala)!
(Ar-Raddu Alal Bakriy, shafi: 349).
Akwai kuma mai tunanin cewa: Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya san zunubai da buƙatun bayi tun kafin su faɗe su, kuma yana da ikon yi musu gafara da ikon biya musu
buƙatunsu, kamar dai Allaah
Ta’aala babu bambanci. (Ar-Raddu Alal Bakariy, shafi:
30).
Akwai kuma mai tunanin cewa, babu wani wuri ko
wani lokacin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba ya nan a
cikinsa! (Ghaayatul Amaaniy: 1/48).
Kai! Shiyasa ma wani daga cikinsu yake faɗa a cikin waƙe cewa:
دَعْ مَا ادَّعَتْهُ النَّصَارَى فِي نَبِيِّهِمْ ... وَاحْكُمْ
بِمَا شِئْتَ مَدْحًا فِيهِ وَاحْتَكِمْ
وَانْسُبْ إِلَى ذَاتِهِ مَا شِئْتَ مِنْ شَرَفٍ ... وَانْسُبْ
إِلَى قَدَرِهِ مَا شِئْتَ مِنْ عِظَمٍ
فَإِنَّ فَضْلَ رَسُولِ اللهِ لَيْسَ لَهُ ... حَدٌّ فَيَعْرُبَ
عَنْهُ نَاطِقٌ بِفَمِ
Aje abin da Kirista suka faɗa a kan Annabinsu, ka hukunta duk abin da ka so na yabo
duk yadda ka so.
Ka jingina duk abin da ka so na daraja ga zatinsa,
ka jingina duk abin da ka so na girma ga matsayinsa.
Domin falalar Manzon Allaah ba ta da iyaka, balle
har mai magana ya iya bayanin ta da baki.
(Deewaanul Buuseeriy, shafi: 241 na Sharfuddeen
Muhhammad Bn Sa’eed Bn Hammaad Al-Januudiy As-Sanhaajiy, wanda ya rasu 696H).
Shiyasa duk ƙoƙarin da Ahlus Sunnah
suke yi na tabbatar da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a
kan matsayin da Allaah ya ajiye shi a kansa, sai ‘yan bidi’a - daga cikin ‘yan ɗariƙu da ‘yan shi’a da sauransu -
sai suke ganin hakan wai tawayewa ko kayar masa da daraja ne! Ƙasƙantar da shi ne!! Wannan kuwa kafirci ne ittifaaƙan!!! Kamar dai yadda
kiristoci suke fushi a lokacin da musulmi suka siffata Annabi Isaa (Alaihis
Salaatu Was Salaam) da siffofinsa na gaskiya, cewa Bawan Allaah, Annabin Allaah
kuma Manzon Allaah! Don haka a kullum suke ta neman hanyar da za su samu daman
yanke hukuncin kisa a kan Ahlus Sunnah Salafiyyah saboda dogewa a kan hakan da
suka yi!
Allaah ya kiyaye.
[5] Na-biyar: Ta yaya Ibn Al-Ƙayyim zai faɗi abin da wannan
mutumin yake zargi, alhali hakan ya saɓa wa aƙidarsa?!
(1) Al-Imaam Ibn Al-Ƙayyim (Rahimahul Laah) shi ne fa ya yi magana a
kan bambancin haƙƙin Allaah da na Manzonsa, kamar inda ya rubuta a cikin littafinsa Ar-Ruuh:
2/766-767:
"وَالْفَرْقُ بَيْنَ تَجْرِيدِ التَّوْحِيدِ وَبَيْنَ هَضْمِ
أَرْبَابَ الْمَرَاتِبِ أنَّ تَجْرِيدَ التَّوْحِيدِ أَنْ لَا يُعْطَى الْمَخْلُوقُ
شَيْئًا مِنْ حَقِّ الْخَالِقِ وَخَصَائِصِهِ، فَلَا يُعْبَدُ، وَلَا يُصَلَّى لَهُ،
وَلَا يُسْجَدُ وَلَا يُحْلَفُ بِاسْمِهِ، وَلَا يُنْذَرُ لَهُ، وَلَا يُتَوَكَّلُ
عَلَيْهِ، وَلَا يُؤَلَّهُ وَلَا يُقْسَمُ بِهِ عَلَى اللهِ، وَلَا يُعْبَدُ لِيُقَرِّبَ
إِلَى اللهِ زُلْفَى، وَلَا يُسَاوَى بِرَبِّ الْعَالَمِينَ فِي قَوْلِ قَائِلِ: مَا
شَاءَ اللهُ وَشِئْتَ، وَهَذَا مِنْكَ وَمِنَ اللهِ، وَأنَا بِاللهِ وَبِكَ، وَأَنَا
مُتَوَكِّلٌ عَلَى اللهِ وَعَلَيْكَ، وَاللهُ لِي فِي السَّمَاءِ وَأَنْتَ لِي فِي
الْأَرْضِ، وَهَذَا مِنْ صَدَقَاتِكَ وَصَدَقَاتِ اللهِ، وَأَنَا تَائِبٌ إِلَى اللهِ
وَإلَيْكَ، وَأَنَا فِي حَسْبِ اللهِ وَحَسْبِكَ، فَيَسْجُدُ لِلْمَخْلُوقِ كَمَا يَسْجُدُ
الْمُشْرِكُونَ لِشُيُوخِهِمْ، وَيَحْلِقُ رَأْسَهُ لَهُ، وَيَحْلِفُ بِاسْمِهِ، وَيَنْذِرُ
لَهُ، وَيَسْجُدُ لِقَبْرِهِ بَعْدَ مَوْتِهِ، وَيَسْتَغِيثُ بِهِ فِي حَوَائِجِهِ
وَمُهِمَّاتِهِ، وَيُرْضِيهِ بِسَخَطِ اللهِ، وَلَا يُسْخِطُهُ فِي رِضَا اللهِ، وَيَتَقَرَّبُ
إِلَيْهِ أَعْظَمُ مِمَّا يَتَقَرَّبُ إِلَى اللهِ، وَيُحِبُّهُ وَيَخَافُهُ وَيَرْجُوهُ
أَكْثَرَ مِمَّا يُحِبُّ اللهَ وَيَخَافُهُ وَيَرْجُوهُ أَوْ يُسَاوِيهِ.
Kuma bambancin da ke a tsakanin tsaftacewa da tace
Tauhidi a gefe ɗaya da kuma
kayar da matsayin masu matsayi a ɗaya gefen shi
ne: Shi dai tantancewa da tace Tauheed tsantsa shi ne, kar a ba wani mahaluki
wani abu na haƙƙin Mahalicci, da
abubuwan da suka keɓance shi. Don
haka ba za a yi ma mahaluki bauta, ko sallah ko sujada, ko yin rantsuwa da
sunansa, ko yin alwashi da shi, ko dogaro gare shi ba. Ba za a allantar da shi
ba, ba za a yi rantsuwa da shi ga Allaah ba, ba za a bauta masa domin ya
kusantar zuwa ga Allaah ba. Kuma ba za a daidaita shi da Ubangijin Halittu ba,
kamar a irin maganar mai cewa: ‘In Allaah ya so kai ma ka so’; ko ‘wannan daga
gare ka ne kuma daga Allaah’; ko ‘ni dai ina ga Allaah kuma ina a gare ka’; ko ‘na
dogara ga Allaah kuma a gare ka’; ko ‘Allaah nawa ne a sama kai kuma nawa ne a ƙasa’; ko ‘wannan daga
cikin sadakokinka ne da sadakokin Allaah’; ko ‘ni mai tuba ga Allaah ne kuma gare ka’; ko ‘ina cikin isuwan
Allaah da isuwan ka’. Sai kuma ya faɗi ya yi sujada ga mahaluki kamar yadda mushirikai suke
yin sujada ga shehunansu. Sai ya aske kansa domin sa, ya yi rantsuwa da
sunansa, ya yi alwashi dominsa, ya yi sujada ga ƙabarinsa a bayan mutuwarsa, ya nemi agajinsa a
cikin biyan buƙatunsa da
muhimman al’amuransa, ya nemi yardarsa da fushin Allaah, amma
ba zai fusatar da shi a cikin yardar Allaah ba. Yana ƙoƙarin kusanta gare shi fiye da yadda yake kusanta ga Allaah, kuma yana ƙaunarsa da tsoronsa da
fatarsa fiye da yadda yake son Allaah, yake tosoronsa, kuma yake fatansa. Ko
kuma ya daidaita a tsakaninsu.
(2) Sai kuma (Ibnul Ƙayyim) ya ce:
فَإِذَا هَضَمَ الْمَخْلُوقَ خَصَائِصَ الرُّبُوبِيَّةِ، وَأَنْزَلَهُ
مَنْزِلَةَ الْعَبْدِ الْمَحْضَ الَّذِي لَا يَمْلِكُ لِنَفْسِهِ فَضْلاً عَنْ غَيْرِهِ
ضَرًّا وَلَا نَفْعًا وَلَا مَوْتًا وَلَا حَيَاةً وَلَا نُشُورًا لَمْ يَكُنْ هَذَا
تَنَقُّصًا لَهُ وَلَا حَطًّا مِنْ مَرْتَبَتِهِ وَلَوْ رَغِمَ الْمُشْرِكُونَ.
To, idan (musulmi) ya kayar da matsayin mahaluki
daga keɓantattun siffofin Ubangijintaka, ya saukar da shi a kan
matsayinsa na bawa tsantsa, wanda bai mallaki komai ga kansa balle ga waninsa
ba, kamar cutarwa ko amfanarwa ko matarwa ko rayarwa ko kuma tayar da matattu,
wannan bai zama naƙasawa gare shi, ko kuma tawayewa ga martabarsa ko darajarsa ba, ko da kuwa
mushirikai sun ƙyamaci hakan!
(3) Daga nan sai ya cigaba da kawo nassoshi masu
tabbatar da wannan matsayin na Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) kamar wannan:
"لَا تُطْرُونِي كَمَا أَطْرَتِ النَّصَارَى ابْنَ مَرْيَمَ،
فَإِنَّمَا أَنَا عَبْدٌ، فَقُولُوا عَبْدُ اللهِ وَرَسُولُهُ".
Kar ku zaƙe wurin yabo gare ni, kamar yadda Kirista suka zaƙe wurin yabon Annabi Isaa Ɗan Maryam. Ni bawa ne kawai. Don haka sai ku ce:
Bawan Allaah kuma Manzonsa. (Sahih Al-Bukhaariy: 3445).
Da maganarsa cewa: Kar ku ɗauki ƙabarina a matsayin Idi. (Al-Musnad: 8804, kuma Hasan ne). Da kuma addu’arsa cewa: Ya Allaah! Kar ka sanya ƙabarina ya zama gunki ana bauta masa. (Muwattaa:
475, mursal). Da kuma: Kar ku ce, in Allaah ya so kuma wane ya so! Amma dai ku
ce: In Allaah ya so sannan wane ya so. (Abu-Daawud: 4980, sahih). Da kuma
hadisi mai cewa: Wani mutum ya ce wa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam): In Allaah ya so kuma kai ma ka so! Sai ya ce: Ka sanya ni da Allaah
daidai ne?! (Al-Musnad: 1839, Sahih Li-Ghairih). Sai kuma hadisin da wani mutum
kamamme ya faɗa a gabansa cewa: Ya
Allaah, gare ka nake tuba, ba ga Muhammad nake tuba ba! A kan hakan sai ya ce:
Wannan ya san haƙƙin gaskiya ga masu ita. (Al-Musnad: 15587; Sanaduhu da’eef, Munƙati’).
(4) Daga nan sai kuma ya shiga kawo ayoyi, kamar
wannan:
{ لَيْسَ لَكَ مِنَ الْأَمْرِ شَيْءٌ }
Babu wani abu na al’amarin a hannunka. (Surah
Al-Imraan: 128).
Sai kuma maganar Allaah cewa: Ka ce: Al’amari
dukkansa na Allaah ne. (Surah Al-Imraan: 145). Da kuma: Ka ce: Ni dai ban
mallaka wa kaina wata cuta ko amfani ba, sai dai abin da Allaah ya so kawai.
(Surah Yuunus: 49).
A cikin Surah Al-A’raaf kuma ya ce:
{قُلْ لَا أَمْلِكُ لِنَفْسِي نَفْعًا وَلَا ضَرًّا إِلَّا مَا
شَاءَ اللَّهُ وَلَوْ كُنْتُ أَعْلَمُ الْغَيْبَ لَاسْتَكْثَرْتُ مِنَ الْخَيْرِ وَمَا
مَسَّنِيَ السُّوءُ إِنْ أَنَا إِلَّا نَذِيرٌ وَبَشِيرٌ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُون}
Ka ce: Ni dai ban mallaka wa kaina wani amfani ko
cutarwa ba, sai dai abin da Allaah ya so kawai. Kuma in da na san gaibu, to da
kuwa na yawaita alkhairi, kuma da mummunan abu bai same ni ba. Ni dai ba kowa
ba ne sai dai mai gargaɗi kuma mai
bushara ga mutane masu imani. (Surah Al-A’raaf: 188).
Duk da waɗannan hujjojin
mushirikai ba su yarda ba, sai da suka cigaba da tsayar da shehunansu da
waliyansu - ba ma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba - a
matsayin da ya saɓa musu. Suka
cigaba da riya cewa duk wanda ya sauke su daga matsayin nan, to ya tawaye su
kenan kuma ya rage musu daraja! Alhali kuwa su ɗin ne suka kayar da matsayin Ubangiji Ta’aala, suka naƙasa shi. Su suke da
cikakken rabo a cikin maganarsa (Subhaanahu Wa Ta’aala) cewa:
{ وَإِذَا ذُكِرَ اللَّهُ وَحْدَهُ اشْمَأَزَّتْ قُلُوبُ الَّذِينَ
لا يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ، وَإِذَا ذُكِرَ الَّذِينَ مِنْ دُونِهِ إِذَا هُمْ يَسْتَبْشِرُونَ }
Idan aka ambaci Allaah shi kaɗai sai zukatan waɗanda ba su yi
imani da Lahira ba su takura. Amma idan aka ambaci waɗanda ba shi ba, sai ka ga suna ta yin bushara. (Surah
Az-Zumar: 45).
Allaah ya shiryar da su zuwa ga gaskiya.
(5) Haka kuma Ibn Al-Ƙayyim ɗin ya faɗa a cikin Nuuniyyah cewa:
للهِ حَقٌّ لَا يَكُونُ لِغَيْرِهِ ... وَلِعَبْدِهِ حَقٌّ هُمَا
حَقَّانِ
لَا تَجْعَلُوا الْحَقَّيْنِ حَقًّا وَاحِدًا ... مِنْ غَيْرِ
تَمْيِيزٍ وَلَا فُرْقَانِ
فَالْحَجُّ لِلرَّحْمَنِ دُونَ رَسُولِهِ ... وَكَذَا الصَّلَاُة
وَذَبْحُ ذَا الْقُرْبَانِ
وَكَذَا السُّجُودُ وَنَذْرُنَا وَيَمِينُنَا ... وَكَذَا مَتَابُ
الْعَبْدِ مِنْ عِصْيَانِ
وَكَذَا التّوَكُّلُ وَالْإِنَابَةُ وَالتُّقَى ... وَكَذَا
الرّجَاءُ وَخَشْيَةُ الرَّحْمَنِ
وَكَذَا الْعِبَادَةُ وَاسْتِعَانَتُنَا بِهِ ... إِيَّاكَ نَعْبُدُ
ذَانِ تَوْحِيدَانِ
وَعَلَيْهِمَا قَامَ الْوُجُودُ بأَسْرِهِ ... دُنْيًا وَأْخَرًى
حَبَّذَا الرُّكْنَانِ
Allah yana da haƙƙin da babu shi ga waninsa, kuma bawansa yana da haƙƙi: su haƙƙoƙi biyu ne.
Kar ku mayar da haƙƙoƙin biyu su zama haƙƙi ɗaya, ba tare da bambancewa ko rarrabewa ba.
Hajji na Allaah ne ban da Manzonsa, haka ma sallah
da yankan hadaya ko layya.
Haka ma sujada da alwashinmu da rantsuwarmu, haka
ma tuban bawa daga saɓon Allaah.
Haka ma tawakkali da komawa ga Allaah da taƙawa, haka kuma fata da
tsoron Allaah Mai Rahama.
Haka kuma ibada da neman taimakonmu da shi, gare
ka muke bauta waɗannan tauhidi
biyu ne.
A kan su ne rayuwar samammu ta kasance, a duniya
da lahira: madalla da rukunnan nan guda biyu.
(Al-Kaafiyatus Shaafiyyah Fil Intisaar Lil Firƙatin Naajiyah (Nuuniyatu
Ibn Al-Ƙayyim), shafi: 806 na
Al-Imaam Muhammad Bn Abi-Bakrin Bn Ayyub Bn Ƙayyim Al-Jawziyyah, wanda ya rasu: 751H).
Shiyasa dole ne a ƙara duban abin da Ibnul Ƙayyim ya faɗa a cikin
Al-Waabilus Sayyib da idon basira, kuma a fassara shi ta yadda zai dace da
addininsa da farko, sannan kuma da ra’ayinsa da fahimtarsa.
[6] Na-shida: Domin a yi wa maganar mai magana
kyakkyawar fahimta kuma a yi mata kyakkyawar fassara ta adalci ya zama dole a
kalli asali da yanayi ko tsarin maganar, kamar a san ko a kan menene yake
magana tun farko, sannan kuma menene ya faɗa kafin da bayan maganar da aka gutsuro daga gare shi.
Da farko littafin Al-Waabilus Sayyib Minal Kalimit
Tayyib kamar sharhi ne ga maganganun cikin littafin Al-Kalimut Tayyib na
Shaikhul Islaam Ibn Taimiyah (Rahimahul Laah). Shi kuwa littafi ne a kan Azkaar
ba a kan Aƙeedah ba. Kuma
maganar ta zo ne a ƙarƙashin bayanin da yake yi
a kan Fa’idojin Azkaar, inda ya kawo fa’idoji fiye da guda saba’in. A cikin fa’ida ta talatin
da huɗu ne ya ce:
أَنَّ دَوَامَ ذِكْرِ الرَّبِّ - تَبَارَكَ وَتَعَالَى - يُوجِبُ
الْأَمَانَ مِنْ نِسْيَانِهِ، الَّذِي هُوَ سَبَبُ شِقَاءِ الْعَبْدِ فِي مَعَاشِهِ
وَمَعَادِهِ، فَإِنَّ نِسْيَانَ الرَّبِّ - سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى - يُوجِبُ نِسْيَانَ
نَفْسِهِ وَمَصَالِحَهَا، قَالَ تَعَالَى : { وَلَا تَكُونُوا كًالَّذِينَ نَسُوا اللهَ
فَأَنسَاهُمْ أَنفُسَهُمْ، أُولَئِكَ هُمُ الْفَاسِقُونَ } وَإِذَا نَسِيَ الْعَبْدُ
نَفْسَهُ أَعْرَضَ عَنْ مَصَالِحِهَا وَنَسِيَهَا وَاشْتَغَلَ عَنْهَا، فَهَلَكَتْ
وَفَسَدَتْ وَلَا بُدَّ، كَمَنْ لَهُ زَرْعٌ أَوْ بُسْتَانٌ أَوْ مَاشِيَةٌ أَوْ غَيْرُ
ذَلِكَ، وَمِمَّا صَلَاحُهُ وَفَلَاحُهُ بتَعَاهُدِهِ وَالْقِيَامِ عَلَيْهِ، فَأَهْمَلَهُ
وَنَسِيَهُ وَاشْتَغَلَ عَنْهُ بِغيْرِهِ وَضَيَّعَ مَصَالِحَهُ فَإِنَّهُ يَفْسُدُ
وَلَا بُدَّ.
Dawwama a kan zikirin Ubangiji (Tabaaraka Wa Ta’aala)
yana samar da aminci daga mancewa da shi, wanda kuma wannan mantuwan shi ne
sanadin taɓewar bawa a cikin
rayuwarsa da makomarsa. Domin mance Ubangiji (Subhaanahu Wa Ta’aala) shi ke
gadar wa mutum mancewa da ransa da abin da ke gyara shi. Allaah Ta’aala ya ce:
Kar ku zama kamar waɗanda suka mance
Allaah, sai shi ma ya mantar da su rayukansu. Waɗannan su ne fasiƙai. (Surah Al-Hasr: 19). To, idan bawa ya manta da ransa sai ya fita batun ƙoƙarin gyara shi, ya mance da shi ya shagaltu da
wanin-shi. Daga nan sai ran ya hallaka ya lalace ba makawa. Kamar dai wanda
yake da shuka ne ko lambu ko tumaki ko makamantansu na abin da gyaruwansa da
samun albarkarsa ya rataya ga kulawansa da tsayuwa a kan gyara shi. To, idan ya
ƙyale shi ya mance da
shi, ya shagaltu da wani abin da ba wannan ɗin ba, ya wofantar da abin da yake zama gyara a gare shi,
ba makawa dole ya lalace!
Wannan shi yake nuna lallai a yi lura sosai wurin
fassara maganganun da ya yi a wannan babin na Azkaar wanda suke da alaƙa da aƙeedah.
[7] Na-bakwai: Cikakkiyar maganar da Ibn Al-Ƙayyim ya faɗa a ƙarƙashin wannan babin ita
ce, kamar haka:
(1) Da farko ya ce:
وَسَمِعْتُ شَيْخَ الْإِسْلَامِ ابْنَ تَيْمِيَةَ - قَدَّسَ
اللهُ رُوحَهُ - يَقُولُ : أنَّ فِي الدُّنْيَا جَنَّةً مَنْ لَمْ يَدْخُلْهَا لَا
يَدْخُلُ جَنَّةَ الْآخِرَةِ. وَقَالَ لِي مَرَّةً : مَا يَصْنَعُ أَعْدَائِي بِي؟
أنَا جَنَّتِي وَبُسْتَانِي فِي صَدْرِي، إنْ رُحْتُ فَهِيَ مَعِي لَا تُفَارِقُنِي،
إنَّ حَبْسِي خَلْوَةٌ، وَقَتْلِي شَهَادَةٌ، وَإخْرَاجِي مِنْ بَلَدِي سِيَاحَةٌ.
وَكَانَ يَقُولُ فِي مَحْبَسِهِ فِي الْقَلْعَةِ : لَوْ بَذَلْتُ لَهُمْ مِلْءَ هَذِهِ
الْقَلْعَةِ ذَهَبًا مَا عَدَلَ عِنْدِي شُكْرَ هَذِهِ النِّعْمَةِ، أَوْ قَالَ: مَا
جَزَيْتُهُمْ عَلَى مَا تَسَبَّبُوا لِي فِيهِ مِنَ الْخَيْرِ، وَنَحْوَ هَذَا. وَكَانَ
يَقُولُ فِي سُجُودِهِ: وَهُوَ مَحْبُوسٌ: اللَّهُمَّ أعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ وَشُكْرِكَ
وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ، مَا شَاءَ اللهُ. وَقَالَ لِي مَرَّةً : الْمَحْبُوسُ مَنْ حُبِسَ
قَلْبُهُ عَنْ رَبِّهِ تَعَالَى، وَالْمَأْسُورُ مَنْ أَسَرَهُ هَوَاهُ. وَلَمَّا أُدْخِلَ
إِلَى الْقَلْعَةِ وَصَارَ دَاخِلَ سُورِهَا نَظَرَ إِلَيْهِ وَقَالَ: { فَضُرِبَ بَيْنَهُمْ
بِسُورٍ لَهُ بَابٌ بَاطِنُهُ فِيهِ الرَّحْمَةُ وَظَاهِرُهُ مِنْ قِبَلِهِ الْعَذَابُ
}.
Kuma na ji Shaikhul-Islaam Ibn Taimiyah (Allaah ya
tsarkake ransa) yana cewa: ‘Haƙiƙa a cikin duniya akwai
wata aljannah, wanda bai shige ta ba ba zai shiga Aljannar Lahira ba.’ Kuma ya taɓa gaya mini
cewa: ‘Wai me maƙiyana za su yi da ni ne? Ni fa aljannata tana cikin ƙirjina, duk inda na ke tana tare da ni, ba ta
rabuwa da ni. Ni tsare ni a magarƙama khalwa ce, kashe ni kuma shahada ce, fitar da ni daga garina kuma buɗe ido ne.’ Kuma ya sha faɗa a cikin ɗakinsa a
kurkukun Ƙal’ah cewa: ‘Idan
da zan bayar da abin da ya cika kurkukun nan na zinare gare su, da a wurina
wannan bai kai godiyar wannan ni’imar ba.’ Ko kuma ya ce: ‘Da ban biya su ba a
kan abin da suka janyo mini na wannan alkhairin.’ Ko dai wata magana
makamanciyar wannan. Kuma ya kasance yana faɗa a cikin sujudarsa a lokacin yana tsare a cikin
kurkukun: ‘Ya Allaah ka taimaka mini a kan zikirinka, da godiyarka, da kyautata
bautarka.’ Maa shaa’al Laah. Kuma ya taɓa gaya mini
cewa: ‘Tsararre fa shi ne wanda aka tsare zuciyarsa daga Ubangijinsa Ta’aala.
Shi kuma kamamme shi ne wanda sha’awar ransa ta kame shi.’ Lokacin da aka
shigar da shi cikin Magarƙamar Ƙal’ah ya zama daga cikin ginin katangarta, sai ya dube ta ya
karanta wannan ayar, ya ce: ‘Sai aka tayar da
wata katanga a tsakaninsu mai ƙyaure, ta cikinsa nan ne akwai Rahama, kuma ta bayansa daga wajensa a nan
ne akwai azaba.’ (Surah
Al-Hadeed: 13).
(2) Sai kuma Ibnul Ƙayyim ɗin ya ce:
وَعَلِمَ اللهُ، مَا رَأَيْتُ أَحَداً أَطْيَبَ عَيْشاً مِنْهُ
قَطُّ، مَعَ مَا كَانَ فِيهِ مِنْ ضِيقِ الْعَيْشِ، وَخِلَافِ الرَّفَاهِيَةِ وَالنَّعِيمِ،
بَلْ ضِدِّهَا. وَمَعَ مَا كَانَ فِيهِ مِنَ الْحِبْسِ وَالتَّهْدِيدِ وَالْإِرْجَافِ.
وَهُوَ مَعَ ذَلِكَ مِنْ أَطْيَبِ النَّاسِ عَيْشًا، وَأَشْرَحِهِمْ صَدْرًا، وَأَقْوَاهُمْ
قَلْبًا، وَأَسَرِّهُمْ نَفْسًا، تَلُوحُ نَضْرَةُ النَّعِيمِ عَلَى وَجْهِهِ.
Kuma Allaah ya sani cewa: Da ɗai, ban taɓa ganin wanda ke
cikin daɗin rayuwa fiye da shi (Ibn Taimiyah) ba, duk kuwa da irin
ƙuncin rayuwar da yake
ciki, da rashin kayan more rayuwa da ni’imomi, sai ma
dai kishiyar hakan. Duk da abin da yake ciki na tsaro da barazana da razanarwa,
amma duk da haka ya fi mutane jin daɗi a rayuwa, ya
fi su yalwar ƙirji, ya fi su ƙarfin zuciya, ya fi su
natsuwar rai. Ana ganin kwarjinin ni’ima yana bayyana
a fuskarsa.
(3) Daga nan ne ya kawo maganar da malamin ɗariƙar gutsuro, cewa:
وَكُنَّا إِذَا اشْتَدَّ بِنَا الْخَوْفُ، وَسَاءَتْ مِنَّا
الظُّنُونُ، وَضَاقَتْ بِنَا الْأَرْضُ، أَتَيْنَاهُ. فَمَا هُوَ إلَّا أَنْ نَرَاهُ
وَنَسْمَعُ كَلَامَهُ، فَيَذْهَبُ ذَلِكَ كُلُّهُ، وَيَنْقَلِبُ انْشِرَاحاً وَقُوَّةً
وَيَقِينًا وَطُمَأْنِينَةً. فَسُبْحَانَ مَنْ أَشْهَدَ عِبَادَهُ جَنَّتَهُ قَبْلَ
لِقَائِهِ، وَفَتَحَ لَهُمْ أَبْوَابَهَا فِي دَارِ الْعَمَلِ، فَآتَاهُمْ مِنْ رَوْحِهَا
وَنَسِيمِهَا وَطِيبِهَا مَا اسْتَفْرَغَ قُوَاهُمْ لِطَلَبِهَا وَالْمُسَابَقَةِ إلَيْهَا.
Kuma mun kasance idan tsoro ya tsananta gare mu,
zatonmu ya munana, kuma ƙasa ta yi mana ƙunci sai mu je wurin shi. Kuma da zaran mun gan shi, mun ji maganarsa, sai
duk komai ya tafi daga gare mu. Sai ya juye ya zama yalwa a cikin ƙirji da ƙarfin zuciya da yaƙini da natsuwa. Tsarki
ya tabbata ga wanda ya nuna wa bayinsa Aljannarsa tun kafin su haɗu da shi, kuma ya buɗe musu ƙofofinta a gidan nan na aiki, har ni’imominta da
iskarta da ƙamshinta suka riƙa samun su, abin da ya
zama mai ƙara musu ƙwazo wurin neman ta, da
yin tsere domin samun ta. (Al-Waabilus Sayyib Wa Raafi’ul Kalimit Tayyib, shafi: 48, na Al-Imaam Abu-Abdillaah
Muhammad Bn Abi-Bakr Bn Ayyub Bn Ƙayyim Al-Jawziyyah, wanda ya rasu: 751H)
(4) Daga wannan bayanin cikakke abin da Ibnul Ƙayyim yake nufi ya fito
fili ga duk mai son gaskiya da adalci, ba mai son zuciya ba.
Abin da yake cewa a taƙaice kawai shi ne:
Idan tsoro a kan sharrin maƙiya daga cikin sarakuna da malaman bidi’a na ɗariƙa da sauransu, ya
tsananta a gare su…
Idan kuma suka fara mummunan zaton cewa, su ma fa
zai yiwu a kama su a ɗaure, irin yadda
aka yi wa malaminsu, kuma da’awar Sunnah da suke kai za ta samu matsala kenan…
Idan kuma duniya ta yi musu ƙunci duk kuwa da faɗinta da yalwarta, domin yadda maƙiya suka haɗe musu kai, suna
ta ƙulla makirci da neman
ganin bayansu…
Idan waɗannan abubuwa
sun taso musu, sai su koma wurinsa. Wato, su tashi su tafi wurinsa a inda yake
tsare a kurkukun Ƙal’ah, a matsayinsa na babban malaminsu mai nuna musu hanyar shiriya da
mafita a cikin al’amura.
To, da zaran sun gan shi a halin da yake ciki na
natsuwa da kwarjini da jin daɗi da kwanciyar
hankali, duk kuwa da kasantuwar a tsare ya ke a cikin kurkuku, a cikin mummunan
hali da ƙuncin rayuwar da ta fi
wacce suke ciki a waje…
Kuma da zaran sun ji maganganunsa da nasihohinsa
irin na malamin Sunnah mai cike da hikima da imani da yaƙini, maganganu masu ratsa jiki masu natsar da rai,
su sanyaya zuciya, su ƙara wa bawan Allaah tsoron Allaah…
Da zaran sun gani kuma sun ji waɗannan abubuwa, shikenan sai wannan ya ƙara musu yalwar ƙirji da samun ƙarfin zuciya, da samun
yaƙini da natsuwa su ma.
Daga nan sai duk damuwarsu ta kau, su ƙara samun yaƙini da rashin tsoro.
(5) Wannan abin da Ibnul Ƙayyim yake nufi kenan, in shaa’al Laah. Wannan
kuwa ba daidai ya ke da irin abin da ‘yan bidi’a masu mayar da shehunansu da
waliyyansu a matsayin Allaah suke yi ba. Waɗanda suke zuwa ƙabrukansu a bayan sun mutu, suna roƙon su irin abin da babu mai iya bayarwa sai Allaah shi kaɗai.
Kuma wannan ba wuri ne da za a janyo ayar:
{ أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضْطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ }
Ko kuwa wanene yake amsa wa mabuƙaci idan ya kiraye shi,
kuma yake yaye masifu. (Surah An-Naml: 62).
Wai don a nuna su Ibnul Ƙayyim ɗin sun kauce wa ƙa’ida ba.
Kowa ya fahimta daga nan cewa, tafiyar su Ibnul Ƙayyim zuwa wurin
malaminsu Shaikhul-Islaam Ibn Taimiyah (Rahimahul Laah) ba irin tafiyar da
mushirikai suke yi zuwa wurin shehunansu ba ne a cikin maƙabartu. Tafiya ce irin ta ziyara da neman nasiha
ko shawara, da neman nuna hanya da jin wa’azinsa, da
sauransu daga malamin da yake raye, wanda suke iya ji da ganin sa. Ba kamar
shehunan da suka mutu amma ake zuwa neman biyan buƙatu a wurin su, aka bar Allaah ba. Don haka, nan
ba wurin da za a janyo waccan ayar da makamantan ta ba ne.
Sai a lura da kyau.
Allaah ya ƙara mana shiriya da tabbata a kan hanya.
Wal Laahu A’lam.
Walaa Haula Walaa Ƙuwata Illaa Bil Laah.
Wa Sallal Laahu Wa Sallama Wa Baaraka Alaa
Nabiyyinaa Muhammadin Wa Alaa Alihi Wa Sahbih.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number:
08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.