𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam shin wasu musulmai suna yin bikin Mauludi wasu kuma basayi. Shin meye Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) da sahabbansa sukace akan bikin Mauludin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ne??
HUKUNCIN
BUKIN MAULIDI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Babu wata ayah acikin Al-ƙur’ani data nuna cewa muyi bikin zagayowar ranar
haihuwar Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam). da kansa ma baiyi ba, kuma
bai bada umarnin ayi ba, a lokacin rayuwarsa da kuma bayan rasuwarsa. Hasali ma
dai yace da sahabbansa kada su zurfafa game dashi kamar yadda nasara suka
zurfafa ga Isah Ɗan Maryam (Alaihimas salaam), Ni bawan Allah ne saboda haka kuce; Bawan
Allah kuma Manzonsa (sallallahu alaihi wa sallam). (Bukhari ya ruwaito shi).
Abinda aka ruwaito shine Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam ya riki ranar da aka haife shi ranar ibadah, Wanda kuma ya
bambanta da biki. An tambayeshi akan azumin ranar litinin, sai yace; itace
ranar da aka haife ni kuma itace ranar da aka fara saukar min da wahyi.
(Muslim, al-Nisaa’i da Abu Dawuda).
Haka kuma mun sani cewa Sahabbai sune mutanen da
sukafi Kowa ƙaunarsa.
Shin ko an taɓa ruwaito cewa Abubakar Al-siddiƙu (babban abokinsa Na hannun damarsa) yayi bikin
maulidi??
Shin ko an taɓa ruwaito cewa Umar ibn Al-Khattab (wanda yayi khalifanci
na shekaru 12) yayi bikin maulidi??
Shin ko an taɓa ruwaito cewa Uthman ibn Affan yayi bikin Maulidi??
Shin an ruwaito cewa Aliyu ibn Abi Dalib (Ɗan’uwansa kuma
surukinsa) yayi bikin Maulidi??
Shin an ruwaito ko da mutum ɗaya daga cikin sahabbai yayi bikin maulidi???
Amsar tambayoyin itace; Basuyi ba, Wallahi!! To
saboda me basuyi ba??
Saboda basu san muhimmancinsa ba?? Kodai basa son
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam da gaskiyar so??
Babu Wanda ya isa yace basa sonsa da gaskiya
saidai wanda yake bin ɓatacciyar hanya
kuma yake jan hankalin wasu su bi ɓatacciyar hanya.
Shin meyasa babu ɗaya daga cikin waɗannan magabata
Abu Haneefah, Maalik, Al-Shaafi’i, Hanbali basuyiba kuma basuce ayi ba, a
akidarsu ma maulidi ba addini bane.
Da akhalari da ishmawi da iziyya, askari, da
muktasar dukkanninsu litattafaine na koyon addini mu daku duk munyi imani dasu,
kuma muna koyan addini acikin su amma a cikin wa’ennan litattafan ba ɗaya daga cikinsu wanda yakawo babi koh fasali na maulidi,
toh meyasa basu kawoba, koh dai dukanninsu sunyi mantuwa shiyasa basu kawoba,
koh kuma dukkanninsu sun ɓoye illimi, koh
kuma dukkanninsu sun jahilta basusan falalar maulidi ba shiyasa basu kawoba,
koh kuma ba addini bane shiyasa basu kawoba saboda haka cikin wa’ennan dole ayi
ɗaya, mantuwa sukayi gaba ɗaya, iliminsune bai kai ba, ɓoye gaskiya sukayi, koh a akidarsu wannan na addini bane
shiyasa basu rubuta shiba.
Idan anyi magana sai suce ba ason waliyi a akidar
ahalussunnah basa kin kowani waliyi ahalussunnah suna son Kowani waliyi, duk
mun yarda da karamansu amma rigimar ba akan kasancewarsa waliyi bane duk mun
yarda waliyine mai karama amma batun abishi wayace abishi, nanne inda rikicin
yake. Mu Annabi zamubi bashiba, don munsan tarihin haihuwarsa, an haifeshi
shekara ta 1150 bayan hijira. Bayan Annabi ya bar duniya da shekara 1147 sannan
aka haifeshi, shi da akace masa mai karama, toh atsakanin shekara 1147 mutane
sunyi azumi, sunyi aikin hajji, sunyi zikiri sunyi salati, salatin da ba
nashiba, zikirinda ba nashiba duk sunyi irin wanda Annabi ya koyarda shi.
(TAMBAYA) shin tayi koh batayiba?, zasu shiga Aljannah koh bazasu Shigaba? amma
fa bashi sukebi ba, ga Abubakar ga Umar ga Uthman ga Aliyu barma ta sahabbai,
ga tabú’ai dukfa ba shi suka biba dan tsakaninsu dashi shekaru daruruwa kuma
muna kyautata zaton en Aljannah ne, basu ma sanshiba a tarihi ba’a yishi bama
lokacinda suke duniya kuma zasu shiga Aljannah Insha Allah, toh meyasa sai
dayazo daga baya sannan yace sai anbishi sannan za’a shiga Aljannah.
WALLAHU A’ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.