𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Wa Rahmatul Laah, Malam, sana’ata ita ce: Yi wa amare da sauran mata kwalliya watau: Make-up. Tambayata a kan sanya gashin-ido (na-kanti) ne da mata ke yi: Ya halatta ko bai halatta ba? Da yawa suna neman a riƙa sanya musu, amma ni ba na sanyawa. Shi ne nake son jin hukuncinsa tukun. shi wannan irin kwalliya da mata suka fito da shi a wannan zamanin yaya yake ne a cikin addini? Yadda mace take sauyawa daga surarta ta asali kwata-kwata, wani lokaci ko mutum mahaifinta ne in ba an ce masa wance ce ba, ba zai ma iya ganewa ba!
HUKUNCIN
SANYA GASHIN IDO A WURIN KWALLIYA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
W Alkm Slm W Rhmt Laah W Brktuh.
Kin yi daidai kuma kin kyauta da kika tsaya neman
sanin hukunci da farko tun kafin ki fara aiki. Allaah ya yi miki albarka, ya
datar da mu gaba-ɗaya ga abin da
yake so kuma yake yarda da shi.
Da farko dai musulunci bai hana mata yin kwalliyar
da ba ta wuce iyaka, ko wacce ta ta saɓa wa ƙa’ida ba:
قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللهِ الَّتِي أَخْرَجَ ِعِبَادِهِ
Ka ce: Wanene ya haramta kayan ado da kwalliya na
Allaah da ya fitar domin bayinsa?
Don haka, halal ne mace musulma ta riƙa yin wanka da wanki,
tana tsabtace jikinta da tufafinta. Ta shafa mai a jikinta da kanta domin ya ƙara laushi da taushi, ta
riƙa yanke ƙumbunanta, ta riƙa sanya kwalli ko tozali
a idanunta, ta sanya zobe da awarwaro da sarka da ɗan kunne irin yadda suka dace da koyarwar shari’a.
Haka kuma ya halatta ta riƙa yin amfani da kyawawan tufafin da aka ɗinka su yadda ya dace, kamar atamfa da shadda da leshi da
sauran makamantansu. Kuma ya halatta ta bayyana hakan nan a gaban muharramanta,
kamar mijin aurenta ko mahaifinta ko kawunta ko baffanta ko yayanta ko ƙaninta da sauransu.
Amma idan kwalliya ta wuce iyaka ko ta saɓa wa ƙa’idar shari’a to a nan ne
musulunci bai yarda ba, kuma ya hana musulma yinsa. A nan ga waɗansu nau’ukan kwalliya da mata suke amfani da su a yau,
amma kuma Malamai suka nuna cewa ba su dace da koyarwar addinin musulunci ba:
1. Ƙarin gashin kai.
2. Aske gashin gira.
3. Aske ko saita ko ƙara gashin ido.
4. Feƙe haƙora don yin wushirya.
5. Rina furfura da baƙin launi.
6. Tsawaita ƙumbuna.
7. Sanya wa ƙumbuna fenti.
8. Mayar da gashin-kai ya koma kamar na turawa.
9. Sanya a-cuci-maza a kai.
10. Amfani da mai ko hoda masu sauya launin fatar
jiki.
11. Amfani da ‘eye-shadow’.
12. Amfani da jan-baki.
13. Yin zane a fatar jiki (tattoo).
14. Mace ta sanya tufafin maza.
15. Sanya matsattsun tufafi masu nuna kaurin gaɓoɓin jiki.
16. Sanya tufafi shara-shara masu nuna launin
fatar jiki.
17. Amfani da tufafin da ke bayyana sashe ko
dukkan al’aura.
18. Amfani da takalma (high-heeled shoes).
19. Sanya tufafi irin na kafirai.
20. Bayyanar da kwalliya ga waɗanda ba muharramai ba.
Hana yin amfani da waɗansu daga waɗannan abubuwa ya
zo a cikin nassoshi sahihai sarihai a fili ƙarara, waɗansu kuma an
fitar da hukuncinsu ne daga gamammun ƙa’idojin shari’a masu hana a yi
amfani da su, kamar cewa suna jawo lahani ko ta’adi ga lafiyar jiki, ko kuma kamar cewa su koyi ne da
kafirai. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ
Duk wanda ya kamantu da wasu mutane, to yana tare
da su.
A nan akwai wasu masu raunin fahimta da suke cewa:
Idan an hana koyi da kafirai a cikin al’amuran rayuwa me ya sa ba mu ga su
kansu malamai sun daina amfani da kayan ƙere-ƙeren zamani da kafiran
suka yi ba, kamar su motoci da jirage da wayoyin hanu da sauransu?!
Amsa a nan ita ce:
Da farko dai ba a yi wa addini irin wannan
tambayar ta nuna raini da rashin kunya! Domin tun tuni Allaah Ta’aala ya ce:
لَا يُسْأَلُ عَمَّا يَفْعَلُ
Ba a tambayarsa (Shi Allaah) a kan abin da ya
aikata.
Kuma Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:
وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إَذَا قَضَى اللهُ
وَرَسُولُهُ أَمْراً أَن يَّكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَن يَّعْصِ
اللهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالاً مُبِيناً
Bai kamaci wani mumini ko wata mumina ba idan
Allaah da Manzonsa ya yanke wani al’amari ya zama suna da wani zaɓi na su na-daban a cikin al’amarinsu.
Sannan kuma ai wannan ilimin na ƙere-ƙere zamanin yinsu ne
Allaah ya kawo shi yanzu, kuma ba wani abu ne da ya keɓanta da kafirai kaɗai ban da
musulmi ba. A yau muna ji da ganin yadda ‘ya’yan musulmi da yawa suke shiga
fagen ƙere-ƙeren kuma suke yin fice.
A ƙarshe kuma, wannan hani da aka yi a kan koyi da su ba a kowane fanni ba ne.
Ya dai shafi irin abin da suka saɓa wa dokokin
shari’armu da shi ne kamar na ƙirƙira a cikin addini, ko
wanda ya saɓa wa kyawawan ɗabi’u da halayenmu na-gari abin yabo. Shi ya sa babu
malamin da ya ƙyamata balle ya
hana tsarin kiliya dama ko hagu a wurin tuki ba, haka ko amfani da jirgi ko
mota zuwa aikin hajji, ko amfani da amsa-kuwwa a wurin kiran sallah da wa’azi da sauransu, ko kuma amfani da hanyoyi da injunan
zamani wurin rubuta Alƙur’ani da wallafa Littaffan Addini, ko shan maganin
da bai ci karo da koyarwar shari’a ba.
Wata kuma ta ce: Tana yin irin wannan ado da
kwalliyan ne domin ta burge mijinta, ta ƙara janyo shi gare ta, ta hana shi kallon wasu mata a waje, musamman dayake
akwai mata kafirai da fasiƙai da suke amfani da hakan suna ɗauke hankulan
maza?
Amsa a nan sai a ce:
Wannan dai ba dalili ba ne, kuma a fili kuskure ne
babba. Wai shi wannan mijin wane irin musulmi ne da ayyukan saɓon Allaah da kafirai da fasiƙai suke tafkawa ne yake burge shi? Wane irin
musulmi ne haka da ya zama cewa kyakkyawar kwalliyar da shari’ar musulunci ta halatta wa matarsa ba ta burge shi, sai
irin wadda shaiɗan ya ƙawata wa mabiyansa ne
yake so?! Kuma ba amfani da irin waɗannan kayayyakin
kwalliyan a cikin gidaje domin wai a burge mazaje ne a yau ya haifar da abin da
ya zama ruwan-dare ba? Inda ake ganin yaran mata da ‘yan mata suna amfani da su
a wajen gidajensu, suna bayyanawa ga samarinsu da sauran waɗanda ba muharramansu ba?! Kuma ga shi nan kullum abin sai
ƙara haɓaka yake yi, duk kuwa da wa’azi da gargaɗin da Malaman Sunnah suke ta yi?! Waɗansu ashararan ma nema su ke Malamai su halatta musu
amfani da waɗannan kayayyakin!!
A taƙaice dai, ko da an samu mijin da yake sha’awar waɗannan kayayyakin
kwalliyan, kuma har yake sayo su domin matarsa ta yi amfani da su, abin da ya
fi a fahimtarmu a yanzu shi ne, bai kamata ta yarda ta yi masa biyayya a kan
haka ba, saboda maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya
ce:
لَا طَاعَةَ لِمَخْلُوقٍ فِي مَعْصِيَةِ الْخَالِقِ
Babu biyayya ga wani halitacce a cikin saɓon Allaah Mahalicci
Allaah ya ƙara mana ilimi mai amfani.
Wal Laahu A’lam
Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.