Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Saci Kudin Mijina Domin In Yi Kasuwanci Da Shi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam. na ɗebi kuɗin mijina dubu saba’in (70K) bai sani ba amma da niyar yin sana’a daga baya in mayar masa. To kuma kuɗin gaba ɗaya sun narke hankalina ya tashi dan Allah ya sani ban ɗauka da niyar sata ba, na ɗauka da niyar mayar masa duk lokacin dana samu jarina. Bayan kuɗin sun lalace na gaya masa cewar yana bina kuɗi dubu saba’in (70K) amma bai yarda ba daga baya ya nemi sanin ya akayi yake bina kuɗi haka in gaya mai, saboda na nemi ya yafe min shi kuma yaƙi yafewa, wai sai na faɗa masa yadda akayi. Shine na rabu da maganar amma malam shin zan iya biyansa a hankali ta hanyar sana’ar da nakeyi in dinga bashi manja inna kin karɓar kuɗin har na biya sa kuɗinsa ko kuwa?

NA SACI KUƊIN MIJINA DOMIN IN YI KASUWANCI DA SHI:

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Gaskiya kin tafka babban kuskure tun farko, watakil ma shi ya sanya jarin naki ya rushe bai yi albarka ba. Domin hakika kin aikata cin amana adukiyar mijinki. Kuma tabbas idan har kika mutu baki tuba ba, Allah zai yi miki hisabi akansa.

Dukiyar mijinki amana ce wacce Allah ya danka ahannunki amatsayinki na matarsa. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace : "MACE MAI KIWO CE AƊAKIN MIJINTA KUMA ZA’A TAMBAYETA GAME DA KIWON DA AKA BATA".

Kinga bisa wannan dalilin, haramun ne ki ɗauki kuɗinsa ba tare da saninsa ba, alhali yana kulawa da abincinki da abin shanki da suturarki bai tauye miki hakki ba. Idan kuma kika aikata haka, to kin fitar da kanki daga cikin sahun mafiya alkhairin mataye, kuma kin shigar da kanki cikin sahun maciya amana kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace "Mafi alkhairi daga cikin mataye, ita ce matar da idan ka kalleta zata faranta maka zuciya, Kuma idan ka umurceta zatayi maka biyayya, kuma Idan baka nan zata kiyaye maka amanar kanta da kuma dukiyarka". (Ibnu Jareer da Ibnu Abee Hatam ne suka ruwaitoshi).

Shawarar da zan baki anan ita ce : Kiji tsoron Allah ki fito ki gaya masa gaskiyar abinda kika aikata masa na laifi, sannan ki nemi yafewar laifin bisa alkawarin cewa zaki biyashi kuɗinsa da kika ɗauka. Idan yace ya yafe miki to shikenan. Idan kuma bai yafe ba, to wajibi ne ki biyashi koda da kaɗan-kaɗan ne.

Allah Maɗaukakin Sarki Yace. "NAGARTATTU DAGA CIKIN MATAYE, SUNE MASU YIN BIYAYYA GA MAZAJENSU, MASU KIYAYE AMANA BISA ABINDA ALLAH YAYI UMURNIN KIYAYEWA (WATO MASU KIYAYE AMANAR JIKINSU DA KUMA DUKIYAR MAZAJENSU).

WALLAHU A’ALAM.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments