Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko Ya Halatta Mace Ta Yi Shugabanci?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ganin yadda wata jam’iyyar siyasa ta tsayar da musulma a matsayin ‘yar takarar gwamnan jiha a Arewa shi ne ake tambaya ko ya halatta mace ta yi shugabanci irin wannan a musulunci?

KO YA HALATTA MACE TA YI SHUGABANCI?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

A baya na amsa wata tambaya makamanciyar wannan a kan Shugabancin Musulma da Kafiri a lokacin zaɓen siyasa, inda na tabbatar da cewa:

[1] Mun sha faɗa tun ba yau ba cewa: Fatawa a kan al’amuran siyasa da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar musulmi a yau, ba abu ne da kowane almajiri ko ɗalibin ilimi ke iya tsoma baki a cikinsa, ta hanyar janyo aya ko hadisi ɗaya ko biyu kawai ba. Wannan fage ne na manyan malamai, waɗanda suka sha ruwan ilimi da fahimta da gogewa a cikin Usuul As-Sharee’ah da Ƙawaa’id Ad-Deen kuma suka ƙoshi.

[2] Siyasar da ake gudana a kanta yanzu ba siyasar musulunci ba ce, don haka ba daidai ba ne a janyo Ayoyin Alƙur’ani ko hadisan Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) don tabbatarwa ko kore wani abu na al’amarinta. Larurar rayuwar da muka samu kanmu a ciki ce ta wajabta mana shiga cikinta, kamar yadda malamai suka tabbatar: Larura tana halatta abin da Shari’a ta hana da gwargwadon hali. Don haka, babu suka ko zargi ga wanda ya ga fa’idar ɗaukar mataimakiya musulma, kamar dai wanda ya ɗauki mataimaki kafiri. Me muka iya yi a baya, lokacin da kafiri ne ma ya zama shugaban ƙasa a kanmu?!

[3] Janyo hadisin Al-Bukhaariy (7099) cewa: Duk mutanen da suka shugabantar da mace a kansu, ba za su taɓa yin nasara ba a nan, yana iya zama kamar yadda Aliyyu Bn Abi-Taalib (Radiyal Laahu Anhu) ne ya ce: Kalmar Gaskiya ce da ake nufin Ƙarya da ita. Domin manufar mai wannan maganar ita ce: Tabbatar da zaɓen jam’iyyar da ke da goyon-bayan mutanen da suke ta tayar da fitina, masu son cigaba da danne musulmi da cutar da su!

[4] Irin wannan matsalar ce ta faru a zaɓen Jihar Taraba a 2015, inda wata musulma ta tsaya takara da wani kirista, har a wurin kamfen aka ji shi yana ƙalubalantarta da cewa: A ina ne musulunci ya yarda mace ta yi shugabanci?! Bai san cewa siffar Imani da Musulunci da ita take da shi ya fi duk wasu siffofin kirki da yake da su a cikin kafirci ba! Shiyasa a lokacin malamai suka yi fatawar cewa: Ita ce ya wajaba musulmi su zaɓa, ba shi ba.

[5] Shugabancin kafiri a kan musulmi babban abin haramtawa ne a asalin ƙaidojin musulunci. Domin a lokacin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hukunta cewa: Kuma kar ku yi jayayya da maabuta shugabanci, sai kuma ya ƙara da cewa: Sai dai in kun ga kafirci a fili ƙarara, wanda a kansa kuke da hujja daga Allaah. (Sahih Al-Bukhaariy: 7056). Daga nan ne a cikin Kitaab Al-Imaamah ko Al-Imaarah, malaman Fiƙhun Musulunci suka tabbatar da cewa yana daga cikin sharuɗɗan shugaba: Ya zama musulmi ba kafiri ba.

[6] Saboda irin bambancin da ke a tsakanin shugabancin musulmi da kafiri ne ya sa ba a yarda kafiri ya auri musulma ba, irin yadda aka yarda musulmi ya auri macen Ahlul-Kitaab a bisa sharuɗɗansa. Domin a bayan aure miji shi ne shugaba a kan matarsa, amma kuma a nan darajarsa ta rashin Imani da Musulunci ta saukar da shi ƙasa. To, ta yaya zaman aure da shi zai yi daɗi a irin wannan halin?!

[7] A lokacin da malamai a yau suka ƙyamaci zaɓen ɗan takarar jam’iyyar adawa ba wai don kawai mataimakinsa kirista ne ba. Amma dai sun kalli wata matsala ce cewa: Yadda Fastocin kudanci - waɗanda kowa ya san irin halinsu - suke ta kartar ƙasar cewa: Sai sun kayar da gwamna mai ci. Sannan kuma an gano: Ba dan takarar shi da kansa ne ya zaɓo mataimakin ba, ƙaƙaba masa shi aka yi kamar yadda rahotanni suka bayyana. Kuma akwai babban bambanci a tsakanin zaɓowa da ƙaƙabawa. Shikenan.

Waɗannan bayanan duk daidai ne tun a wancan lokacin har zuwa yau, a cikin wannan siyasar ta dimokuraɗiyyah da ake gudanarwa a ƙasar nan.

Abin dai da nake ganin ya dace in ƙara a nan kawai shi ne:

[i] Bai kamata musulmi a duk wata jiha irinsu a Arewa su zauna su zuba ido ‘yan siyasa su riƙa yin yadda suka so da alamuran siyasar jihohinsu ba. Ta yaya za su bari a riƙa ƙaƙaba musu shugabannin da suka san ba su dace da ƙaidoji ko koyarwar addininsu da aladarsu da rayuwarsu ba? Koko ana nufin a ce babu wani musulmi namiji mutumin kirki da ya cancanci a tsayar a matsayin ɗan takarar gwamna a jihohin ne, sai dai mace ko kuma sai kafiri?! Meyasa sai a bayan an gama tsayarwa ne musulmi za su koma suna tambayar malamai a kan halacci ko rashin halaccin hakan? Haba?!

[ii] Kodayake Najeriya ba daula ce Islamiyyah ba, amma dai ai kowa ya san akwai musulmi marinyaja a cikinta, musamman a yankin Arewa, waɗanda duk mai son cin zaɓen siyasa sai ya nemi haɗin kansu da samun goyon bayansu. Waɗannan musulmi ne da aka san ya wajaba su tafiyar da rayuwarsu a bisa dacewa da koyarwar addininsu da kyawawan al’adunsu gwargwadon ikonsu da iyawarsu. Bai halatta gare su su saɓa wa dokokin shari’ar musulunci ba, matuƙar dai suna da iko a kan hakan. Babu wata yarjejeniyar zamantakewa da sauran kafirai yan ƙasa a da can, da yanzu, da nan gaba ma, da za ta hana su ko ta rage musu ƙarfin bin dokokin addininsu, muddin dai suna iyawa. Kuma bai halatta su goyi bayan duk wani shirin da zai kai ga hakan ba.

[iii] Sulhun Hudaibiyah ba dalili ne a kan musulmi a jihohin Arewa su yarda da zaɓen musulma mace ko kafiri a matsayin shugabanni a kansu ba. Domin da farko dai hakan ya saɓa wa nassoshin addininsu, kuma shi ke kai su ga cigaba da zama a cikin ƙasƙanci da wulaƙanci har a yankunansu da garuruwansu da kuma gidajensu. Kuma dole ne mu gaskata Allaah Taaala Mabuwayi Mai Girma da ya ce a kan kafirai:

إِن يَثْقَفُوكُمْ يَكُونُوا لَكُمْ أَعْدَاءً وَيَبْسُطُوا إِلَيْكُمْ أَيْدِيَهُمْ وَأَلْسِنَتَهُم بِالسُّوءِ وَوَدُّوا لَوْ تَكْفُرُونَ ۝ لَن تَنفَعَكُمْ أَرْحَامُكُمْ وَلَا أَوْلَادُكُمْ ۚ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يَفْصِلُ بَيْنَكُمْ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ

‘Muddin suka samu iko a kan ku, maƙiya za su zama a gare ku, kuma za su shimfiɗa hannuwansu da bakunansu a gare ku da cutarwa ne, kuma su yi burin da ma a ce kun kafirta. ۝ Kuma zumuncinku da ‘ya’yanku ba za su ta taɓa amfanar ku ba. A ranar Ƙiyama ce zai rarrabe a tsakaninku, kuma Allaah mai ganin duk abin da kuke aikatawa ne. (Surah Al-Mumtahinah: 2-3).

[iɓ] Sannan kuma shi sulhun Hudaibiyah asalinsa ai doka ce daga Allaah wanda kuma ta saɓa wa tunanin duk masu tunani a lokacin. Shiyasa Allaah da kansa ya sanya wa musulmi natsuwa, ya ƙarfafe su, tare da yi musu albishir cewa wannan sulhun wani mataki ne zuwa ga samun abin da suke nema, watau: Fat-hu Makkah. (Surah Al-Fat-h: 18). To, wane malami ne a yau yake da tabbacin cewa zaɓen mace musulma ko kafiri a matsayin shugaban ƙasa ko gwamnan jiha ko shugaban ƙaramar hukuma zai kai ga samun cin nasara da ɗaukakar musulmi a kan kafirci? Hasali ma! Ba irin waɗannan ayyukan saɓon ne suka kai mu ga shiga halin da muke ciki a yanzu na ƙasƙanci ba?!

[ɓ] Sannan ta yaya wani zai yi tunanin cewa ta hanyar zaɓen wata musulma ko wani kafiri a kan musulmi ne za a iya samun adalci mai kai wa ga samun tsaro a kan Larurorin nan guda biyar ko shida na al’umma. Watau: Addini da Rayuwa da Mutunci da Hankali da Dukiya da kuma Dangantaka, alhali kowa ya san a ƙaidar dimokuraɗiyya adadin mutane ne kawai ake nema ba tare da kallon addininsu ba?! Kuma ina maganar tsare mutunci ko hankali ko dangantaka a tsarin da ya amince a fili cewa, a yi ta watanda da kuɗaɗe a wurin zaɓen fid-da gwani na ‘yan takara, kamar yadda aka gani a kwanan baya?!

[ɓi] Manufa dai: Abin takaici ne kuma abin kunya a duk tsawon shekarun nan a ce manyan Arewa: malamansu da sarakunansu da ‘yan bokonsu da ma’aikatansu da masanansu su bar harkar zaɓen shugabannin siyasarsu a hannun waɗansu tsiraru ‘yan duniya kawai. Kuma babu abin da za su iya yi sai dai idan an fitar da ɗan takara su kuma su yi ta jayayya a tsakaninsu: Ko ya dace ko bai dace ba! Me ya hana su da kansu su zauna, su zaɓo wanda ya dacen su gabatar da shi tun farko?

[ɓii] Idan dai har akwai tunanin samun adalin shugaba a cikin mata musulmi ko a cikin kafiran da muke zama da su a Arewa, ta ya ya ba za a samu ninkin ba-ninkinsu a cikin maza musulmi ba? Meyasa musulmi ba za su yi ƙoƙarin fitar da mutanen kirki daga cikin masana masu kishi da himma da ƙoƙari daga cikinsu, su saka su a cikin harkar nan tun daga farkonta har zuwa ƙarshenta ba? Don me za su ƙyale maƙasƙantan mutane maƙwaɗaita mahandama azzalumai su zama jagorori a cikin al’amarin da ya shafi makomar rayuwarsu da addininsu da iyalinsu da dukiyoyinsu da sauransu?!

[ɓiii] Ƙiri-ƙiri dai ga shi ana gani: Gwamnatin da ke kan karaga a yau musulmin Arewa ne suka haɗu suka zaɓo ta suka ɗora ta, da kyakkyawar fatan za ta taimaka wurin sauƙaƙe matsalolin tsaron da ya dame su, ta kawo musu harkokin cigaba. Amma a yanzu za a iya cewa matsalar tsaron kamar ƙara haɓaka kawai ta yi, kuma ayyukan cigaban da aka gudanar a Kudu ya fi na Arewar nesa-ba-kusa ba. Sannan kuma a yanzu da take haramar tafiya sai ta ga abin da ya fi shi ne: Ta miƙa ragabar jagorancin ga mutanen Kudu, waɗanda tun tuni suke ta ƙulla makircin da ke janyo ana ta kashe mana jamaa a can ɗin. Kamar dai wannan shugaban, shi kansa ɗan takarar da suka miƙa masa tikitin takara a jamiyyar ba wani fitaccen mabiyi ko mataimakin musulmi da musulunci ba ne. Amma kuma matarsa - kamar mataimakin wannan shugaban mai barin gado - fitacciya ce mai kaifin raayi na gani-kashe-ni kuma mataimakiya sosai ga addininta na kirista a fili. Haka ma yawancin yayansa! Wannan ne ake tsammanin zai yi wa Arewa adalci, har kuma a yi tsammanin za a samu kariya ko tsaro a kan larurorin nan guda biyar ta hannunsa? Menene musulmi yan ƙabilarsa ma suka samu a lokacin da ya yi gwamna a jiharsa a shekarun baya?! A bincika mana?

Laa haula Wala Ƙuwwata Illaa Bil Laah.

[iɗ] Kar in manta: Maganar da ake cewa: ‘Allaah yana taimakon gwamnati mai adalci ko da kafira ce, amma ba ya taimakon gwamnati mai zalunci ko da musulma ce’, wannan ba hadisin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba ne, saɓanin abin da waɗansu marubuta suke tunani. Magana ce ta hikima kawai da waɗansu malamai suke faɗi, domin zuga mutane ga yin adalci da nisantar zalunci. Sai a kiyaye. Shiyasa shi kansa Shaikhul-Islam Ibn Taimiyah (Rahimahul Laah) da ya ambaci maganar, bai kawo inda ya ciro ta ba, kuma ma bai nuna cewa tabbatacciya ce ba. A wuri na farko cewa ya yi: ‘An riwaito!’ A wuri na biyu: ‘An ce.’ A na uku ma ya ce: ‘Kuma an ce!’ A wurin malaman riwayar hadisi kuwa duk waɗannan siyaghut Tamreedh ake kiransu. Daga jin su kowane ɗalibi ya san maganganun da suka zo a bayansu ba su tabbata ba, hatta a wurin shi kansa mai faɗin su.

[ɗ] Sannan abin da yake ƙara ƙarfafar hakan ma shi ne cewa, maganar ma ba ta da wani lafazi ayyananne. Wani lafazin cewa ya yi: Allaah yana taimakon adilar gwamnati ko da kuwa kafira ce, amma ba ya taimakon azzalumar gwamnati ko da kuwa musulma ce. (Majmuul Fataawa: 28/63). A wani lafazin kuma sai ya ce: Allaah yana tsai da gwamnati adila ko da kafira ce, amma ba ya tsai da gwamnati azzaluma ko da kuwa musulma ce. Ko kuma cewa: Duniya tana dawwama tare da adalci da kafirci, amma ba ta dawwama tare da zalunci da musulunci.’ (Majmu’ul Fataawaa: 28/146).

A ƙarshe dai: Bai halatta musulmi a ƙasar nan su cigaba da ƙyale alamuran siyasa da zaɓen shugabannin al’umma a hannun mutanen da ba su yarda da addininsu ya zama shi ne mai jagorancinsu mai nuna musu hanya ba, a daidai lokacin da abokan zamansu suke ta shugabantar da manyan mabiya a cikin addininsu. Kar kuma manyansu su tsaya ga maimaita bayanin wai jama’a suna iya zaɓen kowane ɗan ƙasa a kowane irin matsayi ba tare da lura da ɓangare ko ƙabila ko addininsa ba, alhali su kuma abokan zamansu, manyansu suna ta kira ga mabiyansu cewa su damu da zaɓen wanda zai kare ra’ayin coci ne kawai.

Allaah ya ce:

{ وَالَّذِينَ كَفَرُوا بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ إِلَّا تَفْعَلُوهُ تَكُنْ فِتْنَةٌ فِي الْأَرْضِ وَفَسَادٌ كَبِير }

Su kuwa kafirai sashensu majiɓintan sashe ne; idan kuma ku ba ku yi hakan ba, to fitina ce za ta kasance a doron ƙasa da ɓarna mai girma. (Surah Al-Anfaal: 73).

Allaah ya ganar da mu.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments