𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assaalamu alaikum Allah ya karawa malam hazaka da
fahimta. Malam tambayata anan sune:
1. Malam na kasance ina dan yin soyayya tare da
romance dan haka meye hukuncin mai yin romance?
2. Malam ban taɓa saduwa da mace ba amma nasan ko ina. To idan na tuba
yaya tubana?
3. Malam ya maganar da ake cewa in kayi zina da wata sai anyi da taka don ance ita Zina bashi ce. meye gaskiyar maganar?? kuma inna tuba za’a dau fansar? Nagode.
HUKUNCIN
RUNGUMAR MACEN DA BA TAKA BA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.
Rungumar Mace Romance Haramun ne. Domin shima wani
nau’i ne na Zina.
Allah maɗaukakin sarki
idan ya haramta wani abu yakan haramta dukkan wata hanya komai kankantarta da
zata kai zuwa ga aikata wannan abun. Saninmu ne romance babbar hanya ce wadda
ke motsar da sha’awa zuwa ga aikata zina.
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga Abu
Hurayrah (Allah ya yarda dashi) Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Yace: ”Allah
yana rubutawa ɗan Adam kasonsa na zina,
zai riski wannan kason babu makawa:
1. Zinar hannu ita ce taɓawa (taɓa matar da bata
halatta gareka ba)
2. Zinar kafa shine tafiya (wajen da bai halatta
gareka ba).
3. Zinar idanu shine Kallo (kallon abinda bai
halatta gareka ba kamar kallon ɓideo da batsa).
4. Zinar kunne shine saurara (sauraran abinda bai
halatta gareka ba).
5. Zinar harshe shine zance (zancen batsa)
6. Zuciya tayi buri tayi sha’awa, farji shi zai
yarda ko ya karyata. Kuma hadisi ne Sahihi.
Hadisi ya tabbata wanda Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam Yace: Abuga Narkakkiyar kusar wuta ta bakin karfe akan ɗayanku shi yafi masa alkhairi akan ya shafi jikin macen
da bata hallata agareshi ba. Albany Yace hadisine ingantacce acikin sahihul
jami’ul kabeer (5045).
Don haka wannan abinda kakeyi shima zina ne. Kuma
babbu shakka duk irin yadda kayi da ‘ya’yan mutane sai an aikata irin haka akan
Matarka Ko Mahaifiyarka ko Ƙanwarka ko ya’yarka, ko uwarka mahaifiya, ko Ƙanwar Mahaifinka, ko Ƙanwar mahaifiyarka, ko kuma ‘yarka ta cikinka.
Ya kai Saurayi Ina kiranka kuji tsoron Allah ka
tuba, tuba irin wadda Allah yake so Ba wai tuba irinta mayaudara ba. Domin
hakika babu alamar nadama acikin maganganunka. Kuma Allah yana jinka. Idan kana
tunanin cewa zaka je kayi Iskanci da ‘ya’yan mutane, Sannan zakaje kace ka
tuba, don kar ayi da ‘Yarka, to kayi kuskure. Allah ya fika wayo, kuma yana nan
yana jiranka a madakata.
Idan ka tuba, tuba Na gaskiya, Allah Zai Karɓi Tubanka Insha Allah.
In kuwa tuban muzuru kayi, to kaima kasan
sakamakon mayaudara shine Tozarta anan duniya da kuma lahira.
Ya Rabbi Ka tsaremuna Imaninmu Da Mutuncimmu Amin
WALLAHU A’ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.