Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Relaxer

TAMBAYA (174)

Assalamualaikum mllm dftn mllm ya wuni lfya mllm mene ne hukunci saka relaɗer a gashi shin haramun ne Dan allh inason Karin bayani akai

HUKUNCIN RELAXER

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Ba laifi bane idan mutum ya canza kalar gashinsa ko Kuma yayi dying ba

Saidai Wanda yake Haramun shine baƙin dying (black color)

Ya halatta asaka wani abu a gashi wanda zaisa ya mimmiƙe (kamar ita relaɗer din musamman idan yazamana a cukurkude gashin yake dukda cewar tanada illa a kimiyyance)

Wannan hukuncin Yana aikine akan yaro da tsoho namiji ko Mace matuƙar abinda aka saka din Mai Tsarki ne (Tahir) Kuma Wanda addini ya halasta ne

Sannan Kuma rina gashi ya koma baƙi wannan haramun ne ga maza da Mata, saboda Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "Ka canza wannan gashin Amman kada ka saka baƙin kala"

(Fataawa al-Lajnah al-Daa’imah, 5/168)

Saidai Kuma wani hanzari ba gudu ba, munsan cewar addininmu yayi hani da amfani da duk wani abu dazai cutarda lafiyar mutum

Kwanannan binciken masana ya tabbatar da cewar amfani da Chemical hair relaɗer da sauran kayayyakin gyaran gashi suna janyo cutar uterine, endometrial da Kuma oɓarian Cancer. Mata baƙaƙen fata da Kuma yan yankin Latin America sunfi kanuwa da wadannan cututtuka saboda yawan amfani dasu tun sunada ƙarancin shekaru. Wannan dalilin ne yasa Attorney Weitz da Luɗenberg suke kai ƙarar duk wani company na Hair and Beauty corporation musamman Saloon saboda illar amfani da wadannan products dinnasu

Wasu daga cikin illolin amfani da relaɗer sune; lung damage (lalacewar hunhu), reproductiɓe disorders (matsalar al’aura), uterine fibroids (matsalar mahaifa), baldness (redewar gashi), early onset menstrual cycles and breast deɓelopment (saurin yin jinin al’ada da Kuma mama), lesion (rauni), scalp irritation (ciwon fatar Kai), Alopecia (zubewar gashi) da dai sauransu

National Institute of Health sun fitarda rahoto cewar: "Ana samun yawaitar masu kamuwa da cutar mahaifa musamman ga mata baƙaƙen fata". Haka Kuma sunyi bincike akan Mata 34,00 yan shekaru tsakanin 35 - 74, mata 378 sun kamu da cutar mahaifa silar amfaninda relaɗer. Matan da basu fiya amfani da relaɗer sosaiba a shekara 70 na rayuwar su, sun kai 1.64% yayinda Matan da suke yawan amfani da relaɗer din akai akai Suka kai 4.04%

Shawarata anan itace, tunda ba ibada bane amfani da relaɗer din, barinsa shine yafi domin kuwa lafiya jarice Kuma maganin Kar ayi...

Wallahu taala aalam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments