Ticker

6/recent/ticker-posts

Yabo a Wasu Wakokin Makada Sa’idu Faru

Citation: Authors (2024). Yabo a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 292-298. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.039.

Yabo a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

Aminu Ibrahim Bunguɗu
aibaminu054@gmail.com
08066357569
Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Maru, Jihar Zamfara

Da

Hassan Isa
hassnisah677@gmail.com
07067773871
Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi ta Maru, Jihar Zamfara

Da

Aliyu Rabi’u Ɗangulbi
aliyurabiuɗangubi@gmail.com
07032567689
Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Gwamnatin Tarayya, Gusau 

Tsakure

A wannan takarda, an nazarci yabo a cikin wasu waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. An zaɓi wasu daga cikin waƙoƙinsa aka fito da ɗiyan waƙoƙin da suke ƙunshe da yabo ta fuskar addini, da yabo ta fuskar asali, da yabo ta fuskar jarunta da kuma yabo ta fuskar kyauta, sannan aka yi sharhi gwargwadon fahimta. An ɗora wannan aiki a bisa ra’in mazhabar Waƙar Baka Bahaushiya wadda Gusau (2003 da 2015) ya assasa. An tattaro wasu matanonin waƙoƙin Sa’idu Faru ta hanyar amfani da Diwanin Waƙoƙin Baka na Gusau (2009), da kuma sauraron wasu waƙoƙin tare da rubuta matanoninsu a takarda. Binciken ya gano cewa Sa’idu Faru ya ƙware wajen yabon sarakuna da ‘ya’yan sarakuna ta hanyar kawo sunayen iyayensu da kakanninsu da danganta su da su, tare da nuna cewa suna da asali mai kyau, kuma sun gaji kula da addini da jarunta daga wajen iyaye da kakanni. Haka kuma Sa’idu Faru mawaƙi ne wanda yake bayyana kyautar da aka yi masa, saboda haka ne waƙoƙinsa suke ƙunshe da yabon waɗanda suka yi masa kyauta ko wata hidima. A taƙaice, an fahimci cewa ɗiyan waƙoƙin da suke ɗauke da yabo a waƙoƙin Sa’idu Faru suna ƙara ɗaukaka darajar waɗanda yake yabon, kuma suna ilmantar da al’umma tarihin wasu masarautu da kuma wasu muhimman mutane. Haka kuma ɗiyan waƙoƙin da suke ɗauke da yabon, suna ilmantar da al’umma muhimmancin kula da addini da kyauta da kuma jarunta.

Gabatarwa

Yabo na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da waƙoƙin baka na Hausa suka ƙunsa. Mawaƙa suna yin yabo a cikin waƙoƙinsu ta hanyar nuna wasu kyawawan abubuwa da suka shafi wanda suke yi wa waƙa. Daga cikin abubuwan da suke bayyanawa akwai; kula da addini da asali mai kyau da iya mulki da kyauta da jaruntaka da kyawawan halaye. Suna yin yabon ne domin su ƙara fito da kimar wanda suke yabo da kuma jawo masa farin jini ga jama’a. Makaɗa Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan fada, kuma ya yi wa sarakuna da hakimai da ‘ya’yan sarakuna waƙoƙi masu yawa waɗanda suke ƙunshe da nau’o’in yabo iri daban-daban. Manufar wannan takarda ita ce tattaro wasu waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru, domin a fito da ɗiyan waƙoƙin da suke ƙunshe da yabo, tare da yin sharhi gwargwadon fahimta.

Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru

An haifi Sa’idu Faru a garin Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara, a wajejen shekarar 1932. Sunan mahaifinsa makaɗa Abubakar ɗan Abdu. Mahaifiyarsa mutuniyar Banga ce da ke ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda. Sa’idu Faru ya yi yawancin ƙurciyarsa a garin Banga, amma daga baya ya koma wajen mahaifinsa a Faru. Ya yi karatu a makarantar allo, amma bai yi karatun boko ba. Makaɗa Sa’idu Faru ya koyi waƙa a wurin mahaifinsa makaɗa Abubakar. Tun yana da shekara goma aka fara zuwa yawon kiɗi da shi gari-gari. Bayan ya shekara goma sha shida ya soma karɓi, a wannan lokaci ne kuma aka haɗa su tare da ƙanensa Mu’azu. Waƙar farko da Sa’idu Faru ya fara yi ita ce waƙar Sarkin Yamman Faru Ibrahim. Daga nan ya ci gaba da yi wa sarakuna da ‘ya’yan sarakuna waƙoƙi. Sa’idu Faru yana da matan aure da ‘ya’ya da kuma jikoki maza da mata (Gusau, 1996:117-125). Makaɗa Sa’idu Faru ya rasu a shekarar 1987.

Hanyoyin Tattara Bayanai

A wannan takarda an yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen tattaro bayanai, waɗanda suka haɗa da sauraron kaset-kaset na CD waɗanda suke ɗauke da waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru, da juyar da matanoninsu a takarda. Kuma an duba Diwanin Gusau (2009) inda aka samu wasu waƙoƙin Sa’idu Faru. Bayan haka, an tattauna da wasu masana irin su Alhaji Ibrahim Ɗanmadamin Birnin Magaji da Dr Muhammad Ammani da Malam Riyalu Hassan Bunguɗu da kuma Malam Ibrahim Magaji Ubandoman Bunguɗu. Bayan haka, an tattauna da wani mai sha’awar waƙoƙin baka na Hausa, wato Abubakar Nahuce (Nabanga) wanda ya hardace wasu waƙoƙin Sa’idu Faru, inda ya yi ƙarin haske a kan wasu ɗiyan waƙoƙin Sa’idu Faru. Kuma an duba wasu littattafai da kundayen bincike da maƙalu da kuma jaridu domin ƙara samun haske.

Ma’anar Yabo

A Ƙamusun Hausa (2006:476) an nuna cewa yabo yana nufin “faɗar wata kalma mai daɗi ga wani mutum da ya aikata wani kyakkyawan abu”. Ɗiso (1997:62) ya bayyana cewa “yabo yana nufin ƙoƙarin ɗaukaka daraja ko kimar mutum ko wani abu a idon mutane ta hanyar faɗar kyawawan maganganu a game da shi yadda duk wanda ya ji waɗannan maganganu zai ji yana ƙaunar wannan mutum ko abin a zuciyarsa”. Haka kuma masana irin su Yahya (1997:117) da Abba da Zulyadaini (2000:43) da Gusau (2008:376) sun nuna cewa yabo yana da wasu muhimman rabe-rabe waɗanda suka haɗa da; yabo na addini da yabo na asali da yabo na kyauta da yabo na iya mulki da yabo na jarunta da kuma yabo na hali mai kyau. Su kuma su Junaidu da ‘Yar’aduwa (2007:94-95) sun bayyana cewa akwai hanyoyi guda biyar da makaɗan fada suke bi don yabon sarakuna. Hanyoyin sun haɗa da; asali/zuri’a da addini da kyauta da zuga da kuma ƙwarewa ga riƙon jama’a.

Yabo a Wasu Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Faru

Sa’idu Faru yana ɗaya daga cikin shahararrun makaɗan fada a ƙasar Hausa. Ya yi wa wasu sarakuna da hakimai da kuma waɗanda suka jiɓinci jinin sarauta waƙoƙi daban-daban. A cikin waƙoƙin nasa, ya ƙware wajen yabon sarakuna da ’yan sarauta ta hanyar bayyana wasu abubuwa masu kyau da suka shafe su. A wannan ɓangare na wannan muƙalar, an fito da wasu ɗiyan waƙoƙin Sa’idu Faru da suke ɗauke da yabo na addini da yabo na asali da yabo na kyauta da kuma yabo na jarunta, tare da yin taƙaitaccen sharhi.

Yabo na Addini

Ibrahim (1983:10-11) ya bayyana cewa makaɗa sukan yabi sarakuna da riƙe addini, da rushe tsafi. Ya ƙara da cewa, bayan jihadin Fulani, sarakunan ƙasar Hausa su ne shugabannin addinin Musulunci a ƙasashensu. Saboda haka makaɗan kan duba baya su faɗi irin yadda kakanninsu suka riƙe addini, sannan su nuna cewa su ma na yanzu haka suke.

Makaɗa Sa’idu Faru ya yi irin wannan yabo a cikin wasu waƙoƙinsa. Ga wasu misalai kamar haka:

A waƙar Mai Babban Rabo Ginshiƙin Sarkin shariffai, Sa’idu Faru yana cewa:

Jagora: Zanna da shiri Madawaki na Sarkin Yaƙi na Binji,

: Jikan Mujaddadi,

: Mai kwana salati na Alƙali Abubakar,

: Mamman Bello jan damishi ɗan Abdu Jatau,

‘Y/Amshi: Muhammadu Bello jan damishi ɗan Abdu Jatau.

(Waƙar Mai Babban Rabo Ginshiƙin Sarkin shariffai, MP3)

A wannan ɗan waƙa Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, inda ya nuna cewa yana kwana salati, wato mutum ne mai ƙoƙarin yin salati da yawan ibadodi. Addinin Musulunci ya yi umurni ga Musulmi su riƙa yin salati. Haka kuma akwai falala mai yawa ga mutanen da suke yawaita yin salati. A cikin sura ta 33, wato Suratul Ahzab, Aya ta 56, an yi kira ga waɗanda suka yi imani, su yi salati ga Annabi Muhammadu salallahu alaihi wa sallama.

Haka kuma a Waƙar Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar, makaɗa Sa’idu Faru ya ce:

Jagora: Abu na Dikko ruwa maganin hwari ɗan Mamudu,

‘Y/Amshi: Garba mai Ɗan’isa da Ƙawari da waɗan Torawa,

: Waliyi ɗan auliya’u,

: Jikan mai girma,

: Daɗai darajam Mamudu an gan ta tun farko.

(Waƙar Sarkin Kiyawa Abubakar, MP3)

A wannan ɗan waƙa, Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Abubakar (1952- 1960), inda ya nuna cewa waliyi[1] ne kuma iyayensa waliyai ne. Ya yi wannan yabo ne domin ya nuna cewa sarkin yana kula da addini da yawan yin ibada kamar kakanninsa, wato su Malam Muhammadu Namoda (1807-1810) da Malam Mamuda (1810-1850) da sauran sarakunan da suka yi mulkin Ƙaura Namoda kafin ya yi mulki.

Malam Muhammadu Namoda da Malam Mahmudu suna daga cikin almajiran Shehu Usmanu Ɗanfodiyo waɗanda suka bayar da gagarumar gudummuwa a lokacin jihadi. Muhammadu Namoda ya halarci yaƙe-yaƙe da dama, kuma ya taimaka wa Malam Ummarun Dallaje na Katsina da Malam Isiyaku na Daura a wajen yaƙe-yaƙen jihadi. Sarkin kiyawan Ƙaura Abubakar Garba ɗa ne ga Sarkin Kiyawa Bashari ɗan Sarkin Kiyawa Buhari ɗan Sakin Kiyawa Mamudu. Shi kuma Malam Mamuda da shi da Malam Muhammdu Namoda ‘ya’yan Malam Aliyu ne (Ƙaura, 2020:139-142)

5.2 Yabo na Asali da Dangantaka

A Ƙamusun Hausa (2006:20) an bayyana ma’anar asali da mafari ko tushe ko salsala. Dangantaka kuma na nufin ‘yan’uwantaka (CNHN, 2006:95). Yahya (1997:120) ya nuna cewa yabo ta fuskar asali ya ƙunshi ambaton kakannin sarkin da ake yi wa waƙa waɗanda suka yi sarautar da sarki yake a kai. Mawaƙan na bayyana cewa wannan sarki yana da asali mai kyawo, kuma kyawawan nasarorin da yake samu, ya same su ne domin haka kakanninsa suka yi. Shi kuma Ɗiso (1997:63) cewa ya yi mawaƙa kan yabi mutum ta hanyar nuna asalinsa ko kuma dangantakarsa da wasu mashahuran mutane. Sukan nuna cewa mutum yana da kyakkyawan asali, suna ambaton sunayen iyayensa da na kakanninsa su yabe su don ya ji daɗi ko kuma su haɗa da shi su yabe su tare. Makaɗa Sa’idu Faru ya yi irin wannan yabo a cikin wasu waƙoƙinsa. Ga wasu misalai kamar haka:

A waƙar Kana Shirye Baban ‘Yanruwa yana cewa:

Jagora: ‘Yan Jidda suna tariya da kyau,

‘Y/Amshi: Domin sun ga Muhammadu Macciɗo,

: Bajimi jikan Ɗanfodiyo,

: Mai gaba da kai bai sha daɗi ba.

(Gusau, 2009, sh. 153)

 

A wannan ɗan waƙar, Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ta fuskar asali inda ya danganta shi da kakansa Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, ya nuna cewa mutanen Jidda da suke ƙasar Saudiyya sun yi masa kyakkyawar tarba a lokacin da ya tafi ƙasar Saudiyya, saboda kasancewarsa jikan mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo ɗa ne ga Sarkin Musulmi Abubakar III ɗan Malam Usman ɗan Sarkin Musulmi Mu’azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usmanu[2].

A waƙar Muhammadun Amadu, Sa’idu Faru yana cewa:

Jagora: Ya gadi Mu’azu ya gadi Atiku,

‘Y/Amshi: Mamman halin Amadu Bello yag gado.

(Waƙar Muhammadun Amadu, MP3)

A wannan ɗan waƙa, Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo inda ya nuna cewa kyawawan halayensa ya gaje su ne daga iyayensa da kakanninsa, wato Sarkin Musulmi Mu’azu da Sarkin Musulmi Atiku da kuma Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello.

Sarkin Musulmi Mu’azu ɗa ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Shehu. Shi kuma Atiku ɗan Mujaddadi Shehu Usmanu ne. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ɗa ne ga Sarkin Raɓah Ibrahim ɗan Sarkin Musulmi Abubakar II ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usmanu[3]. Saboda haka idan aka dubi wannan bayani za a ga cewa waɗannan mutane da aka nuna cewa ya gaje su, ‘ya’ya ne da jikokin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

5.3 Yabo na Kyauta

A Ƙamusun Hausa (2006:27) an bayyana ma’anar kyauta da bai wa mutum wani abu don ra’ayi ba tare da ya yi wani aiki ba. Yahya (1995:41) ya nuna cewa mawaƙa kan yabi sarakuna ta fuskar kyauta, su kuma sarakunan suna yi wa mawaƙan kyautar kuɗi da tufafi har zuwa abin hawa kamar dawaki da motoci da sauransu.

Makaɗa Sa’idu faru yana yin irin wannan yabo a cikin waƙoƙinsa daban-daban. Yakan yabi sarakuna da ‘ya’yan sarakuna saboda kasancewarsu masu kyauta ko kuma saboda wata kyauta wadda suka yi masa. Ga wasu misalai daga wasu waƙoƙi kamar haka:

A waƙar Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari, Sa’idu Faru yana cewa:

Jagora: Baba ya ba mu bandura guda duk na lailai,

‘Y/Amshi: Ya ba mu bandura guda duk na yadi,

: Ya ba mu fam goma yac ce mu ɗunka,

: Ga takalumma na fam shidda-shidda,

: Hula kalabus guda goma yab ban

: Doki da kaya da kuɗɗin ciyawa,

: Kyauta irin taka jikan Mu’azu,

: Don ba a cewa mutum ba kamatai,

: Sai Larabawan Masar masu girma.

(Waƙar Bajimin Gidan Bello Mamman na Yari, MP3)

A wannan ɗan waƙa, Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo inda ya nuna cewa ya ba su kyautar bandur[4] guda na lailai, wato yadi talatin na farin yadi, da kuɗi fam[5] goma domin su ɗunke yadukan, da takalma na fam shida-shida da kuma huluna guda goma, da kuma doki da kayansa da kuɗin da za a sayi ciyawa a ba dokin. Sa’idu Faru ya yaba sosai da wannan kyauta domin ya nuna cewa da wuya a samu mai iya yin irin wannan kyauta.

A waƙar Kana Shirye Baban ‘Yanruwa, Sa’idu Faru yana cewa:

Mu’azu: Ni ko daɗinta da nij jiya,

: Can dauri zaman daji mukai,

: Da kay yi waƙar Sarkin Kudu,

: Mamman yaɗ ɗaukan yar riƙe,

: Mun san manyan mutane ƙwarai,

: Mun san ƙananan mutane kuma,

: Mun kammala duk mun ƙasura,

: Barwa mu shidda muna gume,

: Sarkin makaɗanmu shina gaba,

: Duk kowane tashi ƙawa daban,

: Yai taiɓa yai ƙaton ciki,

: Kowag ga shi zaune ga inuwa,

: Ko da makaɗan sarkin Masar,

‘Y/Amshi: Yag ga Sa’idu sai rainai yai haki.

(Gusau, 2009:153)

A wannan ɗan waƙar, makaɗa Sa’idu Faru ya yaba wa Sarkin Kudun Sakkwato, wato Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo a kan kyautuka daban-daban da yake yi masa a matsayinsa na ubangidansa. Ya bayyana yadda rayuwarsu ta canza da shi da yaransa a sanadiyyar ɗaukar nauyin hidimominsu da sarkin ke yi. Wannan bayani na Sa’idu Faru ya nuna irin yadda sarakuna suke ɗaukar nauyin mawaƙansu, musamman a zamanin da.

A waƙar Mai Babban Rabo Ginshiƙin Sarkin Shariffai Sa’idu Faru na cewa:

Jagora: Ba mai kyauta irin mamman duk ƙasah Hausa,

‘Y/Amshi: Ɗan jemage shi yah hwaɗa man babu wasa,

: Cika ni aza ni Mamman yakai in za ya kyauta,

: In ya ba mutum fam tamanin sai da riga,

: In ya ba mutum fam talatin sai da riga,

: In ya ba mutum fam bakwai ya mai garaje,

: Shi na iya ba ka doki na fam metin da sirdi da kayanai haɗaɗɗi,

: Kuma ya haɗa da yaron da zai ja ma kinami.

(Waƙar Mai Babban Rabo Ginshiƙin Sarkin Shariffai, MP3)

A wannan ɗan waƙa Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo a kan irin kyautar da yake yi, inda ya nuna cewa duk ƙasar Hausa babu mai kyauta kamar sa. Ya nuna cewa idan ya ba mutum kuɗi kamar fam tamanin ko fam talatin, sai kuma ya haɗa masa da riga. Kuma yana bayar da doki tare da kayan dokin da kuma yaron da zai jan kinami[6], wato wanda zai riƙa jan dokin.

A waƙar Sarkin Fulanin Bunguɗu Shehu, Sa’idu Faru yana cewa:

Jagora: Zamana kiɗi ga Baciri,

‘Y/Amshi: Allah ya sa muna maimaitawa,

Jagora: Ga furata mai nono,

: Ga tuwona mai nama,

: Ga gidana ga matana,

‘Y/Amshi: Kowa kag gani da ingarman doki.

(Waƙar Sarkin Fulanin Bunguɗu Shehu, MP3)

A wannan ɗan waƙa Sa’idu ya yaba wa Sarkin Fulanin Bunguɗu Shehu (1974-1979) inda ya nuna cewa a lokacin da ya zauna a wurinsa ya samu kyakkyawar kulawa domin an riƙa ba shi fura da nono da tuwo tare da nama, kuma ga doki an ba shi.

A waƙar Ɗanmadamin Sakkwato Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu, Sa’idu Faru yana cewa:

Jagora: Ga babban wa mai kamar uba,

: Mai kyautar doki na Audu,

‘Y/Amshi: Bello Wakilin lokal atoriti.

(Waƙar Usmanu na Bunguɗu, MP3)

A wannan ɗan waƙa, Sa’idu Faru ya yabi yayan Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu wato Magajin Garin Bunguɗu Alhaji Bello (1980-1995), inda ya nuna cewa mutum ne wanda yake bayar da kyautar doki. Sa’idu Faru ya nuna Magajin Garin Bunguɗu Alhaji Bello mutum ne mai ƙoƙorin yin kyauta.

A waƙar Turakin Argungun, Sa’idu Faru yana cewa:

Jagora: Shi ka ba ka mota ta shiga,

: Ya ba ka naira wajjen ɗari biyat,

‘Y/Amshi: Don ka aje kana kwasah hetur.

(Waƙar Turakin Argungu, MP3)

A wannan ɗan waƙa Sa’idu Faru ya yabi Turakin Argungu wato tsohon gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Muhammadu Kangiwa, inda ya nuna cewa yana bayar da kyautar mota, sannan ya bayar da naira ɗari biyar domin a riƙa sayen man fetur ana zuba wa motar.

5.4 Yabo na Jaruntaka

Yahya (1997:123) ya nuna cewa, mawaƙa na bayyana cewa sarki ya gaji zama sadauki, shirye yake ko da yaƙi ya taso. Kuma mawaƙan kan bayyana kokuwar neman sarauta da ya yi da shi da sauran ‘ya’yan sarauta, ita ma wani yaƙi ne wanda ya zama barde, ya fatattaki abokan hamayya.

Makaɗa Sa’idu Faru ya yi irin wannan yabo a cikin wasu waƙoƙinsa daban-daban. Ga wasu misalai kamar haka:

A waƙar Sarkin Fulanin Bungudu Shehu, Sa’idu Faru yana cewa:

Jagora: Kai aka tsoro ba ka da tsoro,

‘Y/Amshi: Baciri kai Allah yab ba.

: Koma shirin yaƙi,

: Jan damishe gidan Kure Shehu.

(Waƙar Sarkin Fulanin Bunguɗu Alhaji Shehu MP 3)

A wannan ɗan waƙa, Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Fulanin Bunguɗu Alhaji Shehu (1974-1979) inda ya nuna cewa jarumi ne wanda ba ya da tsoro, kuma abokan hamayyarsa suna jin tsoronsa. Ya kira shi da sunan kakansa Baciri domin ya nuna cewa ya gaji Sarkin Fulani Muhammadu Baciri a ɓangaren jaruntaka.

Sarkin Fulani Muhammadu Baciri ya bayar da gudummuwa sosai a lokacin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Ya yi yaƙe-yaƙe da dama waɗanda ya samu nasara a kan abokan gaba waɗanda suka riƙa nuna ƙiyayyarsu ga addinin Musulunci. Sarkin Fulani Shehu (1974-1979) ɗa ne ga Sarkin Fulani Amadu (1943-1974) ɗan Sarkin Fulani Muhammadu Mahe (1915-1927) ɗan Sarkin Fulani Ibrahim II (1891-1915) ɗan Sakin Fulani Muhammadu (1825-1869) ɗan Sarkin Fulani Muhammadu Baciri (1785-1825) (Gusau, 1986:2-7).

A waƙar Sarkin Yaƙin Banga Alhaji Sale, Sa’idu Faru yana cewa:

Jagora: Ban da gudu ban da razana,

‘Y/Amshi: Ka san sarki ba shi waiwaya,

: Ko da jan Gwamna yag gani.

(Gusau, 2009:150)

A wannan ɗan waƙa Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Yaƙin Banga Sale a ɓangren jarunta inda ya nuna cewa sarkin ba ya ja da baya a fagen daga, kuma ba ya jin tsoro ko razana a ɓangaren yaƙi ko kuma a wajen gudanar da al’amurran mulki.

6.0 Kammalawa

A wannan takarda, an yi bayani a kan yabo a wasu waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru. An kawo taƙaitaccen tarihin mawaƙin musamman abin da ya shafi haihuwarsa da ƙurciyarsa da fara waƙarsa da kuma rasuwarsa. Kuma an yi bayanin hanyoyin da aka bi wajen tattaro bayanai. A takardar, an kawo ma’anar yabo daga wasu masana daban-daban. Sannan kuma an kawo misalan wasu ɗiyan waƙoƙin Sa’idu Faru waɗanda suke ɗauke da nau’o’in yabo iri daban-daban tare da yin sharhi gwargwadon fahimta. An gano cewa Sa’idu Faru ya ƙware wajen yabon sarakuna da ‘ya’yan sarakuna ta hanyar kawo sunayen iyayensu da kakanninsu da danganta su da su, tare da nuna cewa suna da asali mai kyau, kuma sun gaji kula da addini da jarunta da wasu kyawawan halaye daga wajen iyaye da kakanni. Sa’idu Faru mawaƙi ne wanda yake bayyana kyautar da aka yi masa, saboda haka ne waƙoƙinsa suke ƙunshe da yabon waɗanda suka yi masa kyauta ko wata hidima, da kuma mutanen da ya samu labarin cewa suna yi wa mutane kyauta. A taƙaice an fahimci cewa ɗiyan waƙoƙin da suke ɗauke da yabo a waƙoƙin Sa’idu Faru suna ƙara ɗaukaka darajar waɗanda yake yabon, kuma suna ilmantar da al’umma tarihin wasu masarautu da kuma wasu muhimman mutane. Haka kuma ɗiyan waƙoƙin da suke ɗauke da yabon suna ilmantar da al’umma muhimmancin kula da addini da kyauta da kuma jarunta.

Manazarta

Abba, M. da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan Waƙar Baka ta Hausa. Zaria: Gaskiya Corporation.

CNHN (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Ɗiso, A.H (1997). Zambo da Yabo a Matsayin Dabarun Jawo Hankali a Cikin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa na Hausa. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M (1986). Taƙaitaccen Tarihin Bunguɗu. Takardar wadda aka gabatar. Maru: Sashen Hausa, Kwalejin Ilimi.

Gusau, S.M (1996). Makaɗa da Mawaƙan Hausa: Fisbas Media Services.

Gusau, S.M (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers.

Gusau, S.M (2008). Waƙoƙin Baka a Ƙasar Hausa Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers.

Gusau (2009). Diwanin Waƙoƙin Baka: Zaɓaɓɓun Matanoni na Waƙoƙin Baka na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Gusau, B.M & Gusau, S.M (2012). Gusau ta Malam Sambo. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S.M (2015). Mazhabobin Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Ibrahim, S.M (1983). Kowa ya Sha Kiɗa. Ibadan: Longman Nigeria Limited

Junaidu, I. da ‘Yar’aduwa T.M (2007). Harshe da Adabin Hausa a Kammale don Manyan Makarantun Sakandare. Ibadan: Spectrum Books Limited.

Ƙaura, H.S (2020). The Emergence of Ƙauran Namoda Emirates in Zamfara State. In Maishanu, I.M, Ƙaura, J.M and Abbas, N.I (eds.) in Zamfara and the Challenges of Socio-Political Transformation From 1764 to 2019 Conference Proceedings.

Yahya, A.B (1995). Ƙawancen Jigo Tsakanin Waƙoƙin Sarauta na Baka da Rubutattu. A cikin Rufa’i, A., Bichi, A.Y., Sani, S. & Sa’id, B. (Eds), Harsunan Nijeriya xviii p.33-51. Kano: Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University.

Yahya, A.B (1997) Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.



[1]. Waliyyi na nufin tsarkakken mutum mai yawan bautar Allah, da tsoronsa har a zuci, wanda abin duniya ba ya rufe masa ido, yana iya nuna abin mamakin da ba kowane Musulmi zai iya yin sa ba (CNHN, 2006:467).

[2]. Alhaji Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, WahasApp, Afrilu, 2024.

[3]. Gusau, (2008:17), da Alhaji Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, WhatsApp, Afrilu, 2024.

[4]. Bandur na nufin ɗauri ko naɗin yaduka da aka haɗa daga masaƙa, wanda galibi yakan kai yadi talatin (CNHN, 2006:35).

[5]. Fam na nufin sule ashirin a tsarin tsofaffin kuɗin Ingila da Nijeriya ta yi amfani da su (CNHN, 2006:132).

[6]. Kinami na nufin fatar da ake ɗaura likkafa da ita a jikin sirdin doki (CNHN, 2006:245). 

Post a Comment

0 Comments