Citation: Adamu, H., Abubakar, A. & Gurori, S.A. (2024). Turken Yabo a Wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru Na Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo. Four Decades of Hausa Royal Songs: Proceedings from the International Conference on the Life and Songs of Makaɗa Sa'idu Faru, 3(3), 307-310. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i03.041.
Turken Yabo a Wasu Waƙoƙin Sa’idu Faru Na Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
Daga
Halima Adamu
Department of Hausa Language
Zamfara State College of Arts and Sciences
halimaadamumayana@gmail.com
(+234) 08064115391
Da
Amina Abubakar
Department of Hausa Language
Zamfara State College of Arts and Sciences
Aminaabubakar397075903@gmail.com
(+234) 08039707590
Da
Samira Adamu Gurori
Department of Hausa Language
Zamfara State College of Arts and Sciences
(+234) 08039492770
Tsakure
Waƙar baka fasaha ce wadda take kallon
fanni na rayuwar Hausawa ciki kuwa har da yabo wanda yake kashin bayan duk wata
waƙar baka ta
sarauta. A binciken ilimi, yabo ba sabon abu ba ne a fagen nazari fanni na
al’ada da adabi musamman a waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru,
saboda irin yadda ya yi amfani da turken yabo cikin waƙoƙinsa domin (kambama) Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo. Haka kuma an tsakuro tubalan ginin yabo a cikin waɗannan maƙoƙi. An ɗora kayan cikin guɗanar da wannan bincike don fito da manufa bisa hanyar dogaro
na nasaba da kyauta da kuma kyakkyawan halaye da mawaƙin ya yi wa uban gidansa. Tattaunawa
da ziyarar gani da ido da karance-karancen litattafai da muƙalu tare da sauran waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru duk
domin kwalliya ta biya. An yi amfani da mazhabar waƙar baka Bahaushiya, wadda Farfesa
Sa’idu Muhammad Gusau ya ɗabbaƙa. Binciken ya yi nasarar gano waƙar Saidu Faru ta Muhammadu Macciɗo cike take da yabo ta fuskar addini da kyauta da
kyawawan ɗabi’u na asalin gidan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.
Gabatarwa
Wannan takarda “Turken Yabo” na ɗaya daga cikin manyan tarukan waƙoƙin sarauta, don
haka aka zaɓi a guɗanar da wannan aiki a kansa. Domin samun sauƙin gudanarwa. An raba wannan takarda zuwa kanun batutuwa kamar
haka: Gabatarwa da taƙaitaccen tarihin makaɗa Sa’du Faru da takaitaccen tarihin Sarkin Kudu Muhammad Macciɗo, da ma’anar turken yabo da nau’o’ insa da kuma misalan
yabo a cikin wasu waƙoƙi Sarkin Kudu Muhammadu
Macciɗo, sai sakamakon
bincike da kammalawa da manazarta da kuma rataye.
Taƙaitaccen Tarihin Makaɗa Sa’idu Faru
Gusau, (1988) ya bayyaa cewa, an haifi Sa’idu a
garin Faru cikin ƙasar Maradun, Ƙaramar Hukumar Maradun
da ke Jihar Zamfara ta
yanzu a cikin shekarar 1932. An yi wa Sa’idu laƙabi da “Ɗan’umma” wanda
matar ƙanin mahaifinsa ta sanya masa saboda kiran ta da yake yi da “Umma”. A
wasu wurare ma cikin waƙoƙinsa yakan ambaci
kansa da wannan laƙabi misali:
Ɗan’umma Rungumi,
Ɗantumba Rungumi.
Wani wuri kuma yakan ce:
Sa’idu malamin waƙa.
Sunan mahaifin Sa’idu Faru shi ne, makaɗa Abubakar Kusu ɗan Abdullahi. Shi kuwa makaɗa Abdullahi, Alu makaɗin kurya ne ya haife shi. Amma mahaifyarsa mutumiyar
Banga ta ƙasar Ƙaura Namoda ce, kuma a can ne Sa’idu
Faru ya tashi har ya girma.Yawancin ƙuruciyar Sa’idu ya yi ta ne a garin Banga, amma daga
bisani sai ya koma Faru wurin mahaifinsa Abubakar. Sa’idu bai samu
dammar yin karatun allo mai zurfi ba. Haka ma bai yi karatun boko ba. Tun yana
yaro ya shiga sha’anin kiɗa da waƙa kai tsaye. Saidu Faru ya koyi waƙa ne ta hannun mahaifinsa makaɗa Abubakar. Waƙoƙinsa suka daɗa kyautatuwa ta hanyar fasaha da hikima tare da ƙwarewar da Allah
ya ba shi. Tun yana ɗan shekara 10 aka soma zuwa yawace – yawacen kiɗa tare da shi. Bayan rasuwar mahaifinsa Sa’idu
Faru ya ɗauki gabatar kiɗa da waƙa a giɗansu.
Wanda ya fara yi wa waƙa shi ne, tsohon Sarkin Yamman Faru Ibrahim. Daganan sai
Sa’idu ya ci gaba da yi wa sarakuna da ‘ya’yansu waƙoƙi har zuwa lokacin
da ya sadu da Sarkin Kudu Alhaji Muhammadu Macciɗo ɗan Sarkin Musulmi Abubakar na III ya zama uban godansa[1]. Ya fara yi wa Sarkin
Kudu Macciɗo waƙoƙi tun a Mafara
wato lokacin yana riƙe da muƙamin uban ƙasarta. Daga cikin
waƙoƙin da ya yi masa a
Mafara akwai wannan:
Gindin waƙar: Kana shire
baban ‘yanruwa,
Na Bello jikan Ɗanfodiyo.
Takaitaccen
Tarihin Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo
An haifi Muhammadu Macciɗo 20 ga Afrilu, 1928 a Ƙaramar Hukumar Ɗange-shuni ta yanzu a Jihar Sakkwato, Nijeriya. Ya yi karatun Islama da na boko, kuma ya riƙe muƙaman aikin
gwamnati da dama. Dangane da sarauta, ya yi Ciroman
Sakkwato a 1952, daga bisani ya zama Sarkin Kudun Sakkwato Hakimin Talatar
Mafara a 1953. A wancan lokacin ne suka haɗu da Makaɗa Sa’idu Faru kuma ya zama makaɗinsa. A 1996 ne aka naɗa Macciɗo a matsayin Sarkin
Musulmi. Ya rasu a shekarar 2006 sanadiyar haɗarin jirgin sama na kamfanin ADC ƙirar boin 373.
Yabo na daga cikin manyan turakun da makaɗan baka suka fi yawaita yin waƙoƙi a kansa. Kunsan
shi ne ma fitaccen turken waƙoƙin baka na Hausa
Domin mafi yawan waƙoƙin manufofinsu
sukan zamanto yabon waɗanda ake yi wa su ne. Yabo shi ne ambaton kalmomin sambarka da nufin
nuna amincewa da hali ko wani abin da mutum ya yi nagari. Ko kuma a iya cewa, yabo wani lafazi ne da ake yi ga
wani mutum domin a nuna halayensa da siffofinsa kyawawa da cewa abin so ne kuma
abin ƙauna ne. Akan gina turken yabo ne ta
amfani da tubalai waɗanda suka haɗa da addini da asali ko nasaba da kyauta ko karimci ko
baiwa da iya mulki (ga Sarakuna) da jaruntakar yaƙi da hali da ɗabi’a da kurari da roƙo da habaici da zambo ga wani, (Gusau,
2009:376).
Ire-Iren Yabo
Waƙoƙin yabo na baka nau’i biyu ne, akwai waƙoƙin yabo ba duniye wanda ya ɗanganci sha’anin duniya kamar yabon Sarakuna da sauran
masu riƙe da sarautun gargajiya. Misalin yabo ba duniye
a cikin waƙar Sarkin Kudu ta “kana shire baban ‘yan ruwa ɗan waƙa na a shirin da
bakwai.
Mu’azu: Laifin Yaro shi yi ƙiuya,
Laifin babba shi yi rowa,
Ina ƙaunar ka Muhammadu.
Sannan akwai yabon waɗanda suka shafi sha’anin addini, kamar waƙoƙin da aka yi waɗanda suka ɗanganci yabon Ubangiji ko Annabawa ko Sahabbai ko
Waliyyai ko sauran Malamai. Misalin waƙoƙin yabo zalla su ne misalin yabo na
Addini cikin waƙar Sarkin Kudu ta makaɗa Saidu Faru ɗan waƙa da ashirin da uku.
Mu’azu: Na gane salon tsuntsaye,
‘Y/Amshi: Masu kan tsai da sallah dun na
sani.
Jagora: Ɗan gamraka bubukuwa,
Amshi: Da tankarki ko kunkumi waɗanda sallah kullum sukai.
Jagora: Ɗan bilbila do
hazbiya,
‘Y/Amshi: Waɗanda Sallah Kullum sukai.
Jagora: Ɗan kaza yarmoli da
shamuwa,
‘Y/Amshi: Waɗannan sallah kullum sukai,
Jagora: Jemage ba a zuwa Hajji,
‘Y/Amshi: In bilangi ɗaudar tai mai yawa.
Yabo a Cikin Wasu Waƙoƙinsa
A cikin waƙar kana shire
babban ‘Yan ruwa ɗan waƙa na uku inda yake
cewa:
“Ɗan Sardauna jikan
Hassan”
Har
zuwa ƙarshe wanda yake
nuna nasabarsa da gidan Sardauna ɗan waƙa na biyar in da
yake cewa:
Ɗan giwa kome taddaɗe,
Na tabbata yin giwa take.
A nan yana nuna yadda Sarkin Kudu Muhammadu
Macciɗo ya yi gadon alheri ga Mahaifinsa kuma
ya ɗauko halayen mahaifin.
A ɗan waƙa na bakwai in da yake
cewa
Mamman jikan Attahiru,
Baba na Sidi maman gwarzon Cika.
A nan yana yabon sa inda ya nuna yadda ya yi gadon arziki shi ɗin ɗan masu arziki ne. A ɗan waƙa na tare in da
yake cewa:
Jagora: Baban gandon gabas raba kaya,
‘Yan amshi: In ga na shamaki mai hana noma.
Wannan yana nuna yadda yake yabon Sarkin
Kudu da yawan alherin shi ga mutane da yadda yake rabon hatsi da sutura da kuɗi ga al’umma. Haka kuma a ɗan waƙa na sha ukku ya
yabi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo in da yake cewa:
Wada duk aka gadon kasura,
Wada duk aka gadon daukaka,
Wada duk aka gadon ci gaba,
Mamman kagaji Abubakar,
Koda sayen halin nan akai,
Baba halin da ka kai kuɗi shikai.
Haka kuma a cikin ɗan waƙa na tara inda makaɗa Saidu Faru yake
cewa:
Ni ce suda waƙa akai,
Tacce lallai waƙa nikai,
Waƙan Mamman Sarkin
Kudu,
Waƙar nan da Ɗan’umma ya mashi.
A wannan ɗan waƙar makaɗa Saidu Faru ya nuna yadda shaharar Sarkin Kudu Muhammadu
Macciɗo ta ke har tsuntsaye suna yabon sa.
A ɗan waƙa na ishirin inda
ya nuna burtu in ya yi yabon Sarkin Kudu to ranar in ya fita kiwo zai samo
abinci sai ya rage misali:
Sai ni ishe burta na kiyo,
Shina ta waƙar Sarkin Kudu,
Ala sabbinani ɗan Amadu,
Allah shi ƙara mai nasara,
Nicce burtu waƙa akai,
Yac ce lalle waƙa nikai,
Waƙar Mamman Sarkin
Kudu,
In na yi ta zani wurin kiwo,
In na zo abinci sai na rage.
(Gusau, 2008:152).
Waƙar Bajimin Giɗan Bello
Bajimin giɗan Bello Mamman Nayari Sarkin Kudu Macciɗo ci maraya, nan ma makaɗa Sa’idu Faru ya yabi Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo da irin halin girma da haƙurinsa. A ɗan waƙa na ɗaya inda yake cewa:
Toron giwa Uban Bello Mado,
Ɗan Hausa ba mai
irin Hanƙurinai.
(Gusau, 2008: 159).
Haka kuma a ɗan waƙa na uku ya yabi Muhammadu Macciɗo inda ya nuna yadda ya gaji ilimi da Addini da nasaba
sosai, inda yake cewa:
Da kyauta da ilimi da neman dalili,
Da godewa Allah da
istingifari,
Da su Bello da
Shehu ya tsarma kowa,
Ka kai kamab Bello
ka gadi Moyi.
Haka kuma a ɗan waƙa na huɗu nan ma ya nuna yadda har yana kwatanta shi da Larabawan
Masar inda yake cewa:
Jagora: Don ba a cewa mutum ba kamatai,
‘Yan amshi: Sai Larabawan Masar masu girma.
Sakamakon Bincike
Kamar dai yadda aka gani a cikin wannan
takarda, makaɗa Sa’idu Faru ya nuna shi turkakken
makaɗin fada ne na Muhammadu Macciɗo. Domin waƙoƙinsa cike suke da kalmomin yabo da alasambarka zuwa ga Sarkin
Kudu Muhammadu Macciɗo. Ya yabe shi ta fuskar addini,
musamman ma saboda kasancewarsa ɗan giɗan Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Haka kuma ya yabe shi da
kyawawan halaye ko ɗabi’u da kyauta da iya mulki da
kyakyawar zamantakewa da jama’arsa.
Kammalawa
Wannan takarda inda a ciki aka yi
tsokaci a kan turken yabo a cikin wasu waƙoƙin Sarkin Kudu Muhammadu Macciɗo na makaɗa Sa’idu Faru. Takardar dai ta nazarci
wasu daga waƙoƙin makaɗa Sa’idu Faru inda aka fito da yabo a
cikin wasu waƙoƙin da aka nazarta.
Manazarta
Adamu,
A. da Gwadabe, M.M (2005). Alhaji
Muhammadu Macciɗo Abubakar III the
19th Sultan of Sokoto, the Bridge Builder. Kaduna: Amana Publishing Ltd.
Britannica,
(2006). Muhammadu Macciɗo Sultan of Sokoto
Nigeria, An ciro a shekarar 2017, dagashafin https://www.britannica.com/biography/muhamadduMacciɗo.
Gusau,
M. (1996). Makaɗa Da Mawaƙa. Kano: Century Research
and Publishing Ltd.
Gusau
S.M (2008). Waƙoƙin Baka A Ƙasar Hausa: Yanaye Yanayensu
da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishing Ltd.
Gusau
S.M (2009). Diwanin
Waƙoƙin Baka.
Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau,
S.M (2014). Waƙar Baka Bahaushiya. Inaugural Lecture
At Musa Abdullahi Auditorium New Complex BUK Monday, May 26, 2014.
Gusau,
S.M, (2003). Jagoran
Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark
Publishers Limited.
Ɗangambo, A.
(2011). Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon
Tsari) Kano: K.D.G Publishers.
Yaro,
Y.I. (1998). Jagoran Nazarin Hausa Zaria: Northern Nigerian
Publishing Company.
[1]
Tattaunawa
da Hon. Ibrahim Muhammad Brnin Magaji Ɗanmadamin Birnin
Magaji a zauren makaɗa da mawaƙan na watsaf wanda yake shugabanta kuma ake aikawa da
tambayoyi dangane da makaɗa da mawaƙa domin bayar da amsa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.